Free chapter · Read without an account
Chapter 38
⚫ *MUMINA KO AZZALUMA*⚫
Available on:wattpad&arewabook
⚫ _SADISAKHNA_⚫
🖤🖤🖤
⚫ _PART 38_⚫
Numfasawa tayi ganin yanda damuwa ta taru a fuskar Jurayyah lokaci guda..... Cigaba tayi dacewa....
"Tohh amma bazanyi miki dole ba idan bakyaso zaki iya........."
"A ɗau mutum a ɗau kayansa.....bayan karbata da kikayi a matsayin ƴar uwa kika yafemin abinda nayimiki? Kuma du ki ɗauki nauyin goge barna da kuskuren danayi a baya. Ahah ahah bazai yiwu ba niya kamata na goge abuna dakaina. Idan mutane suka kalleni da ɗa ga banida aure suka tsangwameni hakan zai bani damar tuna irin badakalar danayi a baya Surayyah, abin yayi yawa duk bayan turaki rana danayi ke kuma kika jani inuwa a hakan saikin bani harda ruwan sanyi? Kekam zuciyarki wacce iri ce Surayyah,a abubuwan danayi miki da watace koda tayi ƙoƙari ta yafemin ɗan da na haifa ko kallonsa bazatayi ba ballantana harta rungumeshi da ɗaukeshi a matsayin dan sa haifa kuma harta saka shi a cikin zuri'arta ya amsa sunan shi jininta ne."
"Naji dai in kin ɗaukeni ƴar uwa yanda kike faɗa to na maida Abdurrahim ɗana,banaso kuma kowa yakalleshi a matsayin ba ɗana ba,amma batun ki raineshi dan ki tuna abubuwan da kikayi bai taso ba,Allah gafururrahim ne mai karbar gafarar bayinsa,sannan bai dace ga bawa ya ƙuntatawa kansa ba dan hakan yasa ace ya tuba. Kawai ki cigaba da tuba da kuma neman ilimi mai bullewa,ni zan taimaka miki da hakan idan mun koma gida"
"Wanne gidan,ahah ni ba binki zanyi ba,wajen iyayena zan koma idan har zasu amimce su karbeni,wacce ta koya miki kika taci a haka nima ita nakeso na koya daga wajenta"
Murmushi Surayyah tayi jin maganar ƴar uwartata.
"Babu wanda zai kaita farinciki da bayyanarki,na tabbata sai tafi ɗokinki akaina,ƴa sukutum haka tara daga sama,waye zaice yaƙi"
Raha da dariya suka cigaba a haka aka kawowa Jurayyah abinci taci ta ƙoshi tayi wanka ta saka kaya a cikin wanda aka kawomusu.
Fitowa tayi daga ɗakin tana ƙarewa wajen kallo,haƙiƙa yaci sunansa private house kam,dan babu wani waje dayake nuna alamar katanga ballantana yabawa wani damar shigowa,ba'a ganin dare yayi na zahiri saidai in fitulun wajen sun sauya kala tukunna.
Da Ahmad ta haɗu wanda yake duba agogon hannunsa lokaci zuwa lokaci ya kalli fuskar wayarsa,da alama akwai abinda yakesonyi mai muhimmanci.
"Inaga yakamata mu fita ai muga mai yake wakana ko?"
Ɗagowa idonsa yayi ya kalleta da mamaki.
"Mai kika ce?"
"Nace tunda na warke inaga yakamata mu fita"
Lallai wannan matar,ohhh daman duk tsawon boye kansu da sukayi na tsawon kwana huɗu badan komai bane sai dan batada lafiya komai?. Shine tayi masa ƙarya tace rayuwar matarsa tana cikin haɗari, ashe itace a haɗarin tasakasu kwana ba ɗaya ba ba biyu ba a cikin fargaba?
Ganin kallon rainin hankalin dayake mata wanda tasan na menene yasa ta kauda kanta gefe tareda cewa.
