Free chapter · Read without an account
🥀His Claimed Rose🥀
by NorthernAngel · His Rose
Haka Noor taje ta gaida family din Maamah, and she was genuinely stunned by their sheer numbers. Dan bayan komawarta gida ma, kan kace me, sun ƙaru—it was like a never-ending stream of arrivals, sai isowa sukeyi, gaba daya drivers ɗin Galado got so busy ranar saboda jeka ka dawon ɗauko mutane daga airport. Wata cousin dinta sa’ar Maamahn ce, she is the elder sister to Aunty Hannah amma maman su daban. Tazo da yayan ta mata biyar—biyu sunada aure, the other three are sophisticated young ladies, inda masu auren suka zo da yaransu. Sai cousins din Maamah na dangin mahaifiyar ta su huɗu da yayan su yara da manya, sai matan cousins dinta su biyar, Two are wives of the same man, while the other three kowa da mijinta, inda suma kowacce tazo da yayanta yan mata biyu. Even those with toddlers came along. Sai sauran cousins dinta both na uwa da uba sunkai takwas, suma da yayansu masu aure da marasa aure hardama yara, second cousins ma duk sunzo. Dayawan su dai sukazo saboda sun kai hamsin, ahakan ma dayawa basu samu zuwa ba wasu kuma basu karaso ba, saboda yanda abun yazo unexpected. Dan mafi yawansu badan bikin Muazzam suka zo ba, na Zara suka zo tunda itace mace, ita ke bukatar dangin mahaifiyar ta acewar su. They insisted that Zara needs her maternal family by her side, saboda da tsiraru ne kawai zasu zo bikin Muazzam amma ana cewa dana Zara za’a haɗa suka fara shiri, danma Zarar taƙi zuwa can gurinsu. They decided to hold their own celebrations here, kamar ko wanne dangin amarya. Kana gani kasan Maamah yar dangi ce ba kadan ba, duk da ita kadai iyayen ta suka haifa amma tanada cousins dayawa duka dangin uwa da uba. Iyayen Maamah tun tana karama suka rasu shiyasa ta tashi a hannun paternal grandparents ɗinta tare da brothers ɗin Aunty Hannah da suma mahaifiyar su ta rasu gurin haihuwar Hannah ɗin. That is why they are so close to Maamah, dan a gida ɗaya suka taso. Kuma shiyasa su ba yayan su kawai ba, hatta matan su sai da suka turo. Bangaren maza kuma samari ne kawai suka karaso kusan su goma, manyan sai ana gobe daurin aure zasu zo, inda harda ƙanin baban Maamah wanda shine ɗan autan iyayensu Maamahn. Even though he is quite elderly, yace dashi za ayi daurin auren yayan Maryam. Sosai sukayi musu kara musamman mazan da kowa sai da ya turo iyalinsa. Muazzam da Omar basu taba tunanin haka ba duk da a kullum suna ce musu bikin Zara acan za ayi ko kuma su suzo nan suyi bikinsu. They never imagined such a huge crowd would show up, dan har wanda they are not in touch with sai da suka gani wanda hakan ba ƙaramin dadi yayi musu ba; it makes them so emotional and grateful, kuma ko ba komai su Hajiya da Yemma zasu ga Zara nada gata. Baffa da yaga sai isowa suke suna ƙaruwa yace Muazzam ya tambayesu ko a kaisu hotel din Galado amma daya tambaya sukace gidan ya ishesu. The mansion provided in the estate was more than enough, dan ba ƙaramin girma ne dashi ba kuma part part ne. So kawai sai Baffa yasa aka dinga order ɗin manyan mattress masu tudu sosai tareda bunky boards ana kaiwa cikin gidan da suke. Ƙawayen Maamah kuwa su bakwai ne kawai suka zo bikin Muazzam, sauran sunce sai bikin Zara yazo dab zasu zo dan sai Zara taje Warri anyi traditional wedding sannan zata dawo Lagos dangin Maamah suyi bikinsu. That’s when all her friends will finally gather. Acikin ƙawayen ta da suka iso akwai aminiyarta wato Umma Deeza da yayanta mata biyu wanda su kadai ne Allah ya bata; ɗaya tana da aure