Free chapter · Read without an account
Book 2 (Thriller)
by Hawwa__B__Kumo · WAZEER!
đź’ đź’ đź’ đź’ đź’
©®AS-2024.
*Bᴀsᴇᴅ ᴏɴ ᴀ ᴛʀᴜᴇ sᴛᴏʀʏ*
*♡WAZEER¸.•💥*
(A Tᴡɪsᴛ Oғ Fᴀᴛᴇ)
BĘŹ.
*HAWWA__B__KUMO.*
(Rᴇᴀʟ Sᴍᴀꜱʜᴇʀ).💕
*WATTPAD:REAL-SMASHER.*
*AREWABOOKS:REALSMASHER.*
*TIKTOK:ASLISMASHER.*
https://www.arewabooks.com/u/realsmasher
••••••••••
*Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ.*
*It's all about:#Love one another,#Twist,#Betrayal,#Friends,#Fate,#Romance,#Hated & #Lost..*
*THRILLER..*
*BOOK 2.*
•••Cikin wani irin ƙaraji Hamood yace "Wazeer! Ok² gani nan a hanya yanzun nan" bai jira me wanda ya kira zai sake faɗa masa ba ya kalli driver ɗinsa yace "yi maza ka shiga mota ka kaini gida" yanda Hamood yayi magana yasa da sauri driver ya amsa tare da zagayawa ya shiga mota,Hamood na kallon Safwa a ƙagauce yace "i'm sorry wife wani uzurin gaggawa ya sameni zanje gida,sai mun yi waya anjima kafin lokacin dinner" Safwa da wannan karon shi ne na biyu da ta taɓa jin sunan Wazeer kuma ta gane abunda yake nufi ta gyaɗa masa kai,a hankali tace "ok!" Yana shirin rufe motar ta ɗan yi dum da sauri tace "arghm.. baka ji ba" Hamood dake cike da gaggawa ya kalleta yana karya kai kamar maraya yace "wife please.. Later za muyi magana,i'm in hurry yanzun nan" tace "ok! But magana nake so muyi dama,ko nace tambaya gare ni da nake neman amsarta" Hamood yace "idan na dawo anjima sai muyi,yanzu dai ayi min haƙuri na tafi" ta gyaɗa masa kai kaɗan tace "shi kenan" yace "alright! Bye²" tace "bye.. Ka kula min da kanka" ya gyaɗa mata kai yana ɗan murmusawa yace "thank u.." Suna barin GRA da wani irin gaggawa Hamood ke yiwa driver ɗinsa magana ya ƙara gudu²,kamar za su tashi sama gudu kawai driver da Hamood ya gigita yake,cikin abunda bai wuce mintuna 5 ba suka iso Tudun wuzirci,kafin driver ya daidaita parking tuni Hamood ya buɗe mota ya sauko tare da nufar cikin gida,yanda yake tafiya zai tabbatar maka akwai wani abu,yana isowa apartment ɗinsu ya buɗe ƙofar da ƙarfi ya shigo. Tsaiwa yayi yana kallon Wazeer daya juyo ya kalleshi,lokaci ɗaya muryarsa a karye ya furta "Son!" Tahowa Wazeer yayi zai fita,da sauri Hamood yasha gansa,yana masa wani kallo cike da damuwa yace "where have you been kwana biyun nan da suka wuce? Ina kaje daka bar gida? Mene ne na duk wannan Son?"
*
Kallonsa Wazeer ya tsaya yi kamar bai gane me yake cewa ba,Dad yace "please Son.. Let's talk" cikin jin zafinsa Wazeer ya girgiza masa kai,wani irin ɓacin rai yana bijiro masa ya buɗe baki yace "me za kace min? Me kake da shi da zan tsaya naji?" Dad yace "amma yana da kyau ka saurareni kaji bayanin da zan yi maka,abunda ya faru wasn't intentional,sam ban san kana son yarinyar nan ba,ban san komai dake faruwa tsakaninku ba,ban san ya akai haka ta faru ba,amma ka yarda da ni wallahil'aziim.." Kafin ya kai ƙarshe Wazeer yayi ƙwafa ya wuce fuuu zai fita,saurin riƙo rigarsa Dad yayi yace "wait Son.." Cikin ihu da zafin rai Wazeer yace "don't call me ur Son.. I'm not ur Son,u better find ur Son somewhere,in ni ɗanka ne da gaske baza ka min abunda kayi ba.. Hummm! Wai ur Son,ain't u ashame of urself? Wait.. Da kace min mata mugaye ne azzalumai,masu son kansu,and what about u? Mene ne bambanci tsakaninka da su?" Ihu Dad da maganganun Wazeer sukaiwa zafi kuma ya ji su a bazata yayi tare da ɗaga hannu zai mareshi yace "Wazeer enough" Wazeer dake kallonsa idanunsa da jijiyoyin kansa sunyi raɗa² yace "ka barni na faɗi