Free chapter · Read without an account
15
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*KOMAI TSANANI*
*By*
*KANSA'U* *BELLO*
*(OUM FATIMA)*
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
*PAGE 015*
*BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*
Koda suka isa Kaduna kai tsaye gidan Iyayen Alhaji Muhammad Ali mai ƙusa wakilan daya tura suka wuce da ita, dama ƙanen Mahaifinsa ne da yayan Mahaifiyarsa ya tura nema masa auren. Bayan sun isa suka saka aka kirawo sa yazo suka yi musu bayanin abinda ya faru cewar Mahaifinta ya buƙaci a ɗaura auren kawai ga kuma Matarsa nan sun taho masa da ita.
Sosai yayi murna yayi musu godiya da alkairi suka tafi, mahaifiyar Alhaji Muhammad Ali mai ƙusa ita ce ta fara sukar auren da cewa wane irin aure ne wannan sai kace an gaji da yarinyar daga zuwa neman aure sai a ɗaura kawai a turo ta babu wasu dangi babu wani shagalin biki, ai wannan kwaɗayi ne kawai da son abin duniya irin na talaka.
"Me yasa za kiyi irin wannan tunanin a kan mutanen da baki sani ba ne, ai wannan din ba komai bane face karamci da ƙaurace wa bidi'a. Sabo da haka kar in ƙara jin irin wannan maganar." Tashi kawai tayi ta bar wurin don ita dai bata yarda da wannan auren ba don tun farko da ya sanar dasu yana neman auren bata goyi baya ba, Alhaji kawai ya goya masa baya.
"Ɗauki Matarka ku wuce Allah ya bada zaman lafiya, sannan kayi ƙoƙarin ganin ka tsayar da adalci a tsakanin iyalinka, sannan ita mai ɗakin naka kayi ƙoƙarin yi mata bayani ta hanyar da zata fahimta sabo da abin ne yazo kai tsaye babu tsammani." Alhaji Ali ya faɗa.
"In sha Allah Alhaji zan yi yanda kace." Ya faɗa yana tashi ya kalli Mamu dake zaune lulluɓe cikin mayafi yace.
"Tashi muje in kai ki gidanki." Babu musu ta miƙe jiki a sanyaye sakamakon irin tarbar data samu daga wurin surukarta. Hanya ya nuna mata ta fice ya ƙara yiwa Alhaji sallama tabi bayanta suka wuce. A motarsa ya ɗauke ta suka nufi unguwar da gidansa yake. Ƙaton gida ne mai kyau irin na wan can zamanin kasancewarsa mutum mai arziƙi, kai tsaye ɗakinsa ya kaita ya zaunar da ita a palonsa yace ta zauna yana zuwa. Zaman tayi har ya fice kafin ta buɗe fuskarta sosai tana ƙare ma Palon kallo wan da yayi matuƙar tsaruwa da tsari irin na wan can zamanin. Ya ɗan jima kafin taji alamar dawowarsa in da tayi maza ta rufe fuskarta ta duƙar da kai.
Alhaji Muhammad shine ya fara shigowa kafin Matarsa Hajiya Alawiyya da ake kira da Inno ta biyo bayansa, sai dai ita tana ƙara sa shigowa cikin ɗakin ta taka birki a bakin ƙofa sakamakon ganin wata mace da tayi zaune saman kujera da lulluɓi irin na amare.
"Ƙara so mana Hajiya." Ya faɗa yana nuna mata wurin zama.
"Me nake gani haka?... Wacece wannan zaune a cikin ɗakinka?... Me kake son nuna min ne wai Alhaji?!!!." Ta ƙare maganar cikin ƙaraji har tana ganin duhu a idanunta tsabar tsoron amsar da zata iya samu daga gare sa. Maimakon ya bata amsa sai ya ƙarasa ya kama hannunta ya zaunar da ita saman kujera yace.
"Ki natsu tukuna sai na baki duka amsoshin tambayoyinki."
"Babu wata natsuwa da zan yi kawai ka faɗa min me wannan take yi a gidan nan, miye alaƙarka da ita?." Tayi masa maganar a tsawace. Ransa ne ya fara ɓaci da abin da take yi ɗin don haka shima a tsawacen yace mata.
"Matata ce ita ɗin sadaki na biya aka aura min aure da ita!." Tamkar saukar aradu haka taji dirar maganar a cikin kunnenta don har wani dum!!! Taji na ɗan wani lokaci kafin ta dawo hayyacinta.
