Free chapter · Read without an account

Page 57

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Jameel ya matso kusa da ita sosai, ya ce; "Zahra ke ce? Ashe zamu sake haɗuwa? Ina mijin ki?"

Bakin Zahra rawa ya ke, ta kasa haɗa kalma guda balle ta furta, maganar sa ce ta ankarar da ita cewa ba fa mafarki ta ke yi ba; "Ina mijin ki? Ko ba tare ku ka zo ba?" Kai kawai ta girgiza mishi. Jameel ya yi ɗan murmushi ya ce; "Har yanzu kina nan da son zaƙi."

Zahra ba ta ce komai ba ta raɓa ta gefen shi ta bar wajen.

Musharraf da ke zaune yana jiranta, ya ƙura mata ido yana kallonta da ta doso shi.

"Me ya faru na gan kin wani birkice? Ina chocolate ɗin?"

"Bana so, mu je gida."

"Ban gane ba ki so ba?"

"Musharraf...Ashe tare ku ke?" Ta ji muryar Jameel daga bayanta, da sauri ta juyo, ta gan shi a bayan ta riƙe da box ɗin chocolate.

Musharraf ya zaro ido, ya ce; "wa na ke gani kamar Jameel? Daman kana ƙasar?"

"Eh wallahi jiya na dawo."

"Sannu da dawowa, ya mutanen gida?"

"Su na nan lafiya." Ya miƙawa Musharraf chocolate ɗin ya ce; "Gashi, har ta ɗauka da ta gan ni sai ta ajiye ta bar wajen, I thought ta ji tsoron kar mijinta ya ganmu tare ne, ashe da kai ta zo."

"Allah sarki, Thank you." Ya karɓi box ɗin chocolate ɗin ya miƙawa Zahra. "Idan ka ɗan huta You can come over to my house for dinner."

Jameel ya yi murmushi ya ce; "In Sha Allah I will find time and come."

Suka yi wa juna sallama, su ka yi musabaha. Zahra ta bi bayan Musharraf da sauri kamar za ta kife.

A bakin gate Musharraf ya yi parking saboda ba zai shiga ba, sai anjima da daddare zai dawo da Zainab.

Zahra za ta buɗe ƙofa ta sauka, ya ce; "Wait."

Juyowa tayi ta kalle shi, sai ya ce; "me yasa  ba ki faɗawa Jameel cewa ba ki da aure ba?"

"Saboda babu amfanin ya sani."

"Ba ki tunanin za ku iya dawo da soyayyar ku ta da? har ma ta fi da ƙarfi."

"Yaya ba ni da ra'ayin yin soyayya kuma."

"Don't you have feelings for him? Da kika gan shi ba ki ji komai ba?"

"Ba ni da feelings ɗin komai akan shi, ban kuma ji komai ba. Yaya I have moved on, na riga da na koyawa zuciyata haƙuri akan abinda ta rasa, kuma ta haddace wannan darasin."

"Kin tabbata ba ki da rogowar feelings for Jameel? Na fa san irin son da kika yi mishi, idan kin ce ba ki da feelings mishi me ya sa kika rikice da kika gan shi?"

"Ban san me yasa na acting that way ba, amma abu ɗaya da na sani shine; babu ko da burbuɗin son Jameel a Zuciyata, ba ma Jameel kaɗai ba, bana tunanin zan ƙara son wani. Definitely ba zan manta memories ɗinmu da Jameel ba, kirki da kulawar, tausayi da ƙarfafawar shi gareni abu ne da ba zan iya mantawa ba, amma babin soyayya mun rufe shi daman Allah bai ƙaddara cewa za mu yi rayuwa tare ba."

"Princess ki cire wannan tunanin ba za ki ƙara soyayya ba, zan iya yarda ba ki son Jameel yanzu, amma ba zan taɓa yarda cewa ba za ki ƙara soyayya ba, sai dai idan zuciyar ki ba ta gan wanda ya yi mata ba."

"Hmmm shikenan Yaya tunda ka kasa fahimta ta."

"Ba kuma zan fahimce ki ba."