abunda ke raina mana.. Ko ba gaskiya na faɗa ba? Ain't ready to hear? Ba kai ka sanar min duk wannan ba? Don kawai kana jin haushin mahaifiyata sai laifinta ya shafeni? Shin mene ne Mimi ta aikata maka? Abunda kayi mata hukunci ne ko ɗaukar fansa? U took me ka bar Nigeria for good 20 years,ka taɓa tunanin ya kamata ka kawoni na ganta? Ka taɓa tunanin bai dace ka raba uwa da ɗanta ba? Ka taɓa tunanin cewa abunda ka aikata zai iya janyo min wani ciwon? Ka taɓa tunanin sanadin da yaja na samu depression? Ka taɓa zama kaji mene ne matsalata me nake so? I have been crying through this years saboda kewar Mimi,ina kuka saboda rashin Mysha,a kullum ina kewarsu ina yin kuka,through this years babu abunda zan ɗorar bayan kewa da damuwa,idan nayi maka maganar Mimi sai ka kawo min maganar da zaisa na tsani mahaifiyata,haka na shafe shekarun yarinta bani da single friend,u stole every bit of shekarun ƙuruciyata,sam ban san daɗinsa ba,ban san ya yake ba,ba ni da kowa dake so na,babu wanda yake zama da ni,babu wanda zan yi sharing farin ciki ko damuwata da shi,why? Me nayi maka?" Cikin kaɗuwa Hamood yace "but i loved u Son.." Da sauri Wazeer dake cike taf da ƙunci yace "u never loved me Mr Hamood Waziri.. This is kind of wickedness,baka san komai ba bayan son kai,da cika buri a rayuwarka.." Dad da ya zazzaro idanunsa yace "Wazeer! Ko ka yarda ko kada kayi ni mahaifinka ina sonka,idan babu soyayya me zai sa na tsaya maka a rayuwa? Na baka ingantaccen ilimi,na baka gatan uwa da uba,na maka kaza³" Wazeer na girgiza kansa yace "duk abunda kayi min ba don kana sona kayi ba,ka yi ne saboda ka cutar da zuciyar da taso ka da amana,zuciyar da ta yarda da kai ta baka amana,zuciyar da har gobe take shirye ta karɓeka,zuciyar dake da adalci,zuciyar da bata san komai ba face alkhairi.. Why are u so selfish Mr Hamood? Me yasa baka san kowa ba sai kanka?" Wannan karon Dad couldn't help it sanda ya ɗauke fuskar Wazeer da mari ji kake tass,Wazeer da al'amarin ya zowa a bazata yayi still yana kallon Dad bakinsa ya kasa rufuwa,cikin damuwa da ɓacin rai Hamood da bai so ya mareshi ba,in fact bazai iya cewa ga abunda ya janyo ya ɗaga hannunsa ya daki ɗan nasa ba,yana nuna shi cikin dakewar zuciya yace "don't dare dare call her name a gabana,i hate that woman.. Na tsaneta da gaske.. I hate her saboda ita taja na rasa ƴata" gyaɗa kansa Wazeer ya dunga yi yana kallon Dad,lokaci ɗaya yayi murmushi me ciwo yace "u slapped me yau saboda ƙiyayyar Mimi,ko kuma saboda cewar na faɗa maka gaskiya ne?" Dad yace "i slapped u saboda kana ƙoƙarin nuna min ban isa ba" Wazeer yace "this is not the truth,kace ka mareni ne saboda ƙiyayyar da kake yiwa mahaifiyata.. Ohh wow! I'm not surprise don ka yi haka,because dama can na san baka taɓa so na ba" cikin hargagi Dad yace "take it duk yanda kaso,amma ka sani duk duniya ni ne gatanka.. Ba ka da kamarni,kuma baza ka taɓa canja haka ba,baza ka taɓa canja ni da wani ba Wazeer,u are dependant,a ƙarƙashina kake,ni ne komai naka a duniyar nan,in kuma kana jin ka isa kace ba haka bane,sai na tabbatar maka da furucin da nayi" bai gama rufe bakinsa ba Wazeer yace "i said it out loud ba haka bane" Dad dake cikin shock yace "ok! Haka kace?" Wazeer yace "sure" Dad da yakai maƙura gurin ɓacin rai yace "tunda ka amsa min da bakinka,ka ƙaryata ni,ina so yanzun nan ka tattara ka fice min daga gidana" gyaɗa kai Wazeer ya shiga yi,lokaci ɗaya fuskarsa ta cika da murmushi me