Free chapter · Read without an account
Chapter 5
PAGE 5️⃣*
Yana aje ledar, naga ya fara cire babbar rigar jikin sa. Da sauri na ɗauke kaina ganin yana ƙoƙarin cire rigar jikin sa.
Aiko ina juyowa nayi mugun gani, dan ya cire rigar daga shi sai dogon wando, da singlet, tumbin ya ƙara zazzagowa ƙasa.
Zama ya yi dirshan a ƙasan carpet ɗin, ya jawo ledojin daya shigo dasu ya fara fito da kayan ciki.
Ɗauke kaina nayi, gaba ɗaya zuciyata ta kasa nutsuwa, Ni kaɗai nasan fargabar da nake ciki akan zaman shi a ɗakina.
Har hararo halin da zan shiga nake, in na shiga hannun wannan azzalumin, daga ganin shi ba tausayi zai yi ba bare ayi maganar sassauci.
"Ki sakko ki ci fa, dan babu abinda ya dame ni, rashin cin da za ki yi ba zai hanani abinda zan yi ba."
Maganar shi ta sa na juyo, addu'o'i na fara ja a zuciyata kawai.
Ina neman tsari da wannan mutumin.
Sai dai addu'a ta bata amso ba, zama ya yi ya dinga haƙar naman kamar wanda bai taɓa cin nama ba, yana gama ci ya kora da madara me sanyin, tare da sakin gyatsa me ƙarfi babu Alhamdulillahi babu komai ya tashi tiɓi-tiɓi ya nufo gadon. Wani uban tsalle na buga da nufin sauka, sai dai na makaro tuni ya kakkane bakin gadon babu hanyar gudu.
Ina ji ina gani ya tarda ni, duk irin kiciniya da tirje-tirje nake da su cizo da yaƙushi a banza.
Yadda kuka san dutse, haka mutumin nan ya koma kamar wani mahaukacin kare ko kurma.
Kwata-kwata duk abinda nake bai san ina yi ba, dan gaba ɗaya kamar ba'a a hayyacin sa ya ke ba. Ina ji ina gani ya rabani da kayan jikina ba tare da tausayi ko imani ba ya fara ƙoƙarin cimma burin shi.
Tun ina kuka da ihu har sai da ƙarfina ya ƙare. Ban ƙara sanin inda kaina ya ke ba, sai da sanyin asuba ya buge ni na buɗe idona a hankali na sauke su akan fankar saman dake wulwulawa. Kaina naji ya wani irin sarawa kamar zai rabe biyu, a hankali na yunƙura da niyar tashi.
Wata irin azaba da raɗaɗi da naji yasa na koma na kwanta ba shiri, tare da fashewa da wani marayan kuka da duk wanda ya ji sai na bashi tausayi.
Uban munsharin da naji an fara saki, yasa na juya gefena a hankali.
Da sauri na runtse idanuna ina jin wata irin tsanar shi ƙyama takaici baƙin ciki, duk suka kama ni a lokaci guda.
Kwance ya ke babu komai a jikin shi, ya wani irin bajewa yana barci da sakin munshari, abin babu kyan gani.
Duk kuma kukan da nake bai ma san ina yi ba, dan da alama yana da nauyin barci.
Na daɗe ina kuka wai ko zai farka ya taimaka min, saboda a kunne na aka sallame sallar asuba, burina na samu na shiga toilet na yi wanka na gasa jikina na yi sallah.
Sai dai ina bai san ina yi ba, ganin haske ya fara shigowa ta window alamar gari ya fara wayewa, dole na fara jan jiki duk da irin raɗaɗin da nake ji na sauka gadon.
A zuciyata Allah ya isa kawai nake jerawa wannan azzalumin.
A haka da jan jiki na kai kaina toilet ɗin, cikin dubara na tara ruwan zafi a kwamin wankan, na surka shi kaɗan.
Da ƙyar na zauna saboda zafin ruwan, amma bani da wata mafita bayan hakan, hakane zai sa naji dama-dama.
Sau uku ina canja ruwa, sai sannan naji dama-dama har na iya miƙewa tsaye.
