Free chapter · Read without an account
PART 14
Cikin mamaki, Amrah ta ce, "Inna, dangina kuma? Ina da wasu dangi da suka wuce ku ne?"
Inna ta ce, "Ba mu ba ne danginki na asali, Amratu. Mu rainonki kawai muka yi, amma ba mu ne muka haife ki ba. Tsintarki muka yi a bakin kogi, lokacin ko cibiya ba a yanke miki ba.
"Watarana da sassafe, Malam ya je bakin kogi kamun kifi kamar yadda ya saba a kodayaushe. Har ya hau kan kwale-kwalensa, yana niyyar shiga tsakiyar kogi, kawai sai ya ji sautin kukan jaririya ya karaɗe kunnuwansa. Ya waiga ko'ina bai ga kowa ba, kuma ya kalli hanya bai ga mace da ta zo wucewa ba, balle ya yi tunanin ko ɗanta ne yake kuka.
"Cikin sauri, ya tuƙo kwale-kwalen ya dawo gaɓar kogin. Ya hau duba ko'ina. A hankali, ya rinƙa jin sautin kukan yana ƙaruwa a kunnuwansa. Sautin ya rinƙa bi har ya zo inda kike kwance can gefen kogin a cikin ciyayi, kina ta tsala kuka. Ba tare da wata fargaba ba, ya sunkuya ya ɗauko ki. Bai tsaya ɓata lokaci ba, ya taho gida da sauri ya kawo min ke.
"Ina karɓarki daga hannun Malam, sai na ji wani sanyi ya ratsa ƙafafuna. Da sauri na duba, sai na ga ashe jini ne yake ta zuba daga ƙasana, wanda yake nuni da cewa ƙaramin cikin da yake jikina ne ya zube. Na ji baƙin ciki da takaicin zubewar cikin, saboda shekararmu goma sha biyar da aure ni da Malam, amma Allah bai bamu haihuwa ba, sai wannan cikin Allah Ya ba ni, kuma ga shi ya zube.
"Lokacin da na kalle ki, sai na ji hankalina ya kwanta, nutsuwa ta shige ni a lokaci guda. Nan take, duk wani baƙin cikina ya kau. Na karɓe ki hannu bibbiyu, na rinƙa rainonki a ɓoye. Ko mutum ne ya zo cikin gidan nan, ba na yarda ya ganki. Akwai wani ruwan asiri da Malam yake baki. Duk kukan da za ki yi, babu wanda zai jiyo sai mu kaɗai.
"Kuma ban taɓa bari mutane sun san cewa cikina ya zube ba. Ƙwarya nake sakawa a duk sanda zan fita daga cikin gidan nan. Da na fuskanci watan haihuwata ya tsaya, sai nace wa Malam ya sanar da jama'a cewa na haihu. Muka yi wa mutane ƙaryar cewa ke ce ƴar da muka haifa. Kowa ya yi mamakin girman jikinki, don ba ki yi kama da sabuwar haihuwa ba, amma ba yadda mutane suka iya, tilas suka yarda da abin da muka faɗa musu.
"An sha shagali sosai. Limamin ƙauyen nan shi ne wanda ya raɗa miki wannan sunan 'AMRATU', amma sai muka ji yara suna kiranki da 'AMRAH'. Tun da muke a duniya, ba mu taɓa jin irin wannan sunan ba, kuma ke kaɗai ce mai irinsa duk faɗin yankin nan, amma ba mu sani ba ko a cikin birni akwai mai irinsa.
"Lokacin da muka tsince ki, ga dukkan alamu iyayenki a birni suke, don ko kaɗan ba ki yi kama da mutanen ƙauye ba. Wannan shi ne sirrin da nace zan faɗa miki, kuma bayan ke, babu wanda na taɓa faɗa wa. Ki ci gaba da kiyaye shi har lokacin da za ki sadu da iyayenki. Saboda numfashina yana barin gangar jikina, karki ci gaba da zama a cikin ƙauyen nan! Ki tafi birni neman danginki. Su ne gatanki..."
Hussain Yusuf✍️
Ku bi channel dinmu domin karanta ci gaba...AMRAH
©Hussain Yusuf✍️