Free chapter · Read without an account
PAGE _______ 70
Kuɗaɗen suka ɗauka tare da shigewa ɗayar motar ciki harda driver container, suka juya suka bar iyakar. Kusan 10 minutes aka buɗe container wasu mutane ne su biyu duk fuskokin su a rufe ba abinda ake iya gani sai ƙwayar idanunsu, Mutum ɗaya suka fitar daga container suka sanyashi gaban motar sannan suka ja suka Miki hanyar da tabi left side nasu suna tafiya akan dogon layin, dan su basu ƙetara iyakar ba su kuma basu cikin ƙasar Nifaz, sun dai raba hanya, a haka sukayi tafiya me ɗan nisa sannan sukayi parking, wasu mutanan ne masu irin shigarsu suka zagaye container. Sauqowa sukayi tare da buɗe mutanan suka firfito dasu sannan suka tisa su a gaba .
Sake nutsuwa su Ash sukayi tare da danne Na'urar sauraron sauti dake kunnuwansu yadda zasuji maganganunsu dakyau, sunyi tafiya me ɗan nisa da ƙafa dan har sun shiga desert kafin su ja su tsaya ɗaya daga cikin mutanan ya ce, "Ai inaga munzo ko?".
Ɗayan ya amsa da, "Yes zamu iya tafiya, mun gama namu aikin"......... Juyawa sukayi suka fara tafiya, sake nutsuwa su Amjad suka yi ko ƙwaƙwaran motsi basa yi sai dai me, kafin ƙiftawar ido komai yayi disconnecting daga kan GPS, video feed da kuma sound ɗin, da sauri Amjad ya tura kujerar sa baya tare da tashi ya matsa wurin su Ash saidai su ma hakan take a wurin su. "Ya akayi haka?"......... Ya tambaya ƙirjin sa na dukan tara tara.
Ashley ta ce, "Ko dai sun gano ne?"......... Kiara ta amshe da, "Akwai matsala fa, dan mun rasa su" .
Dunqule hannu yayi ya nausa a iska tare da saurin ɗaukan wayar sa yayi Kira a headquarter ɗin su ta ƙasar Nifaz ya bada sanarwar a aika musu da sojoji kan iyaka a kuma rufe boarders ɗin ƙasar gabaɗaya, yana gama faɗa bai tsaya sauraron answer ba ya kashe ya kira Juraysh, ringing take amma ba'a ɗaga ba jijjiga wayar ya shiga yi yanajin kamar ya tashi sama. Da sauri kuma ya danna wayar ya kashe lokacin da Juraysh ɗin ya amsa saboda kwata kwata ya manta cewa a gida basu san waye shi ba, juya akalar kiran yayi zuwa headquarter ɗin tasu ya sake shaida musu a tsayar da duk wasu kaya da zasu fita ta ruwa daga ƙasar Nifaz ɗin sannan ya kashe Kiran ya wuce ya ɗauko sectra tiger smartphone ɗin sa ya kunna yayi connecting da VPN ɗinsu, kira yayi zuwa headquarter ɗinsu ta Brussels amma bai samu Sir Richard ba ance suna meeting, Sir Johnson dake kan layi Amjad ya shaidawa halin da ake ciki saboda yana so su ma su zama a ankare a kuma shaidawa duk sauran countries da abun ya shafa domin su baza jami'an su.
Cire na'urar sauraron sauti dake kunnensa yayi ya wurgar cikin takaici da baƙin ciki ya sake komawa kan computer ɗin ya cigaba da ƙoƙari ko zaiyi connecting amma ba abinda ya samu, ba tare da ya ɗago ba ya ce, "Ash Kira Philip kice babu wani second option da za'a yi trying?".........." Okay"....... Ta faɗa tana me dannawa Philip kira saidai amsar da ya basu itace Babu, dake a handsfree tasa yaji komai kafin yace wani abu sectra tiger smartphone ɗin sa ya fara Ƙara ɗagawa yayi ganin daga Brussels ɗin ne, cikin faɗa sir Richard ya ce, " Agent Amjad ya akayi haka ta faru ? Yanzu ake sanarmin saqonka, meke faruwa?".
