Free chapter · Read without an account
Scent Of A Galado Bride
by NorthernAngel · His Rose
7:00 pm, Zafar ya sauka Abu Dhabi, a Al Bateen Executive Airport—the exclusive hub for private royals and tycoons. The air was warm, smelling of salt and desert luxury. Tuni ya isa inda wata Rolls-Royce Spectre take a fake, reflecting the amber lights on its polished black surface. Driver ɗin dake tsaye a jikin motar ya miƙa masa gaisuwa cikin girmamawa. Yana isowa suka gaisa, daga haka Zafar ya karɓi key ɗin motar da kansa ya shiga ya fita daga airport ɗin. Since he landed at a private terminal, babu wani dogon layin immigration; his Private Liaison ya riga ya gama komai na takardunsa, providing him a seamless entry into the city. It took him about 20 minutes ya isa Vendôme at the Emirates Palace. The grand gold-and-marble entrance loomed ahead, a fortress of opulence. Yana isowa ya ciro wayar sa ya kira Zara. Tana picking, Zafar yace mata, in his low, commanding voice that made her heart skip, “Where exactly are you?” Zara ta kwatanta masa inda suke da friends ɗinta having their Bridesmaid’s Brunch on the sprawling terrace. Zafar ya buɗe motar ya fito, his presence immediately cutting through the crowd of tourists. Yana ƙarasawa side ɗin ya hangota ta fito cikin pink fitted gown da ɗan ƙaramin crown akan ɗankwalinta. Sosai yaji daɗin ganinta da ɗankwalin, as he didn't expect her to keep it so modest yet elegant. Tayi kyau sosai; even though there was a light touch of makeup on her face, her natural glow was unmissable. Wani irin bright smile ta saki tana ganinsa, wanda shima ya mayar mata yana buɗe mata hannunsa in a rare display of public affection. Ae kuwa da gudunta ta ƙaraso tana hugging ɗinsa very tightly, ta matse hannunta a wuyansa, inhaling the familiar scent of his Shumukh cologne. Sai dai Zafar had other plans; cak ya ɗagata in a bridal style, carrying her like the prize she is. Tuni ƙawayenta da Cindy, da few celebrity friends ɗinta dake wurin, suka fara ihu, their phones out to capture the moment. Daman tun daga isowar sa wasu sun fara video. After Zafar finished spinning her around while she laughed, ya juya ya nufi hanyar fita. Zara ta ɗagawa mutanen hannu alamar bye, nan ma aka sa wani ihu as the videos continued until they disappeared behind the Palace's heavy doors. Straight mota ya nufa da ita. Yana zuwa ya buɗe front seat ya sakata ciki, ya ɗago mata ƙasan gown ɗinta dake flowing ya saka cikin motar with a gentleness that contradicted his hard exterior. Zara dai sai kallonsa take, her eyes full of raw emotion, searching his face for the reality of this moment. Yana gamawa ya matso dab da ita; tana zaune a front seat shikuma yana tsaye, blocking out the rest of the world. Ahankali ya sa hannu ya fara rubbing cheeks ɗinta softly with his thumb. In a raspy, low whisper that vibrated in her chest, he said, “Hey.” And that is when Zara trashed; ta fashe da kuka sosai tana kifa kanta jikinsa, ta rungume shi daga inda yake tsaye, her fingers digging into his white shadda. Zafar yayi a soft smile yana sauke ajiyar zuciya, ya ɗaura hannuwansa a bayanta, holding her as if he’d never let go. Kusan 10 minutes suna haka, the only sound being her soft sobs. Sai da Zafar ya tabbatar kukan nata ya tsagaita ya ɗagota, sannan ya sunkuyo dai-dai fuskarta yana goge mata hawaye, his own eyes dark with an intensity that bordered on tears. In