ɗayar kuma ta dai taba aure ta fito kuma nurse ce. Umma Deeza itace tayi komai da uwar ango keyi. She basically took over all the motherly responsibilities. Yan ɗakinta kuma da business parners ɗinta suma dayawa basu gama ƙaraso wa ba wanda sunce sai gab da biki dan akwai wayanda acikin Lagos ɗinma suke. Har ɗaki Aunty taje ta samu Yemma da gulmar irin yadda dangin Maamah suka cika gidan wanda tana farawa Yemma ta dakatar da ita. Yemma told her clearly that it wasn't her business. Nan ma Aunty na fita sai da yan uwan Yemma suka yiwa Yemma maganar surukar tata ta fiye gulma Allah yasa ba haka yar take ba. Washe gari da daddare around 9pm bayan an gama kamun Salma dangin Maamah kuma sun dawo daga gidan su Surrayah for another event, tunda satin yakama suke events kala kala. They are definitely people who love big celebrations. Sun so suyi a Adamawa ko Abuja inda sukafi zama amma ganin Galado basu koma Abuja ko Adamawa ba, dan suma ɗin yan Adamawa ne. Shiyasa mahaifin Surrayyan yace suyi zaman su anan din tunda dangin ango na nan, yafi sauƙi ma. Su Surayya na zaune a nan Ikoyi tun bayan da suka dawo Nigeria, after her father finished serving in the United States (D.C.) as the Nigerian Ambassador from 2019 to 2023. Inda anan ne suka haɗu da Muazzam while studying at Columbia, NYC. Sosai aka karrama dangin Maamah wanda hakan ma baiyiwa su Ummi dadi ba dan ba haka akamusu ba kwana biyun da sukaje. Noor kuwa inka ganta zaka sha mamaki ganin yanda ta shige cikin dangin Maamah musamman iyayen anata sha’ani da ita. Bayan dawowarsu ne kuma gurin 9pm Omar ya tura Zwar ya kira masa Noor, inda ya fada mata ta dan dakata da tafiyar saboda yan matan nan da suka zo daga Niger duk sunce zasu je suma. They all insisted on joining the trip. Daman kuma da passport ɗinsu dan by flight suka zo Nigeria, so za’a nemar musu express visa and it’ll take 24hr. Batayi musu ba dan sosai take son ta saba da yan uwansa saboda ba ƙaramin tashi hankalinta yayi ba akan maganarsa da Hasina dataji abakin Zara kuma ta tambayi Yusrah ta bata labarin komai. Bayan nan Omar ya kira Zara ya sanar mata tayi expecting yan matan. Zara was filled with shock and frustration. Abunda ta tsara da mutane kadan ya koma babban event, sai da ta kira event planners ɗinda aka haɗata dasu acan daga nan aka fara neman bigger hall wanda dole aka canza schedules din. Washe garin daya rage saura kwana hudu ɗaurin aure Noor da matan nan suka ɗaga zuwa Dubai. A ɓangaren Salma kuwa, duk da anata hidima, hakanan dai akayi bikin amma kana ganin amarya kasan ba lafiya. Her glow was completely overshadowed by a severe fever and a splitting headache wanda kukan da take tayi ba ƙauƙautawa ya janyo mata. Ahakan aka kamata jiya, yau kuma Mother’s Eve akayi wanda Aunty ce ta tsara abunta to her taste. What added to their anxiety was the fact that Zafar was nowhere to be found; babu shi, babu labarin sa. Yemma ma tadan leƙa wurin event ɗin, sai dai ko 30 minutes batayi ba ta koma gida, inda su Ummi suka yi ta damunta da waya complaining cewa ango har yanzu bai ƙaraso ba. Anan ne Yemma tasa aka kira mata Muazzam inda ta tambayesa inda Zafar yake. Even from Muazzam, the answer remained the same: "He is in Angola for a business emergency." Sosai ran Yemma ya fara ɓaci da Zafar, because she had call his PA again to give him a message that he must be present for today’s event, amma duk da haka bai zo ba. Out of frustration, she sent him a very stern email—the kind she knew he wouldn't dare ignore. Ae kuwa as expected, sai gashi washe