cike da ƙunci yace "ka koreni daga gidanka saboda na faɗa maka gaskiya?" Hamood yace "na koreka saboda ba ka da tarbiyya,har ni zan yi magana ka mayar min ba tare da tsoro ba? Who do u think u are Wazeer? Kai yaro ne wanda na raina cikin soyayya da kulawa,amma yau da ni kake sa'insa? Ina faɗa kana bani amsa,are we mate?" Wazeer yace "u said na bar maka gidanka,right?" Hamood cikin ihu yace "ka fice ka bar min gidana,babu ni babu kai tunda ban isa da kai ba" Wazeer yace "ok! Zan tafi and dama ba zama nazo yi ba" Dad da gabansa ke dukan 💯² yace "kuma ka tattara komai da kasan ya fito daga gurina,i so mean komao dana mallaka maka ka dawo min da shi,daga yau in ka isa kaje ka nema da guminka,ka yiwa kanka komai da nake maka,shi ne zan tabbatar da abunda ka faɗa,zan tabbatar cewa ka haifu,kuma ba ni Hamood Waziri ne mahaifinka ba.. After then u can leave my house for good.." Gyaɗa kansa Wazeer ya ci gaba da yi yace "deal.. But ina so ka sani,Allah shi ne gatana,kuma gatan kowane bawa.. All this years shi ya rayani na kawo yau.. Yanda ka furta ka tsani mahaifiyata a gaban idona yau sosai² yasa ƙimarka zubewa,and maganar in na isa na dawo maka da duk wani asset daka bani i will,yau ɗin nan zan bar gidanka kamar yanda ka nema,i know ba ni da sauran amfani a gurinka,so zan ƙarasa sauke maka nauyi na tafi,zan bar cikin rayuwarka saboda na zama annoba,but ina so ka ƙaddara,daga yau kuma daga yanzu duk inda za mu haɗu,ba na so ka nuna ka taɓa sanina,ina so ka goge duk wata alaƙa dake tsakaninmu,ka fiddani daga cikin rayuwarka,ka shafe duk wata alaƙa data taɓa haɗamu,nima zan manta cewar na sanka,i'm sure zan rayu cikin yardar Allah,but ni da kai ina so kowa yabi hanyarsa,hanyar jirgi daban na mota ma haka.." Yana faɗan haka ya shiga zaro key ɗin mota da sauran abubuwan da yasan sun fito daga Dad ɗin nasa ya ajiyesu saman couch,Hamood da bai taɓa zaton abunda maganarsa zai haifar ba kenan yace "Wazeer!" Wazeer bai saurareshi ba yana gama ajiyewa ya wuce ya nufi hanyar fita yana faɗin "na barka lafiya and for good.." Yana faɗan haka ya wuce cikin sauri ya fita zuciyarsa na masa ƙuna.
*
Daga ciki Hamood da ya taso da ƙyar ya buɗe,ganin driver ɗinsa yasa shi sauke numfashi,cikin girmamawa driver yayi masa sallama ya amsa,sanda suka gaisa kafin maganarsa a hankali kuma cike da damuwa ya furta "ohh! An tashi dinner?" Driver ya amsa yace "ehh ranka ya daɗe" Hamood da bai kula da Safwa ba sam har sannan yace "but na ce fa ka dunga tafiya da key ɗin,idan an gama hidimar sai ka dawo da shi,think haka zai fi" driver yace "ehh ranka daɗe ba maganar mukullin bane,dama Hjy ce tace na rakota" cike da mamaki Hamood yace "wace Hjy?" Driver ya ɗan waiga tare da kallon Safwa,sam ya rasa wane suna zai faɗawa Hamood da zai gane,kawai yace "gata nan ai tare muke" dubansa Hamood ya kai inda yake ganin alamar tsaiwarta,Safwa ta taho tana cire niƙab ɗin da ta sa,Hamood cikin shock ɗin ganinta a lokacin da bai zata ba yace "Safwahh! Da wannan daren? Why kika zo?" Wani irin kallonsa take tun farkon tsaiwarsa,sosai taga alamar rashin lafiya a jikinsa don ko ya yi rama sosai a cikin kwanakin,bata iya cewa da shi komai ba ta taho za ta shige,hanya Hamood ya bata ta wuce ciki,lokaci ɗaya yana kallon driver ɗinsa yace "ka jira a waje za ka mayar da ita gida yanzun nan" driver ya amsa respectfully tare da juyawa,saurin mayar da ƙofa Hamood yayi ya rufe,lokaci guda ya nufo inda Safwa take tsaye.