Alwala na ɗauro ina tafiya a hankali na fito, cikin dubara nake komai har na zura doguwar riga, na sa hijabi na tada Sallah. Na daɗe zaune ina kai kukana wajen Allah, akan Allah ya zaɓa min abinda ya fi zama alkhairi a rayuwata.
Can naji motsi na juya na kalli gadon, shi na gani ya farka ya tashi zaune, kuma har lokacin bai suturta jikin shi ba, ko kunya ba ya ji shi gashi ba kaɗan ba.
Kauda kaina nayi na cigaba da azkhar ɗina, dan bai ganni ba da alama barcin bai gama sakin shi ba.
Ji nayi ya buga wani irin ihu, yana nuna ni.
Cikin tsoro na kalle shi, da sauri na ƙara kauda kaina ina kallon gefena ko yaga wani abin tsoro ne, dan har lokacin ba komai a jikin shi yana tsaye bakin gado.
"Baki da hankali baki jira ni ba ki ke sallah?."
Ya faɗi hakan yana nufo inda nake.
Cikin mamaki nake kallon shi, wanne irin in jira shi in zan yi sallah? Sai kace shi zan wa sallar.
Jin da nayi ya fincike dardumar da nake kai, har sai da nayi baya na faɗi, cikin jin zafi nace "Wash me na maka?."
Rufe ido ya yi ya fara faɗa "Ya za ki yi sallah ba tare da izinina ba, gashi yanzu kin ɓata min komai kin ɓata min aiki, wayyo Allah na wannan yarinyar baki da hankali wallahi."
Yana gama faɗin hakan ya wuce ni tiɓi-tiɓi ya ɗauki wayar shi dake gefen gado.
Sakin baki da hanci nayi ina kallon ikon Allah, wanne irin sai na jira shi zan yi sallah? Ban gama tunani ba naji ya danna kiran waya.
Cikin tashin hankalin dake shinfiɗe a fuskar shi ƙarara yace
"Hello Malam Barka da safiya." Jim kaɗan naji yace "Ina fa lafiya yarinyar nan ta ɓata mana aiki baki ɗaya."
Bansan me wancan yace ba naji yace "Kasan nauyin barcina fa Malam, to Wallahi sai farkawa nayi na ganta zaune har ta gama sallah, ta cuce ni wallahi."
Gaba ɗaya ban fahimci abinda yake nufi ba, kaina duka ya ɗaure, ina mamakin duk akan sallar da nayi ya shiga tashin hankali haka? Ko kuwa wani abin na masa daban da ya tashi hankalin sa?.
Da sauri naga ya aje wayar, ya juyo ya kalle ni a wani irin fusace ya yi ƙwafa ya nufi toilet a yadda ya ke bai ɗaura komai ba, ya banko ƙofar.
Na daɗe zaune yadda kuka san wadda aka dasa a wajen, gaba ɗaya ban san dame zan kira abinda ya faru yanzu ba.
Har ya fito toilet ɗin ɗaure da towel a ƙugun shi, jikin sa sai maiƙo ya ke kamar ba wanka ya yi ba watsa ruwa ya yi.
Haka ya nufi kan gado, cikin mamaki naga ya ɗauki kayan da ya cire jiya ya saka ba tare da ya goge jikin sa ba.
Yana sawa ya ɗauki dardumar da ya yi cilli da ita, ya shimfiɗa cikin mamaki nake kallon shi ganin ba gabas ya kalla ba kuma ya tada Sallah.
Sai da ya yi raka'a biyu, ya daɗe bai ɗago ba.
Ba tare da sallama ba naga ya jawo wani dogon carbi ya fara ja.
In ba ƙarya nayi ba, ya fi awa yana zaune, dan ƙarshe tashi nayi na koma kan gado saboda yadda jikina ke amsawa, ga wani irin zazzaɓi da ke son rufe ni.
Duk da kuwa tarin yunwar da nake ji, amma nafi buƙatar hutu akan abincin.
