Free chapter · Read without an account
Page 18
by Rahma Kabir · MIJIN ARO
Sarac Stars R Pen...✍️
Zuhura.
Jiki a sanyaye ta samu napep ta hau tana lissafi kala kala dan ta gane ruwa ba sa'an kwando bane, duk yadda take ganin zata zuba mulki a gidan Mahmood da kamar wuya wai guguwa da auren nesa, domin ganin Nuratu yau kaɗai da kuma abinda ya wakana ya tabbatar mata da Nuratu ba kanwar lasa bace, duk da tasan wacece ita tunda tsakaninsu kamar hanta da jini ne, a zatonta yadda Nuratu take da sauƙin hali abin duniya bai dameta ba to haka take riƙe aurenta shiyasa har ta bata damar shigowa cikin gidanta, ashe kallon kitse take yiwa rogo duk da tasha bata labarin yadda suke soyayyarsu a cikin hira da yadda taga suna gudanar da rayuwarsu in tana gidan sai take ganin ta fi Nuratu wayewa da sanin makamar aikin oza room, ashe dai ba duhun kai gareta ba ta san komai kuma ta iya komai kawai dai sirrin ciki sai hanji ne. Zuhura ta nisa tana lissafin anya zata iya zama da Nuratu? dan tasan babu wata riba da zata ci da kishi da ita saboda Mahmood ita yake so a fili da badini, sannan kuma shi ɗin kiwon Nuratu ne ta gama koyar dashi duk wani salonta ya haddace, ita saura zata samu, in har ko zata yi kishi da Nuratu tofa babu ribar da zata ci sai faɗuwa, sai ta soma jin kota fasa auren ne kawai ta bar mata kayanta, wataƙila ma Nuratu tace ta aure shi ne dan ta hukunta ta da baƙin cikin da zata ƙunsa mata a cikin gidan nasu, da tunani barkatai ta isa gidansu Salame wacce ta sameta tayi ɗauri ƙirji tana shafa kurkur a jikinta, Zuhura ta aro jarumta ta saki murmushi dan ba zata so Salame tasan komai ba, dan tasan duk shawarar da zata bata ba mai ɓullewa bace, kuma ma zata rainawa cika bakin da take yi akan iskanci da zata zuba a gidan Mahmood, Salame ta katse mata tunani da cewa.
Wai har kin dawo? na ɗauka zaki jashi kuje park shan iska ki fara ɗana tarkonki.
Hmmm kin san shi ba mai irin wannan rayuwar ba ne, kuma sauya shi a lokaci guda ba abune mai sauƙi ba, shiyasa muna gama magana na dawo, yace zai ƙara mini dubu hamsin.
Gaskiya yayi kaɗan, ina laifin dubu ɗari biyu zuwa da hamsin haka.
To ya na iya kinsan sai a abinda matarsa tace zai yi.
Zuzuu anya haka ta barshi kuwa?
Cewar Salame tana riƙe haɓa, Zuhura ta taɓe baki.
Ina zan sani mace da mijinta, kuma a gaskiya Nuratu bata taɓa sanar dani tana yin wani abu ba, kuma banga alamar haka ba, sannan da tana yin wani abu zan sani dan bata ɓoye mini komai.
Hmmm ke dai ga mutum kawai, ai duk shaƙuwarku ba lallai ta faɗa miki tana bin malamai ba dan abun sirri ne, dan haka kema in zaki tashi tsaye to.
A'a ba zan yi asarar kuɗina ba wlh, dan na yarda da Nuratu ba zata yi wani abu mara kyau ba.
Ba anan take ba, ba a yabon ɗan kuturu sai ya girma da yatsa, amma bari ki shiga cikin gidan in kin fara cin ubanki zaki tashi tsaye ai. Bari na gama mu fita dan yau gasassahen nama nake so na ci.
Nifa na zo ki ara mini kuɗi ne.
Kamar nawa?
Dubu ɗari biyar ina so zan yi sabon gado ne, bayan biki Mahmood zai bani kuɗin na mayar miki.
Eh kuma fa gaskiya ya dace ki sauya kayan gado, to amma a ina za a yi miki?
Inda Nuratu tayi oder a MG furnitures company, so nake na siya wanda yafi nata kyau, kin san ba ta daɗe da sauya kayan ɗaki ba.
Shegiya tawa kanki na ja bari mu fita, daga can saina cire miki kuɗin.
Cewar Salame tana miƙewa ta ɗiba ruwa a rijiya ta zuba na zafi data gani a murhu ta shiga bayi, ba jimawa ta fito ta shirya cikin riga da siket na leshi, ta yiwa fuskarta kwalliya ta fesa turare sai suka fito. A hanya Salame ta cigaba da ɗaura Zuhura akan yadda zata kafa kujerar zama a gidan Mahmood ta ce.