___

Tunda Mama ta yi nasara wajen lalata maganar Yusuf da Zahra hankalin ta ya kwanta, ta ji cewa matsalar ta akan Zahra ya ja, yanzu Mommy za ta fuskanta gadan-gadan har sai ta kwace mijinta. Ta fi kowa sanin irin son da Daddy ke da shi wa Mom, don haka rabuwa da ita ba abu mai sauƙi ba ne, amma sai ta yi iya ƙoƙarin ta wajen ganin ta yi nasara. Mutum ɗaya ce tak za ta iya sa Daddy ya rabu da Mommy kuma ya aikata ko ya ƙi ko ya so, itace IYA. Mama ta yanke shawarar da Iya za ta yi amfani wajen fitar da Mommy a cikin gidan, duk inda za ta yi sai ta cusa wa Iya ƙiyayyar Mommy ta yadda Iya za ta tilastawa Daddy sakinta. Amma ta yaya za tayi hakan? Ita da Iya ta fi tsana akan kowa a gidan.

***

Sati ɗaya Zahra ta ɗauka tana koyon aiki a ƙarƙashin jagorancin MD. Sun saba sosai kamar Yaya da ƙanwa, Yaya Bilal ma take kiran shi akasin kowa da ke kiran shi da MD. A cikin sati ɗayan nan ta koyi abubuwa dayawa da ke bawa MD mamaki, bama shi kaɗai ba hatta Imam da MD ke ba wa feedback ya yi mamakin abubuwan da ta koya a ƙanƙanin lokaci haka. Yanzun haka tana da marasa lafiya da MD ya ba ta ragamar kula da su ita kaɗai, sai dai ta neme shi akan abinda ya shige mata duhu. Shaƙuwa sossai ta shiga tsakaninsu har ta kai ga ya haɗa ta abota da matar shi Harira. Zahra sun saba sosai da Harira kamar sun daɗe da sanin juna, Harira Business Woman ce tana sana'ar siyar da kayan kitchen da kuma turare; Na wuta, na wanka, na mopping, Humra and more, tana da yara biyu; Kamal da Kamila. Sosai Zahra ke siyan Kayan ƙamshi a wajenta kasancewar ta ma'abociyar son ƙamshi.

Zahra na shigowa office daga ward ta tafi duba marasa lafiyar da ke ƙarƙashin kulawarta, ta saki murmushi ta ce; "Ashe baƙuwa mu ka yi yau?"

Harira ta yi dariya ta ce; "Tuntuni na zo, har na ce zan tafi tunda ba ki dawo ba, amma Yayanki ya ce sai na jira ki."

"Ai kuwa ya kyauta. Ya fita ne?"

"Eh yanzu suka fita da DR. Aliyu."

Zahra ta taɓe baki ta zauna, ta ce; "Wash na gaji."

"Sannu aikin ku nan is not easy, balle ke da har yanzu ba ki fara shift ko ba."

"Gaskiya babu sauƙi, amma ina jin daɗin yin aikin saboda abinda raina ke so ne."

"Haka ne, Allah ya yi jagora, ga abinci na kawo mu ku." Harira ta faɗa tana turo basket da ke ɗauke da kula ɗin abinci da su plates."

"Wannan ƙaton kular, me kika mayar da mu ne?"

"Da DR Aliyu fa na zubo, saboda Dear ya faɗa min yana office yau."

"Ok matar Dear."

Zahra ta ɗan ci shinkafar da Harira ta kawo, sai ta hau kan computer ɗinta tana updating report ɗin patient ɗinta, tana yi suna ɗan hira. Suna a hakan for almost one hour kafin MD ya dawo, bai daɗe ba ya ƙara fita.

Harira ta miƙe ta ce; "Zahra bari na tafi gida, yaran nan sun kusa tashi a makaranta."

"Ok, mu je na raƙa ki."

Har bakin mota ta raƙo ta, sai da ta gan fitarta daga harabar asibitin kafin ta juya ta koma. Tana shiga ta gan Imam a tsaye; "Ina MD?"

"Ya fita amma ban san inda ya tafi ba."

Har Imam ya fita sai ya dawo, ya ɗan kalleta ya ce; "ki daina sa kayan da yake exposing jikin ki, be decent ke musulma ce kuma kin fito gidan mutunci." Ya fita ya barta tsaye. Zahra ta kalli kanta ta gan abinda ya ma kayan jikinta amma ba ta gan anything wrong ba. Baggy jeans ne ta sa mai faɗi sosai da top, sai ta yafa gele. Duk da faɗin Baggy ɗin bai hana fitowar curvy shape ɗinta ba. Taɓe baki ta yi ta ce; "Ni dai na san ba abinda ya yi wa suturata."