"Sir an samu matsala ne, mun rasa mutanen Kuma plan ɗin mu ya rushe ".
"Whatttt Kun rasa mutanen fa kace, Amjad ya zakayi wasa da rayukan jama'a, ai anyi dakai cewa zakayi amfani dasu ne wurin kama me laifi ba wai ka salwantar da su ba ".
"I'm sorry sir but dole ne mu rasa wasu rayukan domin ceto wasu, Ina buqatar a nema min izinin shiga Bangkok yau domin aiwatar da wani bincike, shi ne kawai second option ɗin da nake dashi sir kuma in sha ALLAH bazan bari wannan damar ta kauce min ba".
Kashewa Sir Richard yayi ba tare da ya bashi amsa ba, yayin da shi kuma ya juya zai fita Ash ta ce, "But Amj........" Tarar numfashinta yayi da cewa, "But what Ash, we don't have a choice , we have to go for the plan B and I have to do it myself, idan wani abu ya samu mutanan nan, zan ɗaura alhakin su a kaina ne cox I was the one that brought up this idea dole ne duk yadda za'ayi na je Bangkok domin ganin nayi Amfani da plan B ɗin nan, just pray for me. In kun fito ku ja curtain ɗin sannan ku sanar dani ta waya saboda na rufe ɗakin. Sannan kuma zaku cigaba da zama a gidan nan kuji da sauran binciken da ya kamata ga Philip sannan ga Widad nasan zuwa gobe shi ma zai dawo ku cigaba da aikin tare ni Kuma zanje can naga yadda za'ayi, in sha ALLAH za'a dace, kuma zamu dinga communicating duk abinda ake ciki har na dawo".......... Yana kaiwa Nan ya juya ya fita yana sanya wayarsa a silent saboda Juraysh dake dawo da kiran da ya masa ɗazu, gidan gabaɗaya ya bari ya nufi Bluevielle wurin Nayrah.
KAKA TSARA KAKA, MY PEOPLE HMMM TO NIMA NA RASA ABUN CEWA, GA FA AMJAD YA SHIGA TSAKA ME WUYA, TO WAI MA YA AKAYI AKA RASA MUTANAN? KO DAI SUN GANE SHIRIN DAKE JIKIN MUTANAN NE? IN SUN GANE WANE IRIN MATAKI SHADOW ZAI ƊAUKA AKAN AMJAD? YA KUKE GANIN AMJAD ZAIYI DA NAYRAH? ZAI SANAR MATA WAYE SHI NE KO YA YA? GASHI KUMA YA SHIRYA TAFIYA BANGKOK DOMIN HAƊUWA DA YARINYAR SHADOW ME KUKE TUNANIN ZAI FARU? SHIN DA GASKE YA' CE GA SHADOW ƊIN? ZAIYI NASARA KUWA? SHIN DA GASKE ACE YA RASA RAYUWAR SA NE AKAN CASE ƊIN SHADOW?.
DUK WANNAN AMSOSHIN NAKU ZAKU SAME SU NE A STEP 2, KU DAI KARKU BARI A BAKU LABARI DOMIN BAMA A FARA WASAN BA.
_______________Zaune suke su duka a ƙayataccen falon baqi na gidan Julaybin ɗin gabansu abubuwan motsa baki ne iri iri a gabansu. Nuhail ne ya ce, "Mr kanar ya kaga yanayin ƙasar tamu?"
Cikin gurbatacciyar turancin sa me haɗe da Indian accent ya ce, "Whl ƙasar ku akwai kyau sosai, mutane naku akwai karamci".
"To Masha ALLAH, batun business na crude oil da zamuyi dakai wanda kazo a Kansa, already munyi magana dakai ka buqaci kanaso kazo, mu da munso daga can ma idan muka gama komai sai a aika ma kamar yadda ake yi amma kace sai ka zo da kanka, to Alhamdulillah yau gaka a ƙasar mu, ya maganar tamu?"........ Shuru Mr kanar yayi kafin ya ce, "A gaskiya farashin ku ya min tsada" .