*
Around 9am Umma da taji shiru ta sake fitowa,ranta a mugun ɓace ganin kusan 2 hours kenan da ake ta jiran Safwa amma shiru har sannan bata shigo gidan ba,gashi ƴan uwan Abba sai mita suke an barsu zaune kamar marasa abun yi,in baza'a kira musu ƴar tasu ba su san inda dare yayi musu tun wuri,fitowa tayi a fusace saboda yanda ƴan uwan Abba suke ta maganganu,sanda ta shigo gidan Mama bata parlour,kai tsaye ta wuce upstairs,ɗakin su Baniynah da tasan can suke ta buɗe ta shigo tana faɗin "wai Safwa don ubanki baki ji saƙona bane? Almost 2 hours nazo nace Babanku na kiranki,amma kin ƙi zuwa dole sai da kika ja min magana sannan hankalinki ya kwanta" wuƙi² ɗin da Radhiya dake kwance tayi ne yasa Umma yin shiru tare da binta da kallo,hankalinta a kan ɗakin da babu kowa sai su kaɗai ita da Radhiyar da kusan ta sume saboda bata taɓa zaton Umma will come har saman ba,a wani iri hankali Umma dake kallon alamun rashin gaskiya a fuskar Radhiya cewa "ina Safwan take don ubanta?" Radhiya tayi shiru ta rasa me za tace,lokaci ɗaya ran Umma ya ƙara ɓaci,tana kallon Radhiya da tayi shiru ta sunkuyar da kanta ƙasa,in a serious note tace "Radhiya tell me ina Safwa? Ki faɗa min tsakaninki da Allah kada ki ɓoye min,ni mahaifiyarta ce zan fahimta,idan kin ɓoye min kin san dai baza ki ɓoyewa Allah ba ko?" Gyaɗa kanta Radhiya tayi a hankali ta ɗago kanta,fuskarta na sauya yanayi tace "wallahil'aziim Umma sanda na hanata zuwa amma ta dage min sai ta je,ban taɓa tunanin ba a daren za ta dawo ba,shi yasa ma banje na sanar miki ba" Umma da tayi galala da baki tace "tun dare bata nan? Bata kwana gidan nan ba? Ina ta tafi? Gurin wa taje?" Umma ta jero mata tambayoyi da yawa,Radhiya ta gyaɗa kanta a saɓule tace "she said that za taje ta duba Hamood,ya sanar mata bai da lafiya tunda aka fara bikinsu and dalilin da ya hanashi zuwa all the event kenan.. Na so da ta yi haƙuri,don babu irin shawarar da ban bata ba,amma ta dage sai ta tafi.." Lokaci ɗaya hankalin Umma ya tashi ta dunga maimaita "can ta kwana gurinsa?" Radhiya ta girgiza mata kai tace "i'm not sure Umma,amma dai ni yanda muka yi da ita kenan da muka dawo gurin dinner" cikin damuwa Umma da hankalinta ya gama tashi ta furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Amma dai Safwa an yi wawuyar yarinya wallahi,yanzu ɗaukan kafa tayi tabi namiji? Meke damunta haka?" Knocking ƙofar ɗakin da aka yi yasa Umma juyawa tana faɗin "wallahi sai na saɓarwa yarinyar nan.. Don ubanki daga ina kike? Ina kika je kika kwana?"
*
Wazeer na fita gidan Hamood ya zube saman kujera tare da dafe kansa dake wani irin sarawa da juya masa,how could he zai yi irin wannan maganar da ɗansa? Me ya kaishi cewa ya bar masa gidansa? Me yasa zai tsaya suyi duk wannan jayayyar da ɗan cikinsa? A fili ya furta "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.." Ba kaɗan ba ya shiga damuwa da tashin hankali,idan da ace ya san abunda maganar da zai yi zai haifar kenan,ko tantama babu ba zai taɓa yi ba,but ya zaiyi tuntuɓen harshe ne dai ya yi,kuma ƙarshe ga abunda maganarsa ya haifar,tambayar da ya fara yiwa kansa shi ne "ina yaron nan zai tafi?" Cikin kiɗima da tashin hankali yayi saurin ɗaukan wayarsa,number Isma'il ya shiga kira,bai daɗe yana ring ba Isma'il ya ɗauka respectfully yace "assalamu alaikum ranka ya daɗe" Dad da har wani zazzaɓi ya fara saukar masa yace "Isma'il duk abunda kake ina so ka bari kabi bayan Wazeer kaga ina zai je" Isma'il ya amsa da faɗin "to ranka ya daɗe.." Hamood ya sauke wayar tare da furzar da ajiyar zuciya,addu'ah yake Allah yasa ba gurin Hooriyah Wazeer zai koma ba,tunanin haka yasa nan da nan hankalinsa ya ƙara tashi,yanda Wazeer ya furta yana son mahaifiyarsa,haka itama Hoor ya tabbatar da irin soyayyar da take masa,babban damuwa da tashin hankalinsa a yanzu bai wuce ace Wazeer ya komawa mahaifiyarsa ba,ya tabbatar muddin haka ta faru ko shakka babu dole Wazeer zai sake tsanarsa ne kawai a rayuwa.
