Free chapter · Read without an account
KUSKURE 1 & 2
*KUSKURE*
Reposting...
"Indo ! Indo !! Indo!!!"
"Naam Aunty"
"Bakiji ni bane tun dazu inata kiranki kinmin Shiru? Ko wulaƙancin ne ya tashi?"
"Aa wlh Aunty banjiki bane d zan fito kiyi haƙuri Dan Allah, gani" wata mata ce da ƴar aikin ta da suke rayuwa gida ɗaya, kamar dai yaro da uban gidan shi.
"Toh naji , ki gama gyara ko Ina na cikin gdn Nan in su Noor sun dawo dg makaranta ki musu wanka su danji iska a jikin su sanan ki shiryasu zuwa islamiya ki tabbata kin dafa musu zabin ransu, Ina nufin abincin da suka fi so kinji ko?" kalaman Nawal ga ƴar aikin nata da umarnin da take bata.
" Maybe bazan dawo d wuri ba Dan zamu tsaya group discussion d fanc Dina Kar asami akasi kinji Koh?" ta sake jadada mata.
" Toh! Aunty insha Allah , su Noor sunce dambun shinkafa sukeso Wanda yaji zogale d hadin da salad ,Kuma babu zogalen ...." Kafin ta ƙarasa NAWAL ta katseta eh na sani zan Aki Dan bala driver yaje gdn Hindu tasa a ɗibo min a bishiya a garden ɗin ta"
"So,ze kawo Miki ki gyara ki tabatar kin wanke d gishiri ki dafa musu ki samusu Komai, enough aciki kinji Koh?"
"Toh Aunty angams in sha Allah,sekin dawo, Adawo lpy" ta faɗa cikin girmamawa.
A yatsune ta amsa mata "Allah yasa na tafi"
Fitar NAWAL keda wuya , Indo t dukafa Aiki gyara can ƙyalƙyale Nan ƙyaƙyale can Nan d Nan komai y zama "very neat nd clean na gidan Dan Akwai Aiki bata da son jikin ta...
NAWAL Ana Hall anata daukan lecture , hannun su rike d handout, da waya Attention ɗin su gaba daya Yana ga lecturan da yake basu darasi .......
Indo ta gama komai na danbu b Abin d ya sura ta jere a dining t hada komai na bukata har na me fada ajin gdn , wato megidan Dan zedawo lunch dan wani lokacin ya rigata fita ko ta rigashi....
Mai gidan Shi ya fara shigowa cikin kamala d kwarjini yayi sallama ,lndo t amsa tamai sannu d zuwa, abin da matar gidan ce ya kamata tayi welcoming ɗin shi,ya tmby ta "lunch is ready" ta daga Kai Alamar eh ....
Direct Dining ya nufa,y duba yaga Abin d Aka girka y jijiga Kai kawai yasan favorite din su Noor ne Dan haka ya zuba kafin y fara Kai Loma sai naga ya Dan tsaya Alamar" he thinking something about her wify or her childs " l d'nt no wooo .......Dan ba kowani time neke kutse cikin mind din mutum ba musamman masu gida irin Bbn so noor.....
Sai daga baya yayi wani malalacin murmushi sanan y yi bisimillah! Y fara cin Abincin .....
Yakai Loma na 4 kenan su Noor d Haneef suka shigo d gudu sakamakon 4eyes d sukayi d dad din su.
D gudu Noor ta tafi gareshi, Haneef ma haka ,shiko dama y gama bude hanayen sa yana sauraran Jin dumin yaran a fafadan kirjin shi ,yanajin su y lumshe ido Yana sumbatar su ,Suma suna mayar Mai, saboda shaƙuwar da ke tsakanin shi da yaran....
Yace "hasken idanuna kun dawo?" Sukace" yes Dad we came back" ya mayar musu "Nima haka yarana kuje kuyi wanka kuzo muyi lunch kun ji?"
Haneef ne y tabe baki yace "ina mom dad?" Noor ko cewa tayi "Ni gaskia sai naci mutumin kafin nayi wanka l'm hungry dad wlh Tana mele baki irin n 'yan Madara d bonvita taɓararun yaran nan.....