***

Ranar Friday da asuba Zainab ta haifi kyakyawar ƴarta mace mai matukar kama da marigayiya mahaifiyar Musharraf. Zahra farin ciki ta rasa yadda za ta saka kanta, ta ma fi Musharraf da aka yi wa haihuwar nuna farin ciki. Tunda ta riƙe baby ɗin ta ƙi ba wa kowa, duk wanda ya zo barka sai dai ya kalli yarinya a hannunta. Saboda zallar farin ciki tunda aka yi haihuwar Zahra ta daina zuwa asibiti, kuma ba ta rubuta komai ba game da fashi da ta ke yi ba. A ranar suna babu yadda su Mommy ba su yi da Musharraf akan a mayar da sunan marigayiya ba, amma fur yaƙi, ya ce; yadda su ke son ƴar uwar su haka ya ke son nashi, ya raɗa wa yarinya suna da Fatima, Zainab ta ba ta ukti as pet name. Zahra ta yi murna kamar an yi mata albishiri da gidan aljanna. Da daddare tana riƙe da Baby tana kallonta tana murmushi, Musharraf ya shigo, miƙawa Zainab yarinyar ta yi ta tashi ta rungume shi ta ce; "Thank you so much Yaya." Godiya ta fara masa har tana hawaye don tun da safe bai samu shiga gidan ba sai yanzu saboda mutane. Murmushi yayi ya lakuce mata hanci, ya ce; "I now have a princess and a little princess. This has always been my dream; Na haifi ƴa mace na saka mata sunan ki, idan na ƙara kuma na saka sunan Mommy, and I'm very happy Allah ya cika min buri na akan na farkon."

Rungume shi sosai Zahra ta yi tana hawaye. Share mata ido ya yi, ya ce; "Kukan me ki ke yi kuma? Are you not happy?"

Hawayenta ta share ta ɗan ja hanci, ta ce; "I'm more than happy."

"Good. Allah ya kawo miki miji, kema ki haifa min takwara."

Murmushi kawai Zahra ta yi, ta sake shi ta tafi wajen Zainab ta miƙa hannu, ta ce; "Bani ƴata."

Zainab ta miƙa mata tana murmushi ta ce; "oh sabon shigar yin ƴa."

"Eh ɗin, ki yi mana idan da sauƙi." Dariya dukkan su suka yi.

Musharraf ya zo ya ɗan lakuce hancin babyn, ya ce; "Little princess, ki ɗauki duka halin Maminki, amma banda saurin kuka da shan zaƙi. Allah ya yi miki albarka"

Zainab ta yi murmushi ta ce; "Ai wannan da halama ta ma ɗauki saurin kukanta."

"Eh abar min abata." Zahra ta faɗa tana rungume Ukhty.

***

Bayan suna da kwana uku Zahra ta shirya ta tafi wajen aiki. Da Musharraf ya yi parking a harabar asibitin sai ta ƙi fita a mota.

"Princess ya aka yi?"

"Bana son Imam ɗin nan ya yi min faɗa, ban ɗauki hutu ba kawai na daina zuwa har na kusan sati biyu fa."

"Ki tafi kawai, faɗa ne kawai zai miki ba zai duke ki ba, idan yana faɗan ki bashi haƙuri kawai komai ya wuce. Ƙilla ma ba zai ce miki komai ba."

"Ai faɗar sa tafi shirun sa, idan na yi laifi bai yi faɗa ba wallahi kallon da yake min yana rikitar da ni, kuma fa Ni kaɗai ya ke wa hakan." Ta faɗa kamar za ta yi kuka.

"Ke ɗin ma don Ni na haɗa ki da shi, kuma na ce ya sa miki ido ya tabbatar kin iya aiki sosai so that idan na gan wasu kuɗi ma su nauyi sun shiga wa Daddy na yi convincing ɗin shi ya gina miki asibiti."

"Yaya ai na iya aikin ko, gashi result ɗin mu ya fito, wallahi I just want to leave this place."

"Princess ki yi haƙuri ki tsaya ki koyi aiki da kyau."

Zahra kamar za ta yi kuka ta fita daga motar ta shiga asibiti, gabanta na faɗuwa, tana matuƙar tsoron haɗuwarta da Imam.

Zahra na shiga cikin asibitin, ta turo ƙofar office a hankali kamar munafuka. Tana shiga ta sunkuyar da kai ta ce; "Yaya ina kwana."