a soft, raspy voice, he said: “Thank you. Nagode, Zara. I don’t usually say 'I love you' because I feel that word is an insult to the depth of what I feel for you. I don’t know how to express it, but just know that I’d die for you—any day, anytime. And I can kill for you. When it comes to you, there are no limits, baby. I can do anything, that’s how much I feel for you.” Ya ɗago fuskarta data sunkuyar, yana kallon cikin idonta possessively, his gaze marking her as his. “Better keep that in mind. Be careful how you dress from now on; you have to stay modest. I don’t even trust women with my wife, talkless of men. And Zara?” Zara dake kallonsa ta ɗan ɗaga gira ɗaya, her breath hitching ganin kallon da yake mata. Zafar ya haɗe rai, looking every bit the dominant Galado heir. “You’re sticking to your word. You’re a housewife now—a complete housewife. I want to always find you at home waiting for me when I’m back from work. Your job is me, and me alone. The only time you’ll leave the estate is travelling for your charity stuffs. You have your brothers close, and Daddy visits Lagos often, so we’ll see him and your cousins. Apart from them, I don’t think you need anyone else in this world. Your friends are free to visit you as much as they want, but you? You stay within my walls. Yeah?” Zara tayi murmushin ƙarfin hali cike da mamaki da ɗan razana. She had said she wanted to be a housewife because she didn't want to work, but she never imagined Zafar would actually restrict her movements this much. But the way he looked at her—as if she was his entire universe—made the cage feel like a sanctuary. If that’s what he wants, she’s cool with it. Ta gyaɗa masa kai tana ɗan murmushi. Har lokacin fuskarsa a ɗaure, his jaw tight as he demanded, “Words, Princess.” Da sauri Zara ta gyaɗa kai tana cewa, “Yes, Insha Allah.” Zafar ya saki wani possessive smile, a look of pure triumph, yana cewa: “That’s my good girl. Now, let’s head to the airport.” 30 minutes flight ne kacal daga Abu Dhabi zuwa Dubai, amma a cikin jet ɗin, it felt like the rest of the world had simply ceased to exist. The cabin was a sanctuary of cream leather and polished mahogany, filled with the intoxicating scent of Oud and Zafar’s expensive cologne. Suna shiga, Zafar ya zaunar da ita sannan ya zauna kusa da ita yana janyota jikinsa, his hand immediately finding its place on her waist, pulling her flush against him. Ita dai Zara har lokacin tana cikin mamakin dokokin daya shimfiɗa mata tun daga fara aurensu, amma tana ƙoƙarin boye halin da take ciki. Sai dai kallo ɗaya Zafar ya yi mata ya fahimci abun da yake ranta, he already knew those rules were going through her mind, amma shima bai nuna mata ya gane mood ɗinta ya canza ba, his expression remaining as unreadable as granite. Ahankali Zara ta ɗaura kanta a kafaɗar sa tana lumshe ido, a contented feeling filling her heart. Tanajin ko zaman gida ne, ko zaman daki ya sanya ta, tabbas zata iya jurewa as long as tana tare dashi, his steady heartbeat under her ear was the only rhythm she needed. Zafar ya kalleta yaga tayi shiru kamar mai bacci, murmushi ya saki yana kissing forehead ɗinta softly with a lingering tenderness. She let out a soft smile tana ƙara gyara kanta akan shoulder ɗinsa, tana jinta kamar a mafarki wai yau itace matar Zafar kuma First Wife. Tunanin haka ya sa ta tuno da Salma. Da sauri ta buɗe idonta ta ɗan kalle