Indo Ce ta fito Tana musu sanun su d dawowa , tace suzo amusu wanka suyi sallah kafin suci Abinci .....
Shiko safwan dad din su Noor.
Haneef yake b amsa d cewa "mom Bata dawo ba Amman munyi waya da ita right now Tana hanya insha Allah kaji?"
Yana lalaɓa su "Kuje kuyi wanka kuyi sallah" Noor d Haneef atare sukace "dad Dan Allah abari muci Abinci kafin wlh mungaji g yunwa" Sai ya amsa musu " to ayi sauri Bana son makara akan ibada" SAFWAN yace ma lndo "to ki bari suyi lunch sai amusu wankan suyi sallah,Bata d zabi tace" to dadyn su Noor "Nan t kwashe lunchbox dinsu d school bag dinsu zuwa room din su domin ajiye musu, na kitchen Kuma ta Kai kitchen ta ajiye.
Sunacin Abinci cikin kwanciyan hankali d Jin Dadi d farin ciki ,har suka kamala aka musu wanka sukayi Alwala sukayi sallah ..
SAFWAN kuwa miƙewa yayi zuwa bed room dinshi domin watsa ruwa shima kafin y fita Dan Akwai inda za shi.
Bayan sun idar da sallah ne Indo ta feshesu d bodyspray na turaren Yara da ALHARAMAIN turen mai maiƙo ta sa musu uniform dinsu ta Basu islamiyabag dinsu ta kamo hannun su zata sadasu d Dan bala driver domin kaisu islamiya .....
SAFWAN ne y fito cikin shiga Mai kyau yanata kamshi shima , yace "you guys ko salama ma baza'amin ba nayi Adu'ar Adawo lpy Koh?" yana tsokanar su Noor.
D gudu Noor taje gare shi tace "sorry dad mun sha'afane bamaso muyi lati ne kasan y sa yadi da mu'alama in akayi lati maimakon yayi dukan lati saidai y Kori mutane su koma gd sede su hakura d karatun ranar shiyisa bamason mu makara"
Dad yace "hakan shine daidai tsarin islamiyar aini yamin sai ku Kara hima d bin doka Dan azauna lpy, duk da Koran man ba mafita bace,
Indo
Na tsaye Tana sauraran uba d 'ya'yan sa ,sai SAFWAN ne yace Mata" jeki kawai bari zan saukesu a makarantar kafin na wuce inda zan je",Dan haka t koma ciki Tana musu Adawo lpy .
NAWAL ba ita ta shigo gdn Ba Sai After 2 ,ita kanta bataji dadin rashin ganin iyalan nata ba ,
bayan Indo t gama Mata sannu d zuwa tayi room din ta Dan taking shower Ko Zata ji iska.
*BY MAMAN SHAHEED*
*KUSKURE* 🙆🏼♀_🤱🏼
( _'yar Aiki ko matar gida_)
_shafi na biyu_
Bayan NAWAL ta fito dg watsa ruwa tayi sallah ,sanan ta afkama Abinci d ci Dama ta kwaso yunwar ta.
Kiran Indo tayi tatambaye ta dadyn su Noor y dawo ne, Indo t sheda Mata y dawo yaci abinci y fita, tace ok ,su Noor sunci Abinci sosai ko ,tace "eh sunci tare ma suka fita d dadyn su ze saukesu a makarantar"
Tace" ok hakan yayi jeki karasa aikin ki" (Allah sarki su injin sarkin Aiki)
Indo t koma kitchen Dan karasa wanke wanken ta.
*WACE CE NAWAL*?
*NAWAL* Yarinyace ga Shareef Ahmad 'yace Kuma ga hasiyatu tanada kanne 3 maza biyu mace d'aya Autar su .
Shareef ba wani shahararen Mai kudi bane da ana faɗan shi kowa zai sanshi Amman yanada Arziki daidai nasa NAWAL itace 'yarsa ta fari , kafin a haifeta saida suka kwashe shekra 3 kafin Allah y Basu cikin ta hakama Akwai tazarar shekaru 5 tsakanin ta d Auwal kafin Aka haifi Ahmad sai husnah Auta (Asma'u) .....
