Free chapter · Read without an account

Chapter 4

by Maman ɗan albarka ce 🥰✍️ · BAƘAR ZUCIYA!.

     *PAGE 4️⃣*

      *AL'AMEN*

   Tun lokacin da Rahamah ta cije shi, ya sawa ransa zai nuna mata kuskuren ta.
Amma kuma daya tuna amarya ce, sai ya ga bari ya bita a sannu gudun kar ta botse masa baki ɗaya.

Allah-Allah ya ke ƴan Kaduna su tafi, dan shi har ga Allah Aunty Zulai ɗin nan ta bashi haushi, ko ledar daya bata, ya bata ne wai ko zata gane nufin shi ta yi kara ta taso Rahamah.
Sai ta amsa ta rufe ƙofar, in da hakan ya bashi haushi sosai, gashi ita ma Rahamah ta ƙi bari ya ganta kwata-kwata.
Shi yasa ya je har ɗakin ya cire kunya dan ya ganta, shine suka ƙare a faɗa a ƙarshe.

Yanzu ma zaune ya ke a tafkeken farlon shi, wanda ke ainahin gidan shi wanda zasu zauna da Rahamah dake unguwar Mile 12.

Ba ƙaramin girma gidan ya ke da shi ba, dan a ƙalla yana ɗauke da part kusan biyar banda na shi, wanda shi harda bene irin me hawa biyun nan.
Shine a matsayin ɓangaren Al'amen ɗin.

Wani mutum ne kusa da kujerar da Al'amen ke zaune. Fari ne sosai mara jiki, daga kallo ɗaya zaka gane asalin bafulatani ne babu sirki.
Sanye mutumin ya ke da riga da wando na wani yadi fari, fuskar shi ɗauke da dogon gemu da saje daya cika ta.
Sai irin hirami nan baƙi daya yafa a kafaɗar sa. Idanun sa sanye da kwalli ya yi rau.

Shi kuma Al'amen sanye ya ke da jallabiya ruwan ƙasa (Brown color).

Kuɗi ne gaban Al'amen dami-dami a wata jaka,
 a hankali ya raba jikin sa da jikin kujerar ya turawa mutumin kuɗin baki ɗaya. Mutumin ya ja jakar ya fara zaro kuɗin yana dubawa.

Can ya ɗago ya kalli Al'amen yana jinjina kai, cikin murya irin ta malaman nan ƴan ƙaƙale yace "Masha Allah ai na faɗa maka, ribar wannan satin sai ta linka ribar shekara guda daka samu, gashi yanzu kaima ka shaida tun ba'a je ko'ina ba."
Ya rufe jakar ya miƙawa Al'amen.

Al'amen yana murmushin jin daɗi, ya amshi jakar yace "Wallahi nima na gani tabbas, dan in ba ƙarya nayi ba zan iya cewa, ribar nan tama linka ta shekarar data gabata."

Murmushi mutumin ya yi  tare da gyara zaman hiramin shi, ya yi gyara murya yace "To ka gani, Fatana zaka dage sosai akan aikin nan.
In har ka dage zaka ga cigaban daya zarce wannan, amma fa ina mai baka shawara da ka bi a sannu, tunda dai yanzu ne aka fara."

"Ai ba sai ka faɗa ba, in sha Allahu duk wani mataki, da sharaɗin da ka ce zan bi su kaga ga lada da addu'o'i da zan samu, ga kuma cigaban da nima zan samu."
Cewar Al'amen kenan.

Miƙewa mutumin ya yi yana ƙara gyara zaman hiramin shi, ya kalli Al'amen ɗin yace "Ni zan tafi, duk yadda za ka yi karka ƙara bari a samu matsala, a daren nan komai ya wakana.
Zuwa sati na gaba da kanka zaka zo ka tarda ni gida, ka bani labari akan cigaban da aka ƙara samu."

Yunƙurawa Al'amen ya yi, da taimakon hannun kujerar daya dafa ya miƙe. Ya kalli mutumin tare da nuna masa jakar kuɗin yace "Ka ɗibi abinda zai ishe ka, kafin ka tafi dan anan nake son cire wanda za'a kai masallacin juma'ar nan."

Tsugunnawa mutumin ya yi, ya ɗauki dami biyu yana murmushi yace "Wannan ma ya isa, sauran in ka kai masallaci sai ka shigar dasu cikin kasuwanci."

Sai da ya rakashi har bakin motar shi, suka yi sallama yaja motar ne gadi ya buɗe masa ya fita.