shi ta ga hankalinsa na kan wayarsa, his jaw tight in focus. Nan take tunani ya tafi da ita; yanzu burinta ya cika, ta zama matarsa. Amma abin da ya rage mata yanzu shine ya zama nata shi kaɗai, she wanted him to be hers and hers alone, an absolute possession. Kamar yadda tabi komai a hankali har ta zama First Wife, haka yanzun ma ba za ta yi garaje ba, zata kiyaye fiye da. She knew she was entering a battlefield, kuma babban makiyinta shine mahaifiyarsa. Ta san cewa yanzu dole Zafar yabi Yemma a hankali tunda aka riga aka yi auren, and for Zafar, keeping the peace meant submitting to his mother’s toxic demands for a while. Wannan yasa Zara ta tabbatar cewa she had to play her cards right. Like a silent chess player moving in the dark, dole tabi komai da lissafi kafin Salma ta samu damar zama comfortable as matar Zafar. She was ready to be the perfect, submissive wife in his eyes, while being a calculated threat to anyone who tried to take her place. Baza ta taɓa barin kowa ya ruguza ruyuwar da take tsarawa kanta a gidan mijinta ba. She has to be in charge, the queen, dole maganarta tazama rule agurin mijinta. It was a game of survival, and Zara was playing to win. Minti talatin bayan tashi daga Abu Dhabi, suka sauka a Dubai International Airport (DXB). Amma shi Zafar, jet ɗinsa kai tsaye ya nufi Jetex Private Terminal. Wannan wurin shi ne the gathering point for royalty and the world's most powerful tycoons. Zafar is not a stranger there, because Dubai tana da wani strategic positioning a fannin global energy market, domin ita ce babban gateway da yake haɗa African resources da kuma global capital. Ga su Zafar, wato The Galados, zuwa Dubai isn't just about the luxury lifestyle—it’s a calculated move of pure power. Saboda yadda DIFC da sauran manyan energy trading hubs suke within reach, so Dubai is the arena where Zafar continues to solidify his status as a global powerhouse. Security clearance ɗinsu bai ɗauki lokaci ba; his Private Liaison ya riga ya gama komai na takardunsa before they even landed. Babu wani dogon layin immigration; within minutes, an yi musu iso zuwa VIP parking lot where the warm desert air met the scent of expensive aviation fuel. Yana riƙe da hannunta suka ƙarasa gurin wata matte black BMW XM Label Red. Ya karɓi key ɗin bayan sun gaisa da drivern sannan ya buɗe mata front seat ta zauna. Cike da kulawa ya gyara mata ƙasan rigarta dake flowing ya saka mata seatbelt, his face so close she could feel the heat radiating from his skin and the faint scent of his Shumukh perfume. Sannan ya rufe ya zaga ya shiga ya tada motar, the engine roaring to life with a deep, muffled growl. The drive was silent, cike da wani irin heavy, sweet tension. There were so many things running through Zara's mind—the weight of the city, the reality of being his wife, and the absolute rules he set back in Abu Dhabi about her being a complete housewife. Shiko Zafar, wata natsuwa ce ta ratsa shi. He was lightly humming along to 50 Cent’s 21 Questions dake tashi ƙasa-ƙasa cikin motar, his left hand firmly gripping the steering wheel yayin da hannunsa na dama yake intertwined da nata. He wouldn't let go of her hand, not even for a second, his grip firm and possessive on her skin as if anchoring her to his side forever. Suna isa Al Barari—a lush, emerald sanctuary hidden in the heart of the desert—gate ɗin ya buɗe automatically bayan yayi