Free chapter · Read without an account

14

by Kansa'u Bello · KOMAI TSANANI

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    *KOMAI TSANANI* 

             *By*

         *KANSA'U* *BELLO* 
    
   *(OUM FATIMA)* 
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


   *PAGE 014* 


 *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*




**** Da dare bayan Abba ya dawo Mabaruka da Mamy suka sanar dashi ƙarya da gaskiya a kan abin da ya faru, ransa a ɓace ya ɗaga waya yayi kiran Khalid yace masa maza yazo ya same sa a palonsa. Bai wani ji ɗar ba ya nufi sashen Abban sabo da dama ya san za'a yi hakan, shi Kuwa a halin yanzu ya daina jin tsoron duk wani abin da za'a masa a gidan sabo da ya lura idan baka tsaya ma kanka ba to babu mai tsaya maka. Shi yasa ya ɗaura aniyar tsaya ma kansa ya kuma tsaya ma ƙanwarsa.

   Da sallama ya shigo Palon bayan an bashi izinin shiga, a zaune ya samu Abba da Mamy a saman kujera Mabaruka na zaune a ƙasa ta ɗora kanta saman ƙafafun Mamy hannunta ɗaure da wani farin ƙyalle wanda ke nuna alamar cewa taji ciwo ɗazun sai da aka gyara mata.

   "Barka da dare Abba, an yini lafiya." Khalid ya faɗa kansa a ƙasa cike da girmamawar da yake bashi ta Uba.

   "Barka dai." Abba ya bashi amsa a taƙaice.

   "Barka da dare Mamy." Ya faɗa yana mayar da akalar gaisuwar tasa kan Mamy da tun da ya shigo take aika masa harara ita da ƴarta.

   "Riƙe gaisuwarka bana so mara kunya." Ta faɗa cikin ɓacin rai don a rayuwa idan kana son kaga fushin Mamy a gidan nan to ka taɓa ɗaya daga cikin yaranta.

   "Khalid me ya haɗa ka da ƴar'uwarka har ka ji mata irin wannan ciwon haka?." Abba ya faɗa yana tsare sa da ido fuska a haɗe, don shima ɗin ba baya bane wurin son yaransa. Cike da ladabi Khalid ya bashi amsa da cewa.

   "Abba hannu ta ɗaga zata dake ni, ni kuma shine na riƙe hannunta... Amma ban san zata ji ciwo haka ba, a gafarce ni Abba." Yayi maganarsa a nutse cikin girmamawa. Kuka Mabaruka ta fashe dashi tana cewa.

   "Wallahi ƙarya yake yi Abba, da saninsa ya ji min ciwo a kan waccen yarinyar.... Kuma har cewa yayi wai ka cinye masu gadonsu, yayi ta faɗar magana mara daɗi a kanka Abba." Ta ƙare maganar tana rushewa da wani kukan don ta ƙara tunzura Abban ya ɗauki mataki mai tsauri a kansa. 

   "Kin ga yi shiru ki daina ɓata bakinki kar ma kije ki fama ciwonki a banza." Mamy ta faɗa kafin ta jiyo kan Abba ta kalle sa tace.

   "Bafa zan yarda ba Alhaji dole sai an hukunta sa a kan abin da yayi wa yarinyar nan." Abba da ransa ke ɓace da batun gado da yaji an ambata ya kalli Mamy bai ce komai ba ya ɗauke kai ya zuba wa Khalid ido. Wato Khalid har yayi ƙwarin da zai fara magana a kan gadonsu, to waye ma ya faɗa masa cewar gadonsu yana hannunsa. Lallai idan yayi wasa yaron nan zai iya fito na fito da shi wata rana a kan gadon nasu daya jima da mamayewa ya mayar da komai nasa, don daga gidan har babbar gonar da Mahaifin nasu ya bar musu ya sayar dasu da sunan zai juya musu kuɗin. Yayin da ya zuba kuɗin a Kasuwancinsa ya ƙara bunƙasa shi yake warkajaminsa dasu tuni yama manta da cewar dukiyar marayu ce, yayin daya kasa kulawa da amanar marayun da ɗ'anuwansa ya bar masa. 

