Free chapter · Read without an account
Page 15
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Turo ƙofar ɗakin Iya ta yi ba tare da sallama ba. Mama ta juyo da fuskar bala’i tana faɗin
“Wani mara hankalin ne ke buɗe mini ƙofa haka…?”
Kafin ta ƙarasa, idonta ya sauka cikin na Iya wacce ke tsaye tana kallonta da wani irin kallon tuhuma. Bata san lokacin da ta yi wurgi da wayar hannunta ba.
“Ni ce mara hankalin,” Iya ta faɗa da murya mai ɗauke da izza.
Mama ta yi murmushi ƙarfin hali,
“Sannu da zuwa I…”
“Dakata da gaisuwarki!” Iya ta katse ta. “Me za ki yi yanzu haka?”
“Ehm… dama wanka zan shiga yanzu,” Mama ta faɗa tana jin tsoro.
“Toh, ko miye za ki yi, na baki minti ishirin ki same ni a parlour,” Iya ta faɗa tana ɗaukar wayar da Mama ta jefar.
Ta fita daga ɗakin ta bar ƙofa a buɗe.
---
Yayin da take sauka daga bene, tana mita kamar wacce a ka yi wa dole.
“Wallahi bana son hawa benen nan amma shegiyar matar Bashir ta sa ni hawa. Allah sai ya saka mini. Haba! Wannan kuwa shigan haƙi ne.”
Ta zauna kan babban cushion tana maida numfashi.
Daddy ya miƙe,
“Toh sai na dawo.”
“A dawo lafiya Daddy,” suka ce masa.
“Iya, bari na wuce office,” Daddy ya ce yana kallon agogon hannunsa.
“A’a, ka dakata! Ina da magana da gaba ɗayan ku.” Iya ta ce cikin muryar isa.
Ta nufi dining, ta ja kujera ta zauna. Daddy ya zauna a parlour tare da su Iman.
A gefe guda, Iya ta miƙa wa Musharraf wayar Mama,
“Duba min wannan.”
“Wayar wa ce wannan?” Musharraf ya tambaya.
“Wayar Sahura ce,” Iya ta ce tana miƙa hannu. “Duba min da wa ta gama waya yanzu.”
“Me za ki yi da wanda ta gama waya yanzu?” Musharraf ya faɗa yana bin ta da wani kallo.
“Mtseew, ba ni wayar!” Iya ta ce ta fisge wayar daga hannunsa, ta miƙa wa Rauda
“Ke Rauda, duba min da wa ta gama waya yanzu.”
Rauda ta shiga call log ta duba sannan ta ce
“Da Hajiya Turai.”
“Waye Turai?” Iya ta tambaya tana gyara zama.
“Abokiyar makircinta,” Zahra ta faɗa tana kawar da kai kamar ba ita ta faɗa ba.
“Ke Zahra!” Musharraf ya daka mata tsawa.
“Kai Musharraf! Kar ka sake! Ni ce na tambaye ta,” Iya ta ce tana huci. “Kin san Turai kenan?”
Zahra ta yi shiru.
“Kai ku bamu waje!” Iya ta ce tana kallon su Musharraf. “Kun gan maza a nan ne? Duk kun bi kun cika waje da ƙamshin turaren maza.”
Bayan sun fice, Iya ta juyo ga Zahra,
“Wacece Turai?”
Zahra ta yi shiru, tana wasa da yatsunta.
“Speak, Zahra,” Raflah ta ce.
“Ki yi mata turancin ƙila ta fi fahimta,” Iya ta ce.
Zahra ta ce
“Turai aminiyarta ce. Duk lokacin da ta zo gidan nan, rikici sai ya tashi, kafin ta tafi ko bayan ta tafi
”
“Daga ina ta fito? Waye mijinta?”
“Ban sani ba.”
“Sahura dai ta rantse ba zata daina bin ƙawayen banza suna zuga ta ba ko?Toh zan ɗauki mataki akan ta.”
Rauda ta ce
“Mama ba zata canza ba. Kinji abinda ta yi wa ƙawayen Zahra jiya kuwa?”
“Me ta yi musu?” Iya ta tambaya.
“Wai ta zazzage su tana kiransu almajirai da ɓarayi.”
“Ɓarayi?” Iya ta ƙara faɗa tana huci. “Me suka sata?”
“Babu komai. Ta ce duk talaka ɓarawo ne. Ta kuma zazzage musu kaya tana ce za ta kira polis,” Zahra ta faɗa cikin baƙin ciki.
“Kai jama’a! Sahura ta koma ƴar daba wallahi!” Iya ta ce tana girgiza kai. " Ni tsoro na ɗaya kar wata rana ta daɓa wa ɗa na wuƙa na shiga uku. Toh wallahi na rantse yau zan bata mamaki, sai na kawo ƙarshen dabancin ta a gidan nan.