Shareef Ahmad baza'ace Mai hamshakin Mai kudi ba Aman yanada wadata d rufin Asiri ko Ace karamin Mai Arziki ne ya Malaki gdn kanshi Mai kyau ginin zamani sanan yanada motar hawan shi Kuma yanada jarin Dan Kasuwa ne Kuma yayi karatun Boko d yayi aikin gomnati daga baya y fada kasuwanci nan yake duk wata hidimar gd d y'an uwa .....
Shareef Yana wadata iyalin sa ,musamman NAWAL taga gata dake bashi d 'yayan d yawa kafin a haifi su Auwal y sangarta ta y Mata yadda takeso har zabin ransa ma duk hakan Yana faruwa ne badon San ran Mama (hasiyatu) ba Dan takan yawaita musu mgn kan y'a mace ce gdn wani zata kodan kalubalen rayuwa ma Bai dace y sangarta ta haka ba , Abbah (Shareef Ahmad) Yana cewa abarshi y nuna Mata k'auna in Basu nuna kulawa akanta ba a kan 'ya'yan makota zasu nuna? ,ita suka Haifa Kuma ita kadaice a gaban su har sai d ta shekara 5 sanan aka Mata kani cikin shekara t 6 Dan haka still gata d sangarta Tana Nan ...
Ahmad ma y taso y joining din su NAWAL fagen sangarta ,haka duk y sangarta yaran Amman yara matan sunfi sangartuwa ,itako mama fadan d yafi karfinta wasa ta Mai dashi aka zauna lpy ,Amman haka besa in sukayi ba daidai ba ta tsawatar musu Dan ko Mai Aikin gdn su dake Abbah y samo ma mama Mai tayata Aiki wai yara sunmata yawa t dinga tayata ba yadda mama batayi ba Dan ganin y rabu d Mai Aiki Amman Sam yace in Bata bukatar taimako yaransa na bukata Dan haka dole tayi Aiki agdn haka ta hakura ,Inna dije Tasha fama d su NAWAL Dan dai biyan ta akeyi Kuma Bata d karfi d tuni tabar aiki a gdn .
NAWAL tun Akan Abban ta d maman ta taci burin ko Aure tayi sai d taimakon Mai Aiki zata iya sarafa kanta d yaranta Dan haka Koda ta girma cikin ikon Allah suka hadu d SAFWAN a shop wright ,cikin lokaci kankani kuwa soyaya Mai karfi ta fizgi zukatan junan su ,cikin salo d iya sarafa soyaya suka Aminta d junan su kan cewa daya baze iya rayuwa ba sai d daya ,zuciyoyin su dai suka zama Abu guda .
Wata Rana SAFWAN sun taba fada d NAWAL shine fadan su na farko atarihin soyayyar , Inna dije ta dakama tsawa har da Alakoron tsaki dare d gyaran harara ,wanan Abu shi y fusata ran safwan Dan wanan shine karo na 5 da takema Inna jide abinda ran SAFWAN Bai so ba Dan matar Tana mutun tashi in ta kawo Mai ruwa ko aka aiketa wajen shi ,shima Yana girmamata amatsayin ta na Mai shekaru ,akan dai Ina dije aka Sami matsala tsakanin 2lovers Dan haka ranar baran-baran akayi ,Abin d y sashi tafiya kuwa Taki karban *KUSKUREN TA* Gani take meye lefi Dan ta hantari Mai yi musu bauta wato Aiki,haka y barta y tafi gd ko sallama babu
Zuciyoyin masoyan sun kwana kunci ranar Dan ko irin musayar kalaman luv din d suka Saba suke wa junan su kullin ranar be samu ba ,dukan su sunji ɗacin Abun ga kowane naji d kanshi akan baze nemi wani ba .
Haka soyayyar su ta fuskanci tazgado (fushi) har na tsawon sati guda kowannen su ya jigata hakuri kawai sukeyi kowa nason gane wa yafi damuwa d wani ,akarshe dai NAWAL CE ta bada Kai bori ya hau.
Ta fara turamai d text ,da kamar baze responding ba daga baya yakasa jurewa shima y Mata reply , Nan komai y wuce suka koma kamar da a soyayyar su ....