" Kamar ya ya ma tsada bayan kuma mun gama magana dakai kan wancan farashin, ka sani muna da mutanen da zamu bawa amma muka keɓance muka baka"......... Faɗar Julaybin.
"Gsky Mr Julaybin wannan shine gskyr magana ku sake shawara".......... Nuhail ne ya ce, "Mu ba wata shawara da zamuyi kai dai zamu bawa lokaci kayi shawara, kasan dai yadda akeyi da refinery ɗin mu a kasuwar duniya".
"Shikenan to, zan sake dubawa"......... Mr Kanar ya faɗa yana tashi ya musu sallama ya fita. Awais ya ce, " Kuji da ALLAH mutum kamar daƙuwa an taimake shi yana neman ya nunawa mutane iya shege, wa ma ya shige masa gaba ya zo ƙasar? shi ma fa riba zai samu ai mai gidansa zai sayarwa".
"Rabu dashi in ma zugashi ake zai dawo ne".......... Julaybin ya amsa ba tare da damuwa ba dan yasan duk inda Mr Kanar ɗin yaje sai ya dawo.
________________"Hajiya Akwai matsala domin maganar da nake miki kotu ta kamo mutanan nan kuma whl kinsan in sukaji Matsi komai zai iya faruwa".
"To yanzu miye abunyi? Kuma ina shi sani yake?".
"Sani ai tuntuni ya gudu saboda yasan zaki neme shi, an tabbatar min kwanan sa huɗu kenan ba'a ganshi ba".
"Ya kamata ka samo mana mafita domin in asirin mu ya tonu whl mun shiga uku, ga tsinuwar jama'a da zamusha..........." Katse ta yayi da faɗin, "zaki sha dai, ni ai ba wanda ya san da hannu na a ciki ballantana ya san fuskata, kuma abinda baki sani ba har Farshad yaron ƙasim datti da aka kashe suna tunanin da sa hannun Amjad, ni ne nan ba wani ba haka zalika hatsarin motar da Nayrah tayi Ni na shiryashi kuma ban so ta fita da ranta ba dan so nayi ta mutu a wannan accident ɗin, saidai duk wannan abun ba wanda yasan dashi saboda na iya taku na"........... Cikin tsantsar damuwa ta ce, "Amma shi ne ka barni na zira jikina har haka "......... Dariya ya kwashe da ita kafin ya ce, "Da kinsan baki shirya ba kika fito, ai ba zancen kare wani a wannan harkar, karki manta sharri fa kika fito ƙullawa ba alheri ba sannan kiyi tunanin wani ya taimaka miki dan ya hango zakiyi tuntube ? Inaaaa ai ba wannan bayanin".
Ajiyar zuciya ta sauke cike da fargaba da kuma tunanin abinda kaje yazo ta ce, " To naji amma dan ALLAH duk yadda za'a yi, kayi kar asiri na ya tonu whl zan tozarta fiye da tunaninka, ni ko ma kashe su ne ayi kawai in dai asiri na zai rufu".
"Ba fa zai yiwu a kashe su ba domin suna hannun hukuma " .
"Innalillahi wa Inna ilaihir rajuun".........Ta faɗa tana zubewa a cikin kujera gabaɗaya duniyar Hajijiya take mata.............
A bangaren su Hajj zawaad kuwa tuni ya gama da Mr kanar saidai yaqi yadda ya barsu su keɓe da Sir juwaira, komai za'ayi yana tsakiya. Sir Ahuoyzah kuwa ce masa yayi Mr Kanar yaqi sauraron sa ma wanda hakan ya sa ya tashi hankalin sa sosai ya shiga neman mafita ido rufe.
