Free chapter · Read without an account
Chapter 32
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
⚫ *BOOK 1*⚫
⚫ _PART 32_⚫
Shekara ashirin da biyar da suka wuce.
2001
A lungu take tsaye lokaci zuwa lokaci take leƙawa kamar mai jiran bullowar wata ko wani. Wata nurse ce ta nufota lullube da zani fari a hannunta,tana zuwa ta miƙamata itama tana waige waige.
"Gashinan bata cikin hayyacinta na ɗaukota,amma bari na koma kar aga bana nan a samu a matsala,kaman fah wata naƙudar ma take inaga ƴan biyune ƴaƴan"
"Ƴan biyu,dama tasan ƴan biyune a cikinta,ko shima zaki kawomin shine inta haihu,ai na ɗau aniyar saina yaƙi Alhaji Salihu da jininsa,wlh zaisan ni yayiwa butulci. Rainon ƴaƴa dama ba wani abu bane a gareni,dan haka kawai cikin yaran da zan hora zan jefasu"
"Ahah Hajiya Zakiyyah wannan ma nayi matuƙar ƙoƙari saboda kuɗin da kika bani bazan iya tsallakewa ba,kawai kije da wannan ɗin nima abin yazomin da sauƙi,tunda dama batasan ƴan biyu bane shikenan bazan faɗa ba"
Tana gama faɗin haka ta koma ɗakin haihuwar da sauri itama ta lullube yarinyar sosai tabi wani lungun tabar asibitin dama garin gabaki ɗaya,fuskarta ɗaukeda murmushin ɗaukar fansa.
Tsohuwar sakatariyar baban su surayyane,tafito yawonta ta samu aikin,tunda ta ɗora idonta akansa taji nan duniya so take ya aureta,ko kuma koda dadirone yayi da ita,ganin take takenta yasa ya koreta kuma yayi mata iyaka dakansa,har ya ƙirata da sunan karuwa,hakanne yasa tayi alwashin sai ƴar sa itama tayi karuwanci indai tana raye. Hakanne yasa ta bibiyi matarsa ganin tanada ciki,tabiya kuɗi aka bata ƴar a lokacin da ko uwar data haife ta batasan mai ta haifaba.
Kwaci tashi asarar mai rai,Jurayyah ta tashi cikin hali na matsatsin rayuwa da kuma jimrar wahala,yayinda a ɗaya bangaren Surayyah ta tashi cikin gata dakuma tarairaya,Surayyah batasan da wanzuwar Jurayyah ba,amma babu wani abu na rayuwarta da ita jurayya batasani ba. Domin muraran Zakiyya wacce suke ƙira da mommy,take rainonta cikin ƙiyayya Na ahalinta,tana nuna mata laifinsu ne yasaka ta tashi a haka. Yara biyar ta raina a tare ciki harda ƴarta zeesha wacce saurayinta yayi mata cikinta yatafi ya barta. Muraran take koyamusu yanda zasu zama tantirai,a cewarta sai sun zama jan wuyoyi kafin zasuyi rayuwar da babu mai tanƙwarasu. Saidai duk da haka abubuwan wahala bata saka ƴar tata,hakanne yasa Jurayyah da sameera suka fita taurin rai, itakuma tafisu kwaɗayi bin maza da son abunsu, sai abun yafara damum zakiyya ganin duk halayyar da take son ƴar tata tayi shi Jurayyah takeyi,jaforanci wayo zuriya sannan namiji bai isa ta sauƙar da kanta dominsa ba,wai ma a hakan tana shan baƙar azaba daga wajen uwar tasu saboda horon da takeyi mata da tsafi. Ita kanta tasan badan taammali da aljanu da take ba da tuni Jurayyah tafi ƙarfinta.
Ganin abin ƴar tata ya fara yawa tun a ƙananun shekaru yasa lokaci ɗaya ta kaita belgium kuma tashafe zancenta babu shi babu almarsa,sai su Jurayyah dasuka cigaba da gagarambarsu. Bayan gama prymaren su ne Jurayyah wacce ake ƙira da Rayyah tanace kan lallai ita boarding zata tafi,lokacin itama zakiyya sun buɗe wata sabuwar ƙungiya ƴan gang ɗinsu ta samun kuɗi,suna shirye shiryenta a India,bata fiye zama ba dan haka ta yarda da turata boarding ɗin.
Ana gobe zasu tafi tashiga katafaren ɗakin uwar tasu, akan zata karbi sauran kuɗin da zasuyi shopping na tafiya makaranta,dan yanzu kam hadadar kuɗine ta ko'ina a gidannasu. Kuma kowa yasani suma sunsan kuɗin jini ne. Domin wani lokacin a gabansu ake wucewa da yara kuma ba'a taba fita dasu sun hallaka,tun suna tsorita har suka saba. Ka wasu kalamai da intayi meeting a gida ake kwana ana karantawa har gari ya waye,don tana ɗaya daga cikin manyan ƙungiya.