Gani nayi ya ƙara tashi ya juya dardumar gabas, ya tada Sallah normal kamar yadda ake yi, ya yi sallama ya zauna cikin mamaki naga harda Alqur'ani ya ɗauka, tiryan-tiryan naji ya fara karatun Alqur'ani, babu ɓata ko gyara yana fitar da kowanne harafi dai-dai, sai dai salon karatun nashi Irin na yarabawa ne, yana yi ne kamar waƙa-waƙa.
Rasa wanne matsayi ya kamata na aje shi nayi, to ita waccan sallar da ya yi ya sunan ta? da uban carbin da ya dinga ja duk da ban san abinda ya ke cewa ba. Dan bakin sa ne kaɗai ya ke motsi.
Yana gama karatu ya ɗaga hannu ya yi addu'a ya shafa, ya tashi ya naɗe dardumar ya maida ta wajen ta.
Ganin ya nufo gadon nayi saurin runtse idanuna kamar mai barci.
Zama ya yi a gefen gadon, ya yi murrmushi me sauti tamkar bashi ba yace "Dama kin daina wahalar da kanki kin tashi, ba wani abu zan miki ba buƙatar hakan bata taso ba."
Ya ɗan ja bargon dana rufe rabin ƙafata dashi.
Da sauri na zabura na tashi ina zare ido. Ya kalle ni tare da fashewa da dariya abin takaici, ya shiga nuna ni yana faɗin "Matsoraciya wato yanzu kin banbance aya da tsakuwa kenan? Ni kinga fita zan yi, kuma ba daɗewa zan yi ba dan haka in akwai abinda ki ke son ci ki faɗa min, sai na taho miki dashi dan nasan ba iya shiga kitchen za ki yi ba.
Kuma ki kasance cikin shiri dan muna da babban baƙo yau a gidannan, bana son ki yi wani abu da zai ɓata min rai ko ki ja min wata asarar kin ji na faɗa miki."
Gaba ɗaya ban fahimci zan cen saba, sakamakon yadda ya yi maganar ta yadda ba zan fahimta ɗin ba.
Dan ni ban fahimci asarar da ya ke nufi na ja masa ba, bare har na ƙara yanzu.
Dan haka na ja tsaki cike da tsiwa nace " Kai ka jiyo mugu azzalumi kawai, kuma abinci bana ci ka barni yunwar ta min abinda zata min."
Cikin fusata ya kawo hannu kamar zai dake ni, ko me ya tuna sai ya dunƙule hannun tare da cije baki cikin kakkausar murya yace "Daraja ɗaya ki ka ci, ke ɗin baƙuwa ce bayan haka jiya da daddare kin bani nishad'i duk da ba yadda na saba samu bane, amma sa'ar ki ɗaya na same ki da mutumcin ki. Da sannu za ki san ko ni waye, watarana ko an baki kuɗi akan ki min rashin kunya ba za ki min ba."
Yana gama faɗin haka ya miƙe, fuska a ɗaure ya fita daga ɗakin tare da bugo ƙofar.
Tsaki naja nabi bayan shi da harara, na maida kaina na kwantar ina jin tsanar shi na ƙara samun wajen zama a zuciyata.
****
Barci ne ya ɗauke ni mai nauyin gaske. Wata azababbiyar yunwa ce ta tashe ni yadda kuka san babu ƴaƴan hanji a ciki na. Da ƙyar na yunƙura na tashi ina jin ciwo a jikina har lokacin, na sauka gadon da dubara na nufi toilet, fitsari na yi na wanke fuskata na fito ina tafiya a hankali jikina duk ciwo ya ke min.
Farlo na fita, a buɗe na tarda ƙofar farlon naja tsaki na je na rufe.
Sai lokacin hankalina ya kai wajen Dining table sai naga kulolin abinci har biyu, sakamakon yunwar da nake ji sai naji wani daɗi a raina.
Ina buɗewa naga shinkafa ce fara, sai wake dafaffe ɗaya ƙaramar kular miya ce da ganda da kifi.
A zuciya nake faɗin
_Da sanyin safiyar nan aka dafa shinkafa_
Sai da na kalli agogo naga har ɗaya ta gota, ashe barci nasha haka ban sani ba.
