Free chapter · Read without an account

MASARAUTAR KAIZUR 7

by Nusaiba Ibrahim Rimi · MASARAUTAR KAIZUR

👑🗡️ MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑 





✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️ 



Page 7




Wata firgitacciyar ƙara gimbiya Hayat ta yi a tsorace,kafin ta zame ta zube kasa sumammiya, tuni kuyanginta suka cika dajin da iface-iface, lokaci guda komai ya yi tsit tamkar babu wani mahaluki mai rai a cikin dajin 

Ba komai bane ya faru face tsalle da Kazuzi ya yi, cikin wani irin tsananin zafin nama ya cafke damisar, ba tare da ɓata lokaci ba ya yi jifa da ita

Miƙewa damisar ya yi yana gurnani yana kallon Kazuzi, Kazuzi ma kallonshi yake yi fuskarsa babu yabo babu fallasa,damisar bai bi ta kan Kazuzi ba ya sake nufar inda Hayat take kwance,da wani irin ƙarfi Kazuzi ya sake damƙarshi,ya ja shi da ƙarfi, ba tare da ɓata lokaci ba aka kaure da kokawa tsakanin Kazuzi da damisar, lokaci guda damisar ta farke ɗaurin da aka yiwa ciwon hannunshi na damtse,kuma a take jini ya ɓalle a hannun

Kallon hannun ya yi sannan ya sake kallon damisar,yana murmushi ya ce"yanzu hankalinka ya kwanta?

To ba abin da kake tunani bane,amma ina gargaɗinka da babbar murya ka fita a harkarta,idan ba haka ba tabbas za kayi nadama"bai rufe bakinsa ba damisar ya sake nufar inda Hayat take kwance da tsananin zafin nama fiye da na baya,wannan karon Kazuzi bai yi wata wata ba,yana damƙar wuyan damisar ya maƙure ta, ba tare da bata lokaci ba ya murɗe mata wuya,bai sake ta ba sai da ya tabbatar bata numfashi sannan ya yi jifa da ita 

Sai a lokacin hankalin kuyangin da dakarun suka dawo jikunansu, ba tare da ya yiwa kowa magana ba ya wuce inda Hayat take kwance ko motsi bata yi, tamkar babu rai a jikinta,bai yi wata-wata ba ya durƙusa ya ɗaga ta ya saɓa ta a kafaɗa,kai tsaye ya miƙe ya nufi cikin masarauta,sauran jama'ar suka biyo bayansu cikin mamaki da ɗimuwa,babu mai iya magana a cikinsu 

Kai tsaye masarautar Tayaar suka koma,kafin su isa labari ya iske mutanen fada cewa damisa ta farmaki gimbiyar Tayaar,don haka kai tsaye sarkin dakaru Amjad ya yi musu umarnin su wuce zuwa fada inda sarki yake jiransu, ba tare da ɓata lokaci ba suka nufi can 

Gaba ɗaya ilahirin fadar kowa yana tsaye a matuƙar razane suna jiran isowarsu,fuskar sarki Iyaad ɗauke da matsanancin tashin hankali da ruɗani,kan Kazuzi a ƙasa,yana zuwa ya kwantar da ita a gaban sarki, kanshi a ƙasa ya ce"ta samu firgici ne shine ta suma,amma babu abin da ya same ta,a gafarce mu idan mun gaza a aikinmu ya shugaba na"yana kai wa nan ya miƙe a hankali ya fice daga fadar 






*DAULAR KAIZUR*


"Amincin Allah ya tabbata a gare ki yake wannan baiwa mai tarin ji da kai"

Ɗaga kai ta yi a nutse tana ɗan murmushi,a hankali ta furta "amincin Allah ya tabbata a gare ku ruhin ƙasar kaizur"

Ɗan murmushi sarauniya Amna ta yi,sannan ta zauna kusa da Munaya tana kallonta,sarki Mu'iz kuwa bai ce kanzil ba,ya zauna a inda ya saba zama yana kallonsu 

"Munaya!

Tsawon shekaru ashirin kenan kina karɓar hukunci iri-iri, kina fuskantar ƙasƙanci da wulaƙanci, menene dalilin hakan?