gari ya diro Nigeria. He sent her a brief apology text ya faɗa mata ya dawo, amma still bata ganshi ba har ya shigo estate ɗin da safe. Dashi dasu Muazzam da friends ɗinsu suka rakashi ya gaida yan uwan Maamah da ƙawayenta, inda kowa sai murna suke da suka gansa. The relatives were so impressed, suna cewa yarsu Zara tayi dace da wannan haɗaɗɗen angon. Daga nan Zafar ya koma The Galado, the family’s flagship luxury hotel where most of their international guests and elite friends had lodged. Ranar Galado family sukayi event ɗinsu can na Fulani cultural display, wanda shi ba ango. Sai washe gari ne yan uwan Yemma sukayi Mothers' Night. Tun daga decor ɗin ranar zaka san ya banbanta da kowane biki da akayi; it was pure class. Zafar showed up, and it made Yemma very happy to see him finally participating. Shima duk da yana nan, Yemma bata wani jima ba tabar wurin ta koma gida. The moment Zafar saw her leave, shima ya fece abunsa, not staying a second longer than necessary. Salma, on her part, was just trying to force a smile and enjoy the fame, dan kuwa high-profile personalities ne ta ko ina suke isowa wurin ko wani event musamman na yau. Washe gari akayi Grand Dinner, which was the joint event for Muazzam and his bride. Zafar and Salma. Even this dinner, sai da akayi da gaske sannan Zafar ya yarda zai je. Ahmad had to call Baffa a waya ya gaya masa halin da ake ciki, and it took Baffa’s intervention—along with him giving Zafar a piece of his mind—before he complied. Nemansa Yemma keyi ido rufe tana ta wayar Muazzam, Ahmad, harma da aminin su Fuad Shettima, amma Zafar yaƙi yadda su haɗu su kuma suna ɗagawa suke ce mata baya kusa, kuma yaƙi kunna wayar sa to avoid her calls. Gurin dinner ɗin kam ya zauna because Muazzam was there, along with a lot of their Ivy League and elite business circle friends. It was a night of absolute opulence. Baban Surayya, the Former Ambassador, was in attendance to grace the occasion. Abbah ma yaje da duk wasu manyan mutane ma, amma Baffa baije ba, preferring to maintain his distance from the loud festivities. Ranar ne kaɗai Salma tayi farin ciki ta saki jiki ganin Zafar na bata attention; she felt like she was finally winning. Ta dinga maƙale Zafar tana nuna closeness, sakamakon shawarar da yan uwa da ƙawayen ta suka bata na cewa ta mallake shi tun yanzu. Inka gansu a wurin dinner ɗin, zakayi tunanin they’re deeply in love, dan Zafar ma ya saki fuskarsa ranar, playing the part of the perfect groom to avoid any scene. Washe gari a gida akayi Wankin Amarya, inda akayiwa Salma traditional milk bath kamar yadda suke a al’adar su ta Fulani to soften and glow her skin. Da daddare kuma, the energy shifted as the men had their exclusive stag nights at a private lounge, a night of high-end cigars, deep conversations, and brotherly bonds. Washe gari, ranar Ɗaurin Aure, kowa ya tashi cikin farin ciki. Amma fa duk farin cikin nan da akeyi, ya biyo bayan Zafar. Daren jiya sam bai runtsa ba; he was full of an electric, restless excitement. Gaban shi har wani faɗuwa yake inya tuna wai yau ne zai mallaki Zara a matsayin mata. It felt surreal, like a fever dream he didn't want to wake up from. His heart was racing with a rhythmic intensity, a mixture of pure adrenaline and a vulnerability he had never allowed himself to feel before. Zafar is not the emotional type—he is the man of steel and business logic—but today, he was completely overwhelmed. Every time he closed his eyes, he saw Zara’s face, and a wave of possessive tenderness would wash