Free chapter · Read without an account

Page 21

by ZAHRA B MRS · Bayan Murmushi

Page 21💬⌨️


Yan kawo lefe sun tsaya dai-dai inda aka kwatanta masu bisa jagorancin Hamma Fahad. Yaya Safiyya tana bayan mota sai yatsina fuska  take, kallon Halima tayi tare da cire black shade ɗin ta.

“Which part of Abuja is this?”

“Lugbe kenan,” Halima ta amsa cikin ladabi.

“Oh, I see. Dole ki san gettoh area, tinda kema family ɗinku akwai mix of talakawa,” inda Sabo Halima ta saba da irin wannan kalaman a bakin dangin mijin nata.

A haka ma baban ta commissioner of health ne na Sokoto, amma an raina arzikin su. Gara kowa akan yaya Ramla tafi kowa bakin hali da tsanar talakawa. Kiri-kiri ta ki zuwa a kawo lefe da ita. Dinner ɗin ma dan Mommy ta kusa mata baki ne, shiyasa zata.


“Sannunku da zuwa, bismillah,” muryar Hamma Fahad ce ta katse tunanin Halima. Leading ɗinsu yayi har cikin gidan, idan security mata sai sauko sa boxes ɗin suke daga bayan Hilux.


An jere boxes rairas a falon su Farhana. Dangin AK sun sami karɓa ta mutunci, inna Jamila sun  bada tukuci daidai abinda zasu iya. Nene kam baki har kunne kamar ita aka kawo wa kayan.


Qanwar Mommy ce ke tambayar, “Ina amaryasu?”

“Inna Jamila” ta amsa da cewa, “Ta tafi gidan yayarta.”


Tinda aka gaisa, yaya Safiyya bata kara cewa Kanzal ba, black shade ɗin ta na nan a fuskarta. Banda tana shakkar Daddy, ai baza ta iya minti 20 a gidanan ba. Sai Halima da sisters ɗin Mommy ke hira dasu Inna Jamila.

“Let’s get going ko,” yaya Safiyya ta ce tana mikewa.

Sallama su Halima suke wa su nene , inda suke cewa, “Sai sunzo daukar amarya.”

Hamma Muhammad da Sameena ne suka bi bayan su yaya Safiyya da drinks 10katon da ruwa 10 katon, sai tarin snacks ɗin da basu ci ba.

Gidan Ramla, yaya Safiyya ta ce su wuce kai tsaye don ta labarta mata irin gidan da AK ya jajubo aure. Yayinda sisters din mommy daya driven ya wuce dasu gidansu AK na abuja Chan suka sauka .

Bayan fitar dangin AK kuwa boxes su  inna Jamila da Hadiza suke ta budewa. A haka har Abbi ya shigo.

“Wannan tarin kayan duk na Farhana ne?” Abbi ta tambaya da mamaki.

“Duk nata ne,” Iro Nene tayi saurin amsawa, “Ka ganmu tin dazu muke bude akwatinan bamu gama gani ba .


Jikin Diddi a sanyaye tace, “Jamila, kayan nan sun yi yawa, kuma ba wani tukuchi muka bayar me yawa ba. Duka-duduka 100k ne a cikin envelope ɗin. Da mun san irin kayan da zasu kawo da duk yadda zamuyi, a kara kudin sun kai 300k.”

“Uhmm…” Nima dai na kasa magana, Diddi, duk sai na ji jikina yayi sanyi.

Hadiza ce ta chafe zancen, “Ai sun san mu ba masu kudi bane, kuma munyi iya yinmu daidai gwargwado. Yanzu dai kayan nan a nema masu daki na musamman shine kawai ya dace dasu.”


Sun sami yaya Ramla da Hanadi a falo. Sun baje suna duba laces, sallama yaya Safiyya ,tare suka dago suna kallonta Bayan hanadi da ramla Sun gaishe ta yaya safiyya ta fara ranting 

Banda taba sanin AK bashi da aji ba sai yau, yaya Safiyya tace tana cire mayafinta bayan ta zauna a kujerar da ke facing dinsu.

“Kin ga unguwarsu amaryar… Gosh.”ta dafe goshi 

Gidan ma a kuntatace, nothing to talk about.


“Ikon Allah,” yaya ramla  tace tana maida hankalinta kan yaya Safiyya. Kiran securities Safiyya tayi tare da basu umarnin dauko abinda aka basu daga gidansu Farhana.

“Kiga kaskanchi… drinks da ruwa 20 cartons! Inaga basu san wa yar su ta aura ba,” cewar yaya Ramla ta mai, “jan tsaki!”

“Nawa ne an envelope ɗin?” yaya Ramla ta ƙara tambaya.

Halima ce ta fito da bundle ɗin 100k guda ɗaya.

“What the hell… 100k a duk wannan abun lefen? Gaskiya dai mutanan matsiyata ne,” cewar yaya Ramla cikin fushi.

“Kuje ku raba komai da komai,” yaya Safiyya tace tana umartar securities ɗin, “ku hada da snacks ɗin gaba ɗaya.”

Yaya Ramla ta ƙara da cewa…


Duk abin nan da ake Hanadi na gefe tana ji, Kanzal bata ce ba, sai ma dadi ta taji a cikin zuciyarta. Ashe ma Farhana low class ce.