recognizing motar Zafar. Villa ɗin Muazzam ne, a masterpiece of modern architecture surrounded by dense tropical greenery. Anan aka sauke su Aunty Hannah da masu gyaran jiki da kuma yan matan Niger ɗinnan da Noor, yayin da ƙawayen Zara suke wani luxury hotel a cikin gari. Zafar ya kashe motar amma bai saki hannunta ba. Ya juyo ya kalli Zara da olive eyes ɗinsa dake nuna tsantsar so da sanyi, yace, “Go and get the things you need. Don’t take too long.” Daga haka Zara ta gyaɗa mai kai, ta fice daga motar tare da jan numfashi. Tana fita, Zafar ya bita da kallo through the tinted glass, wani faint smile ya subuce masa. Ya lura yadda jikinta yayi sanyi, wani irin calm nervousness ya shige ta. Duk wannan rawar kan na dā, yanzu ya koma natsuwar da take nuna cewa ta fara gane nauyin matsayin da take kai. Amma Zafar yasan Zara sarai; yasan lokaci take buƙata ta saki jikinta da sabuwar rayuwar su. And being the Silent Killer that he is, he was ready to be patient. He wouldn't rush her; zai jira har sai ta saki jikin nata, he would wait until she felt completely safe in his arms again. He watched her disappear into the villa, his heart beating with a triumph he had waited twelve long years to feel—the hunt was over, and the prize was finally his. Zara tana shiga ciki ta yi sallama, ta gansu gaba ɗayansu zaune a parlour sunata hira, hayaniyar su kawai ke tashi. The atmosphere was thick with the scent of Arabian oud and the high-pitched excitement of a bridal house. Su ba su je Bridesmaid’s Brunch ba, amma dasu akayi Spa Day, Bridal Shower, da kuma Lingerie Shower. Wannan karon ne dai suka ce ba za su je ba, preferring the intimacy of the villa. In kaga Noor a cikinsu zakayi mamaki saboda ko Zara bata saba dasu yadda Noor tayi ba; she blended in so naturally with the Niger girls, engaging in their sophisticated banter as if she had known them for a lifetime. Suna ganinta suka fara guɗa, a loud, piercing celebration knowing the groom had finally arrived to claim his prize. Noor dai sai murmushi take tana kallonta, her eyes reflecting a complex mix of emotions, wondering if she’ll ever witness this happy day for herself or if she’s destined to remain in the shadows of an unrequited love. Zara duk ta sakar musu murmushi tana ɗaga musu hannu ta wuce, navigating through the sea of expensive silks and designer bags. Yayin da suka yi ido huɗu da Noor, the air between them suddenly chilled. Zara ta watsa mata wani kallo tana cewa, “Shishshigi.” Noor dai bata kulata ba, maintaining her poise with an elite calmness; she wasn’t always ready to indulge Zara’s childish antics, especially not today. Zara na shiga cikin hallway ɗin, ta nufi upstairs zuwa bedroom ɗin Aunty Hannah. Ta buɗe ta ganta kwance kan gado tana video call da mijinta, suna hirar su in their mother tongue, her face glowing with the comfort of a long-term marriage. Tana ganin Zara, tace mishi tana zuwa, then she hung up and turned to her with a knowing look. “Har ya iso?” Zara ta gyaɗa mata kai, her heart doing a frantic dance. Aunty Hannah ta saki guɗa tana cewa, “Toh bari azo a haɗa miki ruwan wanka.” Zara ta yi saurin cewa, “Aunty, zan yi wankan a can, jirana fa yake” Wani kallo Aunty Hannah ta juyo ta mata, a look that tolerated no nonsense. “Ke don Allah cire kaya, ban son sakarci kinji.” Zara ta zunburo baki ta fara cire kayan jikinta tana ƙunƙuni like the pampered princess she