Free chapter · Read without an account
Chapter 3
by ZAHRA B MRS · Bayan Murmushi
Page 3💬⌨️
The following year result ya fito na samu nayi passing exams dina gaba daya Alhamduillah ,na saka Abu zaria a first choice dina ba tare da sanin iyaye na ba,na sha wuya sosai Kafin diddi ta amince da zuwa na Abu zaria a cewar ta Nima nayi joining dinsu Adda Sabrina a university of abuja .
Lokacin tafiyata makaranta yana ƙaratowa, inda Diddi da Abbi ke ƙoƙarin ganin komai ya tafi daidai.
“Farhana, ga kayan gwanjo nan da na siyo miki daga Nyanya Market. Ki wanke ki goge, ke ma ki samu na canzawa a makaranta.”
Na ji zuciyata ta cika da tausayinsu. Cikin rauni na ce,
“Na gode Diddi. Allah ya ƙara buɗi.”
Hamma Fahad ne ya raka ni makaranta, inda muka tarar da Hamma Sajid yana jiranmu. Tun a hanya na fara kewar su Diddi, domin ban taɓa tafiya mai nisa ba tare da su ba.
Ko a Ilorin ma, kullum muna tare – kafata kafar Diddi.
Lokacin da muke sallama da Hamma Fahad, ya ƙara jaddada mini na riƙe sallah, na ji tsoron Allah, sannan na riƙa tuna nasihun Abbi.
Daga nan sai ya É—auko wayar Tecno M3 É—in da yayan Diddi ya aiko mini daga Ilorin, tare da gargadi mai tsanani kada na yi misusing É—in wayar.
“Ki yi karatu sosai,” ya ƙara faɗa.
.coursemate ɗin Hamma Sajid ce ta yi leading dina zuwa hostel ɗina, Alexander Hall. A nan na tarar da wasu ’yan mata biyu a cikin ɗakin.
Na yi sallama tare da shiga É—akin.
“Hey, ke ce ta cikonmu kenan?” muryar da na ji kenan bayan na shiga da sallama.
“Well, sunana Nusaiba Zakari, daga Kaduna. Ina karantar Microbiology, 200 level. Ke fa?”
Cikin jin kunya na ce, “Maryam Farhana, daga Abuja. Microbiology, 100 level.”
Sai a lokacin É—ayar ta É—ago ta kalle ni a É—an dakile, ta ce,
“Am Fateeha Yunus, from Kano. Microbiology, 200 level.”
Nusaiba ta taimaka min wajen arranging kayana. Har ta dafa min taliya ma ta kawo min.
Da farko na ƙi amsa, amma sai ta ce,
“Farhana, ki saki jiki. Mun zama ’yan uwa.”
Ta kuma ce mini bunk mate É—ina ba ta nan a lokacin, amma daga baya zan ganta.
Fateeha kuwa dai ba ta ƙara kula ni ba .
Bayan na gama setting sabuwar wayata, sai na kira ’yan gidanmu. Daga nan na install WhatsApp, sannan na kwanta barci.
Ban jima da kwanciya ba na ji wayata tana ringing.
Na É—an yi mamaki. Waye haka da daddaren nan?
Da na duba sai na ga international number.
Na É—aga.
“Hello guy, ina ka shiga ne? Ina ta kira.”
, “Wrong number. Ba wanda kake nema ba.” Na faɗa tare da ending call ɗin.
Bayan kusan mintuna goma, aka sake kira.
Na É—aga.
“Don Allah kar ki kashe. Ni ne na yi missing number ɗaya. I’m sorry.”
“It’s fine, ba damuwa,” na amsa.
Sai ya ƙara da cewa,
“Sunana Jafar Hadii, daga Adamawa. Amma ina karatun Medicine a Cyprus. Ke fa?”
Na amsa cikin nonchalant voice,
“Farhana… daga Zaria.”
Sai ya ce,
“Don Allah Farhana, ki saving number na mu dinga gaisawa.”
“Okay… good night.”
Na faÉ—a sannan na kashe wayar.
Washegari da safe sai ga bunkmate É—ina ta shigo. Ta gabatar da kanta da cewa sunanta Precious Ebuka, daga Anambra State. Engineering department 300lvl
fara tas, yar duma-duma,
Na ce, “Wow, nima yayana Sajid Ibrahim Matazu a department ɗinku yake shima 300lvl
Sai ta ce cikin fara’a, “Oh really? It happens cewa shi ne ma class captain ɗinsu.”
Ranar Monday muka shirya zuwa class da wuri.
“Ki jira mu tafi tare, tunda department ɗinmu ɗaya,” Nusaiba ta faɗa yayin da take ƙoƙarin saka takalminta.
Tuni Precious ta riga mu fita.
A lokacin na lura Fateeha tana shiryawa, amma tana ta sharena kamar ba ta san da wanzuwata ba.
Tana sanye da wata beautiful abaya wadda ban taɓa ganin irinta ba. Ta kuma ɗauko Apple iPad ɗinta, kallo daya zaka mata ka gane ta fito daga gidan masu kuɗi – rich and elegant.
Nan take na dubi kaina.
Ina sanye da long gown ɗaya daga cikin kayan da Diddi ta siyo mini a gwanjo. Doguwar riga ce har ƙasa, tare da pencil jeans da fashion veil.
Sai na ji kamar na Raina kaina
,da Sauri nayi auziiyya hamdala nayi,inda muka nufi department dinmu tare.na shiga class
naga an cika kowani seat da mutane .empty seat daya ne ,nufar seat din nayi tare da sallama ,dagowa tayi tare da gabatar da kanta tana murmushi hey am zainab adetayo, am maryam farhana Ibrahim na mayar mata da martanin murmushin ta
Bayan murmushi
XahraB(Mrs)
arewapen _ZAHRA B MRS