Da zaki ji shawarata da kin siya turaren mallaka ki aje dan zai yi miki amfani, in ba haka ba kina zaune zaki ga tana juya shi hatta kema baki tsallake ba dan dole sai kin bi ta. Shiyasa tace ki aure shi, ƙila tayi hakan ne domin ta rama cin amanarta da kuka yi.
Allah ko Salame? kina ganin zata iya yin haka?
Ki zauna kin ji karki nimawa kanki mafita.
Jikin Zuhura ya ƙara yin sanyi tace.
Ko dai na fasa auren nan ne ayi duk wacce za ayi, dan wlh guiwana ya sare.
Dalla kin cika tsoro, ai irin wannan ba ja da baya har sai anga abinda ya turewa buzu naɗi.
Haka Salame ta cigaba da bata magana wanda yasa Zuhura sake samun ƙarfin guiwa taji babu ja da baya, daga can inda suka je suka wuce gidan yaya Salima a unguwar Rimi, nan ma suka cigaba da tsara shirye shiryen biki, Salima tace.
Wai ke a ina kika haɗu da mijin naki da ko sunansa bamu sani ba? ni fa nayi mamakin aure nan cikin sauri haka.
To Anty mijin auren ne yazo shiyasa ba jinkiri.
A ina yake? Sana'ar me yake yi? Kin ga dai yanzu rayuwar ta zama sai a hankali, Allah yasa me gwaɓi kika samo yadda ba zamu sayar da akuya ba ta dawo tana ci mana danga.
Anty wannan da 'yan kudinsa dan matarsa har da mota take ja, kuma yana kula da iyali sosai.
Yauwa koda naji, ai auren mai maiƙo shine ribar mace, kinga dai yadda nake juya kuɗi a gidana, kuma ko mijinki na farko kinga irin gatan daya yi miki dan haka ki dage damtse ki kama zuciyar angon naki, duk da bamu san wacece matarsa ba amma dole sai kin shirya dan wannan zamanin ba a zama haka sakaka, ko ni da ba ni da kishiya ban zauna ba balle ke.
Kai anty nifa bana so na sa kaina a wannan layin, Ni ban gina kaina ba kullun kuɗina yana a hanyar niman magani.
Ta ƙare maganar tana taɓe baki, anty Salima ta riƙe baki tana dubanta, zata yi magana Salame ta rigata.
Tun ɗazun maganar da nake ta ɗaurata akai kenan na rasa irin ƙaramin tunanin Zuhura.
Barta idan jikinta ya gaya mata zata nima bamu sani ba. Yau she kuka yi maganar ranar da zaki tare da kuma Ranar da za a kai kaya.?
Mun gama tsara a washegarin ɗaurin aure ne zan tare haɗe da kayana gabaɗaya, gado da wardrobe ne kawai dan yace a gidansa zan zauna falo ɗaya ne da za muyi amfani da shi kuma akwai komai a ciki.
Sai kika yarda ya haɗaki da matarsa, aiko kishi irin wannan wlh babu daɗi gwara tun wuri kice ya sauya miki gida.
Anty abin ne yazo a ƙure kuma ko nayi magana zancen ɗaya ne bai da kuɗi.
Salima taja tsaki tana miƙewa.
To ai bai zama dole ayi auren yanzu ba ya bari sai ya shirya sai a yi.
Tana ƙare zancenta ta wuce kitchen duba girkinta, Salame ta kwashe da dariya tana cewa ƙasa ƙasa.
Wai damma bata san wa zaki aure ba, ƙila in taji sai ta kusa rufeki da duka.
Kin ga kiyi shuru, ban shirya bayyana komai ba dan Allah.
Cewar Zuhura tana ɗaura hannu a bakinta tare da yin maganar ƙasa ƙasa. Haka suka dinga hira har zuwa bayan sallar isha'i, wani Saurayin Salame ne yazo ya ɗauke su a mota, sai da suka sauke Zuhura a gida kafin suka wuce hotel dan yau ba gida zata kwana ba.
*****
Nuratu.
