Free chapter · Read without an account
10
by Kansa'u Bello · KOMAI TSANANI
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*KOMAI TSANANI*
*By*
*KANSA'U* *BELLO*
*(OUM FATIMA)*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*PAGE 010*
*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*
Koda Amina ta kawo ma Inna Sahura kuɗin cinikin da aka yi faɗa sosai ta shiga yi don bai kai abin da Nanah ta saba kawo mata ba, hakan ya faru ne sakamakon Amina ta rage kuɗin da yawa ta ɓoye. Kullum dama sai ta zari wasu cikin dabara taje tayi zubin ƴar banki da suke yi a maƙotansu, kullum kowa zai bayar da Naira ɗari (100) a saka a banki a rubuta masa sai sallah saura kwanaki kaɗan za'a buɗe kowa a bashi nasa kuɗin yaje yayi sayayyar sallah.
Inna Sahura ta san ana yi kuma ko wace uwa tana ba ɗanta idan ya dawo daga tallah, amma bata taɓa bawa Nanah ta zuba ba, ita kuma bata taɓa ɗaukar mata ko sisi ba sabo da ba haƙƙinta bane.
Washe gari ma duk yanda taso Nanah taje tallah kasawa tayi don haka dole ta kira mai chemist ya mata allura ya bata magani. Haka ta biya kuɗin tana ta mita ba don tana so ba sai don bata son asarar cinikin da Nanah keyi mata. Kwana biyu Nanah tayi a kwance kafin ta ɗan samu sauƙi, ko warkewa bata ƙarasa yiba ta koma tallah.
Azumi yayi ta miƙa wa cikin sauri ba tare da an farga ba, an kammala goman farko cikin amincewar Allah, inda masu hankali da sanin ya kamata suka mayar da hankali wurin yin ibada. Yayin da mutane irin Inna Sahura suka mayar da hankali da lokacinsu kacokan wurin neman kuɗi da tara abin duniya, wanda minti biyar da zasu ware a rana su karanta Alqur'ani mai girma basu dashi. Sallar ma ba yinta suke a kan lokaci ba, sannan idan an yi ma babu cikakkiyar natsuwa don ana yi ana lissafa abinda aka kashe a sana'a da abin da ake son samu a jiki. Da an kammala kuma ba'a tsayawa ayi istigifari a roƙi Allah biyan buƙatun duniya da lahira, ina sallar ma ana yi ana tuninin dafin awara da aka ɗora kar ya tafaso ya zube. Ko kuma miya saman wuta kar ta ƙone.
(Mutane da yawa basa mayar da hankali wurin yin ibada a watan Ramadan, sun fi mayar da hankalinsu kacokan wurin neman kuɗi da tara abin duniya. Wanda duk abinda baka tara ba a wata goma sha ɗaya dake cikin shekara, sai wata guda ɗaya mai ɗumbin falala da Allah ya ware mana. Maimakon mu mayar da hankali wurin yin ibada da neman kusanci da Allah, mu roƙe sa arzuƙin duniya dana lahira domin watan neman biyan buƙata ne. Mu tubar wa zunubanmu domin watan gafara ne tun da bama da tabbacin cewar watan zai ƙara zaga yo wa ya riske mu cikin rayayyu. Amma ina yayin da wasu bayin Allan ke yin karatun Alqur'ani da sallolin dare da nafil-fili da istigifari, wasu kuwa na can na ƙoƙarin ganin sun tara abin duniya wanda zasu barshi a nan inda suka same shi don iya amfanin da zai musu kenan, ibada kuwa idan ka yita zata amfane ka duniya da ƙiyama, Allah ya kiyaye ya ganar damu gaskiya.)
An shiga goman tsakiya wacce ake kira goma ta wuya itama an kammala ta cikin amincewar Ubangiji aka shiga goman ƙarshe wacce ake kira ta ɗokin sallah inda hankalin jama'a gaba ɗaya ya koma kan ɗinke-ɗinken kayan sallah da sauran sayayyar sallah. Saura kwana biyar sallah su Amina suka buɗe ƴar bankin su, inda kowa aka bashi adadin kuɗin daya zuba.