Cikin hanzari da ɗan gudu-gudu Al'amen ya juya ya nufi sashin nasa. Yasan yanzu baƙin sun tafi, dan sun yi waya da Habu direba, yace sun shirya ɗazu dan dama shi tuni ya riga daya sallame su. Ya bawa Hajiyar sa dubu goma-goma yace a bawa baƙi da zasu tafi su sha ruwa a hanya.
Kuma ya bawa Habu kuɗi har dubu talatin ya sai musu abinci a hanyar su ta komawa.
Yana da tabbacin zasu ji daɗin kyautar nan, har ma su ƙara ganin mutumcin sa.

Yana shiga farlon, kai tsaye saman bene ya nufa, yana haurawa ya tura ƙofar ɗakin dake farko dan dama ƙofa biyu ce a saman.
Wani haɗaɗɗen farlo ne ya bayyana, ya fara takawa cikin hanzari ya nufi bedroom. 
Wasu irin haɗaɗɗun kayan gado ne a ciki, masu shegiyar tsada daga gani ba ƴan nan bane na waje ne.
Kan tamfatsetsen gadon ya nufa, ya ɗauki wayar shi da wasu makullaye.
Har ya juya zai fita a ɗakin, ya tuna wani abu da sauri ya koma ya nufi wata loka, yana buɗewa ya ɗauko wata leda baƙa dake ƙulle. Ya zura ta a aljihun sa, sannan ya jawo ƙofar ya fita ya nufi ƙasa. Kai tsaye daya fito wata haɗaɗɗiyar mota ya shiga ya jata da nufin barin gidan.

A bakin get me gadi na hango shi, ya miƙe a guje ya buɗe ƙofar yana ɗaga masa hannu cikin kirari yana faɗin "Sai Jagaba Jagaban mu maganin kukan mu, na gaida uban gidana maganin kukana, Barka da fitowa Jagaban talakawa."

Yana zuwa daidai inda me gadin ya ke, a hankali ya zuge glas ɗin motar, yana sakin murmushin jin daɗi ya leƙo da kanshi yace "A'a Malam Iliya Barka da safiya, fatan ka tashi lafiya."

Da sauri mai gadin ya ƙara matsawa kusa da motar, yana wani irin washe baki yace "Lafiya lau Jagaban mu, ya kwanan amaryar da baƙi."

Amsa masa ta yi da "Lafiya lau." Yasa hannu a aljihun jallabiyar shi, ya ciro kuɗi ya irga dubu uku ya miƙawa malam Iliya yace "Gashi ayi cefane ko."
Da sauri malam Iliya ya amsa yana mai jin daɗi a ransa, ya shiga rattaba godiya da fatan alkhairi.

Cikin jin daɗi Al'amen yaja motar ya fita a gidan, iya wannan ya ishe shi farin ciki, yaga ana nuna masa shi mutumin kirki ne, babu abinda ke bashi nishad'i bayan haka.

Kai tsaye Family hause ya nufa, idanunun shi cike da mararin ganin Rahamah, yana hasasowa kan shi yadda zai ganta yana son wannan tsiwar tata, ba ƙaramin kyau take masa ba in tana yi, ga wani irin ƙamshi na musamman da ya ji yana tashi a jikin ta a Jiya da ya rungume ta. So ya ke ya ƙara shaƙar k'amshin, tunda ya ke bai taɓa jin turare me daɗi da kwantar da zuciya ba irin wanda ta yi amfani da shi.

Yana cikin tuƙin wayar shi ta shiga ƙara, ganin sunan dake yawo a jikin fuskar wayar, ya ja tsaki tare da katse kiran ya cigaba da tuƙin. A ransa yana jin, a yanzu ko kira nawa number za tayi ba zai ɗauka ba, dan baya buƙatar abinda zai ruguza masa wannan farin cikin nashi.

*****
     
   *RAHAMAH*

Tunda na kulle ƙofar farlon, na nufi bedroom ɗina na shiga shima na kulle shi ina sauke ajiyar zuciya. 
Sai da naji hankalina ya ɗan kwanta, sannan na nufi toilet da nufin nayi wanka. Ina fitowa wanka na duba cikin kayana na ɗauki doguwar rigar abaya baƙa, bayan na gama shafe-shafe na na saka rigar, ɗankwalin abayar na ɗaura a kaina nabi lafiyar gado dan Ni kaina nasan jikina na buƙatar hutu.

Cikin barcin da nake, kamar a mafarki naji ana bugun ƙofar sama-sama.
Tsaki naja na maida kaina na kwantar, ina faɗin "Duk nacin ka duk maitar ka zaka gaji da bugu ka tafi, dan ni ba mahaukaciya bace da zan buɗe maka ƙofa."