over him, making his breath hitch. Allah Allah yake lokacin yayi a ɗaura auren kar wani abu ya faru a fasa. He was paranoid that the universe might suddenly snatch this happiness away. Tun asuba ya shigo estate din akayi sallah dashi. Ana idarwa bayan karatu ya shigo tare da Baffa, sai dai bai kalli hanyar wing ɗinsu ba to avoid any confrontation with Yemma. Baffa yabi zuwa nasa wing ɗin, and Zafar followed like a shadow. A bedroom ɗin Baffa ya kwanta wai zai dan runtsa, yayin da Baffa ke terrace ɗinsa enjoying the morning breeze while sipping coffee. Sai dai har 8am Zafar yakasa baccin; his mind was too busy counting the minutes. Allah Allah yake lokaci yayi, ya kira Ahmad a waya yasa ya kawo masa kayansa and everything he needed for the big day. Ƙiri ƙiri Zafar ya maƙale ma Baffa safiyar nan. Baffa ko private library ɗinsa ya nufa, Zafar was right behind him. Abun ma ba ƙaramin dariya yabawa Ahmad da Muazzam ba; seeing the formidable Zafar clinging to his father was the highlight of their morning. Baffa ma yana sane dashi ya kyalesa; duk sunsan tsoron Yemma ta rutsasa shi kaɗai ne. He was playing it safe. Duk wani abunda zaisa a fasa auren nan, Zafar was avoiding it at all costs, shiyasa ya maƙale tare da Baffa dan yasan ba abunda Yemma zata iya a gaban Baffa. Yemma ma tana sane da cat-and-mouse game ɗin da yake da ita; she had sent him countless messages, but his phone remained switched off. He was effectively in a fortress, waiting for the words that would make Zara his forever. Around 9:00 am, Zafar ya shiga wanka ya fito ya saka jallabiyarsa. Ya fito parlour yana tunanin kardai Baffa yayi nisa, salon Yemma tazo ta ritsa sa. A parlour ya samesu tare dasu Muazzam, Omar, da Ahmad suna breakfast a dining. Baffa na ganinsa ya nuna masa seat ɗin kusa dashi yace ya zauna yayi breakfast. Zafar ya zauna ya zuba abincin, amma ya kasa ci; sai juya fork ɗin hannunsa yake cikin abincin. His legs were bouncing restlessly beneath the table, his heart hammering against his ribs in a way he couldn't control. Gani yake anya Zara zata zama matarsa kuwa? It felt too good to be true, like a beautiful mirage that might vanish if he blinked. Kowa kallonsa yake. Muazzam dake cin abincinsa, yayi yar dariya calmly yace, “Zafar, you’re being like a child right now.” Seriously Baffa ya girgiza kai yace, “Baka san halin Aziza bane Muazzam, barshi yayi.” Dariya dukkanninsu suka sa, Zafar dai bai kulasu ba. Ganin 9:45 am yasa ya miƙe, but calmly Baffa said, “Sit down and eat.” Zafar ya koma ya zauna yana janyo wayar Omar dake kan table ɗin ya duba time. Ahaka ya tuttura abincin. Zuwa lokacin jama’a sun taru, and the atmosphere outside was reaching a fever pitch. Ba abunda kake ji sai ƙarar motoci, hayaniyar jama’a, da kiɗe-kiɗe da kirarin maroƙa. Yarbawa da Hausawa duka Baffa yace kar a hana su shigowa estate ɗin; he wanted the celebration to be felt by everyone. Haka suka ci abunci suna kallon Zafar na tuttura abincin kamar mai yiwa kansa ɗure, har dai suka gama. Shima ya miƙe, daga haka kowa ya wuce domin shiryawa. Ɗakin Baffa ya shiga. Baffa kuma daya gama shiryawa tsab, ya ɗauki babbar rigarsa fara ƙal dake parlourn ya saka ya ƙara fesa turare sannan ya fara amsa wayar sa daketa ringing. Zafar ya shirya tsab cikin farar Super-Deluxe Swiss Shadda. Yana tuna ranar da Zara ta ce masa sai yasa farin kaya ranar aurensu, and he wasn't about to disappoint her. Ya shafa turarensa na Shumukh—the world's most expensive perfume, letting the scent define his presence. Ya saka takalminsa