is. Sanin Zara bata jin kunyar tsirara gabanta, Hannah ta girgiza kai at her niece's lack of inhibition. Just as she was about to leave the room, Zara called out, “Aunty.” Hannah ta juyo, seeing her standing there in just her intricate lace bra and matching panties, looking every bit the model. Zara tace, “Toh hakin mayen fa? Baki bani na daren ba.” Aunty Hannah ta jingina jikin kofa tana kallon ikon Allah. Ita dai bata taba ganin amaryar da bata gujewa maganin mata ba sai Zara. Babu ruwanta, shan abun ta take willingly, even the most bitter traditional concoctions. Har wasu herbs da Mommy ta ba Cindy ta gaya mata yadda zata ringa haɗa mata su shima tass Zara ke shanyewa duk da ba daɗi ne dasu ba. Duk irin wannan abubuwan Zara doesn’t joke with them; she was prepared to be the perfect wife in every sensory way possible, and she had no room for misplaced modesty. Aunty Hannah ta sake girgiza kai tana cewa, “Allah ya shiryeki, yanzu zan kawo miki ae Zara.” Daga haka ta juya ta fice. Zara kuma ta janyo wayarta ta hau kiran Zafar to tell him she had to bathe first, but his line wasn't going through—likely due to the high-security signal jammers often used around the private estates in Al Barari. Meanwhile, Aunty Hannah na saukowa ƙasa, ta nufi parlour inda yan matan suke. Ta kalli Noor tana cewa, “Noor, jeki gayawa yayanki ya shigo ciki yaci abinci, Zara wanka zatayi yanzu.” Noor ta miƙe tana murmushi, “Toh Aunty.” Ta fice zuwa compound ɗin where the matte black BMW XM was parked like a dark beast under the villa’s lights. Ta ƙarasa ta buɗe front seat ta shiga, the cool interior air hitting her skin. Zafar, who was busy on his phone, looked up and gave her a small, affectionate smile. “Noorin Yemma.” Noor gave him a quick hug, “Hey other half.” Ta ɗago tana masa her softest, most charming smile, “Congratulations yaya. Allah ya baka ikon adalci tsakanin matan ka.” Zafar ya amsa da “Amin,” before his tone shifted into that of a stern brother. “When are you going back? I wanted to talk to you and Yemma. Karim yaso zuwa ɗaurin aure you know, but Allah bai yi ba. But Noor, he went to Kâala.” Nan da nan mood ɗin Noor ya canza, the light leaving her eyes as she stared at her brother in shock. Zafar ya gyaɗa mata kai, delivering the blow with clinical precision. “He wants you back, Noor. He was pleading so...” Cikin tarar numfashinsa, Noor’s voice broke. “I’d rather die, yaya.” Cikin lallashi Zafar yace, “Calm down Noor, nobody is forcing you, you know that. Kawai dai I want you to reflect on this. It’s high time you let go of whatever it is you’re holding, Noor. Omar made it clear to Baffa since last two years that he’s over you. Kiyiwa kanki faɗa. Karim is your blood, kina tunanin mamanshi na jin daɗin ƙiyayyar da kike nunawa ɗanta? At least give him a chance, we all know Karim is the best man you could ask for. Ke ba yarinya bace yanzu fa; for how long will you be like this? Chasing a man who doesn’t want you? I don't like seeing you like this, Noor.” Noor, whose heart felt like it was being shredded by his words, couldn't take it anymore. Tears began to flow down her cheeks as she opened the car door without looking at him. “Aunty tace ka shiga kayi dinner, Zara will be taking her bath.” Daga haka ta fita daga motar tana nufar cikin gidan da sauri, her heart heavy with shattered emotions.. Bayan fitar Aunty Hannah, ɗaya daga cikin masu gyaran