*
Shigowarta ciki da sallama yasa Umma dake zaune tana jijjiga kai saboda al'ajabin abunda ya faru ɗago kanta ta kalleta,turus Safwa ta tsaya cikin tsoro da mamaki,Umma dake ƙare mata kallo duk da akwai niƙab a fuskarta,but muryarta da saman idanunta was abunda suka tabbatar mata zargin da take,cikin tarin takaici,kunya gami da mamaki Umma ta miƙe tana faɗin "kin dawo? Sannu da zuwa.. Ya kika baro shi? Ya jikin nasa?" Rasa me Safwa za tace da Umma tayi,duk tsiwarta da kaifin harshenta yau sai taji sun yi mata nauyi ta kasa cewa komai,Umma dake cike da haushinta tana girgiza kanta tace "tohh! Sai kizo muje Babanku na nemanki za kuyi sallama da baffaninki kafin a san meke faruwa kuma.." Kanta Safwa ta sunkuyar ƙasa,cikin ƴar kunyar data kamata lokaci ɗaya ta furta "Umma kiyi haƙuri don Allah.. Wallahi ban yi niyyar kwana ba shi ya nema,ni kawai zuwa nayi in dubasa.." Cikin ɓacin rai Umma dake jin kamar ta rufeta da duka ta hantareta "inyi haƙurin ubanki.. Ni za ki mayar yarinya? Ni za kima wannan cin fuskar Safwa? In ba don kin matsu ba,kin gaji da zaman kina Allah² ki bama namiji kanki,har ina jiya? Me akai² yau da baza ki iya haƙuri har a kaiki gidansa ba,saboda gindinki na ƙaiƙayi shi yasa kika ga bari ki ɗauki ƙafa ki bisa ko? Kuma don rashin kunya yanzu kin ɗauko ƙafa kin dawo ki nuna mana ke isasshiya ce kin san namiji?" Ina ƙasa ta buɗe Safwa ta shige don kunya,Umma cikin ɓacin rai ta ci gaba da faɗin "tunda uwata ta haifeni wallahi ban taɓa jin anyi haka ba sai a kanki,kuma bazan munafurceki ba amma wallahi kin matuƙar ɓata min rai,banda Allah yasa har yanzu bayan mu babu wanda ya san kin fita,wallahi² da tuni na aika miki da kayanki tunda kika zaɓi kaiwa mijin kanki har kuka yi abunda kuka yi.. Wace irin jaraba ce ma wannan tsakani da Allah,dukanku ace babu me iya haƙurin ganin faɗuwar rana" yanda Umma ta buɗe murya tana faɗa ne yasa Mama saurin saukowa,yanda take tsallako stairs kaɗai zaisa ka fahimci akwai abunda ya fito da ita,tana isowa cikin parlon take faɗin "haba Hjy Murja.. Me yasa za kiyi haka fisabilillah? Wannan faɗan a yanzu bai da amfani,kuma ba mafita bane garemu,tunda Allah ya sa ta dawo babu wanda ya sani ai bai dace a ɗaga maganar ba,da kin jira har a watse a taron bikin,sai kiyi mata magana daga ke sai ita,ki ganar da ita kuskurenta,amma yanzu da kika fara maganar idan wani yazo yaji fa? Kinga abunda ake gudu ne zai faru.. Ni wallahi da kin bi ta tawa ko tari baza ki mata ba,zuba mata ido kawai kika yi,za kiga yanda za ta shiga taitayinta.. Ai idoma ya ishi duk me hankali"
*
Knocking ɗin da kunnuwansa suka jiyo kamar ana yi a gidan yasa shi saurin tashi yana mamaki da tunanin "who's this? Waye zai zo gurinsa? Ya san babu wanda yasan inda yake,in fact bai yi maganar da kowa ba hatta Mimi,even though sun haɗu a AKTH da ita,to waye zai zo gurinsa shi kuwa? Wata zuciyar tace "maybe ur neighbors.." Kasancewar ciki akwai wanda suka haɗu in just 2 days ɗin da yayi da terewa a unguwar,sauka yayi daga saman katifar ya nufi ƙofa,yanda yake tafiya kawai ya isa bayyana maka duk inda jarumi yake ya kai ko ma ace ya wuce,ƙaramar ƙofa ya buɗe har sannan yana mamakin wanda ke tsaye next to his door,fuskar Hamood his Dad was abunda ya fara cin karo da shi sai Isma'il dake tsaye jikin mota yana kallonsu,cikin tarin shock,ɓacin rai,muguwar zuciya ya dunga kallon Dad ɗinsa da yake kallonsa kamar maraya,ba tare da ya iya cewa komai ba ya juya ciki da sauri tare da turo ƙofar zai rufe,da sauri Hamood dake ta kallonsa ya furta "wait Son.." A zuciye Wazeer da sunan da Dad ya kirashi ya tunzuro ya wani irin buga ƙofar,banda tuna cewar mahaifinsa ne,sannan da Isma'il da ya gani tare da shi,da babu abunda zai hana bai shutting door ɗin on his face