"Ina nufin dama abinda yasa nace mu buya shine Hajiya zakiyya zata iya tracking namu ta jikina,sannan a wannan lokacin tariga tasan saboda ku na butulce mata,to idan tagano Surayyah zata iya kamata tasakani miƙa wuya,wanda hakan yana nufin ta samu abinda takeso daganan kuma sai tafara shirinta na gaba na cutar da ahalinka dana Surayyah."
Y gamsu da bayaninnata amma bai nuna hakan ba sai ma shiga ɗakin da Surayyah take yayi.
Su kaɗaine dama suka saura,dan safwan ya ɗauki ƙanwarsa sun tafi ana nemansa a asibiti,yaso ya ɗanyi magana da Jurayyah amma fir taki bashi dama,hakan yasa Surayyah ta bashi shawarar ya barta sai ta warke zuciyarta ta samu nutsuwa tukunna.
Hanyar gida ya nufa wanda hakan yasa Jurayyah yin magana wacce take riƙe da Abdurrahman,ita kuma Surayyah tana shayar da Abdurrahim wanda yake ta Kuka ,tunda yafara ƙoshi sai rigimarsa ta karu.
"Amm abban farhan ni inaga nazan koma can ba,idan babu damuwa ka ajiyeni a gidan su Surayyah kawai"
"Kiji wai gidan su Surayyah,kice gidanmu dai kawai"
"Akwai dalilin yin hakan,su Abban ma suna gidanmu,kafin fitowarmu an sanar dani harin da aka kai gidannaku wanda mutanen waccar matarne,tace komai mai zai faru su tabbatar sun kace Abbanku da umma,dayake daman na saka tsaro A ko ina tun farkon faruwar abun,ti abun yaxo ya dasauƙi,bayan an kamasu ne suke bayyana cewa tana gadon asibiti ashe wutace take cin jikinta taƙi warkewa,shine tace su aikata kisan saboda karta durƙushe ita kaɗai. To hakanne yasa duk da am kamasu nace su dawo nan estate ɗin na ɗan wani lokaci kafin komai ya daidaita. Tunda har yanzu bamusan adadin mutanen ta ba"
Surayyah ba ƙaramin kiɗima tayi ba jin abinda yafaru,banda Jurayyah wacce ita rashin lafiyarta ne ma yabata mamaki ba abinda tayi ba,dan tafi kowa sanin ta zatayi yafi haka.
****
"Haba mommy yanzu a halinda kike ciki kika bada order a kashe wani,bakya ta neman lafiyarki na wannan abun daya sameki?"
"Ko wutar nan zata zagwanyeni na zama ƙwaralgwal bazai dameni ba in har zan raba Salihu da rayuwarsa shida Amina,gaba tsakanina dasu bazata taba ƙarewa ba. Dan haka nake umartarki da ko ƙasa ta rufemin ido ban yarda ki tsaya daga turbar tana sakaki ba,kina jina ina?"
"Tabbb"
"Mai kika ce ?"
"Babu abinda nace ni,ko na faɗama gaskiya ni ganin halinda kike ciki yasa na tsorata da rayuwar da muke ciki. Wannan fansar babu inda zaikai mutum sai wahala da karshe marar kyau,ni gaskiya tuba zanyi kema ki tuba kanki mutu a haka"
"Ehh Me kike ce bana jinki"
Kallon mahaifiyartata tayi,sai a sannan takula da wani ruwa dayake fitowa daga kunnannata da kuma idanuwanta wanda naman gefensu ya jagwanye,kenan abun har yakai bataji sosai?.
Jijjiga kai tayi cikeda tausayamata,duk tasan itace tajawowa kanta da kanta amma uwa uwa ce.
***
"Wai mai kike nufine,haka zaki cigaba da zama muna zuba miki ido,daga kinji sallama saiki gudu ɗaki kice shine yazo?"