Ina kallo duk suka kawo gida suka nuna ma Inna Sahura suna ta murna, sauran yaran gidan kowa ya ɗauki nasa kasancewar gidan baban gida ne na gado ɓangarori da yawa ne a ciki. Kowa sai ya tambayi me yasa Nanah bata yiba sai Inna Sahura tayi sauri ta bayar da amsa da cewa.
"Duka yaran a wurin samarin su suke samu suna zubi, ita kuwa taƙi kula kowa sabo da mugun halinta ai kuwa dole ta shaƙi baƙin ciki don tana kallo yara zasu je kowa ya sayi abin da yake so, ita kuwa dole ta haƙura da iya abin da ta samu a gida." Jin haka yasa duka matan gida suka goya mata baya a kan hakan suka amince da cewar da tayi girman kai ne da ita alhalin ba ƴar kowa bace ita.
Tana ji tana gani duka sa'o'inta suka je suka yo sayayyar kayan sallah masu kyau, ita kuwa iya atamfar da Inna Sahura ta ɗinka musu ce ita ma kuma sai da kowa ya zaɓa aka bata a ƙarshe, ɗinkin doguwar riga ne wacce taso ɗage mata kasancewarta doguwa. Sai wani shegen hijabin roba data saya mata irin ɗan arhar nan da takalmin roba sai ɗan kunne da lalle.
Duk irin kuÉ—in da Nanah ta tara mata a azumin nan bai sa tayi mata abin kirki ba, sauran yaranta kuwa tana kallo kowa yaje ya sayo takalmin kwali da mayafi har da jaka, undies da tarkacen kayan kwalliya dana kitso.
Taji babu daɗi a kan hakan da aka mata amma sai dai kasancewar ba wannan bane a gabanta yasa bata wani nuna damuwa ba, a halin yanzu ta gama gajiya da zaman nan ɗin wanda har take jin gara ta koma wurin Mama. Idan kuma ta tuna da tashin hankalin data baro a can sai taji gaba ɗaya rayuwar ta fice mata a kai, bata da wani zaɓin ɗaya wuce tayi kuka ta share taci gaba da jiran yanda Allah zai yi da ita.
Ana haka aka gudanar da bikin sallah wanda ko wane yaro ya fito tsaf domin Iyayensu sun musu kaya masu kyau, ƴan matasa kamarta kuwa da yawa samari sun ƙara musu yayinda ita kuma ta tsira da ɗinki kala ɗaya da Inna Sahura tayi mata shima saboda gudun bakin duniya ta iya ɗinka mata shi ɗin. Haka dai aka yi shagalin sallah aka ƙare ƙawayenta nata mata dariya da shigar da tayi, yayinda suke cewa shegen girman kanta ne ya hana ta bawa masu sonta dama ita ma da an mata.
Washe garin Sallah Inna Sahura ta koma sana'arta sabo da ranar Idi ne kawai bata yi abin sayarwa ba sabo da azabar son kuÉ—inta, Nanah taci gaba da tallaha kamar yanda ta saba tana kawo mata kuÉ—i tana tara wa don amfanin kanta dana Ć´aĆ´anta, don Paracetamol wannan idan zata saya mata tayi ta mita kenan.
A cikin shekara ɗaya da Nanah tayi a hannun Inna Sahura da Kawu Basiru kai ba zaka taɓa cewa ita ce ba, domin kuwa gaba ɗaya ta jigirce da wahala ta koma abin tausayi ga yawan jinya. Ana haka ne ta kwanta rashin lafiya wan da duk nacin Inna Sahura sai da ta haƙura ta dai na ɗora mata sana'a, sai dai tun da ta kira mai chemist ya duba ta sau ɗaya bata ƙara bi ta kan ta ba don tace ba zata iya asarar kuɗaɗenta ba. Abu kamar wasa ciwo ya fara cin ƙarfinta ta yanda ko tashi bata iya yi, amma duk da haka Inna Sahura ta kasa cire kuɗi ta kai ta asibiti. Duk ma wanda yazo mata da maganar sai ta masa tatas tace idan tausayi ne dashi ya ɗauke ta ya kaita mana, ɗan abincin da take bata ma yanzu abun ya fara isar ta domin kuwa tana cikin jerin mutanen da in dai ba zasu amfana da mutum ba to ba zasu iya amfana masa ba.