MD ya kalleta ya yi murmushi, sai ya ce; "Hajiya Zahra uwar jego, sai yau?"

Zahra ta sunkuyar da kai ta yi shiru. "Je ki zauna, bani da abin faɗi sai DR Aliyu ya zo."

Sumi-sumi Zahra ta je ta zauna gabanta na faɗuwa jin sunan Imam da MD ya ambata. Tana nan zaune shiru MD ya miƙa mata wani file ya ce; "check this patient in room 8."

Zahra na fita da kaɗan Imam ya shigo ɗauke da wani file, ya ajiye a gaban MD ya ce; "Ina ganin daga sati mai zuwa za ka koma ɗayan asibitin, Ni zan kasance a nan, tunda yanzu I'm a bit stable." Juyowa da zai yi ya hangi jakar Zahra da ke kan table da take using, ya ɗan kalli MD, ya ce; "Fatima ta zo ne?"

"Eh, na tura ta duba mara lafiya."

"Ok, idan ta dawo ka ce mata ina neman ta."

"Ok Sir."

Zahra na shigowa office da file ɗin mara lafiya da ta duba, ta zauna a kujera tana faɗin; "Wash na gaji."

"Ai ba wash ba, tashi za ki yi yanzu ki tafi DR Aliyu na neman ki."

Zahra ta gyara zama a zauren, ta zazzaro ido; "Me na yi to yake nema na?"

"Au ba ki ma san abinda kika yi ba, well idan kin tafi zai faɗa miki."

"Yaya wallahi bana son faɗar shi ne."

"Zahra kin yi abin faɗa dole a Miki, kuma wanda ke son ka shi ke maka faɗa don ka gyara, yanzu ki je ki ji faɗar da zai miki, ki ba shi haƙuri, ki kuma ɗau gyara."

Kai Zahra ta gyaɗa kamar za ta yi kuka. Ta fita daga office ɗinsu tana tafiya a hankali. A daidai bakin ƙofar office ɗin Imam ta tsaya shiru gabanta na faɗuwa, ta yi kusan mintuna goma tana tsoron shiga kafin ta ɗan yi ƙarfin halin tura ƙofar ta shigo. Imam na aiki a laptop ɗin shi  ta shigo, bai ko ɗago kai ya kalleta ba, daga ƙamshin turarenta da yanayin yadda aka turo ƙofar a hankali ya fahimci ita ce.

"Ina kwana." Zahra ta furta a hankali.

Ba tare da ya amsa gaisuwar ta ba, ya buɗe drawer ya ciro wani folded paper ya miƙa mata. Hannu na ɓari Zahra ta amsa paper ɗin tana jiran ƙarin bayani.

Bayan shiru na ƴan mintuna, Imam ya ce; "Is for you."

Zahra ta ɗan kalle shi, sai ta warware paper ɗin, Zaro ido ta yi, ta ce; "Suspension letter, na me? Me na yi?"

"Kin iya karatu, sai ki karanta ki gani.

"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un." Zahra ta faɗa tana dafa goshinta. "Dan Allah ka yi haƙuri wallahi Yaya da Mommy za su yi min faɗa."

"Oh ba wai kin gane kuskuren ki bane ma? Ke dai kawai tsoron faɗa kike yi."

"Wallahi I have realised my mistake, ka yi haƙuri zan gyara, na yi alƙawarin ba zan sake maimaita irin kuskuren nan ba."

Imam dai bai kuma ce mata ƙala ba, da ta dame shi da magiya ma sai ya ɗauki laptop ɗin shi ya fita ya bar mata office ɗin. Zahra ta fita riƙe da paper ɗin a hannu ta tafi office ɗinsu. Jakarta ta ɗauka, ta saka letter ɗin a ciki ta kalli MD da ya lura da mood ɗinta ya canza amma sai ya fuske a tunanin shi ƙilla Imam ya yi mata faɗa ne, ya ce; "Yaya zan tafi gida."

"Gida? Saboda me? Saboda an yi miki faɗa?"

Kai ta girgiza ta ce; "Bai yi min faɗa ba, Suspension ya ba ni." Ta ƙarasa faɗa tana goge hawayen da ya gagaro mata.

"Wane irin Suspension?"

Paper ɗin ta ciro daga jakarta ta miƙa masa.