na handmade crocodile skin loafers, sannan ya saka babbar rigarsa itama ya bita da turare. Daga nan ya saka baƙar hularsa, a perfectly hand-knitted Zanna Bukar cap. Ya ɗauko agogonsa na Patek Philippe Grand Complications, ya saka. Ya fito cikin sauri yana gyara babbar rigarsa. Yana isowa parlour yaga Baffa da Muazzam dake sanye cikin farar shadda sak irin tasa. Suna ganinsa suka haɗa baki gurin cewa “Ango, ango!” Wani murmushi Zafar ya saki wanda Zara kaɗai ke ganin irinsa—it was soft, genuine, and brimming with an unspoken triumph. Unexpectedly, yayi hugging ɗin Muazzam, dai-dai shigowar su Ahmad da Omar. Da sauri Ahmad ya ciro wayar sa yana snapping ɗinsu, capturing the rare display of emotion. Muazzam yayi mamaki saboda Zafar was never a hugger; in fact, he usually avoided physical touch, but today, the walls he built around his heart had completely crumbled under the weight of his excitement. Ahankali ya cikasa, Zafar na kallon Muazzam with a rare, heavy sincerity in his eyes. Ya furta masa, “I appreciate everything, brother. Allah ya saka da alkhairi. I’m taking this responsibility seriously, and I won’t let you down. You’ll have every reason to be proud of me as a brother-in-law, InshaAllah.” It was a powerful moment of brotherhood, bridging the gap between being friends and becoming family. Cike da tsokana Ahmad, who was busy capturing everything on video, started making high-pitched “Aww” sounds in a feminine voice, mocking the sentimentality of the moment. Dariya dukkanninsu suka sa, breaking the tension. Muazzam yayi patting kafaɗar Zafar da karfi, his face beaming with genuine respect, yana cewa, “There’s no doubt in my mind. I’ve always trusted your word.” Zafar ya gyaɗa kai gratefully, a small, triumphant smile playing on his lips before he turned to Omar. Suka yi handshake da wani firm, brotherly embrace—the kind that signals absolute loyalty. Zafar ya sake cewa, “Thank you, brother!” Omar ya gyaɗa kai shima, his gaze steady. “I trust you, brother.” Zafar replied with a final, “No disappointment, InshaAllah.” Baffa, who had been watching the scene with a proud, silent dignity, finally spoke, “Toh, MashaAllah, sai muje ko?” Ahmad, ever the attention-seeker, cut in: “No! Baffa he didn’t thank me, saura ni.” Zafar gave him a playful, exasperated look kafin ya ƙarasa gaban Baffa. He lowered his head slightly in a gesture of deep respect, “Baffa na gode, Allah ya ƙara girma.” Baffa ya gyaɗa kai, his smile reaching his eyes as he offered a final piece of fatherly advice: “Don’t disappoint me. Allah ya baka ikon adalci a tsakanin matanka.” An emotional “Ameen” echoed through the room, though the weight of those words hung in the air. Suna fitowa daga wing ɗin baffa, the scene was pure chaos—the elite kind. Mata ne ta ko ina ke kai kawo, Daga haka suka fito inda mata ne ta ko ina ke kai-kawo, a sea of expensive lace and the heavy scent of Oud and Turaren Wuta filling the compound. Everywhere they turned, voices called out “Ango! Ango!” Masu guɗa nayita yi. Dashi da Muazzam, they could barely keep up with the greetings, forcing polite, bright smiles. Ahmad dai sai mita yake an godewa kowa banda shi. Zafar, finally losing his patience but with a smirk playing on his lips, juyo sharply yana haɗa hannayensu biyu, “Toh baba Ahmad na gode, shikenan?” Baffa na dariya yace “Rabu da shi babban mutum, ae baiyi ƙarya ba, baban ne kai.” Daga haka suka fita daga Manor ɗin, inda suka fara cin karo da mutane da a fleet of black luxury SUVs and armored convoys