Saboda ɓatan abin da tun farko kin san ba naki bane, menene dalilin da ya sa ba za ki bayyana shi ba? ke a daina azabtar da jikinki?mu ma zuciyoyinmu su huta da azabtuwa?"

Kan Munaya a ƙasa, cikin rissinawa ta ce "gaisuwa gare ku ya shugabanni na,kuma ruhin gari mai albarka kaizur 

Munaya baiwa ce mai amana,bata taɓa cin amanar wani ba,ko da ace Sarkin kaizur ne

Munaya bata salwantar ba,bata da riba a hakan"

"Na sani,amma menene dalilin da ya sa kika amsa ke kika fitar da shi daga ɗakinshi?"

"Saboda ni na aikata hakan ranki ya daɗe!"

Shiru sarauniya Amna ta yi na ɗan lokaci kafin ta ce"to menene dalilin da ya sa kika aikata hakan?"

"Saboda soyayya ranki ya daɗe "

Sarauniya Amna ta ce"ba dai soyayya ba,an saka ki ne"

Shiru Munaya ta yi na ɗan lokaci, kafin ta ce"ba saka ni aka yi ba, amfani aka yi da ni,na gane hakan"

Zaro idanu sarauniya Munaya ta yi cikin firgici ta ce"amfani da ke?

Wanene ya yi amfani da ke?"

Ba tare da bata lokaci ba ta ce"ina son a ba mu waje ranki ya daɗe!"

Wani mugun kallo sarauniya ta yi mata ta ce"a cikinmu wa zai ba ki wajen?ni ko Mai martaba?"

Kan Munaya a ƙasa ta ce"mai martaba ranki ya daɗe,tunda maganar tamu ce ta mata"

A wani irin fusace sarauniya ta saukewa Munaya mari,sannan ta hau faɗa tana faɗin"kina matsayin baiwa ƙasƙantacciya wadda take ƙarƙashin hukunci ko a gaban dubban mutane ba sai an ba ki izini za kiyi magana ba?har kike cewa wai mai martaba ya ba ki waje?"

Miƙewa mai martaba ya yi,ya dubi sarauniya ya ce"ku yi magana,dama nima na gaji da jin maganganun tsinanniya irin ta,na gaji da ganin fuskar da ta fi komai muni a idanu na"yana kai wa nan a maganarshi ya juya ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake kallon sashen da suke ba

Yana fita sarauniya Amna ta watsowa Munaya wani mugun kallo, Munaya ta yi ɗan murmushi, sarauniya ta ce

"Ya tafi,me kike so ki ce?

Kar dai ki manta ko me kika faɗa zai koma kunnenshi"

Munaya ta jinjina kai ta ce"haka ne!

Dama game da ɓatan ɗanki yarima Sahal ne"ta ɗaga kai tana kallon sarauniya da ta ƙagu ta ba ta amsa, kafin ta cigaba da magana sarauniya ta ce"me kika sani game da ɓatan nashi?"

Munaya ta sake duban sarauniya ta ce"Kamar yadda na gaya miki a baya cewa amfani aka yi da ni to haka ne, Urwa da Umayr da aka kashe akan wannan rigimar duka basu da laifi, ballantana Ya'aƙub da babu abin da ya sani a kai

Wasu manya ne a cikin masarautar nan suka sa aka sace Yarima Sahal,ban san niyyar su ta yin hakan ba,amma na fi tunanin saboda mulki ne"ta ƙarashe magana idanunta ƙyar akan sarauniya Amna 

A wani irin gigice sarauniya Amna ta riƙe hannayen Munaya da suke ɗaure a cikin sarƙa,muryarta tana rawa ta ce"manya a cikin masarautar nan?

Su wanene haka?kuma menene dalilin su na yin hakan?"

Munaya ta ce"Nima ban sani ba ranki ya daɗe,amma Kamar yadda na faɗa da farko wataƙila shirinsu ne akan kujerar kaizur"

Shiru sarauniya Amna ta yi tana kallon Munaya cikin tsananin tashin hankali da ɗimuwa, kafin ta ce"wanene a cikin MASARAUTAR KAIZUR da yake jin zai iya samun mulki muddin ya ga bayan ɗana Sahal?"