Duk wani shirye shirye an fara dan saura kwana uku ɗaurin auren Mahmood da Zuhura, har anyi fentin ɗakin da zata zauna. Ko da Mahmood ya sanar da Nuratu cewar mama tace nan Zuhura zata zauna bata wani damu ba, dan tasan ba yi da halin kama haya duba da yana cikin rashin kuɗi, duk da ta bashi aron dubu ɗari shida amma basu ishe shi biyan buƙatunsa ba sai kayan da Haj. Ladi tace ya kawo sune kawai ya samu damar siya, sauran kuɗi ya siya kayan abinci da cefane wanda mama tace ya kai mata, sai ya ƙarawa Zuhura wasu kuɗi, duk da aure ne da ba shiri amma wasa wasa ya kashe kuɗi ba laifi, danma Nuratu tace ta yafe kayan faɗar kishiya yaji da hidimarsa. Ita tunda taga auren yazo kuma da gaske ba fashi sai ta ƙara sakawa zuciyarta haƙuri da juriya tare da niman taimakon Allah akan samun ƙarfin zuciya, dan kusan kullun sai tayi kuka in kishin ya motsa mata sai dai in ta tuna da aure ne ba zina ba sai taji 'yar natsuwa tare da jin ƙarfin guiwa. Gidan nasu babba ne da katon falo sai ɗaki uku a falon, ɗaya yana ɓangaren dama sai kuma guda biyu a jere ɓangaren hagu duk da bayi a cikinsu, kuma tanan ne kitchen yake da store a ciki, wannan guda biyun sune ɗakin yara Anwar da Ashraf sai kuma Yasmeen da Nauhal (afwan an samu kuskuren suna ashe Naufal sunan namiji ne Nauhal ne mace. so sunan Naja'atu da taci sunan mama Nauhal). Wancen ɗakin dake gefe shine na baƙi. Sannan sai wani korido da yake kallon ƙofar falon anan dinning yake, sai ɗakin Mahmood dake gefen dama ƙofarsa yana kallon ƙofar ɗakin Nuratu dake hannun hagu, ta bayan gidan akwai fili madaidaici yana ɗauke da bishiyar mangoro dana gwanda, sai wani fili daga gefe wanda an katange shi an saka ƙofa ta nan cikin gidan, rashin kuɗi ya saka Mahmood kasa gina shi sai ya bar gurin a haka Amma duk lokacin damuna yana shukar farin wake, in ya nome baya sayarwa sai dai ya ɗibawa mama da 'yan uwa na kusa sai gidansu Nuratu, sannan sauran su aje suna amfani da shi.
Nuratu ta fito daga ɗakinta tana sanye da T-shirt sai ƙaramin siket, anan ta samu Anwar a falo yana riƙe da remote sai sauya tasha yake yi, tace cikin mamaki.
Iye zama kayi, to ka gama aikin dana saka ka?.
Na gama, Kuma har Yasmeen na taya ta wanke bayinsu.
Kasan Allah in bai fita yadda nake so ba sai kun sake wankewa. Maza fita ka taya Baba mai gadi gyaran bayan gidan.
To yace mata kana ta juya zuwa ɗakin Mahmood dan tayi masa nasa gyaran, aiki ne da ta sabawa kanta duk bayan wata biyu zuwa uku, haka take wanke tiles ɗin bayi tun daga na jikin bango har ƙasa da tuntun kashin, sai take samun toka ta tankaɗe tare da gishiri da omo ta haɗa su guri guda ta yayyafa masa ruwa kana ta riƙa ɗiba da sosan buhu tana wanke tiles ɗin, duk wani jurwayi da datti zai fita bayan ta watsa ruwa mai kyau da ta saka hypo da izal sai bayin yayi fes yana kalli da sheƙi, hatta tuntun kashin haka take yi masa ta wanke ciki da waje, da ta gama ta fito ta soma cire yanar bango ta kaffaɓe ƙura sannan ta goge abinda ya dace a goge da tsumma mai danshi, sai da ta gama da dakunan da falo kafin ta nufi kitchen, shima haka ta goge tile ɗin bangon zuwa yin mopping ɗin ƙasa, tuni gida ya ɗauki haske ta sakar masa turare mai ƙamshi sannan ta samu damar ɗaura girkin dare, wanda lokacin ku san biyar saura, aikin ya ɗaukesu dogon lokaci kafin suka gama, tuwon shinkafa tayi musu biyar agushi sai ta yi musu tsumin tsamiya, sai bayan sallar magrib ta samu kanta wanda tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi tasa hula da hijab ta gabatar da sallar margrib da Isha'i, tana kan dadduma Mahmood ya shigo ɗakin cike da fara'a.
Uwargida ashe kina ciki.
Wani irin kallo tayi masa wanda ya saka shi gimtse fara'arsa yana riƙe bakinsa kana ya samawa kansa gurin zama yana cewa.
Kiyi haƙuri suɓul da baka ne na manta kince baki son sunan uwargida.