jikin ne ta shigo ta wuce bathroom ta haɗawa Zara ruwan wankan da aka cika da aromatic oils and traditional scents. Matar ta fito tace Zara ta shiga, Zara ta gyaɗa mata kai kawai. Bata shiga ba har sai da Aunty Hannah ta dawo da cups jere a tray ta ajiye mata a gaba. Zara dake kwance kan gadon daga ita sai innerwear tana danna wayarta, ta miƙe zaune. Nan fa ta fara ɗaga cups ɗin tana shanyewa har sai da ta shanye duka ukun tass. Daga haka ta tashi ta buɗe mini-fridge ɗin dake ɗakin, ta ɗauki soft drink ta hau sha. Bayan ta sha kusan rabi ta ajiye ta shiga ban ɗaki. Aunty Hannah dai sai binta da kallo take tana dariya ƙasa-ƙasa; tasan yau dai reality will set in. Duk wannan rawar kan, tasan zuwa gobe babu shi. Zara ta shige bathroom ta nufi gaban mirror inda tayi brush ta wanke bakinta da scented mouthwash. Ta ɗago tana kallon kanta a madubi, harda juyawa. Wani irin expensive glow fatarta take yi saboda gyaran da ta sha. In each country they visited, she explored the most prestigious spa salons. Today, she just finished her Moroccan and Turkish Hammam ritual, and yesterday she had the Versace-inspired Diamond Glow Spa treatment. Gaba ɗaya gyaran ciki da na waje aka mata; her skin felt like impossible silk, yana ɗaukan ido ga wani sanyayyan ƙamshi da ya riga ya zauna a jikinta. Ta wuce inda aka haɗa mata ruwan wankan a jacuzzi bathtub, ƙamshinsa ya riga ya gauraye ko ina. Ta cire sauran kayan jikinta ta shiga, ta fara wankan. Tsawon 30 minutes tana zaune a ciki tana chat a wayarta. Kwatsam, Video Call ya shigo ta Snapchat—Zafar ne. Tunowa da tayi yana jiranta yasa ta zaro ido da sauri ta yi picking. Fuskarta ce kawai ta nuna a screen ɗin, but he still took a sharp breath because the background betrayed exactly where she was. Zafar ya gyara murya, his voice deep and teasing. “Why are you chatting in the bathroom? Baki san ina jiranki ba?” Zara ta ɗan turo baki, “Toh fa wanka nake yi.” With a low, commanding voice, Zafar said, “Show me.” Zara ta ƙara turo baki tana maƙe kafaɗa. Zafar yace, “Come on, Princess. I just want to see if you’re actually bathing.” Zara ta bashi wani bored look, “I am a twenty-three-year-old married woman, Zafar, not some three-year-old kid.” Zafar bai san lokacin da yayi dariya ba. “Okay, married woman. Now your husband is asking you to tilt the camera down. I want to see my gift—the full package.” Zara ta sake maƙe kafaɗa, kafin tayi magana aka turo ƙofar bathroom ɗin ana salati. Zara ta zaro ido ta kashe wayar ta jefar cikin ruwan tsabar rikicewa. Aunty Hannah dake tsaye tana kallonta tace, “Zara! Wallahi ki rage wannan rawar kan. Yanzu uban mi kika nuna masa a video call ɗin?” Zara ta turo baki tana kawar da kanta gefe. Nan fa Aunty Hannah ta hau ta da faɗa akan ba’ayi wa namiji rawar kai haka. Zara dai bata kulata ba, ta ciro wayarta ta miƙe tana fitowa daga cikin ruwan completely naked. Aunty Hannah dai sai faɗa take har da sako maganar da Zara ta taɓa yiwa Zafar akan Omar. Zara ko jinta ba ta yi ba; ta nufi towel warmer, ta ɗauki towel ta hau goge jikinta. Tana gamawa ta fito, Aunty Hannah na biye da ita. A bedroom ɗin ta tarar da mai gyaran jiki tana jiran ta da Shamla a hannunta don yin Dukhan (Smoke Bath). Zara ta ƙarasa ta zauna, fuskarta a ɗaure don haushin faɗan da Aunty Hannah ke mata. Wani daddaɗan ƙamshi na Acacia wood and sandalwood ya cika ɗakin yayin da hayakin yake shiga fatarta. The heat