Shiru suka yi su duka biyun, kafin Amna ta ce"Yarima Zaffar ko Yarima Jamal?

Su kaɗai ne masu gadon sarautar wannan birni idan babu sarki Mu'iz 

Amma ta yaya za su iya cin amanar sarki? musamman ma Yarima Zaffar,ke ma kin san ƙarya kike yi,hakan ba abu ne mai yiwuwa ba"

Munaya ta rissina ta ce"nima na san da hakan ya shugaba ta,ban tabbatar da su wanene ba,amma tabbas manya ne a masarautar nan,kuma su ma za su iya gadon masarautar "

Shiru sarauniya Amna ta yi tana jin tana sake shiga ruɗani,a hankali ta ce"tabbas zan yi bincike,zan saka mai martaba ya yi bincike akan duk wani mahaluki da yake da alhakin gadon MASARAUTAR KAIZUR, muddin na samu mutum da hannun shi a ciki tabbas zan ɗauki mataki mafi muni,ke kuma ki jirayi dawowa ta"tana kai wa nan ta miƙe da sassarfa ta fice daga ɗakin, Munaya ta bi ta da kallo tana murmushi wanda ita kaɗai ta san ma'anarshi 





*DAULAR TAYAAR*


Yau kwana biyu kenan da faruwar tsautsayi ga gimbiyar Tayaar, wato Hayat, an samu ta farfaɗo,kuma zuwa yanzu zabure-zaburen da take yi ma ta daina 

Sai dai tun da aka gaya mata Kazuzi ne ya ɗauko ta tun daga dajin Lahur zuwa gida take jin haushin shi sosai, kwata-kwata bata yaba masa ba na cetar rayuwarta da ya yi, don haka ma ta ƙudurce a ranta sai ta yi masa gargaɗi mai ƙarfi 

Kazuzi yana zaune a lambun gimbiya bayan ya kammala aikin da badakare Amjad ya saka shi na gyaran lambun, cikin nutsuwarshi yake ƙarewa ko'ina na lambun kallo,a hankali wani abu da ya shuɗe ya gifta a idanunshi 



✨

"Sadaukin sadaukai!tsoro mai ban tsoro!wanda mutuwa take tsoro,takawarka lafiya abin alfaharin Baruda,kai ne sarki ko da ba'a yarda ba"

Ɗaga kai ya yi yana kallonta, murmushi take yi tana wasa da gashin kanta,ya gyara zama yana kallonta,ta ƙaraso ta zauna a kusa da shi tana kallonshi tana murmushi,ya ce"kin fi taurari haske a cikin Baruda,ina roƙon abin bauta mafi haske ya rufe idanun wasu mazan daga ganin wannan haske,sai ni kaɗai,kar wani ya yi min shigar sauri"

Dariya ta yi da sautin muryarta mai daɗi,ta kalle shi tana murmushi ta ce"a tunaninka a kaf ƙasar Baruda birni da ƙauye akwai wanda ya isa ya mallaki Malli?

Ai ko da ace mutuwa ce ta raba mu kowa ya san Malli matar Kazuzi ce abadan,babu wanda ya isa ya mallaki wannan Malli ɗin sai sadauki Kazuzi "

Janyo ta ya yi jikinshi yana murmushi sosai,ya ce"na san da haka nima 

Ke ce ƙwarin gwiwa ta a cikin daular Baruda,duk wani farin ciki da walwala ke ce sila 

Muddin akwai Malli a gefena bana damuwa, komai na duniya ba komai bane akan Malli 

Ki zama ba kya kusa da ni bani da maraba da bawa"

Igiyar tunanin shi ta yanke a daidai nan saboda ruwan da ya ji an watsa masa,ya ɗago da sauri yana kallon Hayat da take kallon shi ranta a tsananin ɓace,cikin hargowa ta fara faɗin 

"Shaiɗancin da ka saba a cikin garin naku za kayi min?"