ba,cikin gidan Dad ya buɗe get ya shigo,ɗan compound ɗin dai² wanda bazai wuce ya ɗauki 5 cars ba,duk da rashin girman gidan amma ya tsaru dai² zaman mutum me neman rufin asirin Allah,ƙofar parlour Dad ya buɗe ya shigo yana kallon komai da irin rayuwar da ɗansa ya fara as ƙasƙanci,Wazeer dake tsaye ya juya baya banda zuciya babu abunda ke tunzurasa,cikin kaushin murya ba kuma tare da ya juyo ba ya furta "what really brought you here? Me ka dawo cikin rayuwata kayi? Did u forget something?" Dad yace "Wazeer listen to me" Wazeer yace "u don't have anything to say to me da zan saurara.. We don't have any relation yet,and we promises for each other cewa babu ruwan kowa da wani,just leave my place please,i don't want you,ban nemeka ba.." Tabbas Hamood ya san haka za ta iya faruwa,but shi a yanzu duk wannan ba shi ne damuwarsa ba,tafiya da shi yake so,su koma gida su zauna tare kamar da shi ne abunda yake buri,jin shiru Dad bai ce komai ba yasa shi juyowa gaba ɗaya,idan kaga yanda idonsa ya canja launi za kayi zaton wani abu ya watsa cikinsu,cikin kumfar baki naman fuskarsa har rawa yake saboda ɓacin rai yace "hey! I said ka tafi,me ka tsaya jira?" Cikin sanyin murya Hamood na rausayar da kansa yace "Son please let's go back home.. Kazo mu tafi,zaman nan bai dace da kai ba,i made a mistake kuma na gane,ur Dad is sorry.. Sharrin shaiɗan ne da zuciya yasa nace.." Wazeer dake kallonsa daga inda yake yace "sharrin shaiɗan? Ohh wow.." Lokaci ɗaya yana kallon Dad ɗinsa da ya koma kalar tausayi yace "i'm not sure akwai wani gida da nake da bayan nan,in fact ni ban sanka ba,waye kai Malam? Mene ne relationship ɗina da kai? Me kazo nema? Waye ni a gurinka? I don't have family,ni kaɗai Allah ya halitta,i'm orphan,no one knows who am i,ni kaina ban san waye ni ba,shin mun taɓa haɗuwa ne somewhere?" Dad cikin nadama yace "please son.. Do u want ur Dad ya durƙusa maka on his knees ya baka haƙuri? Kana son ganin zubar hawayen mahaifinka? Kana so kace min baza ka koma gida ba? Why Son?" Cikin fushi Wazeer yace "capital YES.. I have nowhere to go,ni ban sanka ba,don Allah ka tafi ka barni nayi rayuwata in peace,ina buƙatar farin ciki,ina buƙatar abubuwa da yawa da na rasa,just leave me and have some peace,ba na son ganinka,ba na son ka sake shiga harkata,na ce ban sanka ba,bamu da alaƙa,sai me?" Cikin ɗaga murya Dad yace "keep that taurin kai da baƙin ranka a side kazo mu tafi gida" cikin ɓacin rai Wazeer yace "ni ba ɗanka bane da za kazo kana min ihu aka,kai da kanka ka faɗa,ain't u?" Hamood yace "na ji na faɗa wancan ranar,but yanzu na zo nace kayi haƙuri ka biyoni mu tafi gida" Wazeer yace "wane gidan? Gidanka kai da sabuwar matarka? I'm not sure if kana da space da zan iya zama" Dad yace "ok! Toh kazo mu tafi zan gina maka gida,and zan maka aure,ka nemo yarinya ko ƴar waye on this Earth,in dai wealth na magani na yi alƙawarin aura maka ita" Wazeer yayi murmushi cike da takaici yace "ko?" Dad yace "💯 percent sure Son,ka biyoni mu tafi gida,i will fulfill my words" taɓe baki Wazeer da kalaman Dad basu wani ɗaɗara da ƙasa ba yayi yace "look Mr Hamood,leave my place please tun muna mu biyu,i don't want to loose my temper.. Ba na so na maka abunda ba shi kenan ba,just leave me alone,kayi tafiyarka ka fita rayuwata da hanyata,ba na buƙatar kowa da komai naka a yanzu,idan kyauta za kayi kana da family,if it's sadaƙa akwai musakai bakin traffic jam,ni ba ni da buƙata a yanzu,i'm living my life cikin kwanciyar hankali,and thanks for your help,abunda kayi ya sa na sake sanin muhimmancin kaina da rayuwata,daga yau kada ka sake zuwa inda nake ko tunanin yin magana da ni,bazan saurareka ba.." Yana faɗan haka ya wuce stairs da sauri,Hamood da gwuiwarsa tayi sanyi yace "Son please.. Stop