Free chapter · Read without an account
MASARAUTAR KAIZUR 10
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
Page 10
Da kallo Amjad da matarshi suka bi Kazuzi da ya fice daga ɗakin babu alamun damuwa a kan fuskarsa,matar Amjad ta fashe da kuka tana riƙe hannun mijinta, cikin kuka ta ce"yanzu menene abin yi abu Huzaifa?
Ina tsoron kar wannan kafirin yaron ya tona mana asiri,mu ba muyi hakan don wani abu ba sai don zaluncin da aka yi wanda ya zama silar mutuwar yaranmu uku,ka je ku yi magana da shi"
Kallonta Amjad ya yi, cikin taushin murya ya ce "kar ki damu Layla,babu abin da zai iya,barazana ce kawai"
Layla ta girgiza kai ta ce "to ka warware abin da ka yiwa gimbiyar Tayaar,a tsorace nake da abin da zai faru, sarki Iyaad zai iya yanke mana hukuncin kisa akan wannan abu da muka yi"
Girgiza kai ya yi, cikin taushin murya ya ce"na gaya miki babu abin da zai iya,yanzu ba sai anjuma ba zan tsaface shi,babu abin da zai iya akai,mantawa ma zai yi da abin da ya gani,ki kwantar da hankalin ki"
Hankalin Layla ya kasa kwanciya,ta dubi Amjad ta ce"ko ka manta ne Abu Huzaifa?
Shima matsafi ne fa,babban matsafi kuma,ba ka tunanin zai iya ɗaukar matakin kare kanshi,kuma a karshe ya ce zai yi mana raddi?"
Ƴar dariya Amjad ya yi, cikin nishaɗi ya ce"a dalilin haka ya sa na saka Waleed ya yanke layar da aka ɗaura masa a dantsensa na hagu,duk wani sihiri da tsafi da yake ji da shi na karya alkadarin "
Murmushi Layla ta yi zuciyarta na sakewa,ta jinjina kai ta ce"na gamsu abu Huzaifa,mu yi ƙoƙarin ganin bayan wannan azzalumin,ban taɓa tsanar wata halitta ba Kamar yadda na tsane shi,yara na huɗu ya kashe min uku ya bar min ɗaya "ta ƙarasa magana cikin kuka sosai"
Zuciyar Amjad ta girgiza,ya dafa kafaɗarta, cikin taushin murya ya ce"ki kwantar da hankalin ki Ummu Huzaifa,nasara akan wannan fajirin kamar mun samu mun gama ne in sha Allah"
💫
Yana barin ɗakin shugaban dakaru Amjad kai tsaye ya wuce ɗakinshi da aka ba shi bayan an fito da shi daga ɗakin duhu, ɗakin bashi da tazara da lambun gimbiya Hayat,a lokacin da aka ba shi ɗakin akwai kayan more rayuwa fiye da lokacin da yake rayuwarsa a Baruda,amma sai da gimbiya Hayat ta saka aka fitar da komai,aka bar masa ɗan mayafin da zai shimfiɗa da wanda zai rufa
Yana zuwa ya zauna akan dandagaryar daɓen da ke ɗakin,ya haɗe kanshi da gwiwa yana tunani,shi ba mutum bane mai yanke hukunci cikin fushi,amma tabbas ba don haka ba babu wanda zai kalli idanun shi da alfahari ya gaya masa shi ya kashe masa Malli amma ya rabu da shi,da sai ya ɗauke kanshi da takobi idan ya so komai zai biyo ya biyo daga baya
Bai taɓa jin zafin gorin rashin asali da aka yi masa a Baruda ba,amma bai san meyasa ba yau karo na farko sai ya ji zafin gorin da Amjad ya yi masa,ya sauke zazzafan numfashi, lokaci guda kuma ya miƙe zumbur kamar wanda aka tsikara ya fice daga ɗakin
Kai tsaye sashen gimbiya Hayat ya nufa,tunda yake a tsawon rayuwarsa bai taɓa shiga ba,ko da ya kasance a cikin masu yi mata hidima ba ya wuce aikace-aikace ko kuma kula da lafiyarta,amma yau kanshi tsaye ya nufi sashen
A bakin ƙofa ya gamu da Huda, fuskarshi babu walwala ya ce"ina son ganawa da gimbiya"
A ɗan daburce ta ce"am.....um... Gimbiya?dama....."