Ba'a daina bugun ƙofar ba, babu jimawa kuma wayata ta fara ringing.
A hankali na jawo ta dan duba wake kiran. Ganin sunan Aunty Fati na ɗauki kiran cikin Muryar barci nace "Aunty Fati."

Daga can taja tsaki tace "Wai ba za ki zo ki buɗe ƙofar ba, ina ta faman bugun ƙofa kin barni a tsaye."

Zabura nayi na tashi ina mutstsuka idona, na lalubi ɗankwalin da tuni ya kunce ya yi nashi wajen na ɗaura. Na sauka a gadon na nufi Ƙofa na fita.

Ina buɗe kofar farlon, naga Aunty Fati tsaye sanye Cikin hijabi har ƙasa, hannun ta riƙe da basket ɗin abinci sai gefen ta Kamal yaranta na biyu hannun sa riƙe da wata leda.

Yana ganina ya yo kaina cikin murna tare da ɗane jikina, yana faɗin "Aunty Rahamahtah."
Nima ɗaukar shi nayi duk da babu laifi yana da nauyi, dan a ƙalla zai kai shekara bakwai ga shi kuma yana da ɗan jiki kaɗan. Cikin murrmushi nace "Kamal ɗina ya kake ina Islam?."

Kokawar sauka ya shiga yi yana faɗin "Aunty Islam na gida, wai ita ba zata biyo mu ba tayi fushi tunda Mami bata kaita Kaduna ba."

Jan hannun shi nayi muka nufi ciki ina faɗin "Ka ƙyale Islam, zamu gauraya ne ba bata da kirki, yarinya sai zuciya kamar tsohuwar kuturwa."

Aunty Fati dake biye damu a baya, ta aje kwandon hannun ta tace "Ai ni na fahimci ma baki ganni ba Rahamah, wato ta ɗan ki kike kenan."

Juyowa nayi na kalle ta, dai-dai lokacin dana ɗora Kamal a kujerar farlon nace "Ki yi haƙuri Aunty Fati, ina kwana."

Sai da ta cire hijabin jikinta ta zauna sannan tace "Lafiya lau, ya kwanan me gidan da kewar ƴan tafiya."

"Lafiya lau Aunty, kamar kin san har na fara kewar su Aunty Zulai."

"Ai dole ki yi, yanzu na kira suka ce min sun yi nisa da tafiya."
Cewar Aunty Fati kenan.

"Allah ya sauke su lafiya." Nace hakan tare da komawa kujerar kusa da ita, muka shiga firar zumunci.
Ta janyo basket ɗin da ta zo da shi, ta firfito min da abincin data kawo min, Indome ce ta mata dahuwar ruwa-ruwa dan tasan cima ta kenan, taji kayan haɗi sosai sai tashin ƙamshi take.
Sai ɗayar da ta soya dankalin turawa ba tare da tasa ƙwai ba,sai stew da tayi daban wadda taji  hanta, sai damamen kunun tsamiya wanda yaji kayan ƙamshi.
Duk cima ta ce ta sani, amma yanzu iya indomen nake da buƙata, sai kunun dana sha kaɗan.

Muna cikin hira na tuna ban rufe ƙofa ba, na tashi da sauri na nufi Ƙofar zan rufe.
Sai naga wata mata na ƙoƙarin shigowa, hannun ta riƙe da kuloli guda biyu. 

Ta kalle ni tare da sakar min murrmushi tace "Amarya kin tashi lafiya, ya kwanan baƙunta."

Da "Lafiya" na amsa tare da miƙa mata hannu dan amsar kayan hannun ta, dan a ƙalla zata iya kaiwa sa'ar Aunty Zulai a shekaru.

Cewa tayi na barshi, na matsa ta shiga farlon.
Bayan sun gaisa da Aunty fati ta juya ta tafi.
Bayan tafiyar ta ina ƙoƙarin rufe ƙofa Aunty Fati tace karna rufe, bansan  wanda zai zo ba, in barta a buɗe tunda gidan ba mu kaɗai bane.

Badan naso ba na bar ƙofar a buɗe, dan bana so ta fahimci akwai matsala ne kawai, da rufe ƙofar zan yi kawai.

Muna cikin fira sai ga Al'amen ya turo ƙofar, da sallama ɗauke a bakin sa ya shigo, hannun sa riƙe da wata baƙar jaka.
Bayan sun gaisa da Aunty Fati, ya nufi bedroom ɗina kai tsaye.

Ganin ina zaune ban motsa ba, yasa Aunty Fati ta galla min harara tace "Ke dai kam Rahamah baki da wayo, kina kallon mijin ki ya dawo, babu sannu da zuwa babu amsar kayan hannun shi ki kai masa ɗaki, ya shiga ɗakin ma madadin ki bishi kin ƙara gyara zaman ki."

