Free chapter · Read without an account

Chapter 10

by Maman ɗan albarka ce 🥰✍️ · KOWA YAƘI JI

_PAGE 1️⃣0️⃣_*

Wasa wasa Maryam tun dawowar ta daga wajen gamji, take faman zuba idon zuwan Haidar ya bata haƙuri ya maida ta, amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa yau har tsahon sati biyu babu wani labari.

Gaba ɗaya zaman gidan ya ishe ta komai bata jin daɗin sa, ga zafi ga sauron tsiya wai a haka ma suna ɗaura gidan sauro amma duk da haka yana shiga ciki yayi ta galla mata ciwo, duk ta fara fita hayyacin ta saboda tsabar tunanin da ya mata yawa.

Babbar damuwar ta a yanzu ita ce rashin kuɗi, dan duk wani kuɗi da ta zo dashi gidan ya ƙare dan ita bata cin abincin gidan sam siyo nata take a restaurant, ko ruwan gidan bata sha illa wanka da wanki kawai suma kayan sawar ta duk sun ishe ta dan dama biyu ne ta ɗauko daga na jikin ta sai wanda tasa a ƙaramar akwatin ta, 
gashi tana buƙatar wasu ji take kamar taje ta ɗauko kayanta tunda ko sakin mace akai ai tana da damar zuwa ɗaukar kaya, sai dai in ta tuna Boka yace karta sake ta taka gidan har sai Haidar ya zo sai ta haƙura.

Zaune take a bakin tsohuwar katifar Mama duk abin duniya ya dame ta ita kaɗai sai magana take da kanta, "Wallahi bari Mama ta zo ta bani kuɗi na data ranta na gaji, gashi yanzu bani da ko sisi ɗan canjin nawa daya rage na karya da shi Wallahi bazan iya ba.

Ladidi ce ta faɗo dakin hannun ta riƙe da wata babbar leda me ɗauke da tambarin wani gidan abinci, sai da ta ƙarewa Maryam kallon idanun ta a kan fuskar Maryam ɗin ganin yadda tayi wani irin baƙi abinka da wadda mai ya gama kwale fuskar gashi yanzu ba  wata kulawa take samu ba sai fuskar ta yi wani iri kamar wadda ta ƙone a  kumatun, wata dariya ce ta kama Ladidi aikuwa ta tuntsire da dariya sai da tayi mai isar ta tukun cikin shaƙiyanci tace
"Gaskiya Maryam zan baki shawara ki san yadda za ki yi ki koma gidan mijin ki Wallahi zai fi miki, kinga yadda kika koma kuwa kamar wata birinya fuska duk ta komaɗe ta jeme kamar wata tsohuwa, dama matsalar mai kenan ai da kinyi zaman ki a yadda Allah yayi ki da ba haka ba "
ta kuma fashewa da dariya harda tsugunnawa.

Wani takaici da haushi ne ya kama Maryam, har zata hau Ladidin da masifa su raba hali sai ta fasa tunawa da bata da ko sisi kuma da alama Ladidi ta shigo da kayan daɗi sai ta sassauta Muryar tayi kalar tausayi tace
"Uhmm Ladidi kin ganni dai ina jiran gawon shanu Wallahi ni kaina na matsu naga na koma ɗakina saboda wahalar gidan nan duk ta ishe ni gashi Haidar shiru yaƙi zuwa"
ta ƙarasa faɗar hakan muryar ta kamar za tayi kuka.

Sassauta dariyar Ladidi tayi ganin Maryam ɗin ta mata magana cikin sanyi duk da ba tayi zaton hakan ba, sai ta ɓoye mamakin ta tace
"Haba Maryam ke yanzu har sai kin jira mijin ki ya zo ya ɗauke ki ya maida ki haba kin so kanki da yawa, ki masa laifi tsaya jiran shi zai neme ki ai ina jin kuna maganar ke da Mama akan kin dakar masa uwar ƴaƴan sa shi yasa ya koro ki, wallahi in kika ci gaba da biyewa Mama zata kaiki ta baro ki, kinga dai uwata ce ko? to Wallahi in nayi aure bazan taɓa zama Mama ta bani shawara akan yadda zan zauna da mijina nabi ba"

Cikin jimami tuna abinda  taji su Mamar na tattaunawa da Hajiya Hajara ta jinjina kanta ta yarda da batun Ladidi gaskiya ne shawarar mama ba abin bi nace tace
"Hmmm Ladidi nima Allah ya sani ina nadamar bin shawarwarin Mama, amma ni yanzu fa babbar damuwata gamji yace min Haidar zai zo da ƙafar shi ya bani haƙuri ya maida ni, kinga har yanzu ba wani labari gashi bani da ƙwandala ta kaina yanzu ji nake kamar nasa hannu aka nayi ta ihu Wallahi"

Ajiye ledar hannun ta Ladidi tayi ta daɗe tana jiran wannan ranar dama, ai duk wanda yace ba zai dogara da Allah ba rayuwar shi na cikin garari bazai taɓa ganin daidai ba, sau tari in taga suna wani abin Maryam da Mama duk da kasancewar ta mahaifiyar ta abin na damun Ladidi, amma bata isa ta fito ta musu magana ba sai su hau kanta da faɗa, shi yasa ta kama kanta take harkar gabanta kawai bata shiga tasu.