was soothing, radiating upwards and relaxing every nerve in her body. Adon kowace ritual, she preferred this one; it felt like a warm, aromatic embrace that made her skin feel incredibly supple and left an addictive, smoky musk on her body that no designer perfume could ever replicate. Zara lumshe idonta tayi, feeling the intense warmth creeping up. Wani irin daddaɗan zafi ne yake ratsa ta ta ƙasanta, a sensation so deep it felt like it was preparing her entire being for the night ahead. The heat was pulsating and therapeutic, making her feel incredibly sensitized and "ready" in a way she couldn't explain. Every inch of her felt soft, primed, and deeply fragrant, as the smoke worked its magic, tightening and soothing her skin simultaneously. It was a raw, feminine power she felt surging through her, making her toes curl in the heavy silk of the Shamla. Kusan minti arba'in da biyar aka ɗauka ana wannan aikin, hayaƙin Acacia wood yana ratsa kowace kafa ta fatar jikin Zara, yana barin wani irin bronze glow mai ɗaukar ido. Tana miƙewa daga kan turaren wutar, wayarta ta yi beeping. Ta duba, sako ne daga Zafar: “I’m coming in to get you.” Wani sanyayyan murmushi ya subuce mata, zuciyarta ta buga. Ta nufi kan gadon inda kayan da zata saka suke a shirye. Bayan masu gyaran jikin sun fita, daga ita sai Aunty Hannah wacce ta kwaso wasu turaruka wanda sukayi saurin gaurayewa da ƙamshin hayaƙin Dukhan ɗin da jikinta ya riga ya sha. Nan ta dire mata su a kan gado; tun daga kan kulakcham kala kala, Khumrah mai sanyin ƙamshi, zuwa oil perfumes masu tsadar gaske da aka haɗa mata bespoke musamman a Dubai. Akwai kuma wani Bespoke Kabbasa Set daga gidan Hind Al Oud—the "Haute Couture" of Emirati fragrance. Zara ce ta zaɓi kowane note na turaren, mixing deep agarwood with sweet musk, because she knew exactly what scent would drive her man crazy. Bayan ta shafa waɗannan mayukan ƙamshin da suka sa fatarta ta ƙara zama tamkar silk, ta shafe jikinta da khumrah, ta hau saka La Perla white lace bra ɗinta da matching panties, kowane zare na lace ɗin yana nuna tsantsar Old Money luxury. Aunty Hannah ta matso tana miƙa mata wani red waist beads mai ɗaukar ido, tana cewa, “Cire na jikinki kisa wanga.” Zara ta kalli jigidan tana ɗan yatsine fuska, “Nawa na gold ne Aunty, wannan—“ Bata ƙarasa ba Aunty Hannah ta katse ta, “Wannan kuma kinsan na menene? Ban shirme Zara, yi maza ki cire na jikinki.” Zara ta kalleta cikin tuhuma, her voice dropping to a whisper, “Is it an aphrodisiac?” Aunty Hannah ta harare ta cikin wasa, “Toh da hwa? Wanga yafi duk wani abu da kika sani.” Zara ta ɗan zaro ido tana murmushi, tuni tasa hannu ta karɓa ta saka. Yayi mata cib-cib a ƙugunta, the red beads popping against her glowing skin. Tana kallon Aunty Hannah tace, “How did you know my size?” Aunty Hannah ta yi dariya, “Muazzam yace mun jikin mu guda, so size ɗina nayi miki.” Zara immediately narrowed her eyes, saboda tasan Aunty Hannah ta fita jiki sosai. Ganin yadda Zara ta ɓata fuska kaman zata yi kuka tana kallon kanta a dressing mirror, Aunty Hannah tayi dariya tana cewa, “Ke wasa nikai miki, maza ki shirya mijinki na jiran ki.” Da sauri Zara ta juya ta ɗauki wata White Silk Abaya from Mauzan. The fabric was exceptionally lustrous, encrusted with thousands of Swarovski crystals that shimmered like a galaxy under the room lights. Ta yafa mayafin a kanta simply, sannan ta sanya