Ɗan turo baki gaba nayi, cikin narke murya nace "Aunty ba sai na bishi bafa, kuma zan masa sannu da zuwa gani nayi fa kina nan, kawai sai na tashi na wani amshi kayan hannun sa na shiga ɗaki dan rashin kunya."

Tsaki taja tace "Ki ji min munafuncin banza.Ni dake wa zai ji kunyar wani, ina ce in Kika zo gidana kina zaune nake tashi, na tarbi Abban Islam na kuma shige ɗakin wani lokacin ma bana fitowa sai ya yi wanka. Shine ke zaki faɗa min wani kunya ki ke j..."

Maganar tace ta katse, sakamakon jin Muryar Al'amen da muka yi yana kiran sunana "Rahamah Rahamah, kina ina ne?."

Dukan mu muka ɗaga kai tare muka kalli ƙofar bedroom ɗina, Al'amen ne tsaye ya zuro kanshi bakin ƙofar yana kirana.

Ƙasa-ƙasa Aunty Fati tayi da Muryar ta tace "Ai sai ki tashi ki je, daga nan in za ki tafi ki kai masa abincin nan, tunda nasan ba cinyewa za ki yi ba."

Cikin jin haushi na tashi na nufi basket ɗin na ɗauka, ina gunguni ina komai na nufi bedroom ɗin.
Yana ganin na taho ya koma ciki, ya zauna bakin gadon yana wani washe baki. 
Ban yarda na shiga ɗakin baki ɗaya ba, na coge a bakin ƙofa tare da ajiye basket ɗin hannuna, cikin turo baki murya a cunkushe nace "Ga abinci nan in zaka ci." Na juya da zummar barin ɗakin.

Muryar shi ce ta dakatar dani, cikin mamaki na juyo ina kallon shi.

 "Rahamahtah dan Allah kar ki tafi yanzu,ki dawo ki ɗan zauna karki sa Aunty Fati ta zargi wani abu. Wallahi ban yi niyar yi miki komai ba, babu abinda zan miki Allah kin ji ma na rantse."

Ba dan ya ce baya son Aunty Fati ta zargi wani abu ba, wallahi ba zan dawo ba. Dan dai kawai nima bana son tasan akwai matsalar ne, dan in akwai abinda na tsana shine ace wata matsala ta ɓullo daga ɓangarena.
Nafi son komai mu yi shi tsakanin mu, in yaso in yaji gashi da kanshi zai fita harkata kowa ya yi harkar shi.

Ban yarda na zauna can ciki ba, daga kan kujerar madubi dake bakin ƙofa na zauna, ya kalle ni cikin tausasa murya yace "Dan Allah ki saki ranki Rahamahtah, ki zuba min abincin naci yau hanci komai ba."

Ina kumbura baki ina komai, na zuba masa soyayyen dankalin da miya, ba tare dana tambaye shi ba na zuba masa kunun cike da wani ƙaton kofi.

Saukowa ya yi daga gadon, fuskar shi ɗauke da murrmushi yana faɗin "Kai amma Nagode, amma kin san bana shan kunun tsamiya dan dai kawai daga hannun ki ya fito shi yasa zan sha."
Ya ƙarasa maganar tare da zama Ƙasan carpet ɗin dake malale a ɗakin, ya wani irin bajewa yana nishi da ƙyar. 
Dana kalle shi sai da dariya ta kusa kama ni, dan zaman da ya yi sai ya zamana tumbin nasa shima ya zauna abin shi daban, kowa na har kar shi kenan.

Harara na galla masa na ɗauke kaina, ba tare da ya ganni ba ya shiga danna ƙatuwar loma.
Dankalin ma, in ba gizo idanuna suka min ba, kusan uku-uku ya dinga haɗawa yana turawa a ƙaton bakin sa.

Abin mamaki wanda yace baya shan kunun tsamiya, sai gashi ya zuƙe kunun tas, harda su lashe baki yana faɗin "Wallahi kuma kinga wannan da daɗi, ai nayi zaton irin kunun nan ne mara daɗi da zaki ji tsami kawai, gashi wannan harda ƙamshin su citta ya ke yi."
Ya ɗago ya kalle ni yace "Ke kika dama mana hala?"

Haushi da takaici da suka kama ni, yasa ban bashi amsa ba na share shi, nayi kamar ban ji abinda yace ba.