ANA WATA GA WATA, SHI KUMA WAYE WANNAN DA YACE SHI YA KASHE FARSHAD SHI KUMA YA SHIRYA ACCIDENT ƊIN DA NAYRAH TAYI? SANNAN KUMA WACECE WANNAN HAJIYAR DA SUKE AIKATA KOMAI TARE? YA ZA'A ƘARE TSAKANIN AWAIS DA MR KANAR? ME ZAI FARU IDAN SIR AHUOYZAH YA GANE HAJJ ZAWAAD YACI AMANAR SA?. WATO MY PPLE HARGITSIN DAKE CIKIN STEP 2 MA BAZAI KWATANTU BA .
-----------------------√
SWORD OF FIRE KINGDOM 🔥
Zaune suke a makeken falon nasu da aka shafe rabin sa da wani irin painting na tigers. "Azal ina so ki je England ki kaiwa queen Elisa ziyara, tunda Anoosha bata nan da sai kuje tare"........ Azal ce ta ce, " Inati ni fa abinda na lura gabaɗaya Anoosha bata son abubuwan sarautar nan ne saisa ma bata son zama tare damu, saboda tasan in dai tana masarautar nan dolen ta ne zaki saka ta ciki a Matsayin ta na little princess".
Murmushin ƙasaita Queen Hirut hirut tayi kafin ta ce, "Rabu da ita zan yiwa Sharutta magana a kanta ko tana so ko bata so dole ta zauna ta dinga kama Miki wasu abubuwan, saboda daga ke sai ita abun bauta ya bani, Azal ko ruhi na ya tashi zuwa sama ku tsaya sosai da ƙafarku kuma karku sare har sai kun ƙarɓo ƴancin mu ta hanyar ƙwatar yankin mu dake Aurellon".
"Baza mu taɓa saduda ba Inati kuma itama Anoosha zan neme ta da kai na saboda mu kaiwa Queen Elisa ziyara tare saboda tafi jin daɗin abun".
Jinjina kai Queen Hirut tayi kafin ta ce, "Ina alfahari dake Azal abun bauta ya sanya miki albarka".
"Mesgalehu (thank you)".......Azal ta faɗa tare da miqewa sannan ta ce, "Zan zagaya gari inati domin naga meke wakana"......... Jinjina mata kai tayi alamar to, daga haka ta juya ta fita tare da Simba da duk inda ta sa Kafa yana biye da ita.
Tana fita daga falon fadawanta na musamman suka rufa mata baya, giwa guda ɗaya ce a ƙofar bangaren Queen Hirut ɗin dan haka ita kaɗai ta kama ta ɗale su kuma suka bita a ƙafa, haka suka dinga zagaya masarautar tasu har suka zagayo ta wurin Dutsen Kurangina, sauka tayi daga kan giwar taje ta tsugunna gabansa tayi yan surkullensu sannan ta miqe ta baro wurin, zagayawa tayi ta fara tattakawa kan dutsen har ta hau can qololuwa tana kallon masarautar tasu kafin ta juya bayanta, zubawa wurin ido tayi can kuma ta juya ta yafito ɗaya daga masu take mata baya tare da tambayar, "Meke faruwa a can ?"....... Sunkuyar da Kai yayi kafin ya ce, "Haisha'an ne da mutanan sa".......... Wani mari ta tsinka masa da bayan hannu kafin ta ce, "Uban waye shi da har zaka wani ce min Haisha'an ne da mutanan sa, shi kansa ba komin komai bane da har zai ajje wasu a ƙarƙashin sa, tukunna ma waya bashi izinin fita daga masarautar saboda ai can ba yankin mu bane?"......... Yana dafe da kumatun sa ya ce, "A gafarce ni li'iliti, na tuba"......... Tsaki taja tana hararar inda su Haisha'an ɗin suke kafin ta fara gangarawa don isa garesu.
Haisha'an yana zaune ne daga shi sai dogon wando saboda har lokacin ciwukan jikinsa basu gama warkewa ba, gefen sa omaine ne da kuma wasu daga cikin bayin masarautar da zasu kai su goma, sun kunna wuta da ƙirare suna jin ɗumi hannayen su ɗauke da Alqur'ani me girma, daga can gefe kuma wasu mutum biyar ne zaune suna hira haɗe da zane zane akan lallausan farin yashin dake wurin sai dai kuma suna sauraren karatun nasu amma da alama su ɗin har yanzu basu karɓi musulunci ba.