René Caovilla silver 3-inch heels, which are famous for their diamond-strung snake straps that wrap around the ankle. Daga haka ta fesa bespoke kabbasa spray ɗinta from Hind Al Oud’s—wanda ya mayar da ƙamshinta wani irin royal aura. Aunty Hannah dai sai kallonta take tana murmushi, ta miƙa mata wasu Gold Van Cleef & Arpels earrings tana cewa ta saka. Zara ta karɓa ta saka, batayi kwalliyar komai ba, kawai ta shafa Dior Addict Lip Glow Oil (Cherry flavor) wanda ya bar lips ɗinta suna walƙiya da daddaɗan ɗanɗanon fruit. Aunty Hannah ta nufi mini-fridge ta ɗauko wani herbal tonic acikin roba da straw tana miƙa mata, “Shanye wannan.” Zara ta karɓa ta fara sha, tana jin yadda sanyin maganin yake ratsa ta. Suka fito daga ɗakin tare, yayin da wata mai aiki ke biye dasu tana janyo Louis Vuitton Horizon suitcase ɗinta. Suna saukowa ƙasa, kowa ya bi su da kallo; nan da nan aka fara guɗa ana hyping Zara. Ita dai sai wani lallausan murmushi take yi, tana taku ɗai-ɗai cikin class da natsuwa. Noor was just smiling from a distance; ita kanta tasan shikenan, yayanta kam sai Allah, saboda irin gyaran da Zara ta sha gaban idonta ba na wasa ba ne. The transformation was breathtaking; she looked like a masterpiece carved out of marble and light. ’Yan matan duka suka miƙe suka rufa musu baya wai za su raka amarya; A suka fara waƙar al’adarsu ta Sahra suna tafi cikin nishaɗi. Suka saka Zara a tsakiya yayin da Aunty Hannah ke riƙe da hannunta. Noor dai ba ta bi su ba, she just leaned against the pillar, watching her brother’s destiny unfold. Haka aka fito compound ɗin, inda Zafar yake zaune cikin mota, yana kallonsu ta tinted glass ɗin. Da sauri ya buɗe ƙofa ya fito, ya zagayo ya buɗe mata front seat. Duk da cikin jerin ’yan matan nan guda goma sha uku da ke tafe suna waƙa, Zafar could spot his wife immediately. Tun daga nesa yake hango kyalkyalin Swarovski crystals na jikinta, and the closer they got, the clearer he could see her—she looked like a vision in white. Haka suka ƙaraso; Aunty Hannah ta sa ta a gaban seat ɗin, ta gyara mata rigarta sannan ta matsa baya kaɗan. Zafar ya rufe ƙofon cikin nutsuwa, ya kalli Aunty Hannah yana murmushi with deep gratitude yace, “Merci beaucoup pour tout.” Aunty Hannah ta yi murmushi, tana kallonsu da wani irin alfahari tace, “Prenez soin de vous deux.” Daga haka ta juya. ’Yan matan dake ta window suna tsokanar Zara, wasu kuma na kallon Zafar; shi dai sai murmushi yake yi har kumatunsa sun fara ciwo don murna. Har sun juya sun fara tafiya, Zafar ya kira su suka juyo. Ya kalli ɗayar da take masifar yanayi da Zara amma da alama ta girmeta, yayi mata alamar ta zo. Tana zuwa yace, “comment t’appelles-tu? Tana murmushi tace, “Meryem,” ta faɗa with her heavy Tuareg accent. Zafar’s eyes immediately softened jin sunan maman Zara gareta. Kansa ya gyaɗa kafin ya buɗe back seat ya ciro wani briefcase ya rufe motar, yana miƙa mata yace, “Allez faire du shopping avec vos sœurs.” With slight hesitation ta karɓa tana murmushi sosai, “Merci infiniment!” Zafar ya isa motar ya buɗe, yana zama a driver’s seat. The engine roared to life with a sophisticated purr. Yana tada motar, ya fice daga villa ɗin, leaving the noise of the celebration behind for the quiet, aromatic luxury of the Dubai night. A cikin motar, the scent of Zara’s Dukhan mixed with Zafar’s expensive cologne created an atmosphere that was thick with unspoken promises.