this childish ka ɗebo kayanka mu tafi gida,zamanka a nan bai dace ba,kai ba gamagarin yara bane,bai kamata kayi rayuwa kamar maraya ba.." Tamkar walƙiya ganin Wazeer kawai Hamood yayi ya dawo da wani irin fushi yace "waye ya mayar da ni marayan?" Hamood na girgiza kansa yace "forget this Son.. Maza je ka ɗauko kayanka mu tafi,u know babu wanda ya san baka gida,Daada da family duk suna neman ka,suna cigiyar inda kake,but ban sanar musu komai ba,kazo ku tafi ka ji,mu koma gida" Hamood ya kai hannunsa zai riƙoshi,da sauri yayi taking steps ɗinsa ya koma baya,yana naɗe hannayensa a ƙirji yayi wani murmushin takaici,a hankali yace "go back home ka sanar musu Abinda ya faru,i think ya kamata su san cewa ni ba ɗanka bane a yanzu,yana da kyau su san cewar ni ba jininsu bane,ban haɗa komai da su ba,ba ni da dangi kamarsu" Hamood yace "please Son let's bygone be bygone.. Ka manta abunda ya faru mu koma kamar da,u know bayan kai bani da kowa a duniyar nan,u are my world,my happiness,and my everything.." Wazeer yace "if i am like this a gurinka baza ka taɓa cewa na fita na bar gidanka ba Mr Hamood,and i have told u.. Zan sake repeating myself,ni da kai bamu da alaƙa ka tafi,ka bar rayuwata" rasa me Hamood zai kuma cewa yayi wanda zai sa Wazeer ya sauko,a yanda ya sanshi da kafiya,taurin kai,baƙin rai,muguwar zuciya,bai jin nan kusa zai iya lallaɓashi ya sauko,tunanin sanar da su Abba was abunda zuciyarsa ta fara masa magana don da gaske yana iya hango rikicin dake tsakaninsa da ɗan nasa,a sanin da yayi masa kuma muddin ba wani da yake ganin girma da jin kunya ne a maganar ba to fa za su kwashi tsayin lokaci ba tare da sun kai ƙarshen matsalar ha,cikin sarewa Hamood na sake ajiyar zuciya ya furta "it's ok Son.. Zan tafi,but zan dawo.." Wazeer yace "don't ever think of zan dawo cikin rayuwarka,bazan taɓa zama ƙarƙashin inuwarka ba,bazan ƙara raɓar arzikinka ba,idan da i was dependant,yanzu i'm not.. Gashin kaina nake ci,kuma zan ci gaba da rayuwa a haka" duk yanda Hamood yake jin zai iya holding maganganun Wazeer kasawa yayi,tabbas yanzu kam ya tabbatar yaron nan ya fishi taurin kai da kafiya,but ai shi ya haifeshi,dole ma ya tanƙwara shi kuma ya saurareshi,for now ya gama yanke zai bashi ɗan lokaci har ya sauko daga fushin don kansa.
*
Tuna yanda daren ya kasance yasa ta sakin murmushi,Hamood ƙarshe ne gurin iya sarrafa mace,ya iya soyayya da kalamai masu kashe mutum,ya iya ririta mace a gado yasa ta yarda da shi,ya san ta kan yanda duk gardamar da za kiyi ki sauko ki bashi haɗin kai. A fili ta furta "where have you been Husby? I'm missing you so bad.. Come home please kafin sha'awa ya cinye ni.. Wayyoo Ummata wallahi Hamood ƙarshe ne a komai,he lack nothing.. Komai nasa is perfect.. Da kin san siddabarun da ya yiwa ƴarki jiya baza ki taɓa ganin laifina ba da naje na kwana.." Tsaiwa Hanood yayi a doorway tare da zubo mata mayun idanunsa,bai taɓa zaton zai zo ya tarar da ita haka ba,in fact kawai ya taho ne amma duka yinin yau a cikin damuwa ya yi shi,and abunda idanunsa suke gani akan Safwa ya sa shi a ruɗani,even though yana tuna cewar she's virgin,but wayewarta yasa shi a tunani,shi dai ya san virginity ɗaya ne a gurin kowace mace,idan aka fasa tantanin budurcinta an fasa shi kenan ba ya taɓa dawowa,and that's abunda ya karanta kuma ya san,tambayar kansa ya fara "meke faruwa?" Lokacin aurensa da Hoor ne ya shiga dawo masa tas a rai,how daren farkonsu ya kasance,wace ce Hoor,kyawawan halaye da ɗabi'unta,sanyin halinta and everything,sanda ya tuna komai take a gurin,duk yanda ya kai da jin haushin Hoor a tsayin shekarun nan,yake gudun wani abu ya haɗa shi da ita,yake hana wani gefe na zuciyarsa yin sanyi da al'amarinta,but bai iya hana kansa tunaninta ba.