Omaine da ya fara hango ta a razane ya ce, "Haisha'an bayan ka li'iliti Azal ce fa take tahowa"........ Juyawa yayi dan tabbatarwa yana ganin ta ya miqe yana faɗin, "Duk ku ɓoye fuskokin ku baza ta gane ku ba tunda ba uniform bane a jikinku"........ Ya faɗi haka yana tashi ya ƙarasa Wurin ta, ja tayi ta tsaya irin tsayuwar rashin mutuncin nan a gadarance ta wani bubbuga ƙafa, gashin ta da iska take kaɗawa yana ta dawowa kan fuskarta, janye gashin tayi daga kan fuskarta ta tare da ƙare masa kallo a ƙasƙance ta ce , "Kai waya baka ikon tara mutane anan, tukunna ma uwar me kukeyi da ku ka tsallake cikin masarauta kuka wuto nan? Da izinin wa kuka fito?".
"Sarki baya buqatar izini domin shiga faɗarsa, saboda nan ɗin nima fada tace"......... Ya faɗa yana sake ɗaure fuska dukda dama fuskar tasa shi ko da yaushe kamar an aiko masa da saqon mutuwa.
"Whatttt, waye kai? da har zaka sanyawa tosasshiyar ƙwaƙwalwar ka tunanin mallakar wata fada, ko fadar aljanu baka da matsayin mallaka ballatana ta mutane, matsiyaci bawa ɗan baiwa jikan bayi....."....... Ai kafin ta ƙarasa ya kaiwa maqoshin ta wani irin damƙa gabaɗaya ya fita hayyacin sa ya wani irin juyewa, "Wace ke da zaki shigo yankina kice zaki ɗaga min murya har ma ki zage ni, yau sai na kasheki, sai na kasheki naga uban da ya tsaya Miki, in kasheki in kashe banza dabba marar amfani". Ya ƙarashe yana huci.
Qaqari li'iliti Azal ta fara tare da ƙoƙarin ƙwace kanta ta hanyar Amfani da ƙarfin tsafin da suke dashi a jikinsu saboda irin haka amma ina ta ƙasa saboda riqo ne ya mata bana wasa ba, idanun ta duk sun firfito. Masu tsaron ta kuma dukkansu suna daga kan dutsen suna kallo dan basu da izinin gangarawa wannan wurin saboda iya kan dutsen nan iyanan ne iyakar masarautar su, kuma tsallaka shi zai zama taka dokar Masarauta ne, shahada ɗaya daga cikin su yayi zai sauka saidai taku ɗaya yayi Haisha'an ya wurga masa wani kallo ai ba shiri ya juya har yana kokarin suɓutowa .
Cikin shaƙaƙƙiiyar Muryarta dake neman daukewa ta ce, "Sim...Simba"....... wani tsalle Simba yayi ya dira har saida kura ya tashi a wurin tare da yin wani ƙara me sauti ya shiga zagaye su amma ya kasa matsawa kusa da Haisha'an ɗin da ya ɗau alwashin barwa Queen Hirut saqo akan ƴar ta Azal...........
