Free chapter · Read without an account
MASARAUTAR KAIZUR 9
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
Page 9
Wani murmushi ya kubcewa Hayat,ta ce"Huda kina yabonshi da yawa fa
Kar fa ki manta ba musulmi bane ballantana na ce za'a yi Ć´ar gida"
Huda ta ƙyalƙyale da dariya ta ce"ya shugaba ta ai ko da ace na so shi ya cancanci a so shi ɗin, kyakkyawa ne ajin ƙarshe,sannan gwarzon jarumi ne,kuma shi namiji ba'a san shi da tsoro ba, sannan mafi girma kuma ya ceci ran shugaba ta har sau biyu,dole na girmama shi na mutunta shi"
Bata san menene dalilin ba,amma haka kawai ta ji gabanta ya faɗi,kuma sam bata yi farin ciki da maganar Huda ba,amma sai ta dake tana yaƙe,ta dubi Huda da take ta ƙara taƙarƙarewa tana faɗar kyawawan halayen Kazuzi,ta ce"to yanzu ta ina kike ganin zan iya mayar da shi kamar ku?
Kar ki manta shine ya kashe min É—an'uwa,silar haka mahaifiya ta ma ta rasu,kuma babu alamar nadamar hakan a tattare da shi fa"
"Shine silar shahadar yarima,ya bar duniya mai cike da ruɗani da ababen ƙi ya shugaba ta,ya mutu akan hanyar daukaka kalmar Allah, wadda Allah ya sanar da mu a Alkur'ani cewa su rayyayu ne
Sarauniya kuma,ki gafarce ni ya shugaba ta, kowanne mai rai sai ya ɗanɗani mutuwa,amma ta hanyoyi dabam-dabam,ko da ace Sadauki Kazuzi bai kashe Yarima ba, tunda kwanansu ya ƙare za su koma ga mahaliccinsu
Maganar nadama kuma,ya shugaba ta ki gafarce ni,bai yi abin da zai yi nadama akai ba har yanzu,shi ba musulmi bane,da musulmai suka tunkare su da yaƙi sai aka ba shi umarnin tunkararsu, kuma ko da ace musulmi ne don musulmi ɗan'uwanshi ya yaƙe shi babu laifi ya kare kanshi
Su ba su san kalmar Allah ba, ballantana su yi tunanin É—aukaka ta,a duba magana ta ya shugaba,amma idan akwai wata matsala a magana ta a yi min aikin gafara "
Hayat da ta zuba mata idanu kawai tana kallonta ta ja ajiyar zuciya,sannan ta ce"na ji duka,kuma zan duba,amma har yanzu ina cike da jin haushin wulaƙancin da ya yi min don yana kallo na ina wanka na yi masa magana
Ya ce wai ni ba mace ba ce, Malli ce kaÉ—ai mace a idanunshi "
Kallonta sosai Huda ta yi sannan ta ce"ya shugaba ta wannan ai ba abin damuwa bane,ba ya faɗa bane don ya wulaƙanta ki,da alamu ya faɗa soyayya ne mai wuyar sha'ani,a duk lokacin da mutum ya faɗa soyayya da wani ko wata,ba sa ganin kowa a rayuwa sai waɗannan masoyan nasu,komai da kowa ba sa wani burge su,duk kyau da ƙawatuwar su kuwa
Yanzu da ace za ki ga yarinyar da yake so É—in ke gani za kiyi bata dace ba ma, saboda bata kai a kira ta mace ba ma,amma ita soyayya ba haka take ba,bata duba komai, sai wanda ake so É—in"
Hayat ta jinjina kai ta ce"soyayya!to Allah ya sa mu dace,amma menene a soyayya ne da yake rufewa mutane idanu? menene abin burgewa a cikinta?"
Huda ta yi Ć´ar dariya ta ce"ya shugaba ta ai soyayya ta yi, ita ce mahaÉ—in rayuwa,sam ba za ki gane me nake nufi ba har sai kin faÉ—a soyayya "
Ƴar dariya Hayat tayi ta ce"to malamar soyayya,bar ni haka da wannan surutun naki, lokacin shiga ta cikin gida ya yi "ta miƙe tsaye,Huda ta rissina ta kwashe mata kilishin da suka shimfiɗa mata,suka nufi cikin gidan
*DAULAR KAIZUR*
"A ina aka tsaya? Har yanzu ban ji amsa daga gare ka ba kamar yadda ka ce za kaje wajen boka lamzur,har yanzu ban ji bayani ba"
ĆŠaga kai ya yi daga inda yake zaune yana kallon uwar sharri da ke tsaye akanshi tana jiran amsarshi ,a hankali ya girgiza kai,ya ce"ban samu yadda nake so daga gare shi ba,asalima ya yi fushi da mu,ya ce kar na sake komawa sai nan da wata shida"
Shiru uwar sharri ta yi na É—an lokaci kafin ta samu waje ta zauna,a hankali ta ce"to yanzu ya za'a yi kenan?