AK ne part ɗin Farhana. Bayan ya kira interior decorators, sun canza kayan da dangin Farhana suka kawo; an mayar da furnitures ɗin nata guest parlour, kayan bedroom ɗin kuma guest bedroom. An zuba masu kyau daidai ta taste dinsa ,yasan halin yan gidansu ,farhana muzanta zatayi idan suka ga furnitures din da aka kawo .5 million yaya safiyya ta amsa a Wajan Ak  matsayin kayan fadar kishiya ,Banda Wanda dady ya qarawa hanadi .


Ringing wayarsa tayi, sunan Mommy ya gani. Har yanzu Mommy sama-sama take masa.


“Abdulkadir, an fada min abin kunyar da dangin amaryar ka sukayi,” ta fada a daya bangaren, bayan AK ya dauki call.

“Subhanallahi! Meya faru?” ya tambaya a rikice.

“Wai 100k suka bayar duk uban kayan da aka kai masu?”

Ajiyar zuciya AK yayi. “Mommy, iya karfin su sukayi. Auren yazo masu a bazata, kuma kinga, ko wata daya ba ayi ba da auren yayarta ba 

Dalla chan yi ma mutane shiru. Muryar yaya Ramla yaji. Wato conference call aka hada kenan.

“Raini dai, ka riga ka ja mana,” ta ƙara da cewa.

“Look Ramla, ba fa tsoron ki nake ji ba. Just 3 years kika bani ba haifata kikayi ba, kince ba ruwanki a sabgar aure ne, why involving yourself yanzu?”

AK ya fada a zafafe, “Kina jin sa ko Mommy? Tinda AK yayi auren nan, Raina mai girma ya shiga tsakani mu.”

“Ya isheku gaba ɗayan ku,” Mommy ta katse su, “ga Daddyn ku ya dawo.” Talk letter ta katse kiran.

A bangaren Farhana kuwa tana gidan Adda Sabrina a cewarta, sai masu kawo lefe sun tafi zata koma gida. Kiran AK ne ya shigo wayarta, amsawa tayi tare da sallama.

“Zanzo gida na kawo miki gate pass ɗin dinner dazu Abdulkarim ya kawo.”

“Bana gida,” Farhana ta amsa a ciki-ciki, har yanzu ta kasa gas gata auren  ta da AK. Gashi wasa-wasa cikin satin nan za a dinner da tariya.


“Ina kk je?”

“Ba izini na,” murya cike da possessiveness AK ya furta.

“Ina gidan Adda Sabrina?” ta amsa a dan tsorace, cos taji yarda voice ɗin nasa ya canza.

“Kika fita ba izini? Kika hau motar haya?”

“Uhmm… am trying to calm myself.” Yace yana maida numfashi .


“Anyways, kanina zai zo ya dawo dake gida, send me address ɗin gidan Sabrina,” AK ya ƙara da cewa, “We will talk idan kin koma gida.” Kit ya kashe wayar.


Ajiyar zuciya ta sauke, dan kwana biyu halayyar AK mamaki yake bata. Kamar wani psycho.


“Farhana, ya naga kamar a tsorace kike da AK?” Adda Sabrina ta tambaya tana ƙara matsowa kusa da ni.

“Uhmm… ba komai, Adda.”

“Talk to me, sis. Me ke faruwa?” Adda Sabrina ta ƙara tambaya.

Murmushi kawai nayi. Zan fada mata cewa AK ya shake ni kwanaki? Ko tarewa banyi a gidan saba?

“Magana nake miki.”

Firgit na kalle ta, waya naga ta dauka kafin ta fara cewa, “Bari na kira Diddi, definitely akwai abinda kk boyewa.”

Fusge wayar nayi tare da cewa, “Wallahi Adda, ba abinda nake boyewa. Kawai dai har yanzu na kasa sabawa da AK ne. I feel lost at times, shiyasa.”

Cike da tausaya wa, Adda Sabrina ta ce, “Kiyi hakuri sis. Ki kara mika lamarin kiga Allah. Kiyi wa mijinki biyayya, ki zama jajartacciya. Kuma naga tsoron sa a idonki, kar ki sake ki bari ya gane kina jin tsoransa.”

Kai na gyada mata. Haka ta ci gaba da rarrashina har aka kira magrib.

Uncle Salim ya dawo. Yadda naga yana tattalin Adda Sabrina sai naji sun birge ni. Ina son soyayya.

AK ya kira tare da sanar dani Abdulkarim yana kofar gidan Adda.

Munyi sallama da Adda akan cewa gobe inshaAllah zata zo taga kayan lefe.

Bakar Benz na gani a kofar gidan. Already AK ya fada min kalar motar da Abdulkarim zai zo da ita.

Gaban mota na karasa inda na ga Abdulkarim — kamarsu daya da AK, tare yake da wani ya juya baya yana waya. Abdulkarim ya gaishe ni a mutunce, cike da girmamawa.

Ina daf da shiga mota, mutumin dake waya ya juyo.

Ras, gabana ya fadi.


Jafar kuma? 😳


Assalamu alaikum, dear readers. 🤍


kuyi haƙuri a duk inda kuka ga typing errors. Ban samu damar yin cikakken editing ba,things are very hectic — ga family, ga office, ga rubutu.

Bayan haka kuma, ina rubuta English version ɗin wannan labari a Wattpad a lokaci guda. Duk ni kaɗai nake kula da komai, so please bear with me.


Nagode sosai da ƙaunarku, haƙurinku, da goyon bayanku. Wallahi ina jin daɗin karanta comments ɗinku da encouragement ɗinku. Allah ya saka muku da alkhairi 🤍


With love,

✍🏽 Author of Bayan Murmushi

ZAHRA B (Mrs)

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.