*WANE NE SAFWAN*?
*SAFWAN* ɗa ne ga Alhaji Bukar ,shi Kuma mijine ga Hajiya Aslamiya ,SAFWAN Su biyar nee gdn su shine na 2 Yanada Yaya 1 Ibraheem sai SAFWAN sai Twins dukansu matane sai Autar su jannah .
SAFWAN sun taso cikin kulawa ,gata ,yalwan Arziki ,hakan besa sun sangarce ba Dan gdn su Sam ba wata Mai akin d take kwana wata datijuwace kawai d take zuwa d yarta matashiya take ma Ammy shara d wanke wanke Tana gamawa take tafiya in anada bukatar ta kiranta ake a waya dake Ammyn ta sai Mata waya ,Dan haka Ammy t goge d Aikin ta har su twins ma suna hidiman gdn sosai , hatta su SAFWAN insun so suna shiga kitchen shida Yaya su dafa indomei ko shayin coffee ko soya kwai Ammy tayi t tsokanar su Alhajin su suna cewa matan su sun huta ,suna cewa wazema mace girki ashema b AUREN mukayi ba ,
duk atajirancin irin na Alhaji Bukar , Yana wadata iyalin sa Dan motar yaransa daban take tun suna ƙanana ta kaisu school ,islamiya ,kaisu gdn zoo yawon shaƙatawa ,kaisu super market siyaya ,wajen wasanin yara ,Yana nuna musu gata d sangarta inda sangartar Yake so suyi baze dinga seta su ba ,amman sakamakon nuna musu daidai d akeyi d sunyi ba daidai ba za'a tsawatar musu ta sigar rarashi d iya sarafa tunanin su Dan haka suka zama Abin Alfaharin iyayen su .
Bayan sun Malaki hankalin kansu Yaya d SAFWAN Alhajin su y malaka musu mota zabin ransu , bayan sun kamala karatu Kuma y sama musu Aiki shi Yaya Yana Aiki a asibi shi Kuma SAFWAN Yana Aiki a Karkashin Alhajin su y bude Mai ƙaramin company suna Aiki kusan tare duk d wajen kowa daban.
Cikin nutsuwa d nuna sha'awar AURE,SAFWAN y bayanama mahaifan sa y samu matar Aure , ganin baida matsala t kowannen fani
Nutsuwa ,Aikin yi, Kuma zai iya rike mace basa haufi yasa suka barshi sai ma mara masa baya d sukayi ,har aka dinga tsokanan Yaya wai y zama Yaya na zaure ,shidai yace b yanzu ba ,Nan su twins suka dinga murna za'ayi biki a gdn su dan suna San taro da mutane.
Cikin lokaci kankani aka yanke bikin SAFWAN D NAWAL ,Batare d ta kamala hada dgree d'in ta ba Dan haka taci Alwashin karasawa ko agdn mijin tane , Koda sukayi shawara d SAFWAN yace Mata b matsala yasan dadin karatu d amfanin sa baze hanata ba ,Dan haka bikin su wata 3 akasa kacal ...
Kwanci tashi asarar Mai Rai komai akasa masa lokaci Mai zuwa ne indai d Rai da lpy ,Dan ayanzu bikin su y gabato , angama shirya komai na biki ,biki na nunama sa'a ango yayi hidima d Amarya , iyayen ango sun nuna bajinta Suma na Amaryar haka Abu dai cikin girma d Arziki aka samu aka Kamala biki Dan dunbin jama'ar da bikin ya samu Abin ba'acewa komai Dan Kaf 'Yan *MAMAN SHAHEED FANC* Sun halaci bikin sunci sunyi guzirin musamman masu Auren group din ,da 'yan matan cikin iyayen karban takeaway ma aka ware musu nasu da ban, anci ansha wasu antafi dashi gd (su Oo har d neman Kari) ,biki y tashi lpy ankai Amarya gdn Angon ta zumudi d farin ciki mara misaltuwa ne ya cika zuciyar ango ,Amaryar ma fa Tana cikin wani yanayi na farin ciki dan yau zasu nuna ma juna zallah ƙaunar da suke ma juna a daren yau ɗinan.