Kitchen na shiga na ɗauki filet, na zuba shinkafar na sa iya kifin dan ganda bata wani dame Ni ba.
Ba dan daɗi ba naci abincin, dan miyar bata min yadda nake so ba.
Bayan na gama na wuce ɗaki, sai da na ƙara wanka na gasa jikina sosai na ɗaura alwala na fito. Sallah nayi na ɗan tattara ɗakin zuwa farlon.
Ban damu da wata kwalliya ba, dan banga abinda zan wa kwalliya ba duk da irin son gayuna kuwa.
Iya riga da sket na atamfa nasa abuna, ko ɗaurin ɗan kwallin ban wani tsaya ba kaina wahala ba haka na coke shi.
Wayata na ɗauko na dawo farlo na zauna, sai na tarda miss call da yawa, harda na su Aunty Zulai da Abbanmu sai Mama Hajara ita ma kira biyu na gani nata.
Wata irin kunya na ji ta kamani, ban kyauta ba tunda su Aunty Zulai suka tafi da na kira sau ɗaya suka ce suna ilori ban ƙara kira ba.
Haka su Abbanmu tunda aka kawo ni, ban kira kowa ba, to ina naga kwanciyar hankali ma.
Kiran Abbanmu na fara yi, na gaida shi cike da ladabi. Ya amsa min yana faɗin "Babu kiran gida Rahamah, ko baki ji kewar mu ba?."
Idanuna ne naji sun ciki da ƙwalla, murya na rawa nace "Ka yi haƙuri Abba, fatan duk kuna lafiya yasu Amminmu da Mama Hajara, da su Yakubu da Ummi da Aminatu."
Amsa min ya yi kowa lafiya, nan ya shiga yi min nasiha akan zaman aure. Cikin mamaki sai naji yace "Al'amen ya kira ni yau, yana ta jera godiya, har ya turawa Baba Usman kuɗi har dubu ɗari uku wai a rabawa duka dangin mu, ya yaba da tarbiyyar ki da hankalin ki. Rahamah dan Allah na roƙe ki ki riƙe mijin ki hannu bibbiyu, daga gani mutumin kirki ne, kuɗin shi bai taɓa burge ni ba Rahamah, karki zauna da shi dan dukiyar shi ki zauna da shi dan Allah.
In sha Allahu ba za ki yi nadamar auren shi ba."
Ni dai sauraren Abba kawai, a zuciyata ina faɗin _Abba baku san wa kuka aura min bane._
Nan ya gama min nasiha, ya ƙara da ban haƙuri da lallashi akan zaman kaɗaici ya kuma ce baya son ya ji ance ga matsala daga ɓangarena.
Ina sallama da Abba nabi sauran kiran, nasha ƙorafi wajen Aunty Zulai akan ban kira ba.
Na dai bata haƙuri wannan ta wuce, na kira su Amminmu da ƙannena muka gaisa.
Ana kiran la'asar Islam ɗin Aunty Fati ta shigo, bayan ta gaida ni ta bani abincin da Aunty Fati ta aiko ta kawo min.
Da ya ke bata wani sakewa dani, bata jima ba ta tafi abinta.
Kaiwa kitchen nayi ina jin daɗi, na huta da cin abincin waɗan can mutanen.
Wajajen magriba sai ga sallamar Al'amen, cikin mamaki nake kallon bayan shi ganin shi tare da wani mutumi sun shigo farlon kai tsaye ba tare da neman izini ba.
A rikice na fara neman ɗankwalina na ɗaura, na haɗe rai sosai ganin mutumin ya zauna a kujerar dake fuskantar tawa, ya wani zuba min ido dake cike da kwalli kamar tsohon boka, ga wani uban carbi fari sai faman ja ya ke yana mui-mui da baki.
Kujerar da nake kai Al'amen ya zauna.
Ya wani ɗora min jabgegen hannun sa a kafaɗa, ya matso da fuskar shi saitin tawa yana wani lumshe ido shi a lallai sai ya nuna min love.