Shi kanshi yasan na ji nayi banza da shi, dan haka ya jinjina kai a ranshi yana cewa _Zan lallaɓa ki har na cimma burina, yarinya sai iskanci kala-kala dan kinga kina da kyau, kuma ina lallaɓa ki._

Yana gama ci na tattara kwanukan na fita. Aunty Fati na ganina ta shiga murmushi, tana ta yabona wai ko Ni fa, yanzu da naje ba yafi ba, ai da ita zai wa kallon babbar banza.

Ni dai bance komai ba na koma na zauna, muka cigaba da firar mu.
Babu jimawa sai ga Al'amen ya fito, yana wata tafiya kamar bijimin sa. Haushi yasa na ɗauke kaina, ina addu'ar Allah yasa kar Aunty Fati ta kalle shi, dan sai naga kamar abincin da yaci yasa tumbin nasa ƙara bayyana.

Sai naga ashe ma tuni kallon shi take, a ranta tana faɗin _Ikon Allah. Ashe dai da suke wa Al'amen kallon me tumbi, dan basu ganshi kusa bane shi yasa. Sai yanzu ta lura da uban tumbin nasa kamar rumbu, ita kanta sai da tace Allah ya bawa Rahamah lafiya._

Sallama ya mana, akan zai je ya duba wani aiki da ya bada a masa, na ginin masallaci, daga nan zai je shagon shi sai ya dawo.

Aunty Fati ce ta bishi da addu'a.

Bayan tafiyar shi wuni guda muna tare da Aunty Fati, sai bayan la'asar ta tafi. 
Gidan ya rage sauran Ni kaɗai, tunda nasan ba girki zan yi ba, sai kawai na shige ɗaki na ƙara kwanciya.

Da Magriba sai ga aiken abinci, wai in ji Hajiyar Al'amen. Dana buɗe da sauri na rufe, dan bana shiri da amala kwata-kwata a rayuwata.
Ita ce cike da kula a mulmule a leda, sai miyar ayayo da d'anyar kuɓewa da stew wadda aka zuba mata ganda da namomi manya-manya.
Miyar ce kaɗai ta burgeni, sanin ba ci zanyi ba, sai kawai na ajiye a farlo na koma ɗaki.

Tunda nasan na rufe ƙofar farlon, kai tsaye bayan nayi sallar isha'i na yi shirin barci cikin shigar doguwar riga har gwiwa, na sa hular net na bi jikina da turaren humra me ƙamshi na shafe, koda ina gida na riga dana saba in zan yi barci sai na shafa humra dan akwai ni da san ƙamshi.

Can cikin barci naji kamar motsin mutum ya shigo ɗakin, cikin tsananin tsoro na tashi ina raba ido cikin duhu, na shiga laluben makunnar fitilar ɗakin dake jikin gado.

Da ƙyar na kunna ɗakin ya gauraye da haske baki ɗaya, Al'amen na gani tsaye cikin shigar manyan kaya, hannun sa riƙe da ledoji.

Muna haɗa ido ya wani washe min baki, yana bin jikina da kallo kamar tsohon maye.
Lura da abinda ya ke kallo, da sauri na jawo bargo na lullu'be ƙirjina, zuciyata na wani irin bugawa, ina tambayar kaina _Ta ina ya shigo bayan nasan na kulle ƙofar?._

Ban gama tunani ba naji Muryar shi "Har kin fara barci kenan My Babynah,  to ki tashi ki sakko tafa samu, dan kaji ne waɗanda suka linka na rannan a girma, sannan na haɗo miki da lemuka masu sanyi dan ki ji daɗin cin su."

Duk da irin tsoro da fargabar da nake ciki, hakan bai hana ni galla masa harara ba, ina jin takaicin maganar shi _Wai na tashi naci kaji sai kace ance masa mayya ce ni, dan tsabar rainin wayo irin nashi harda wai sun fi na rannan, ko an faɗa masa naci wancan ne bare wannan._

Maida kaina nayi gefe nace "Bana ci. Dan Allah na roƙe ka ka fita a ɗakin nan, in ka fita ka ja min ƙofar."

Dariya ya yi ya nufo bakin gadon, yana faɗin "Wanne irin na fita daga ɗakin ki, bayan ni ɗin mijin ki ne kuma sabon ango a daren nan."

Yana nufo gadon ina ja baya, ganin haka yasa ya fashe da dariya yace "Au Wai gudu ki ke? Ki kwantar da hankalin ki, komai a sannu nake so mu yi shi, bana son wannan tsoron da ki ke nunawa dan Allah."

Ganin bai hau gadon ba, ya tsaya ya aje ledar hannun sane, hakan yasa na sauke ajiyar zuciya ina ƙara ƙanƙame bargon dake jikina.

*****

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.