"Me naji ka faɗa Alhaji?..." Ta faɗa tana fatan jin saɓanin amsar daya bata ɗazu.
"Ai kin ji abin da na faɗa sarai, Matata ce ita ɗin yau aka ɗaura mana aure da ita, matata ce ta sunnah." Ya sake bata amsa kamar yan da ta buƙata ya koma kusa da Mamu da jikinta ya fara rawar tsoro ya zauna yana ƙoƙarin yi mata magana ya tsinci muryar Inno na faɗin.
"Zancen banza kenan kake yi Alhaji Wallahi ba zai taɓa yiwuwa ba, ni zaka tozarta ana zaune ƙalau?!." Tayi maganar cikin ficewar hayyaci tana nufar in da Mamu ke zaune zata finciko ta yayi hanzarin riƙe mata hannu.
"Wane irin shirme ne kike yi haka!?." Yayi maganar a tsawace.
"Sakin ta zaka yi yanzun nan don wallahi ba'a haifi Macen da zata shigo min gida a matsayin kishiya ba." Ta ƙare maganar cike da hayagaga. Ganin da yayi ba zata natsu suyi magana cikin kwanciyar hankali ba yasa ya kama hannunta ya jata da ƙarfin tsiya ya kaita ɗakinta ta kulle sannan ya dawo ya shiga rarrashin Mamu tare da kwantar mata da hankali. Cike da kulawa da soyayyar da yake mata ya kama hannunta ya riƙe cikin nasa yace.
"Ki kwantar da hankalinki kin ji ko, babu abin da zai faru ita haka take nuna ɓacin ranta. Amma da zarar ta huce komai zai wuce, zata fahimce ni idan nayi mata bayani a natse. Yanzu zaki fara zama a nan ɗakin na kwana biyu kafin nan za'a gyara maki naki ɗakin a zuba maki kayan ɗaki." Kai kawai ta iya ɗaga masa don har ga Allah a tsorace take, bata saba da rigima ba sabo da ita kaɗai Iyayenta suka haifa kuma kowa ji yake da ita a gidansu babu mai yi mata tsawa bare duka. Yanzu da taga abin da Matarsa keyi sai tsoro ya kamata, lallaɓa ta yayi da wayo da dabara har ta manta komai suka raya darensu cikin aminci, soyayya, tausayi, da kulawa.
★ Washe gari Alhaji Muhammad Ali mai ƙusa da kansa yaje ya ɗauko Mahaifinsa ya kawo shi har gidan ya haɗa su ya musu nasiha ya rarrashi Hajiya Alawiyya ya yi mata bayanin yan da auren ya kasance, tana jin shakkarsa shi yasa ta amince da auren a gabansa. Addu'a yayi musu baki ɗaya ya musu sallama ya koma gida. Tun da Alhaji Ali yazo ya musu nasiha sai Inno ta ɗauke kai daga kan Alhaji Muhammad da Mamu ta barsu suka ci amarcinsu na kwana bakwai ba tare data sake tayar da wata rigimar ba, ba don ta haƙura ba sai don shawarar da Inna Mahaifiyar Alhaji Muhammad ta bata kasancewarta ƴar ƴar'uwarta don auren gida ne aka yi musu. Ita ce ta taushe ta a kan tabi komai a hankali don Alhaji ya goyi bayan auren in ta tayar da fitina zai daina ganin mutuncinta. Amma idan ta bari komai ya lafa amarya ta saki jikinta sai tabi ta hanyar kirsa da makirci ta fitar ta fitar da ita a gidan cikin kwanciyar hankali ba tare da wani ya zarge ta ba, da wannan shawarar tayi amfani ta bawa Alhaji haƙuri a kan abin da tayi. Sosai yaji daɗin hakan ya nuna mata cewar komai ya wuce ya haɗa su ya sake yi musu nasiha ya nuna wa Mamu cewar ita ce ƙarama ta girmama ta, sannan ita da take Babba ta riƙe girmanta sai su zauna lafiya.
Alƙawarin za suyi abin da yake so duk suka yi masa wani da hakan ya faranta masa, Mamu baiwar Allah dake da ƙananan shekaru zuciyarta ba komai ta amince da Inno in da take mata biyayya sau da ƙafa tamkar ita ta haife ta, zuwa lokacin tuni an gyara ɗakinta an zuba mata kaya ta tare abinta. A lokacin Inno yara biyu ta haifa Mace da Namiji, Namijin shine Babba mai suna Mudansir sai Macen mai Suna A'isha. Haka Mamu ta rungumi yaran nan tamkar ita ta haife su, duk wata wahalar Kashi da fitsarinsu wanka da wankinsu duk ita ce wan da tana hakan da zuciya ɗaya sabo da ƙaunar da take yiwa yaran.