    Ajiyar zuciya ya sauke ya sassauta fuskarsa sabo da tunanin daya zo masa ya kalli Khalid yace.

   "Da gaske ne abin da ta faɗa?."

   "Har ma sai ka tsaya tambayarsa Alhaji ai ka san yaron nan zai aikata fiye da haka ma, kuma Mabaruka ba zata ƙir-ƙiri maganar haka kawai ta masa ƙarya ba tun da bata san da ita ba." Hannu Abba ya ɗaga mata alamar baya son taci gaba da magana ya zuba wa Khalid ido yana son jin amsa daga bakinsa. Kansa ya duƙar ƙasa yace.

   "Ba haka bane Abba gorin gida suke mana kullum nida Lily shine yau da tayi min nace muma ba daga sama muka faɗo ba muna da Iyaye kuma muna da gida idan bata yarda ba zata iya tambayarka sabo da yana hannunka." Zuwa yanzu sosai mamakin yaron ya fara kama Alhaji Bala ganin yanda ya kalli idonsa yayi bayani a natse babu tsoro bare shakka, tabbas nan gaban yaron nan zai zama tsayayyen da zai iya tunkararsa kai tsaye don son ya ƙwaci haƙƙinsu dake hannunsa, wan da shi kuma baya jin zai iya basu don a halin yanzu dukiyar da yake taƙama da ita duka tasu ce. Sabo da a shekarun baya ya haɗu da ƙaddarar ƙarayar arziƙi sakamakon kayan sa da suka ɓata, ganin zai durƙushe gaba ɗaya ne yasa ya yanke shawarar sayar da gidan ƙanensa da ƙatuwar gonarsa dake can ƙauyensu ya sake tada jari ya tashi Kasuwancinsa.

  Ajiyar zuciya ya sake sauke wa a karo na biyu ya fuskanci Khalid da kyau yace.

   "Kan jina ko? Daga yau kar na sake jin wannan maganar a bakinka, kai ma nan gidanku ne zaku iya zama a cikinsa har ƙarshe rayuwarku, sannan kar ka ƙara aikata makamancin abin da ka aikata wa ƙanwarka don ita Mace ce ba ƙarfinku ɗaya ba zaka iya illata ta." Abba ya faɗa kafin ya juya ga Mabaruka yace.

   "Ke kuma daga yau kar wan da ya kara yi musu gorin zama a gidan nan, sannan kar ki ƙara cewa zaki dake sa tun da ba girmarsa kika yiba... Ku tashi ku bani wuri na gama magana." Abba ya faɗa yana kallon su duka. Cike da mamakin rashin ɗaukar matakin da bai yi ba Hajiya Masa'uda ta kalle sa tace.

   "Amma Alhaji...." Hannu ya ɗaga mata ya dakatar da ita kafin ta faɗi abin da tayi niyya ya kalli yaran yace.

   "Kuje na sallame ku." Ba musu Khalid ya miƙe ya fice itama Mabaruka tabi bayansa tana ƙun-ƙuni tamkar zata fashe. Sai bayan sun gama ficewa ne ya kalli Hajiya Masa'uda da ranta yake a matuƙar ɓace yace.

   "Ke kina ganin idan yaron nan yaci gaba da ɗaga maganar gadonsu har ya nema a kwai abin da zai rage min idan na basu?... To daga yau kar wan da ya ƙara musu gorin zama a gidan nan na faɗa muku." Cikin ɓacin rai itama tace.

   "Babu abin da ya shafe ni da wannan, abin da na sani kawai shine idan ya ƙara taɓa min yara a gidan nan kotu ce zata raba mu tun da kai na lura ba daukar mataki zaka yi ba sabo da tsoron kar yace zai karɓe gadonsu dake hannunka. Yo Allah na tuba duka ma Khalid ɗin guda nawa yake?.... Yaushe aka haife sa da zaka nuna kana jin tsoronsa?!." Ta ƙare maganar cikin ɓacin rai.