sun cika ko ina, gleaming under the Lagos sun. Baffa ya shige cikin jama’a with the ease of a man used to being the center of gravity, suma suka haɗe da abokan su. Baffa tuni yafara gaisawa da yan uwan Maamah maza da shigowar su kenan. Nan yakira Zafar ya gaishe su shima. Maza ne su bakwai, harda ƙanin baban Maamah wanda yake ta tsokanar Zafar a matsayinsa na kaka, causing Zafar to offer a rare, shy smile. Ko ina hayaniya, the air was vibrating with the sound of talking drums and the loud, rhythmic praises of the maroƙa singing the lineages of the angwayen. In the middle of the chaos, Zafar ya ciro wayarsa daga aljihu and turned off flight mode. As soon as the network came up, ya turawa Zara message: ‘Minutes away to forever.’ He watched the "delivered" sign for a second, his heart racing with pure joy. Daga haka ya shige masallacin su Muazzam na biye dashi. 30 minutes later, aka gama duk wani sacred marriage rite. The atmosphere was solemn, filled with the scent of incense and low prayers. A gaban taron jama'a aka ɗaura auren “Zafar Omar Galado da Zara Ali Amadi”akan sadaki Misƙali na Zinari guda biyu (Two Gold Dinars). Zafar ɗinne da kansa ya ciro wani custom mahogany wooden box daga aljihunsa. His hands were steady as he handed it to Abbah wanda shine waliy ɗinsa, shi kuma ya miƙawa yayan maamah (cousin) wanda Muazzam yayi masa karar ɗaura auren Zara. The glint of the gold coins inside the box made everyone whisper in admiration. Bayan angama, aka ɗaura auren Zafar da Salma. Nan ma Abbah ne waliyin Zafar, babah kuma waliyin Salma, akan sadaki 2M wanda Ahmad ne ya biya. Ahmad had intended to pay for Zara’s dowry as a gift to his brother, but he realized Zafar had far more personal, symbolic plans for her. On the other side, Baffa ne waliyin Muazzam, paying his 1M dowry with the quiet dignity of a patriarch. Daga cikin gida kuma da suka kasa kunne suna jiyo duk abunda ake fada a speaker, anan aka fara guɗa inda yan asalin estate ɗin kuma suka cika da mamakin yanda aka fara ɗaura auren Zara kafin kowa. The breach of seniority was so obvious; normally, Salma should have come first. Sosai abun ya ɓatawa Yemma rai, her face hardened into a mask of silent fury as she listened. Bangaren Salma kuwa, kuka ta saka—not the tears of a happy bride, but tears of pure humiliation and rage. Su Hajiya suka dinga lallashinta da cewa ai abinda ma Zara bata gari, so ita za’a fara kaiwa ɗakin miji. But even they were just trying to keep their composure, dan ransu ya gama ɓaci. Musamman tun jiya da home decorators suka zo aka nuna musu wannan villa ɗin dai na da, akace nan zasu shiga. Sosai ransu ya ɓaci dan saboda abunda yasa basu saka kaya tuntuni ba, ganin ba’a gama mansion ɗin ba wanda da suka san da maganar Zara, suke tunanin su biyu zasu zauna a ƙaton gidan. They felt insulted, saboda suna zuwa da masu interior decorators dan su duba tsarin asan irin luxury furniture da za’asa, sai armed securities suka hana su shiga. They stood their ground, blocked the entrance, kuma suka ce "Strict order from Muazzam Galado" ne cewa ba'a yarda kowa ya shiga ba without his direct permission. Abun ya zama a total humiliation a idon ma'aikatan. Da suka samu Hajiya Maama ta kira Baffa ya gaya musu cewa Salma wannan villa din nata da aka nuna tun asali nan zata zauna, mansion kuma shi kansa Baffa ya ce bai san me Muazzam yake shiryawa a kai ba. The message was clear: Zara was the priority, and the new mansion was off-limits. Sosai akayi tashin hankalin da babu wanda yasan anyi acikin