Taɓe baki tayi ta kawar da kai zuciyarta yana yi mata suya, duk haushinsa take ji wanda bai rasa nasaba da walwala da ta ga yana ciki ba, kuma ta ɗaura hakan akan farin ciki yake yi da auren da zai yi, ƙila da Malika zai aura da yafi yin rawar ƙafa da rawar jiki tunda ita budurwa ce, ta kula sam wasu mazan basu da kunya idan aka zo maganar ƙara aure, wani abin yinsa suke yi kamar cikin gushewar hankali, duk da gashi dai laifi yayi mata ta kuma laƙa masa auren da yace baya so, amma ga dukkan alamu bakinsa ne kaɗai yake furta baya so amma zuciyarsa da gangan jikina yana so. Ƙishinsa ne ya motsa mata wanda taji zuciyarta yana yi mata zafi, sai taja guntun tsaki wanda yasa Mahmood aje wayarsa da yake duba saƙon Zuhura na zancen bai tura mata kuɗin wanke kai da na lalle ba.
Hasken Mahmood lafiya? Allah yasa ba laifi nayi ba.?
Mahmood dan Allah ka fita bana son ganinka.
Cikin sauri ya miƙe ya zo ya zauna a gabanta saman sallaya, ya amshe carbin da take ja ya aje gefe.
Me nayi miki? Ki faɗa mini damuwarki.
Damuwata a yanzu shine kayi nesa da ni.
Ta faɗa cikin rauni da ƙaraya wanda har idonta ya kawo kwalla, Mahmood cikin damuwa yace.
Nuratu kalaman bakina sunyi kaɗan akan yadda zan fayyace irin girman da kike da shi a cikin idanuna, faɗin kalmar so yayi kaɗan akan irin son da nake yi miki, wlh ke ce zaɓina. Bari inyi miki mai kankat ke ce Raina, ina nufin in babu ke to babu sauran numfashi na a duniya.
Ya ƙare maganar yana ƙara damƙe hannunta cikin nashi, A wannan lokacin kuka ne ya kufce mata mara sauti, ta yarda da duk maganarsa domin taga zahirin haka a cikin kwayar idanunsa, duk maganar da ya yi daga cikin zuciyarsa yake fitowa, ta yarda yana sonta kuma ba zata iya hana auren nan ba dan bata san ta ina zata fara ba wajen kare shi daga aikata zina, sai ta kuma rushewa da sabon kuka wannan karan har da shassheƙa, Mahmood jawota jikinsa yayi yana bubbuga bayanta tare da faɗa mata kalaman soyayya wanda kullun baya gajiya. Buga ƙofar da Anwar yayi shine yasa ta zame daga jikinsa ta tashi ta shiga bayi ta wanke idonta kana ta fito, lokacin shima ya miƙe yana jiran ta fito, ya kalleta yana cewa.
Ina fatan jinin nan ya tafi gabaɗaya ko?
Nuratu ƙuri tayi masa da ido tana dubansa dan ta kasa bashi amsa, ya saki murmushi.
Kina kallona ina ta magana. Kin san nayi kewarki sosai fa.
Murmushin yaƙe tayi kana tace.
Kaima kasan yana ɗaukewa zan baka haske akan haka, mu je muci abinci.
Ta ƙare maganar tana yin gaba shima ya rufa mata baya, Nuratu ta saki ajiyar zuciya dan bata shirya bashi kanta ba a kurkusa, har yanzu wannan tabon da suka dasa mata a zuciya bata manta shi ba kuma shine ya kashe mata duk wani karsashin sha'awar Mahmood, dan ta mance rabon data ji shauƙinsa a gangar jikinta, kawai dai rayuwa take yi lami tamkar an kashe mata sha'awa. Haka suka ƙarasa dinning ta zubawa kowa abincin suka fara ci, Mahmood yana kula da rashin walwalarta dan a kwanakin nan tafi son zama ita kaɗai ta takurawa kanta da tunani.
Zaku iya fara biyan kuɗinku na cigaban wannan littafin MIJIN ARO zango na biyu domin saura pages biyu mu gama zango na ɗaya mu tsunduma a zango na biyu wanda sai kun biya kuɗinsa kafin zaku samu cigaban wannan labarin ɗoɗar har zuwa ƙarshensa In Sha Allah. ₦700 ne kuɗin, dan Allah ku mara mini baya, domin kunsan akwai tarin darussa dana tanadar muku cikin wannan hikayar.
Pay ₦700 to 9034940106 RAMATU KABIR MONIEPOINT. Sai a tura shaidar biya a WhatsApp ta number nan ***.
Rahma Kabir ce Matar MG. [5/16, 12:37 PM] Rahma Kabir: *MIJIN ARO*
Na
©®Rahma Kabir MrsMG.