   Kallon baki da wayau ya mata ya miƙe ya shige bedroom ɗinsa dai-daita lokacin da Hajiya Zuhura ta shigo, ta sha wanka tana ta baza ƙamshi abinta kasancewar ita keda turaka yau. Wani mugun kallo ta watsa wa Mamy lokacin da suka haɗa ido tace.

   "Uban me kike yi a dakin Mijina bayan kin san cewa yau girki na ne?." Kallon sheƙeƙe mai cike da rainin wayo Mamy ta bita dashi taja tsoki ta watsar ta nufi ƙofa zata fice.

   "Kan babbar Bala da rawanin nan, ke kin isa ina maki magana ki watsar dani baki bani amsa ba?!." Mumy ta faɗa cikin ɓacin rai da azabar kishin dake cin zuciyarta tana tare mata hanya, don a tunaninta wani abin tazo karɓa wurin Mijinta aka munafunce ta. Mamy na ƙoƙarin yin magana Abba ya fito yace.

   "Menene kuke yi haka sai kace wasu ƙananan yara?... Ku ko kunya bakwa ji kun haife duniya amma ku tsaya kuna cece kuce sai kace wasu Kaji?!." Ya ƙare maganar ransa na ɓaci da wannan rashin hankalin nasu. Duk da cewa ya san Mumy (Hajiya Zuhura) ita ke jawo rigimar a kullum sabo da rashin haƙurinta, zargi, da mitar tsiya a kan abu idan ta kama. Ita kuma Mamy (Hajiya Masa'uda) idan kaji ta buɗe baki tana tijara to yaranta aka taɓa mata a gidan haka take tun lokacin daya aure ta, tafi kowa son ƴaƴanta a gidan duk abin da da suka yi basa laifi a wurinta.

   Mumy na ƙoƙarin fara mitar tata ya dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu ya nuna mata ƙofar bedroom ɗinsa yace.

  "Zo ki shige." Harara ta maka wa Mamy kafin ta wuce tana kwarkwasa tamkar wata ƙaramar yarinya duk don ta cusa mata haushi. Sai da ta shige kafin ya kalli Mamy yace.

   "Yi haƙuri jeki ɗakin ki." Ƙwaffa taja sannan ta wuce tana bugo masa ƙofa da ƙarfi. Koda ya shiga mita Mumy ta taso sa a gaba da ita a kan haƙurin ɗaya bawa Mamy ita bai bata ba bayan kuma ita aka yiwa laifi aka shiga haƙƙinta. Sabo da yana son ta bar sa yayi tunani a kan matsalar da yake tsoron zata iya taso masa nan gaba yasa ya bata haƙurin ita ma ta rabu dashi.


 *Bayan sati biyu.....* 

Bari mu wai-waya baya don jin wace alaƙa ce ke tsakanin Familyn Alhaji Bala da wanda suke kira da Dadyn Abuja?.