Sosai Alhaji Muhammad yake jin daɗin zama da ita sabo da yan da take kyautata masa, duk abin da ya umarce ta babu musu zata yi shi koda bata son hakan a cikin zuciyarta, haka duk abin da ya hana ta ta hanu kenan duk son da take yi wa abin kuwa. Haka a ɓangaren Mahaifinsa yana sonta sosai yana kuma kyautata mata, a ɓangaren Mahaifiyarsa ne dai ta kasa samun karɓuwa duk da bata mata rashin mutunci sabo da Alhaji Ali baya bari. Ana haka ne ita ma Mamu Allah ya bata rabo ta samu juna biyu ita ma wan da hakan ya tayar da hankalin Inno don bata so ta haihu a gidan, so take ayi yanda za'a yi ta kaɗa ta ta tafi ta bar mata gidanta daga ita sai ƴaƴanta.
Ita kuwa Mamu sosai tayi farin ciki da ƙaruwar data samu don haka take kaffa-kaffa da lafiyarta, sai dai hakan bai sa ta daina kulawa dasu Mudansir ba sai dai idan bata da lafiya ne. Inno kuwa ganin in tayi wasa Mamu zata kafu a gidan ta yan da ba zata iya fitar da ita cikin sauƙi ba. Don kuwa tuni mamu ta shiga zuciyar da yawa daga cikin dangi sabo da kyawawan halayenta da girmama kowa da take yi a cikinsu. Hakan yasa Inno ta fara shirya wa Mamu tuggu da makirci kala-kala a wurin Alhaji, wan da yau da gobe tun baya yar da har ya fara yarda suka fara samun saɓani. Kullum sai ta dai-daici lokacin dawowar Alhaji gida zata takali Mamu da rigima ta rinƙa faɗa mata magan-ganu mara sa daɗi, ita kuma Mamu bata iya rigima ba sai dai tayi ta bata haƙuri wan da take juya haƙurin da take bata ta mayar dashi cewa zaginta tayi, haka zata yi ta kukan munafurci a gaban Alhaji.
★ Yau ma hakan ce ta kasance sai da ta dai-dai ci lokacin shigowar Alhaji ta fito ta fara takalar Mamu da rigima, baiwar Allah da take cikin damuwa tun da Inno ta fara fito mata da waɗan nan sababbin halayen ga laulayin ciki tana fama dashi, gata bata da wasu dangi a kusa da zata je ta rage damuwa. Yau tun da safe take fama da kanta bata jin daɗi don haka ta daure da ƙyar ta fito ƙofar ɗaki tace.
"Inno don Allah kiyi haƙuri ki yafe min idan wani abu na maki amma ni ban san me nayi maki ba kike min haka." Dariya Inno ta sheƙe da ita tace.
"Har ni zaki tambaya abin da kika min, ki aure min Miji amma shine kike cewa baki san abin da kika min ba." Ta ƙare maganar tana jin tamkar ta shaƙo wuyanta ta take ruwan cikinta har sai shegen cikin ya zube yabi rariya.
"Kiyi haƙuri Inno ba laifi na bane shine da kansa yace yana sona aka aura masa n..." Bata ƙara sa rufe baki ba Inno ta ɗauke fuskarta da zazzafan mari a fusace ta fara magana.
"Ni zaki kalli idona kice min wai Mijina yana sonki, to yau kuwa babu abin da zai hana ina take ruwan shegen cikin nan yabi rariya sai dai ayi duk ma abin da za'a yi." Ta faɗa cikin rufewar ido tana nufar in da Mamu take.
Cikin mummunan tashin hankali Mamu ta fara jada baya tana cewa.
"Don Allah kiyi haƙuri kar ki zubar min da cikina Wallahi ina son cikina kuma shima Baban Mudansir yana son sa, ni dai kar ki taɓa min cikina." Bata lura da shigowar Alhaji ba sai ganin Inno tayi ta dafe fuska ta fashe da kuka tana cewa.
"Yau abin naki har ya kai ki ɗaga hannu ki mare mamu duk irin kulawar da nake baki a gidan nan amma shine zaki min wannan sakamakon?.".....
Manage Please bana jin daɗi ne.