Kawu Basiru ganin yanda yarinya ke ƙoƙarin mace wa yasa yaje ya samu Inna Sahura a kan ta bayar da wani abu a kaita asibiti, balbale sa tayi a kan ba zata bayar da ko sisinta ba ai shine dolenta me zai hana shi ya ɗauke ta ya kaita da kuɗinsa. Ran Kawu Basiru ya fara ɓaci a wannan karon don haka yace.
"Amma gaskiya Sahura baki da imani, yanzu duk irin bautar da yarinyar nan tayi maki da irin kuÉ—in data nema maki ba zaki iya bayar da koda dubu biyu bace a kaita asibiti a duba lafiyata ba. Yanzu kuma idan ta warke sai kice zaki É—ora mata tallah ko?."
"Kaga Malam rufe min baki ba zan bayar ɗin ba ai ba nice na haife ta ba bare a min dole, waɗan da na haifa dai ba yanda zan yi dole zan ɗauki nauyin su amma Wallahi banda ƴar ƴar'uwarka da ban haifa ba, mu da muke dolen ka baka ɗauke nauyi mu ba ba zaka ƙara min wani a kai ba. Kuma da kake maganar tana nema min kuɗi ai ba a kyauta take min ba tun da nima ina ciyar da ita da mata tufafi ehe, duk ma inda zaka ɗauke ta ka kaita bai dame ni ba in Zulai zaka kai wa can ku kuka sani." Ta ƙare maganar cikin ko in kula taci gaba da kasa abincinta a robobi ta ɗora wa Abdul Malik ya tafi tallah.
Abin duniya ya yiwa Kawu Basiru yawa gashi bashi da ko sisi bare ya saya mata koda magani ne, gidan Inna Zulai ya tafi yayi mata bayani abin da ke faruwa, cikin jin haushi tace.
"To yanzu da kazo kake gaya min me kake so in maka? Ina ce kai da Matarka kuka haɗa kai kuka nuna min fin ƙarfi a kan ƴar ƴar'uwata, wato sai yanzu da wahala ta samu shine za'a neme ni to babu abin da ya dame ni kuje can ku ƙarata kai da ita!." Ta ƙare maganar cikin ɓacin rai.
"Haƙuri zaki yi naka dai dole naka ne ba yanda zaka yi, yanzu idan muka bar yarinyar nan a ɗaki ta mace Ramatu muka yiwa kuma kin san ba zata taɓa yafe mana ba. Don haka kiyi haƙuri ki kawo abinda ya samu muje a kai ta asibiti." Kawu Basiru ya faɗa. Da irin waɗan nan magan-ganun ya lallaɓa Inna Zulai ta amince suka tafi ta duba jikin Nanah wacce taji tsoro ganin yan da ta ƙare gaba ɗaya ta lalace.
"Innalillahi wa inna ilaihirraju'un! Yanzu haka yarinyar nan ta zama Basiru, amma gaskiya Sahura an yi muguwar Mace yanzu sabo da Allah idan ƴarki ce zaki iya zuba ido ki barta cikin wannan halin bayan kina da damar da zaki taimaka mata, duk irin bautar da ta maki?!." Inna Zulai ta faɗa cikin ɓacin rai. Ita ma Inna Sahura taso wa tayi suka kaure da cece kuce sai da ƙyar Kawu Basiru ya hana su suka yi shiru. Kallon Kawu Basiru Inna Zulai tayi tace
"Maganar gaskiya babu kuɗi mai yawa a hannuna don cinikin furar yanzu ba samu wa yake yi sosai ba, amma abinda za'a yi shine ka maza ka kira Bala mai chemist yazo duba ta, bari in ɗauraye mata jikin kafin ka dawo." Inna Zulai ta faɗa tana miƙewa ta ɗauki bahon wanka ta ɗebo ruwa a rijiya ta kama Nanah ta kai ta bayi ta mata wanka ta sauya mata kaya, sannan ta dama furar da tazo da ita ta bata tasha da ƙyar wacce tana kurɓa ta fara sheƙa amai. Sai da ta kammala ta gyara mata jikinta sannan ta ƙara bata ragowar ta shanye kuma cikin sa'a bata amayar da ita ba.