Ka ga abubuwa ba sa tafiya yadda ake so"
Uban shaiɗanu ya girgiza kai ya ce"kar mu yi gaggawa,muka yi jimirin shekaru ashirin ma,don dai wata shida sai ya gagara?aiki ɗaya ya rage,wanda daga shi ne ni da ke mun samu burinmu da biyan buƙatarmu"
Jinjina kai uwar sharri ta yi,sannan ta ce"Allah ya nuna mana, lokaci ya yi da za mu cimma burinmu,mu canja tsarin wannan zalunci irin na wannan mutumin"uban shaiÉ—anu ya jinjina kai, kafin ya yi magana uwar sharri ta sake faÉ—in "amma da sharaÉ—i,kar ka yi tunanin za ka ci amanar uwar sharri, don tabbas za ka haÉ—u da sharrin da ya girmi tunaninka "
ĆŠaga kai ya yi yana kallonta da mamaki ya ce"me ya kawo wannan maganar ne kuma uwar sharri?"
Murmushi kawai ta yi, sannan ta gyara rufin fuskarta, ba tare da ta yi magana ba ta bar wajen,ya bi ta da murmushi,a ranshi yana ayyana abubuwa da yawa
*DAULAR TAYAAR*
Kwana biyu kenan da tattaunawar gimbiya Hayat da kuyangarta,ta gamsu sosai Da maganar Huda,amma bata san yadda zata yi don ta yi masa magana ba,asalima tun daga ranar bata sake fitowa daga sashenta ba ballantana har ta saka shi a idanunta,asalima wata kunyar shi take ji saboda abubuwan da ta rinƙa yi masa a baya
Tana zaune a É—akinta, kuyanginta guda biyu suna taya ta shiryawa bayan ta fito daga wanka sai ta ga abu ya gifta,da farko bata kawo komai ba, musamman da ta ga alamu cewa su Huda ba su ga komai ba,sun cigaba da yi mata hira yadda suka saba
Sake ganin giftawar abu ta yi,ta tsayar da su Huda, lokaci guda suka yi shiru suna saurare
Kamar an ce kalli can,ta hango wata ƙatuwar kada a kwance a gefen gadonta ta buɗe baki, ihu ta kurma tana nuna ta da yatsa,su Huda suka gigice, don da alamu ba sa ganin abin da take gani,nan da nan suka rikice, ɗaya kuyangar mai suna Humaida ta fice daga ɗakin da gudu ta nufi inda su mai martaba suke don a nema mata iso ta sanar da abin da ya faru
Kafin sarki Iyaad ya zo inda Hayat take tuni ta suma,abin mamaki har yanzu babu wanda ya ga komai a É—akin,mai maganin masarautar aka kira don ya duba ta
Sai dai tsawon kwana goma tun daga wannan ranar gaba É—aya gimbiya Hayat ta zama wata iriya,bata da aiki sai zabura da firgita,gashi kuma har yanzu lokacin ta kasa magana ballantana ta gayawa mutane abin da yake faruwa da ita,aikin kenan daga kuka sai zabura
đź’«
Duk abin da yake faruwa Kazuzi yana da masaniyar komai,sai dai bai taɓa nuna ya sani ɗin ba ko da a fuska ne,amma abin da yake ji game da halin da gimbiya take ciki yana damunshi
Don haka a yau bayan ya fito daga lambun gimbiya da yake gyarawa kullum duk da bata fitowa yanzu,kai tsaye ya wuce wajen ɗakunan dakarun gidan,yana zuwa bai yi wata wata ba ya faɗa ɗakin da yake buƙata ba tare da wata shakka ko tsoro ba
Dakare Amjad da yake zaune tare da matarsa ya yi firgigit yana kallon Kazuzi da ko sashen da matarshi take bai kalla ba,ya ƙure shi da idanu, Amjad ya miƙe a firgice yana kallonshi, kafin ya ce"mahaukacin ina ne kai da za ka shigowa mutane ɗaki ba tare da neman izini ba?
Ko a addinin naka ba'a koya maka ladabin sanin dokar shiga waje sai an nemi izini ba? musamman idan mutum yana tare da matarsa?"
"A addini na an koya min ladabi da neman izini ne daga waÉ—anda suka cancanci hakan kaÉ—ai,don haka yanzu magana nake so na yi da kai,za ka wuce ta lalama ne ko kuwa?"