Zama tayi kusa da Maryam tare da dafa ta tace
"Maryam ke yanzu kina ganin asirin da kike shi zai sa Haidar ya dawo gare ki? da zaki gane da kin tattara komai kin watsar ki tuba ki komawa Allah ki nemi gafarar shi akan abubuwan da kikai, dan wallahi nasan ba dan Allah Haidar ya aure ki ba, duk abinda kuke ina sane ƙyale ku nayi kawai na zuba muku ido,
Ki bar wani asiri ki tashi ki nemi soyayyar gaskiya daga ga Haidar in ya soki falillahil hamdu in bai soki ba ki barshi ya zauna da matar shi da yaran shi cikin farin ciki kamar yadda suke da ki fita a rayuwar su in da rabo kema zaki samu naki masoyin"

Jin yadda take ƙoƙarin yi mata wa'azi ba gaira ba dalili daga faɗa mata matsalar ta, hakan yasa Maryam fara hasala dan ita ta tsani wani wa'azi a yanzu burinta ta koma gidan ta, ta ɗora daga inda ta tsaya sai ta ɗauki mummunar fansa akan Salmah har sai ta gudu da ƙafafunta.

Ture hannun Ladidi tayi daga kafaɗar ta tace 
"Kinga Ladidi ba na faɗa miki matsala ta bane bafa dan ki sani gaba ki wani bani shawara, na dai faɗa miki ne a matsayin ki na ƴar uwata in ba haka ba kin isa kima ji"

Tashi Ladidi tayi ta kama haɓa tace
"Au daga faɗa miki gaskiya sai bak'ar magana, ai nayi zaton kin gane gaskiya ne shiyasa kika tunkareni, ashe dai halin na nan a ƙoƙon rai to ai sai kiyi Indai jujin ki asiri wallahi akwai ranar ƙin dillanci"

Ita ma tashi tayi cikin hayaniya da jin haushi tace
"Bazan ga wannan ranar ba muddin kuɗi suna maganin damuwa sai na komawa Haidar, kuma ku zuba ido ki gani kina gidan nan zai zo mu tafi, na fahimci baƙin ciki kike min dan kinga na samu shiga ke har yanzu kina nan babu mashinshini sai yawon banza da kika sa a gaba"

Inda sabo Ladidi ta riga da ta saba da gorin rashin aure har a gari ma yi mata ake, tun hakan ba damun ta yanzu sam baya damun ta cikin dariya ta shiga nuna Maryam ɗin da hannu tace
"Wai ke yanzu Maryam baki ji kunyar cewa haka ba, ke in ba ƙaddara ba da raban wahala me Haidar zai yi dake fisabilillahi, Jibe ki fa ke ba kyau ba bare ace ga ki kin kusa tardo shi a shekaru, ke bari na ƙarƙare miki batun wallahi Haidar ba sa'an ki bane ko kusa ko alama in dai ba asiri ba ko a ƴar aikin sa baki isa ki zo ba wallahi, ji ki fa abu sam babu tsari an riga da an gama yawon ta zubar dama aka cuci bawan Allah aka tarwatsa masa farin ciki wallahi kinyi asarar halin ki kin cuci kanki kin cutar da yarda da amanar da Salma ta baki, amma da sannu zaki girbi abinda kika shuka"

Faɗa ne sosai ya kaure tsakin su, tun suna yi da baki Har takai sun fara kaiwa juna hannu, aikuwa Allah ya bawa Ladidi sa'a ta ɗaga Maryam ta nana da ƙasa ta bita ta zaune ta shiga dukan ta kamar Allah ya aiko ta, tun Maryam na kare kanta tana ramawa har ta kasa hakan, sai da Ladidi ta naɗa mata ɗan banzan duka.

Mama da dawowar ta kenan daga gidan Aminiyar ta Hajiya Hajara tun daga zaure take jin muryoyin su, Maryam na ihun zata kashe ta ita kuma Ladidi na faɗin sai ta nakasta  ta.

A guje ta ƙarasa ko takalmin ƙafar ta bata cire ba ta faɗa ɗakin, ganin Ladidi akan Maryam yasa ta fincike ta da ƙyar ta yarda ta gefe ta fara magana cikin masifa
"Kashe ta kike son yi Ladidi? yanzu dan bana gidan shi kenan sai ku maida shi gidan dambe, sai kace ba ƴan uwan juna ba, wallahi kun bani mamaki ace kuna girma kuna cin ƙasa ba zaku gyara ku daidaita junan ku ba"