Ita kanta zeesha dasuka nema suka rasa rana ɗaya zancen da tayi musu duk ƙaryane,neman kungiya tayi a karon farko domin itace abinda tafiso fiyeda komai,sai tasaka wani aljani ya biye ruhinta da kamanninta ta yaudaresu, Da zummar inta shayar da dodo jini mai yawa bazai nemeta ba.
Wani akwati tagani akan drawerta,da alama saƙo aka kawomata ko buɗewa batayi,don a daure yake da wani farin ƙyalle.
Har zata fita saikuma taje wajen akwatin ta saka hannu zata warware ƙyallen,tana tabawa taji kaman wani abu ya caketa a jiki,saurin ɗaukewa tayi tana kallon inda jini yafito,tsotsewa tayi da gudu tabar ɗakin.
Ta manta da abinda ya faru koda suka isa makarantar sai taga jan akwatin a jakarta,bata kawo komai a ranta ba ta ajiyeshi a locker.
Farkon zuwansu tayi wata ƙawa inayah,wacce suka haɗu a bakin get tana zaune da akwatinta. Jurayyah ta tambayeta ina iyayen ta sai tace mata wai yanzu suka tafi kafin su iso. Kowa tsoronta yake baya kulata duk da batada hayaniya,iya Jurayyah ce kawai ƙawarta,ita duk abunda mutane suke faɗa ita bata gani kuma bata jin komai akanta. Ganin haka yasa itama bata sakewa da kowa a makaratar sai Jurayyan.
Bangaren hajiya Zakiyya kuwa datazo taga babu akwatin hankalinta ya tashi,domin kyautace da shugaban kungiya yayi mata na wani aljani,saboda aika ko bada shawara,domin yana ɗaya daga cikin aljanu masu kaifin basira da hangen nesa. Jini tagani wanda ya ɗiga a wajen,hakan ya tabbatar wani yabada jininsa ya mallakeshi kenan,to waye ya taba. Ganin babu mai bata amsa dole ta haƙura.
Lokacin da Inaya taga jan akwatin a wajen Jurayyah taso rabata dashi,amma firr taƙi,musamman data gano cewar aljanine a ciki,haka kawai zata sakashi wani aikin taga zayyi ko bazayyi ba. Kokuma tasakashi ɗebo mata bayanai gameda Hajiya zakiyya,wani yayi wani ya gagara. A haka tacigaba da gudanar da rayuwarta,gagara da taƙadaranci iri iri. Zaman ta da aljanin yasa tasan harkar tsafi dasu siddabaru iri iri,duk da wani abun bawai yi take ba. Abinda yabata mamaki shine yanda Inaya take gane abubuwan da take ko bata faɗamata ba. Sai daga ƙarshen karatunsu tagane ashe biri yayi kama da mutum. Itama jinsin boyence shiyasa tasan abubuwa dayawa.
Bayan gama secondrynsu Sun dawo gida Hajiya zakiyya ta fara saka Jurayyah akan harkokinta datakeyi a garin kaduna. A fili tana nuna sonta,amma har yanzu baƙin ƙudurinta na son ganin jinin Alhaji salihu ya tozarta yana ranta,duk da cewar soyayyar Jurayyah tashiga ranta,saikuma salon aikinta da ƙudurinta sai ya sauya. Musamman data gano cewar Surayyah kamarsu ɗaya da Jurayyah,kuma ta auri abokin adawarta,tunda yafara yin company a kaduna sai nata companyn na Red belt yayi ƙasa,gashi lokaci ɗaya ya cika neman securety da ma'aikata duk ya ɗebe mazajen dasuka cancantan Lokaci guda,saboda ya fita saka kuɗi. Shi bai santa ba amma shine babban abokin takararta,duk da tanada ruwan kuɗi da take karba a wajen Dodo amma kuma sanuwa da iya tafiyar da business batadashi sosai,kuma batason kowa ya fita,shiyasa tazama hidden enemy ɗinsa amma bai sani ba.
Tundaga wannan lokacin ta miƙawa Jurayyah madubin rayuwar Surayyah,yazamana ta ɗau tsawon shekaru tana ganin rayuwarta kuma tana kwaikwaya sannu a sannu. Saida ya zamo idan ka haɗasu bazaka taba gane wacece wannan ba. Kuma taboye bayanan Jurayyah,yanda sai anyi dagaske a gano wani abu daya shafeta,koda za'azo bincike wani lokacin.
Burinta shine ruguza ciki da zuciyar Ahmad,ta mallaki komai nasa ta hanyar Jurayyah,sannan bayan burinta ya cika saita tozarta Jurayyah tasa iyayenta su gane mai yafaru daga nan saita kasheta, shikuma dama Ahmad Jurayyah tagama zautashi yana tunanin matarsace tayi masa,wacce itama anriga an kasheta a inda aka tsareta.
Sai komai yalafa ta dawo da ƴar ta da kowa ke tunanin ta bata tasakata akan komai nata ta gajeta.