Bayan mintuna goma sha biyar, Mama ta sauko.
“Sannu da gajiyar hanya Iya,” ta ce da fuskar ƙyashi.
Iya ta ɗaga mata hannu ta dakatar.
“Raflah, ku zo nan. Ke kuma A’isha, haura sama ki kira min Amina!”
A’isha ta tafi, ta dawo da Mommy.
Bayan kowa sun haɗu, iya ta gyara zama.
“Na tara ku ne saboda wata magana da ta taso,” Iya ta ce tana kallon kowa.
“Wai a ce kamar Ni Fatima zan zo gidan nan amma ban ci arzikin Sahura ta zo ta gaishe ni ba balle ta sa ƴaƴanta su zo. Wai shin me kika mayar da ni ne? Ko haka kike wa Hanne?”
Mama ta sauke kai tana cewa
“Wallahi Iya ban san kin zo ba, da…”
“Karya kike, munafuka!” Iya ta katse ta cikin masifa. “Ke da ki ka ɗauki waya kina faɗa wa ƙawayenki cewa jarababiya tsohuwa ta zo!”
“Wallahi ba da ke nake yi ba…”
“Ki faɗa wa wanda bai san halin ki ba. Toh bari kiji! Ni ba jarababiya ba ce, sai dai uwarki Hanne mai ƙosai!. Iya ta faɗa cikin faɗa.
"Kuma ki sani daga yau bana buƙatar gaisuwar ki, babu dole tunda ban haɗa komai da ke ba, kawai ɗa na ki ke aure. Amma ki sani, jikoki na ba ki isa ki raba ni da su ba!”
Daddy ya yi numfasa, ya ce
“Iya ki yi hakuri. Zan yi magana da ita.”
“A’a! A yau zan ɗauki mataki da kaina. Wallahi ba zan bar wannan maganar ta shuɗe ba!” Iya ta ce tana nuna Mama da yatsa.
“Ke Sahura, daga yau na haramta wa wata Turai shiga gidan nan! Tunda ba gidan uban ki bane. Kuma wayarki, na amshe! Ba za ki riƙe wata waya a hannunki ba har sai na bar gidan nan. Na gaji da cin mutunci da ki ke yi mini da ƙawayen ki ta waya!”
Iya ta faɗa tana kallon ta directly babu ko kiftawa.
“Sai kuma, duk wata magana ta Zahra ko ƙawayenta ba ta shafe ki ba! Idan ki ka ci gaba da tsangwamar ta kuma za ki gane ni ce Iya,” ta faɗa cikin ɗaga murya da gargaɗi."
Daddy ya girgiza kai yana jin kunya, ya miƙe,
“Iya, zan shiga office…”
“Ka tafi! Amma ka sani, ni zan rufe duk harkar da za ta jawo mini baƙin ciki a gidan nan. Idan ba ɗan Adam mai manta laifinsa yana hangen na wani ba, har Sahura ta mance lokacin da ta ke talaka, a talakar ma ƙasƙantaciyar me aiki, har ta manta lokacin da ta sata wa Marigayiya Hadiza sarkar zinari ɗinta. Wai amma yau har tana da baƙin cewa wasu talakoki, ɓarayi.”
Mama ta kasa magana saboda tsananin kunya.
Mommy ta ce da taushi
“Iya ki yi hakuri, ba lallai ki mata faɗa haka a gaban yara ba…”
“Toh ai a gaban yaran nake so in yi faɗan, saboda su ma su gyara idan sun fara banzan hali. Ko ke kin isa ki hana ni?!”
Mommy ta yi shiru don ta san halin Iya, ba ta bar kowa ba .
Iya ta yi gaba da masifa, ta bar Mama a nutse da baƙin ciki.
Daddy ya kaɗa kai ya fita. Musharraf da Abdul suka mara masa baya cike da takaicin abinda Iya ta yi .
Zahra da Raflah suka koma dining
“Gaskiya bakin Iya ba ya da filter,” Zahra ta ce.
“Ina fa. Amma gaskiya Iya ba ta kyauta ba." Raflah ta amsa.
Rauda da gefe ta ce "Me ta yi na rashin kyautawa."
Raflah ta ce "Gaskiya bai kamata ta yi mata irin maganar nan a gaban yara ba."
"Ita Maman idan za ta yi rashin mutuncin ai ba ta la'akari da wannan, beside this is not the first time Iya is warning her." Rauda ta faɗa cikin halin ko in kula.
---
A ɗakin Mama kuwa, tana kuka tana cewa
“Wallahi bazan bar wannan cin mutunci ba. Sai na rama, sai na ga bayan Zahra da duk wanda ya goya mata baya. Wannan rantsuwa ce!”