Wani mugun kallo da ya watsa mata ne ya sa ta matsa masa ya wuce jikinta yana karkarwa,bai sake kallonta ba ya kutsa kai cikin ɗakin gimbiya
A kwance ya ganta tamkar gawa,mai maganin gargajiya da aka kira yana ta ƙoƙarin gano abin da ya same ta,amma yadda a tsawon kwanakin nan bai samo komai ba yanzun ma hakan take,gefe kuma ga kuyanginta guda biyu Humaida da Bilƙees, Kazuzi ya dube su gaba ɗaya fuska babu rahama, cikin dakakkiyar muryarshi irin ta mazan fama ya ce"ina buƙatar ganin kowa ya fita"
Mai magani ne ya ɗago ya kalle shi,dama su Humaida da Bilƙees tuni jikinsu ya fara kyarma,mai magani ya ce cikin kwantar da murya
"Haba yaro!
Me za ka iya yiwa gimbiya?menene dalilin da ya sa kake so kowa ya fita alhalin kai baligin namiji kana ɗakin?menene dalilin....."
"Cewa na yi kowa ya fita,ba magana na tambaya ba"ya faɗa cikin tsawa
Da gudu suka fara fita a tsorace,suna daf da fita ya ce "ke!"cikin tsawa
A tsorace Humaida da Bilƙees suka tsaya jikinsu yana kyarma,da yatsa ya nuna Humaida ya ce"ke!
Zo nan,ke kuma fice ki ba ni waje"a guje Bilƙees ta juya ta fice daga ɗakin kamar zata kifa don tsoro
A razane Humaida ta ƙaraso wajen da Kazuzi yake, tana zuwa ta zube a gabanshi,tana shirin fara gaishe shi cikin tsawa ya ce"ɗauko min abin da shugaban dakaru Amjad ya ba ki ki ɓoye a ɗakin nan"
Ƙara firgita ta yi,tana shirin fara rantse-rantse ya daka mata tsawa,take ta fashe da kuka,tuni fitsari ya kubce mata,ya sake cewa cikin dakewa "fito min da abin da Amjad ya ba ki,kar ki bari na sake tambaya"
Cikin kuka Humaida ta ce"ka yi min aikin gafara,na rantse bai ba ni komai ba"
"Ƙarya kike yi!
Tunda kika ji na faɗi haka ya kamata ki san na san komai,don haka ba ni kawai"
Tana kuka ta ce"na gaya maka ban san komai ba akai,ka gafarce ni don...."damƙar gashin kanta da ya yi da tsananin ƙarfi,hakan ya sa ta yi ta ƙwala uban ƙara, cikin kukan azaba ta ce"zan ɗauko,ka yi min afuwa zan ɗauko maka"
Sakinta ya yi yana kallonta,jiki na rawa ta miƙe ta nufi bayan ƙayataccen gadon gimbiya Hayat ta zaro wani ƙulli,ta ƙaraso ta durƙusa ta miƙa masa,bai amsa ba ya ce"kwance ƙullin "
Babu musu ta kwance jikinta yana rawa,wani dunƙulallen abu ne a cikin tsohon tsumman da aka ƙulle ya bata umarnin ta fasa shi,babu musu ta lalubo abin fasawa ta fasa,take gimbiya Hayat ta kama wata iriyar jijjiga, Kazuzi ya mayar da idanunshi kanta amma bai yi yunƙurin zuwa inda take ba
Sake mayar da kallonshi ga Humaida ya yi, wadda take durƙushe jikinta yana ta rawa, hawaye wani na korar wani,cikin kakkausar murya ya ce"wuce ki rufe ƙofar ɗakin nan"
A gigice ta miƙe tana faɗin "in tafi?"