Da ƙyar Maryam ta tashi ta kalli Mamar sheƙeƙe da kumburarran bakin ta tace 
"Dole kice mu haɗe kanmu mana tunda ke burin ki kiga na dawo gida na zauna, wato tunda ƴar ki bata auro ba ni dana tashi na nemar wa kaina wajen zama shine kike son ki kashe min aure na dawo na zauna mu jeru, saboda banzan burin ki na ƙwadayin maza da kika ɗorawa kanki, to Wallahi Haidar yafi ƙarfin iskancin ki sai dai ki barmin kayana inda kika barshi, ai duk naji abinda kike faɗawa ƙawar ki na kina son Haidar ya sake ni tunda ƴar ki ba tayi aure ba nima gwara na dawo mu zauna, sannan kina sha'awar Haidar tun da kika ganshi da farko kawai dan na aure shine yasa kika barshi, amma yanzu ba zaki barshi ba in ya sake ni zaki kame shi yana biya miki buƙatar ki, tunda in kika aure shi za'a ce kinyi abin kunya mijin ƴar ki kika aura, to Wallahi duk naji komai shi yasa na ke kallon ki kawai harda sace min laya ta ai nasan ita ce, shine yanzu ita ma tijararriyar ƴar ki zata sakoni gaba da wani banza wa'azin ta ban sani ba ko auren Haidar ɗin take so ita ma"
ta ƙarasa faɗar hakan tana jefan su da wani mummunan kallo kamar idanun ta zasu faɗi.

Tunda Maryam ta faɗi taji komai Mama tayi mutuwar tsaye ta kasa cewa komai, sai faman raba ido da take gaba ɗaya jikin ta yayi la'asar.

Ladidi ce ma da haushi ya kamata, ganin yadda Maryam ke ci ma uwarta mutumci a gaban ta ita kuma tayi shiru yasa ta kalli Mamar cikin takaici tace
"Kin ga illar abin ko Mama gashi nan son zuciyar ki ya jawo ana zagin ki a gabana amma ban isa na rama miki ba, Abinda nake faɗa miki kenan tun farko kika ƙi jina, nace ki daina shigar nan da kike kisan kin girma Mama kina da kamata ace baki daina harkar banza ba, yanzu fa da ba dan banyi aure ba da tuni kin ajiye jikoki, me ma ya kaiki tunanin bin Haidar Mama me yasa?" 
Ta ƙarasa cikin karaji tana jin ciwon halin uwar tata na bin mazan bariki abinda ko ita bata yarda ta aikata iyakarta yawon dai amma namiji bai isa ta mallaka masa kanta ba.

Jin Mamar tayi shiru cikin kunyar abin da aka faɗa a kanta yasa Ladidin juyawa ta fuskanci Maryam dake ta faman jijjiga tana harare harare ta nuna ta da yatsa tace
"Ke kuma na dawo gare ki kinci sa'a ne kawai na ƙyale ki saboda ita taja rainin da kika mata da Wallahi sai na koya miki hankali, yadda ko ance ki zagi wata ma ba Mama ba ba zaki iya ba, shegiya mara asali wadda bata san halacci ba wadda bata san masu taimakon ta ba, ai ina ga da ba dan Mamar ba da yanzu Allah yasan ina kike, shine yanzu kin girma zaki nuna mata halin tsintacciyar mage kenan ko?"

"Koda ta riƙe ni ai ba tilasta tata akai ba a lokacin da ta barni yadda kowa ya barni, sai me uwar da ta haifeni ma ta gudu ta barni bare wani bare ai abin ba zai min ciwo ba ko"
Cewar Maryam tana wani kayayyak'owa.

"Ki tattara ki bar min gida na Maryam yanzu ba sai an jima ba nake so" cewar Mama ta fice a ɗakin ba tare da ta ƙara kallon ɗaya daga cikin su ba dan ita tasan me take ji a zuciyar ta.

Shewa tayi tare da dukan cinyar ta duk da kuwa na ƙarfin hali ne tace
"Tafi nono fari Wallahi, dama meye a gidan naki banda tsiya da talauci da kuka gada"

"A cikin tsiyar dai kika girma har kika zama mutum kuma a tattara a bar mana gida tunda ba gidan mai dattin hula bane"
Cewar Ladidi kenan ta fice ta barta a ɗakin.

Haɗa kayanta Maryam tayi tsaf ta gama yanke abinda ya kamata tayi a zuciyar ta ta fito ko kallon ɗayan ɗakin ba tayi ba ta fice gidan tana kad'a makullin motar hannun ta.

**************

*_SALMAH_*

Jin shiru an daina buga ƙofar yasa nayi zaton ya tafi, dan haka na je bakin ƙofar sai da na leƙa ta Ƴar Kofar makullin naga ba kowa tukun na  buɗe ƙofar, dan na yanke zanje gidan Mama uwani na nemi shawarar ta dan ban san abinda ya kamata nayi ba akan salim gashi yana shan duk magungunan da aka bamu amma ciwon kan shiru bai dakata ba,
Na'im na goye a bayana na kulle su Umar a ɗakin na bar musu komai dan kar yayi kuka Salim dama barci ya ke,
na fice cikin sanɗa daga farlon cikin ikon Allah har na fita gidan gaba ɗaya banga Haidar ba.

*****

*_😍MAMAN ƊAN ALBARKA CE 😍✍️✍️_*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.