****
Farkon faruwar komai.....
Sanyin hannunsa ya shafa mata,hakan yasa ta noƙe tareda rufe har kanta. Buɗewa yayi shima ya shiga cikin salo na jan hankali.
"Nureety yana ganki a cikin bargo har kinyi sallahr yau,nasaba kullum inna dawo kina kan sallaya,yau harkin kwanta?"
"Uhmm yau ni bacci nakeji,jiya baka barmu munyi bacci da wuri ba Hayatee dan ma yau su farhana na wajen Ummi"
"Mene korasu can kikayi,ba nace banason suna zuwa kwana can ba,ni nafison ki kulamin dasu da kanki nureety tarbiyyarki tana burgeni"
"Uhmm ni bani na kaisuba, Nimrah ce tazo ta tafi dasu,kuma itama ummi ce ta aikota"
"To shikenan amma next kice na hana kinji? Yanxu barina tayaki baccin nima,idan inajin ɗumin jikinki nima baccin yafimin daɗi"
"Kaii Hayatee to amma iya baccin zamuyi koh?"
"Kin cire implant ɗinma amma har yanzu nauyin baccinki bai raguba,kodai kodai mun samu wani"
"Habadai wancan satin na cire implant ɗin fah"
"Ahh to ba sunce zaka iya samun ciki immediately bayan ka cire ba,yau bazan fitaba sai ƙarfe Sha ɗaya dan haka muyi bacci kafin tara"
"Uhmm tun jiya ka faɗa da daddare ai,shiyasa ma na kwanta abuna"
Bacci suka sha har ƙarfe goma saura,da sauri ta tashi tayi musu abin karyawa bamai wahala ba,bayan sun karya sunyi wanka yashirya ya fita.
Gyaran gidannata tafara kaman koda yaushe, ta sassaka turare bata ɗora abinci ba ganin ita kaɗaice,kuma dama su farhan ba a wajenta suke ba. Ta kwanta kenan akan kujera zata ɗan danna wayarta taga wani message yashigo ta whatsapp ɗinta mai one time open. Ƙirjinta ne ya buga dummm,domin hoton Ahmad ne a ɗaure da igiya cikin wani baƙin jeji. Bata gama dawowa hankalinta ba number ta ƙirata.
Hannunta yana rawa kamar bazata ɗaga ba saikuma ta danna ta kara a kunnenta.
"Mijinki yana hannunmu,idan kinason ya dawo gida to ke kizo,address ya sauƙa akan wayarki karki bata mana lokaci sannan karki faɗawa kowa idan kinasonsa a raye"
Kashe wayar tayi saikuma tafara tunanin gaskiya bada gaske bane,domin inda gaske suke meyasa basu nemi kuɗi ba ko kuma su ƙira wani nasa,saisuce tazo.
Ƙiranne yasake shigowa amma har ya katse bata ɗaga ba. Message ne yasake shigowa da video a haɗe. A can bangaren su Jurayyah kuwa sanye take da irin dake jikin Surayyah,jira take ta fita itakuma tashiga gidan,don angama shirya komai.
Buɗe saƙon tayi mai ɗauke da videon Ahmad bakinsa yana fitar da jini. An rubuta cewar 'baki yadda damu ba ko,wata takarda zakiyi signing na share wanda shi yaƙiyi,idan kuma bakizo ba nan da wasu awanni zamu kasheshi.
Tashi tayi jikinta yana rawa,ranta yacika da wasi wasin shin taje kokuma kartaje tarkone. Number Ahmad ta ƙira, ƙira har sau goma amma baya shiga. Da sauri tashiga ɗaki tasaka mayafin abayar taja mota tafita batareda kowa yasani ba.
Tana zuwa daidai inda aka faɗa mata taga akasin abinda yake playing a videon,wajen dai shine amma babu abinda yake faruwa a wajen. Jikinta ne yafara rawa ta lumshe idonta a hankali,shikenan an ci nasara abokan gaba sun yaudareta tafito daga gida. Duk faɗan da Ahmad yake mata akan karta yarda da wani abu idan an fada mata waya,kokuma karta fita batareda masu tsaro ba duk ya tashi a banza,dama an ce wanda baiji bari ba. To amma ya zatayi,hankalinta ya tafi akan ceton mijinnata abin sonta,wanda batasani ba maimakon ceto jefashi ma tayi a bala'i.
Ƙarar takun mutum taji,tana waiwayawa ta zare ido,ganin mai kamarta ce sak kaman an tsaga kara a gabanta. Dede da kayan jikinsu ma iri ɗayane. Murmushi Ta sake mata mai ƙayatarwa kafin ta shaƙa mata wani abu a hancinta.
"Barka da zuwa sabuwar rayuwa ƴar uwata"
Shine abinda taji sama sama kaman a mafarki kafin duhu ya lullube dukkan ganinta da jinta.
Amin magana ta wannan layin
***
Sadi-sakhna ce.