Amjad ya jefe shi da kallon tsana, kafin ya yi magana matarshi ta fara magana cikin fushi
"Tsinuwa da la'nar Allah gami da azabarshi su tabbata ga zindiƙi kafiri kuma azzalumi irinka,wanda bai san darajar rai ba ballantana ya san darajar wani, kuma ka gaggauta fice min daga ɗaki,ko na kai ka ƙara inda za'a ƙarar da rayuwarka"
Kazuzi ya kalli yadda take faɗa da tsananin ɓacin rai,amma sai ya ɗauke kai ya mayar da kanshi ga dakare Amjad da yake watsa masa nashi kallon tsanar,bai damu ba ya ce"ka wuce mu yi magana,idan kuma ba za ka fita ba babu laifi sai mu yi a gaban matar taka, duk da cewa ba abin mamaki bane idan ya zamana kai da ita abokan cin mushe ne"
Dakare Amjad ya ce"duk abin da za kayi kar ka fasa,amma kai ba ka isa ka saka na fito daga É—akin matata ba, fita na ce"
"Zan fita,amma sai ka warware abin da ka yi"
Kallonshi Amjad ya yi a É—an ruÉ—e, Kazuzi bai damu ba ya ce"ka warware abin da ka yi mata tsawon kwanaki, saboda ita ba Ć´arka ko matarka ba ce shiyasa za ka cuce ta,idan har kai namiji ne ubanta za ka cewa ya É—aura É—amara,kai ma ka É—aura ku É—auki takubba a ba ku fili ku gwabza
Namijin gaske ba ya laɓewa a bayan tuggu da makirci ko asiri ya yi cin amana"
Dakare Amjad cikin rashin damuwa ya ce"ba zan warware ba!
Idan har tsafi abin ƙi ne kai bai kamata ka faɗi hakan ba, saboda shine ya gina daularku ta zalunci Baruda,da shi aka raine ka ka zama mutum,kuma shine yake ba ka nasarar yaƙi
Kuma da kake maganar namiji,idan Ni da na laɓe a bayan asiri don ganin bayan yarinyar don ɗaukar fansa,to kai kuma menene makomarka?
Ba zaka iya ɗaukar fansar ba kenan?tsafin naka ya daina tasiri ne? shi yasa ka zaɓi zama bawan da mace ta mayar tamkar karenta?
Kar ka ɗauka ban san irin wahalalliyar rayuwar da ka yi a Baruda ba,amma ka zaɓi ka zamar musu bawa don baka da galihu daga kai har wanda ya tsince ka,don sanannen abu ne kai ɗin baka da asali!idan ubanka Murad bai sanar da kai ba ni yanzu na sanar da kai,ya ɗaura maka baƙar laya a damtsenka na hagu wadda take ba ka ƙarfin da za ka iya karawa da rundunar da bata da iyaka,ni na bawa Waleed izinin ya tsinke ta, don yana daga cikin matakin nasara ta shine na fara karya ka,tabbas sai na ɗauki fansa akan abin da ka yi min na kashe min yara na
Na samu nasarar farko ta hanyar ganin bayan budurwar ka Malli,zan yi nasara akan Sarkin Tayaar ta hanyar ganin bayan tilon Ć´arshi,kuma babu wanda ya isa ya ya dakatar da ni!!!"
Tabbas maganganun dakare Amjad sun yi tasiri a zuciyar Kazuzi, zuciyarshi ta yi rawa musamman ambatar Malli da Amjad ya yi,amma sai ya dake ya yi murmushi,sannan ya fara magana
"Ka yi gaskiya!
Tabbas da tsafi aka raini Kazuzi,amma idan ka yi tunanin tsafi shine ƙarfin Kazuzi baka yiwa kanka adalci ba, kai ganau ne ba jiyau ba,ka ga asalin Wanene Kazuzi lokacin da ka tura damisa ta farmaki gimbiyar Tayaar
Maganar Malli kuma haka zancen ka yake,malli ita ce dukkan rayuwa ta,mutuwar ta daidai yake da rasa farin ciki na,ka yi nasara sosai da ka saka aka kashe min ita
Sai magana ta gaba,me ma ka ce? yadda ka ga bayan Malli sai ka ga bayan gimbiyar Tayaar ko?za mu gani idan za ka iya hakan,ban zo nan don bani da yadda zan yi ba,ko don ban san yadda zan yi da abin da ka yiwa Ć´arinyar da bata ji ba bata gani ba,sai don ka san cewa ina sane da abin da ka yi,kuma idan ka cigaba kamar yadda na faÉ—a za kayi nadama mara amfani a rayuwarka
A ƙarshe,da alfahari nake faɗa cewa Ni Kazuzi ibn Murad tsintacce ne kamar yadda ka faɗa, wulaƙantacce a Baruda kafin na zama mayaƙi,kuma a ƙarshe bawan mace,ina alfahari da hakan tunda ban kasance maci amana ba a tsawon shekaru na rayuwa ta!
Ina yi maka jajen ranar da asirinku zai tonu ku ji kunya a bainar jama'ar da suka ɗauki yarda suka ba ku,kuma ba ku cimma mugun ƙudirinku akansu ba,don muddin Kazuzi yana cikin Tayaar har abada ba za ku cimma mugun ƙudirinku ba"yana kai wa nan ya juya da takunshi na isa ya fice daga ɗakin ba tare da ya sake saurarar abin da za su faɗa ba
#Nusy_bee