  
★ Yau ta kama ranar da mutanen gidan gaba ɗaya zasu wuce Abuja sabo da bikin da za'a yi a gidan mutumin da suke kira da Dadyn Abuja wan da ya kasance yayan mai gidan ne wato Alhaji Bala wan da suka haɗa Uwa ɗaya dashi. Hajiya Maryam Mahaifiyar su Alhaji Bala wacce suke kira da Mamu haifaffiyar garin Kano ce don a nan ta buɗe idonta, sai dai asalin iyayenta baƙin haure ne da suka zo daga wani Niger can wani ƙauye suka yada zango a garin Kano har suka kafu. Aurenta na fari wanda aka mata na saurayi da budurwa wani attajirin mutun ta aura a garin Kaduna. Harkar Kasuwanci take kawo shi Kano wan da a nan ya haɗu da ita sakamakon wani tsau-tsayi da ya faru na bige almajirin Mahaifinta da mota da yayi kasancewarsa malamin addini dake koyar da almajirai. Abinda ya haɗa su da Malam Buba Mahaifin Mamu shine almajirinsa ya taɓa bigewa da mota wanda ya ɗauke shi ya kai shi asibiti aka yi masa treatment kasancewar bai ji ciwo sosai ba sabo da a hankali motar ke tafiya. Tambayar almajirin yayi ɗan wace makaranta ne ya kwatanta masa shine ya mayar dashi, sun gaisa da Malam ya bayar da haƙuri a kan abin da ya faru. Malam ya karɓe sa hannu biyu ya nuna masa cewar babu komai haka Allah ya ƙaddara kuma ai abin yazo da sauƙi tun da bai ji wani ciwo sosai ba. Godiya yayi wa Malam sosai ya ciri kuɗi masu yawa ya bashi, sam Malam yaƙi karɓar kuɗin sai da yace sadaka ce ya bayar a raba wa almajirai kafin ya amsa. Lokacin da zai tafi ne Mamu ta fito daga cikin gida sakamakon aiko ta da Innarta tayi ta amshi kuɗin cefane a wurin Malam, gaishe sa tayi da ladabi sannan ta ƙara sa wurin Malam ta faɗi saƙonta. Kallo ɗaya da mutumin ya mata Allah ya jarabce sa da soyayyarta mai tsanani wan da tun da ya tafi ya kasa sukuni sai da ya dawo ya yiwa Malam bayanin abin da ke cikin zuciyarsa game da ita.

   Ya sanar dashi cikakken sunasa Alhaji Muhammad Ali mai ƙusa, ɗan asalin jahar Kaduna ne a wani ƙaramin ƙauye, amma a yanzu suna zaune a garin Kaduna da Iyayensa da iyalinsa. Yana da Mata ɗaya da yara biyu, sannan sana'ar ƙusa ita ce sana'ar sa. Malam bai ƙi amincewa ba sabo da ya yarda da mutuncin mutumin da kamslarsa don haka yace ya bashi lokaci zai yi bincike da shawara kafin ya sanar dashi duk hukuncin daya yanke, godiya ya masa ya tafi bayan alkairin daya kuma yiwa Malam ɗin wanda yaƙi karba sai da kansa ya bawa wani Almajirin Malam yace su raba.

 ★ Bayan kwana biyu Malam da kansa ya shirya shida aminsa suka je har garin Kaduna suka yi bincike a kan Alhaji Muhammad Ali mai ƙusa in da suka dawo da sakamako mai kyau. Bai wani tsaya bata lokaci ba koda ya dawo ya sanar dashi cewa ya amince ya bashi auren Maryama ya turo magabatansa kawai a ɗaura musu aure. Godiya sosai Alhaji Muhammad Ali mai ƙusa yayi da jin wannan labari in da yana koma wa bai tsaya ɓata lokaci ba ya turo waliyyansa suka zo nema masa aurenta, wan da Malam ya buƙaci da a ɗaura auren kawai ba sai an yi ta kai-kawo ba. Basu ƙi amincewa ba suka biya sadaki nan take aka ɗaura musu aure. A gaban shaidun da Malam ya kira wo.

   Bayan an ɗaura Malam ya shiga ciki ya sanar da Mahaifiyar Mamu cewar ya ɗaura mata aure yanzu, bata damu ba kasancewar ta san da maganar dama, sai dai bata yi tunanin cewa za'a ɗaura auren a yau ba. Amma duk da haka addu'ar Allah ya sanya alkairi tayi wa tilon ƴarta data haifa a duniya kafin ta shiga ɗaki ta sanar mata cewar ta shirya za'a kaita gidan Mijinta.

  Bata da ja a kai don duk hukuncin da Iyayenta suka yanke a kanta biyayya ce tata, don haka da taimakon Mahaifiyarta ta shirya tsaf aka haɗa mata ƴan kayanta suka wuce Kaduna cike da kewar Iyayenta.....


  Barkammu da dare.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.