Wani mugun kallo ya watsa mata,a gigice ta ce"ka yi min aikin gafara"sannan ta wuce bakin ƙofar ta rufe,ya mayar da kallonshi ga Hayat da ke kwance a ƙasa, zuwa yanzu ta daina jijjigar,tana kwance ta yi shiru,a kausashe ya fara magana
"Daga yau bana buƙatar ƙara ganinki a duk wani abu da ya shafi gimbiya,ki san me za ki gaya wa mutane,amma na haramta miki zuwa inda take,idan kuma kika kuskura na ganki ko a kewayen ɗakinta ne,kar dai ki manta nine KAZUZI IBN MURAAD,ina nan a yadda kika san ni ko na ce kike jin labari na, bambancin wajen zama kawai na samu,don haka tashi ki fice daga ɗakin nan"
Babu musu ta miƙe jikinta yana kyarma ta nufi ƙofar ɗakin,a kausashe ya ce"zo ki kwashe tarkacenki"babu musu ta dawo ta durƙusa ta kwashe abin da ta kwance, sannan ta koma bakin ƙofar ta buɗe ta fice, Kazuzi ya mayar da kallonshi ga gimbiya da ke kwance
Bai yi mamakin ganin idanunta a buɗe ba tana kallonshi,don ya san zuwa yanzu abin da aka yi mata ya sake ta,ya rissina a gabanta kanshi a ƙasa kamar yadda ya saba, cikin taushin murya, Kamar ba shine ya gama daka tsawa yanzu ba ya ce"fatan tsawon rai mai albarka da lafiya mai amfani ga gimbiyar Tayaar "
"Kazuzi ibn Murad!ba ka san sunana ba?"ta faɗa cikin sanyin murya tana ɗan murmushi
Kallonta ya yi a ranshi yana mamakin murmushin da ya ga ta yi,kafin ya yi magana sai ga sarki Iyaad da Sarkin yaƙi da dakare Amjad sun shigo a firgice, Amjad ya nuna Kazuzi da ke durƙushe gaban Hayat yana faɗin "ka gani ya shugaba na!
Wannan fajirin ya kori kuyangi da mai maganin gimbiya don ya samu damar aikata alfasha da ita,ya shugaba na wannan bawan yana da tsaurin idanu da yake tunanin zai iya aikata alfasha da gimbiya,ya kamata a ladabtar da shi ko hakan zai zama darasi ga ƴan baya"
Cikin tsananin ɓacin rai da baƙin ciki sarki ya dubi Sarkin yaƙi ya ce"a kama shi "a take gimbiya Hayat da ke kwance ta yunƙura tana ƙoƙarin yin magana,a ɗan tsawace Kazuzi ya ce"A'a ya shugaba ta!
Abu ɗaya nake so da ke, na san kin ji komai,zai yi kyau ki rufa asiri ko don sake bayar da dama, mutum zai iya dawowa kan hanya idan aka ba shi lokaci ba'a hukunta shi akan laifin da aka san ya aikata ba"yana kai wa nan dakarun da suke tare da Sarkin yaƙi suka damƙe shi, ba tare da ɓata lokaci ba suka yi waje da shi
Hayat da ke kwance ta bi su da kallo tana hawaye,sarki Iyaad ya ƙaraso kusa da ita hankali a tashe yana faɗin"sannu ƴata!