TO FA MEKE FARUWA KUMA? GA FA HAISHA'AN YANA ƘOƘARIN KASHE UWAR MASU GIDA THE GREAT PRINCESS OF SWORD OF FIRE KINGDOM. ME HAISHA'AN KE TAƘAMA DA SHI NE WAI? IYAKAR DA MASARAUTA TA HANA ƘETARAWA SHI YA ƘETARA HAR YANA IKIRARIN FADAR SA CE , LALLE AKWAI TASHIN HANKALI. ANYA BASHI BANE SHADOW KUWA🤔 TO BA RUWANA KAR AJE A SANARWA AGENT AMJAD NACE KU DAI MU HAƊE A STEP 2
---------------------√
Dariya yake irin tasu ta manya kafin ya ce, "Ai ranka ya daɗe yanzu rabi da ƙwatan mutanen dake ƙasar Nifaz Hankalin su kaɗan ne daga mata har maza saboda ƙwayoyin da muka shigo musu dashi sunyi matuqar tasiri dan maganar da nake ma yanzu duk inda muka kaɗasu nan zasubi, babu wasu masu nutsuwar da wai in wani abu ya faru zasuyi zurfin tunani domin gano dalilin assasa shi instead ma sai kaga sun maida hankali kan wani abun da bashi da muhimmanci, kaga ɗalibai suna sha a matsayin maganin da zai sauqaqa musu karatu ta hanyar ɗauke musu gajiya da hana su bacci, ma'aikata ma haka, matasa masu zaman banza tare da yan matan dake cikin damuwa, a ganinsu hanya ce da zata sauqaqa musu basu san kuma mune suke sauqaqawa ba".
Girgiza kai babban mutumin dake zaune yayi kafin ya ce, "Munsa hannu a project ɗin nan na farin da za'a kawo domin a bi gonaki a sake su dan haka suna hanya ya kamata ku shirya da mutanan ku yadda abubuwan zai wakana akwai Budget me ƙarfi da za'a rarraba dan wannan ba irin wancan bane, saboda a yayin da duk amfanin gonakin su ya lalace dole ne zasu haqura su rungumi abincin waje da muhimmanci, dama kuma kaga noma da kiwo na ɗaya daga cikin abinda zai yi wahalar kawarwa amma yanzu da zarar an kawar dasu sauran abubuwan zasu zo da sauki".
"Yaushe kayan zasu iso ?"......... ɗayan ya tambaya. "Nan ba da jimawa ba dama suna jira ne amfanin gona ya gama tsiro wa, amma nasan zasu sake neman mu, so zamu zama cikin tsammanin su".
WANNAN SHI NE ANA WATA GA WATA, SU WAYE WA'ANNAN? DAGA INA SUKE ƘARƁAR WANNAN UMARNIN ? MEYE GOAL ƊIN SU NA YIN HAKAN? WANNAN AIKI NASU ZAI YIWU KO BA ZAI YIWU BA ? IN BAI YIWU BA WAYE ZAI DAKATAR DASU? DAGA INA ZAI FITO? MY PEOPLE HMMM CAKWAKIYAR TANA STEP 2, DAN ZAKU SHA RUWAN MAMAKI, TUNANIN KU ZAI JUYA FROM LEFT TO RIGHT, ABUBUWAN DA BAKUYI ZATO BA ZASU FARU, ZUKATA ZASU RAUNANA, AKWAI DISAPPOINTMENT SOSAI AMMA KUMA ZAKU NISHADANTU ZAKU MA KU ILMANTU KU DAI KU KASANCE TARE DANI.
*TO MY PPLE YANZU FA WASAN YA FARA, YANZU NE AINAHIN BLOOD CROWN ZAI ƊAU SAITI, SAI DAI KUMA STEP 1 YAZO GANGARA, DUK KUMA ABINDA ZAKU GANI A YANZU SHIMFIƊA NE KAWAI, AINAHIN GUNDARIN LABARIN YANA STEP 2. STEP 1 NE KAWAI FREE STEP 2 ZUWA ƘARSHE PAID NE AKAN #500 KACAL, KU HANZARTA KUYI PAYMENT KAR A BARKU A BAYA, DAN BAMA A FARA KOMAI BA ABINDA KE CIKIN STEP 1 BAIFI KA SANYA COKALI A KOGI DOMIN ƊAIBO RUWA BA. KU DAGA JIN SUNAN KUNSAN AKWAI RIKITA RIKITA, HARGITSI, TASHIN TASHINA, SARQAQIYA DA KUMA ZAZZAFAR ƘURA. KU HANZARTA KUYI PAYMENT, 2356673754, RUKAYYA AHMAD MUHAMMA UBA BANK . SAI KI TUROMIN EVIDENCE TA WANNAN NUMBER ***.*
SAI MUN HAƊU A STEP 2.