Ba'a daɗe ba Kawu Basiru yazo da Bala mai chemist ya duba ta ya mata allurai da ƙarin ruwa sannan yace lallai su kai ta asibiti a mata awon jini domin tana buƙatar ƙarin jini. Tashi sosai hankalinsu yayi sabo da basu da halin kaita asibitin don daga Kawu Basiru har Inna Zulai ɗin ba wani abu gare su ba, shi yana zaune baya sana'ar komai ya sakar wa Inna Sahura nauyin riƙe gida shi yasa take masa rashin mutuncin data ga dama bai isa ya tanka mata ba, sai ta hau shi da mahaifa da gore-gore akan abin da take yi.
Ita ma Inna Zulai ɗin Mijin nata duk ɗaya shida Kawu Basirun don shima babu abin da yake tsinana wa, ita ce ke yin ƴar sana'a take riƙe su ita da yaranta guda biyu Mace da Namiji waɗan da suka rage mata don duka yaran data haifa koma wa suke yi tun suna yara.
"Yanzu meye abin yi Basiru? Kana ji dai maganar ƙarin jini da yayi, ina muka ga kuɗin nan?!." Inna Zulai ta faɗa cike da damuwa.
"Tun da dai an saka mata ƙarin ruwa da allurai har ta samu bacci ina ga mu dan saurara muga abin da Allah zai yi, maganar jinin kuma zan je in sassaƙo gamji a tafasa a riƙa bata tana sha in sha Allah jini zai wada ce ta. Cewar Kawu Basiru.
"Haka ne amma maganar gaskiya kamata yayi ka nemi kuɗin mota ka kai yarinyar nan wurin dangin ubanta tun da mu dai bamu da halin da zamu iya riƙe ta, shi kuma Ya'yan Mahaifinsu yana da halin da zai haɗa duka ita da Khalid ɗin ya riƙe, kai ko Khalid zai iya kula da ƴar'uwarsa a yanzu." Inna Zulai ta faɗa tana gyara ma Nanah dake bacci hannun da aka jona mata ƙarin ruwa.
"In sha Allah hakan zan yi, ni wannan karon Khalid ɗin ya jima bai zo ba ko rasuwar Baba bai sani ba fa, sannan Ramatu tun da ta tafi har yau bata taɓa zuwa ba kuma babu wanda yaje yaga halin da take ciki sai da ta turo yarinyar nan muke ji daga gare ta. Ko rasuwar Baba ita ma bata sani ba, gaskiya ya kama ta mu daure a cikinmu wani yaje ya sanar da ita." Cewar Kawu Basiru.
"Gaskiya kam ya kama ta a sanar da ita domin duk lokacin data samu labarin rasuwar Baba kuma ba'a sanar da ita ba a kan lokaci abin ba zai mata daÉ—i ba, sai dai Basiru ka san yanda kuÉ—in mota ke tsada. Daga nan zuwa Zamfara fa dole sai mutum ya shirya." Cewar Inna Zulai.
"Haka ne da wannan kuma, Allah dai ya bada yanda za'a yi." Kawu Basiru ya faÉ—a.
Ranar a nan Inna Zulai ta yini suna tattaunawa irin ta ƴan'uwa ita da Kawu Basiru, ko da dare yayi zata tafi roƙonta yayi a kan ta kwana ta kula da Nanah ya kuma yi alƙawarin tana samun sauƙi zai nemi koda aron kuɗin mota ne ya kaita wurin ɗan'uwanta. Da wannan Inna Zulai ta haƙura ta kwana kula da Nanah wacce jikinta ya rikice da dare don har suma ta riƙa yi.....