Bai yi miki komai ba dai ko?"bata iya cewa komai ba,ya kama ta ya zaunar da ita,da idanu ya bawa bayi da sauran dakarun da suke ɗakin umarni, suka rissina sannan suka fice daga ɗakin
Ya yi farin ciki sosai saboda alamun sauƙi da ya gani a tare da ƴar tashi,duk a tunaninsa aikin mai magani ne,ya kwantar da ita akan gadon sannan ya juya ya fice daga ɗakin
*DAULAR KAIZUR*
"Na san kin san su wanene suka sace min ɗa,ko na ce da haɗin bakinki aka sace shi,har zuwa yanzu na kasa gane dalilin ki na aikata hakan, Munaya! gobe idan Allah ya nuna mana da rai da lafiya, za'a sake fitar da ke a yi miki rajamu Kamar yadda yake a ƙa'ida duk shekara,idan na ga dama zan bari mutane su jefe ki har mutuwa,don haka tun wuri ki gaya min,ina ɗana Sahal yake?
Kasancewar shi a raye ya tabbatar min da cewa kin san inda yake,amma a kwanakin nan na ga alamu yana cikin matsala, Munaya,ina ɗana Sahal yake?"
"Allah ya ja da ran shugaban Daular kaizur,na yi magana tun a farko,ban san inda Sahal yake ba,Nima ba zan so ya nisance ni tsawon shekaru ba, aƙalla ko gani na yi ya wuce zan ji sanyi a raina
Idan har baka gamsu da maganar da nake ta maimaitawa ba tsawon shekaru ashirin a yiwa mutane izinin su jefe ni har mutuwa"
"Munaya!"sarki Mu'iz ya daka mata tsawa, cikin ɓacin rai ya cigaba
"Da alamu taurin kai da izza tana damunki,yanzu ba sai anjuma ba zan saka a yi min maganinki"ya mike a zafafe ya fita,jum kaɗan ya dawo da wasu zaratan dakaru su uku,ya dube su fuskarshi a matuƙar haɗe ya ce"ku yi mata hukunci,kar ku saurari kukanta,kar ku saurari magiyarta,kuma kar ku saurara mata,kar ku duba kasancewarta mace ko don shekarun girma"yana kai wa nan ya juya a fusace,su kuma suka kama Munaya don aiwatar da aikin su
Iya azaba sun ganawa Munaya amma ta dake,ko sau ɗaya bata nuna musu raki ba,sun dake ta,da suka ga dukan bai yi ba suka ɗaure ta kanta a ƙasa suka rinƙa nana mata ƙarfen da ya yi ja a wuta,sai da suka kwashe fatar bayan nata duka, sannan suka lafta gishiri a wajen,bayan sun gama ɗanyen aikin suka sake mayar da ita suka ɗaure ta sannan suka fice daga ɗakin
Washegari da sassafe aka fito da ita bainar mutane,sarki Mu'iz da muƙarrabanshi suna zaune a inda suka saba zama, cikin su har da sarauniya Amna, Yarima Zaffar da Yarima Jamal,aka kai ta inda aka saba ɗaure ta,bayan komai ya natsa shugaban dakaru na ƙasar kaizur,wato Dawud ya dube ta ya ce"Munaya!
Sarki ke umartarki ki sanar da mutane inda kika ɓoye yariman kaizur,don tabbas idan kika yi turjiya ba za ki kai wata shekarar ba"
Shiru ta yi tsawon wasu daƙiƙu, Dawud ya sake maimaita abin da ya gaya mata, kanta a ƙasa ta ce
"A yi min afuwa ya shugaba na
Tabbas ni mai laifi ce a cikin MASARAUTAR KAIZUR,kuma na san laifi na ya wuce yadda za'a yi min afuwa
Amma ina roƙon wannan sarki mai adalci da ƙaunar talakawan shi,da ya bincika jama'ar da ke cikin fada,tabbas a cikinsu aka samu wanda ya sa aka ɗauke Yarima,ni amfani aka yi da ni,tun daga lokacin da aka kawo ni MASARAUTAR KAIZUR zuwa lokacin da aka sace Yarima,an cimma wani buri ne,kuma wannan burin da ake son cimmawa ba iyaka kan yariman kaizur ya tsaya ba,har da kai ya shugaba na
Idan na faɗi wani abu wanda ba daidai ba ina roƙon tausayawa da rangwame daga wajen wannan sarki mai adalci
#Nusy_bee