Free chapter · Read without an account
PART 20
Kallo ɗaya Amrah ta yi wa farin mutumin, sai ta ji zuciyarta ta buga da ƙarfi, hakan bai taɓa faruwa da ita ba, tun lokacin da ta fara azabtar da mutanen ƙauyen. Jikinta ya hau rawa da zafi, tsigar jikinta ta tashi. Wani irin tsoron baƙon ya mamaye ta, wanda hakan yake nuna cewa mutumin nan ya fi ƙarfin duk wata mugunta da ta sani. Cikin ƙanƙanin lokaci, ta dawo ainihin siffarta, sannan ta yanke ƙauna ta ɓace ɓat daga wajen, tamkar iska.
Farin Mutumin, wanda ke kan dokinsa, ya ja linzami dai-dai inda Amrah ta ɓace. Ya tsaya, yana ƙare wa wajen kallo. Ya ɗan jima yana kallon sararin samaniya, sannan ya juya dokinsa, ya nufi cikin ƙauyen da gudu.
A hanya ya haɗu da jama'ar ƙauyen, sun ɗebo kayayyakinsu, suna niyyar yin hijira daga ƙauyen. Suna hango shi ya nufo su a sukwane, sai hankalinsu ya tashi matuƙa! A zatonsu, Amrah ce ta sake rikiɗa don ta ci gaba da azabtar da su. Ihu da kuka suka cika wajen, wasu har da birgima a ƙasa, suna neman gafararar Amrah.
Farin Mutumin ya tsayar da dokinsa. Ya ɗaga musu hannu, cikin tattausan lafazi irin na Larabawa, ya ce, "As-salāmu ʿalaykum yā ahla hādhihi al-qaryah!"
Duk da ba su gane yaren da ya yi musu ba, amma sun gane sallamar. Sai dai, babu wanda ya amsa, saboda tsoro ya hana su magana. Da ya ga shirun ya yi yawa, sai ya sauko daga kan dokinsa. Ya matso kusa da su, yana kallon idanuwansu. Cikin sassanyar muryarsa mai daɗin sauraro, Farin Mutumin ya fara magana da harshen Hausa.
"Ku kwantar da hankalinku, ni ba mai cutarwa ba ne. Sunana Hisham bn Hashim, na zo daga ƙasar Nijar. Na zo nan ne domin in kawo muku hasken Musulunci. Na san duk halin da kuke ciki, kuma ina tabbatar muku daga yau, babu abin da zai ƙara samunku."
Maigari ya ce, da muryar tsoro, "Ya kai wannan baƙo, ka yi sani cewa, sharrin waccan yarinyar ya wuce duk yadda kake tunani! Muna da yakinin cewa har aljanu suna shakkar Amratu, balle kai da ka zo yau."
Hisham ya yi murmushi, fararen haƙoransa suka bayyana. Ya dubi Maigari, ya ce, "Matuƙar ina cikin ƙauyen nan, to Amrah ba za ta iya aiwatar da wani mugun abu a kanku ba."
Hamrah tana tuƙi cikin nutsuwa, tana sauraron karatun Alƙur'ani, sai ta lura da wata farar mota mai baƙin glass tana biye da ita, duk inda ta shiga. Ba ta damu ba da farko, har ta isa makarantar. Abin mamaki, farar motar ita ma ta shigo cikin harabar, ta yi parking kusa da ita. Amma har Hamrah ta fito, wanda ke cikin motar bai fito ba.
Da aka tashi daga lecture, sai Hamrah ta ga motar ta sake biyo ta. Nan take, zuciyarta ta shiga dukan uku-uku. Ta ɗauki waya, ta kira Daddy ta sanar da shi.
Alhaji Kabiru, cikin tsananin firgici, ya tambaye ta, "Daughter, kina dai-dai ina?"
"Na kusa isa gida," Hamrah ta amsa.
Alhaji Kabiru ya ce, "To, hanzarta sosai! Idan kika ga sun shigo layinmu, ki yi gaggawar sanar da ni."
Hamrah ta zage da tuƙi, ta ba motar tazara sosai. Tana zuwa layinsu, ta rage gudu, amma sai ta ga farar motar ta wuce da gudu! Ta sauke ajiyar zuciya mai tsawo. Tana shiga gida, Daddy ya zo da sauri, hankalinsa a tashe, yana tambayarta ko lafiya.
Hamrah ta yi murmushi, ta ce, "Calm down, my Dad. Ba abin da ya same ni."
"Alhamdulillah!" Alhaji Kabiru ya ce. "Amma my daughter, daga yau, idan za ki fita, zan rinka haɗa ki da masu tsaronki."
Hamrah ta ɗan ɓata rai. "Amma Dad, ka san bana son wanda zai rinƙa takura min ko?"
"Daughter, akwai wani mutum da nake gujewa. Yana da mummunar manufa a kanki. Ina tsoron kar ya cutar min da ke," in ji shi cikin damuwa.
Hamrah ta kalle shi cike da mamaki. "Dad, waye wannan mutumin? Me na yi masa yake son cutar da ni?"
Hussain Yusuf✍️AMRAH
©Hussain Yusuf✍️