Kallonta kawai yake yi ba tare da ya yi magana ba,ta ƙara fusata sosai, cikin ɓacin rai ta fara masifa tana kai masa duka,amma ko gezau, sai kallonta kawai da yake yi, dakarun da suke tsaron lambun suka taho da gudu don jin ba'asi, idanunta a rufe ta ce"ku kira dakare Amjad!"babu musu wani badakare ya juya don kiran shugaban dakaru 

Bayan sun iso ta dubi Amjad idanunta suna kaɗawa ta ce"ku tafi da shi,ku azabtar da shi,har sai ya faɗi dalilin da ya sa ya ƙura min idanu yana kallo na a yayin da nake wanka,kar a ba shi ruwa da abinci sai sau ɗaya a rana,a tabbatar an ɗora shi a SIRAƊIN UƘUBA irin wanda bai taɓa hawa ba tsawon rayuwarsa"shi Kazuzi sai yanzu ma ya ji laifinshi, Amjad ya rissina ya ce"an gama ya shugaba ta,sannan ya finciki Kazuzi, Kazuzi bai yi musu ba ya bi shi suka tafi 

Duk da hukuncin da ta saka ayi wa Kazuzi hakan bai saka ta huce ba,cikin tsananin ɓacin rai ta nufi sashenta, kamar yadda ta saba idan ranta yana ɓace sai da ta kori kowa a sashen sannan ta kwanta akan gadonta tana sauke numfashi cikin ɓacin rai

Ta rasa me zata yi wa wannan ƙasƙantaccen bawan ta ji sanyi a ranta,gaba ɗaya ya raina matsayinta,ba ita ba ma,ya raina dukkan wani mai matsayi a Tayaar,amma zata yi duk mai yiwuwa ta yi maganinshi 




💫

Da gasken gaske su Amjad suke ganawa Kazuzi azaba iri-iri,kuma ko sau ɗaya bai taɓa yunƙurin kare kanshi ba,hakan ya bawa dakarun mamaki,kuma ya yi musu daɗi, waɗanda suke jin haushinshi suka samu damar rama duk abin da ya yi musu

A cikin kwanaki uku sun yi nasarar galabaitar da Kazuzi irin yadda suke so,sai dai babu alamun rissinawa ko tsoro a tare da shi,kuma sam babu alamun damuwa a kan fuskarsa 

A wannan ranar ne gimbiya Hayat ta saka aka fito da shi,kai tsaye aka nufi lambunta da take zaune ita da amintattun kuyanginta kamar yadda suka saba,suna nan a zaune dakare Amjad ya shigo da Kazuzi da taimakon wasu dakarun,suna zuwa suka jefar da shi a gaban gimbiya

Murmushi mai kyau Hayat ta yi tana kallon Kazuzi, kafin ta ce"a kwance masa igiyar"babu musu aka kwance masa igiyar,ta dubi dakarun ta ce"za ku iya tafiya"suka rissina suka juya suka fice daga lambun

Cikin isa Hayat ta kalli Kazuzi ta ce"na san baka yi nadama ba yanzu ma,don da alamu kana da girman kai da ɗaukar kanka wani,bayan kai ɗin ba wata tsiya ba ce illa bawa ƙasƙantacce 

Ko babu komai zuwa yanzu ka gane ni ba kalar matan da kake kalla bane lokacin da kana garinku na zalunci,ba zan ce ka daina ba,amma hukunci yanzu aka fara ɗauka a kanka"

Gyara zama ya yi yana yin ƙasa da kai,ya ce"ki gafarce ni ya shugaba ta,ban san me kike magana akai ba,amma a duk lokacin da kike shirin ɗaukar mataki akaina a shirye nake na amsa ya shugaba ta

Amma ina so ki sani cewa,babu wata mace a idanun Kazuzi sai MALLI!duk wata mace koma bayan Malli namiji ne a idanun Kazuzi!!!"

Da tsananin mamaki take kallonshi,da farko kasa magana ta yi, kafin ta ce "har ni?Nima kana nufin namiji ce?"

Kai tsaye ya ce"har ke,ki gafarce ni ya shugaba ta"ya ɗaga kai ya kalle ta ya ce"an sallame ni?zan iya tafiya?"





#Nusy_bee

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.