A takure nake sosai, dan kusan rabin cinyar shi akan tawa take. Dan kujerar me biyu ce shi kaɗai ma ya isa ya cinye ta. Kauda kaina nake ta faman yi, dan in ba ƙarya hanci na ya min ba kamar ina jiyo wari-wari na tashi a hammatar shi.
Ga ya kawo bakin sa dai-dai fuskata yana magana, sai feshin yawu ya ke min, iskar dake fita a bakin sa kanta na min wani irin wari wari.
Gaba ɗaya zaman wajen a takure nake.
Gyaran murya mutumin ya yi yana wani ƙasa-ƙasa da ido yace "Jagaba a ɗan rage haka mana, bari mu gama magana in ya so in na tafi ayi soyayyar ko."
Ya ƙarasa maganar cikin ƴar ƙaramar dariya.
Washe baki Al'amen ya yi, babu zato naji ya yi kin kiss gefen kumatuna ya sake ni yana gyara zaman shi yace "Ai yarinyar ce Malam ke sa na rasa nutsuwata."
Dariya ya yi kaɗan ya gyara zaman hiramin shi, ya shiga ƙare min kallo yace "Ai babu laifi naga Kyakykyawace dai-dai da yadda nace maka."
Gaba ɗaya rasa tunanin da ya kamata nayi nayi, anya Al'amen yasan meye Musulunci kuwa? In ya sani me yasa ya ke abubuwa kamar jahili, Ni kaina duka ya ɗaure na rasa a wanne matsayi zan sa shi, wasu abubuwa nake gani a tare da shi, tun safiyar yau har zuwa yanzu waɗan da basu yi kama da koyarwar addinin Musulunci ba.
Tun daga kan ihun da ya min akan nayi Sallah, zuwa sallar da shi ya yi ba tare da ya kalli gabas ba. Zuwa wayar da ya yi da maganganun da ya faɗa min na karna ƙara ja masa asara. Sannan ga shigo min gida da ya yi kai tsaye da wannan mutumin da sam bai min kama da mutanen kirki ba, kama ya ke min da irin malaman tsubbu ɗin nan.
"Yanzu dai ba wannan ke Amaryar mu wajen ki na zo takanas, nasan baki Sanni ba tunda yau kika fara gani na.
Ni sunana Malam Mustafa, Ni ne ke kula da duk wasu harkoki na cigaban kasuwancin mijin ki, Alhamdulillahi kuma ina alfahari da hakan, tunda kullum yana ƙara ganin buɗi da yalwa a cikin kasuwancin nasa dan yana taimako sosai a ciki."
Gaba ɗaya maganganun sa ƙara tsunduma ni cikin kogin tunani suka yi, magana ya cigaba da yi "To yanzu kin take wani Sharaɗin mu ne yau, amma bisa dole mun miki uzuri sakamakon rashin sani ne ya jawo hakan.
Ya kamata ace kafin ki yi sallah ki nemi izinin mijin ki, ya faɗa miki yadda za ki yi, sai kika kalli gabas kai tsaye ba tare da cika umarnin mu.
Ya kamata ace kin fara kallon arewa tukun, sannan ki ja carbi akwai addu'o'in dana koyar da shi, in ya koya miki sai ki yi su. To daga nan zaki iya sallar ki ki kalli gabas harma da sauran ibadun ki, muna dai so ace ita wadda ake kallon arewa ɗin kika fara."
Gaba ɗaya ji nayi jikina na wani irin rawa, nan da nan zuciyata ta fara min zafi. Buɗe baki na nayi da nufin sauke masa kwandon fitsara daga shi har wanda ya kawo shi. Sai dai muna haɗa ido jikina ya yi wani irin lak'was kamar an watsa min ruwa, yadda kuka san an sa makulli an kulle min baki gaba ɗaya na kasa magana.
Sai faman raba ido da nake, zuciyata na wani irin zafi kamar ana hura min wuta a cikin ta.
*_🥰MAMAN ƊAN ALBARKA CE 🥰 ✍🏻✍🏻_*