mazan, dan har Baffan yana gama faɗa ya kashe wayarsa. Hajiya Mama ta kira Abbah da Babah tace musu, To wannan karon ƙura ta kai bango, dan wallahi indai tana numfashi Zara ba zata shiga gidan nan ba, sugawa Baffa. Toh, yanzu da Salma ke kuka, sai suka hau hure mata kunne akan ta kwantar da hankalin ta. “Abunda Zarar bata dawo ba ma, balle taje garinsu balle kuma ta dawo anan, yaushe akayi bikin har aka kawota ɗakin mijin?” Ummi ta karɓe zancen Hajiya Maamah da cewa, “Ke dai kawai ki kwantar da hankalinki. Kar kuma kisa shashanci ko ki biyeta. Ki saki jiki ki hayayyafa, gida ya zama naki. Kinayin ciki ma dole a baki mansion ɗinnan. Ato! Haihuwa ai gadonta kika yi, ba ita ba da ubanta ya fi shekara 45 a duniya kafin ya sameta.” Duk suka amsa da “Wallahi kuwa!” Daga haka aka gyara mata makeup ɗinta aka fito da ita, anan gidansu aka ringa hotuna. Zafar yazo harda hugging ɗinta yayi kamar yadda akeyi a modern weddings, aka yi ta ihu ana hotuna. It was a perfect scene for the cameras, although Zafar’s mind was clearly miles away. Bayan an gama suka koma Manor, inda Yemma ta fito. Despite her internal fury, bata nuna komai ba a fuskarta; she played the part of the proud mother to perfection, sai ma rungume ɗan nata da tayi aka sha pictures nan ma, maintaining the Galado family’s public image. Ana cikin yi ne wayar Zafar ta ɗanyi beeping daga aljihunsa. Ciro ta yayi ya ɗan fita daga mutane ya duba, his expression shifting into something softer and more intense. Text message ne daga number da yayi saving da Nyx. Message content ɗin kamar haka: “Enough of the elders, I’m waiting for you..”
Wani murmushi Zafar yayi, a look of pure anticipation. Ya ɗago kansa ya kalli mutanen dake parlourn Yemma—the noise, the fake smiles, and the endless protocols. He had fulfilled his duties, and now it was time for his own happiness. Fita yayi ba tare da kowa ya lura ba, slipping through the corridors like a ghost. Yana fitowa compound ɗin Manor ɗin, yaga duk mazan na shirin zuwa reception ɗin, but he had a different destination. Wing ɗinsu ya nufa cikin sauri, yana zuwa ya shiga elevator zuwa Garage, the underground sanctuary where their most elite fleet was kept. Yana isa ya tarar da EA ɗinsa, Tijjani, a bakin BMW ɗinsa a tsaye. Yana ganin Zafar ya taho da fara’a yana cewa, “Ango, ango!” Wani murmushi Zafar yayi, the joy of the moment finally feeling real. He headed to the biometric key-box, opened it, and grabbed his keys. Suka koma gurin motar, and Zafar’s business-mind clicked back in for one last brief, his voice cool and authoritative yace, “Tijjani, I need you to ensure all operations remain seamless at the headquarters while I’m away. Monitor the energy portfolio closely and provide me with a comprehensive daily brief via email. If anything requires my direct authorization, flag it as urgent.” Tijjani ya gyaɗa kai cikin girmamawa, understanding the weight of the responsibility “Understood, Sir. I will oversee all pending matters and coordinate with the department heads. You don’t have to worry about anything; the office is in capable hands like always. Just focus on your honeymoon.” Zafar ya amsa, “Good. I’ll only be out of the country for a week, InshaAllah.” Daga haka Tijjani ya tada motar suka fita daga estate ɗin within a heavy-duty security convoy, bypassing the traffic and the noise of the reception. Suka nufi airport inda Zafar’s private jet was already fueled and prepped—zai ɗaga zuwa Dubai gurin amaryarsa, the only woman who truly held the keys to his heart…