*
Kallon Safwa data maka wani ubansun shade a idonta Muniba ke yi babu ko ƙiftawa,Safwa da kamar ba ita ba saboda ƙibar da tayi ta ƙara kyau da gogewa,wayewarta ya danna fitowa fili tace "i'm so surprise Muniba.. Ban taɓa zaton cewa za ki iya son abunda ni na so ba.. Ban taɓa zaton za ki iya cin amanata ba.. Ban taɓa zaton za ki iya yarda da auren Ex-boyfriend ɗina ba.. But i was wronged.. Sai kawai naji maganar sama ta ka kamar saukar aradu" ba Muniba kawai ba,Baniynah kanta sakin baki tayi tana kallonta,cikin wani irin yanayi tana jifan Safwa da kallon tsantsar jahilci tace "Safwa! I think babu haramci in Muniy ta so Aliyu.." Safwa na sakin dariya tace "auu haba?" Baniynah data ƙule tace "dubawa za kiyi" cikin kaushin murya Safwa na kallon Muniba tace "bari kiji Muniba.. Ina so ki fita hanyar Aliyu.. Babu ke babu shi,aure tsakaninku bazai yiwu ba,ki cire tunanin cewa za ki zama matarsa,don bazan taɓa bari haka ta faru ba" Muniba da kallon Safwa kawai take tun zuwanta,tana murmusawa irin murmushin tura haushin nan tace "a matsayinki na wa kike warning ɗina? His Mom? His wife? Ko kuma wa?" Safwa tace "ni a matsayina na matar babansa kuma tsohuwar budurwarsa.. Na ce ki rabu da shi,idan ba haka ba.." Cikin fushi irin wanda babu wanda ya taɓa sanin Muniba na da shi tace "idan ba haka ba me? Safwa ba na son jahilci.. Mene ne ruwanki da zancen aurena da Aliyu? Ke wace ce ɗin Aliyu nace?" Cikin fushi Safwa tace "i'm warning u Muniba,ki rabu da Aliyu" a tsawace kamar za ta tada iskokai Muniba tace "bazan rabu da shi ba.. In kin isa ki rabani da shi mana.. Did i forced Aliyu yazo ya aureni? Na bishi na roƙeshi na haɗa shi da Allah yazo ya aureni saboda na rasa manema ne? How dare u Safwa za kizo gidanmu kice za ki min kashedi? Ke wace ce? Who do u think u are?" Yanda Muniba ke faɗa zaisa kayi zaton aljanu gareta,cikin hayaniya da borin kunya Safwa ta miƙe tana karkaɗa jiki tace "wallahi² in kika dage sai kin auri Aliyu za kiyi nadama,Aliyu belongs to no one than me,Aliyu nawa ne har gobe da jibi.. A kansa wallahi zan iya aikata komai,i mean it.. If kin ji warning ɗina,ki yiwa kanki faɗa and to stay away from my man.. Idan ba haka ba kuma zan sa ki zama abun tausayi.. Zan ajiye miki darasin da zai zama izina ga ƴan baya" shewa Muniba tayi tana kallonta tace "ohh wow! Yanzu kam na tabbatar da abunda kike son bayyanawa,wato uban bai isheki ba kike so ki haɗa da ɗa? Shin ke wace irin jahila ce Safwa? Me yasa ƙwaƙwalwarki ba ta gaya miki dai² ne? Ke wace irin dabba ce da bata iya banbance tsakanin halak da haram? A ina kika taɓa jin anyi wannan kwamacalar? A ina kika taɓa ganin an haɗa son uba da ɗa?"
'''#Turƙashi! Wannan shi ne ana zaton wuta a maƙera,sai aka ganta a masaƙa.. Me kuke zaton zai faru Habibaatiiy? Shin me Hamood ya aikata haka? Ya kori ɗansa daga gida yanzu kuma yana bibiyarsa,yin kansa ne ko kuma akwai wata a ƙasa? Shin kuna ganin Wazeer zai yarda ya dawo gida kamar yadda Hamood yake bibiyarsa? Yau nake jin sabon salo amarya ta kai kanta ga miji ba tare da ƴan rakiya ba.. Shin me Safwa take nufi ne? Me yasa ta ɗauki al'amarin Muniba cin amana? Wannan ƙulla²r duk me ya kawo ta? Me zai faru ga mutanen nan? Ya akai Wazeer ya nemo Muniba? Yaushe soyayya ta ƙullu har akazo maganar aure? Lallai in haka ne sai nace tsugunne bata ƙare ba,domin sanin yadda akayi aka haihu a ragaya,ku dai ku biyo ni muje zuwa.. Littafin Wazeer yanzu muka fara,ku da jin salon kun san daban yake,me kuke jira ne har yanzu baku shigo cikin tafiyar nan ba? The book is on 🔥 hurry up kada ayi babu ku.. Za ku samu Littafi na 1 kyauta,for Book 2 & 3 na kuɗi ne,make ur choice and pay,Regular ₦500 single posting,VIP ₦1000,SP 2K all into 0060746882-Hauwa Muhammad Usman,access bank. Then u show ur evidence of payment via ***/***.'''
🤔..'''
#Follow
#Comment
#Vote
#Share fisabilillah!
#WATTPAD:@REAL-SMASHER
#AREWABOOKS:@REALSMASHER
#TIKTOK:@ASLISMASHER
#ASLI-SMASHER.