"Kallon Hajiya hunaiza Safeenah tayi ta haɗa kai da tafin hannun ta ta dafe,abinda duniya ya taru ya isheta,ita yanzu ba kunyar abinda ta aikata bane yadameta,shin ya zaayi a magance shi tunda ta riga ta aikata,ga ciki a jikinta wanda yake gasata da laulayi,gefe ɗaya kuma ga ubansa wanda kullum cikin farautar yanda zai ganta yakeyi. Tun anayiwa abun rufa rufa yanzu kusan kowa ya sani, hatta jiya saida tazo tayita masifa wai ta rike mata kuruwar ɗa,ta sau mata shi ya samu yayi abin kansa tunda itama bata damu dashi ba tayi aure ta barshi duk irin son dayake mata. Wai ma batasan Asirine ya kamashi ba da abin sai yafi haka muni.
"To ummah yakikeso nayi,wannan abun fah babbar mai laifi kece,koma mai ya faru kece kika ƙullashi,gashi yanzu ni abun yashafa tunda rayuwata ya wargaza"
"Hungo naki nan dacewa dukka laifinane,da nayimiki magani sai nace ki kasa saita gindinki ga wanda akayiwa kika je kika yasar a titi? Ko ni na ɗoraki a wannan harkar,ina bansan kinyi ba saida abin yafi ƙarfinki kika nemeni?"
"Ni wlh ba laifina bane nina ce kuyi da ɗirkamin tsimin mata ga babu miji kusa,nayi ta daurewa har naji abun ya hau kaina"
Shuru hajiya Hunaiza tayi daga biyewa safeena,tabsrgaza ce dai an tafkata saidai kar a ƙara kawai.
In za'abi ta mai kaya to abi ta mabi sawu ma,in safeena nada laifi to tabbas itama da laifinta,gabaɗaya ido rufe take bin zugar ƙawaye da soyayyar ƴaƴa,gashi sun kaita sun barota bayan sun azata kan keken bera.
***
Ahmad ne yafara shigowa sannan yabar su Surayyah a waje,tana bawa Jurayyah ƙarfin gwiwa wanda batasan taya zata fara tunkararsu ba,bayan rayuwar da tayi dasu na kusan tsawon shekara guda tana basaja a matsayin ƴar uwartata.
"Assalamu alaikum"
Shine abinda yace lokacin daya shiga falon,kaman yanda ya buƙata kafin su iso kowa ya taru a tsakiyar falon ya zauna inda ƙannensa ke zaune,ciki harda su safeena,wanda saida akayi mata jan ido kafin tazo,duk bobboye cikin jikinta takeson yi,amma kowa in mai hankali ne kuma yasan ciki yana kallonta yasan tanada shi. Saidai ba kowane yakawo bana ahmad bane,tunda bawai fitowa yayi ba.
"To dama kaman yanda nace a hallara a waje ɗaya idan na iso akwai bayanin dazanyi,kwanaki nayi ta ƙorafin cewa Surayyah ba matata bace amma babu wanda ya yarda dani,saima wasu kallon na zauce sukeyimin,a gafarceni Abban Surayyah nasan a lokacin ranka ya baci bakaji daɗin abinda nayi ba. To amma maganata gaskiya ce,wacce na rayu da ita tsawon wata tara zuwa goma ba matata bace ba,hasalima tsawon zaman danayi da ita wani abu bai taba haɗamu ba,saboda ban yarda cewa ita matata bace,tun kafin nasan gaskiya zuciyata takasa aminta da ita".
Dukkan su zuba masa ido sukayi na mamaki,ince dai ya daina abunnan kwanaki,to kuma menene ya ɗagoshi yanzu.
"Yanzu dama mai sunan manya abinda kasake taramu ka jaddada mana kenan wannan shirmen,idan ba matarka bace to aljana ce. Ince haka akazo aka cemana kunyi tafiya kaida ita na wasu kwanaki,shine daga dawowarku ka cigaba da wannan maganganun da munyi tunanin ka dainasu. Kuma a gaban ita Surayyah saboda kaci fuskarsu ka tozarta ƴarsu?"
Amin magana ta wannan layin
***
Sadi-sakhna ce.