"What! Har na wata uku?" Ya furta bayan ya karanta content ɗin letter ɗin. Kai Zahra ta gyaɗa tana kuka.

"Zahra kin yi kuskure, me yasa ba ki sanar da shi akan ba za ki zo kwana biyu ba? What you did was very wrong, amma In Sha Allah zan yi magana da shi ya rage miki kwanakin suspension ɗin nan, ya yi yawa."

MD ya ɗan yi mata faɗa, sai ya ɗora da lallashinta kafin ya raƙa ta har bakin gate ɗin asibitin, ya tare mata abin hawa.

Zahra na isa gida ta wuce Iya da ke zaune falo tana kallo. Iya ta bi bayanta da kallo ta ce; "Wannan kuma kukan me take?"

Zahra ta kwanta kan gado tana kuka, a wannan yanayin bacci ta sace ta.

Da azhar ta farka ta yi sallah, sai ta sauko ƙasa yin lunch. Musharraf da ya zo haɗa mata lunch basket ɗinta ya kalleta, ya ce; "Why are you home?"

"Shi ya ce na dawo gida." Ta faɗa tana goge hawaye.

"Shi wa?"

"Imam."

"Saboda me?"

"I didn't take permission before staying off work, don haka ya ba ni suspension na wata uku."

"Subhanallah, Zahra what have you done?"

Zahra ta fara shesheƙa.

"Is ok, kar ki yi mini wani kuka a nan. Zan kira shi mu ji yadda za a gyara abin."

Mommy da Daddy ma ba su iya yi mata faɗa ba da su ka ji abinda ya faru saboda ganin yadda Zahra ta shiga damuwa.

Imam na kwance a ɗaki yana kallon wani action movie, ya lulluɓa a bargo saboda sanyin AC da ya ƙure, wayar sa da ke gefen sa ya fara ruri, miƙa hannu ya yi ya ɗauka.

"Hello..."

"DR ya yammacin?"

"Alhamdulillahi."

"Na kira ne concerning Zahra."

"Na san za ka kira, amma gaskiya za ka yi haƙuri, Fatima have to serve this suspension. Fatima na ƙoƙari sosai wajen mayar da hankali akan aikinta, but ba ta ɗauki aikin da seriousness ba, wannan suspension ɗin zai sa ta gyara wannan halin nata."

"Hmmm, DR ban ƙi taka ba, amma ina roƙon alfarmar da ka rage mata tsawon kwanakin suspension ɗin."

"MD ya riga neman mata wannan alfarmar, but I'm yet to decide, yanzu na ba ka dama kai ka deciding kwanakin da za ta yi a suspension ɗin."

Shiru Musharraf ya yi yana ɗan nazari, idan ta shi za a bi ayi haƙuri kawai Zahra ta resume aiki gobe.

"Musharraf ina sauraron ka." Imam ya katse mishi tunani.

"Errm Please can you make it one week?"

"Shikenan, Allah ya kaimu."

"Ameen, na gode, Allah ya bar zumunci."

"One more thing..." Sai ya ɗan yi jim na wasu lokuta;"Ka rage pampering ɗin Fatima saboda kadda ta sangarce."

Murmushi Musharraf ya yi ya ce;"Zan yi ƙoƙari."

___

Washegari Zahra ta yi kusan dukkan aikin gidan, just to keep her busy ta ɗan rage tunani. Tana jera breakfast a dining Daddy ya sauko, Dinning ɗin ya nufa, ya ja kujera ya zauna, ya ce; "Yau Uwata da kanta ta yi girki kenan."

Zahra ta yi murmushi ta ce; "Should I serve you?"

"Yes Please. Wai ina Mommynku ne?"

"Tana garden ta yi baƙuwa."

Bayan Daddy ya gama break fast, ya ɗan yi wa Zahra faɗa akan kadda ta ƙara yin absent a wajen aiki ba tare da kwakwarar hujja ba, kuma idan ta kama ta nemi izini.

***

Imam na shiga asibiti ya fara da duba marasa lafiya a ward, kafin ya wuce office. Yana aiki a system ɗinsa aka shigo aka sanar da shi cewa ga patient an kawo emergency kuma duka likitan na busy.

"Ina DR Fatima?" Ya tambaya.

"Ba ta zo ba ko." Nurse ɗin ta amsa.

Ɗan dafa goshinsa ya yi da ya tuna cewa ya bata suspension, daman ya mance gabaki ɗaya.

A ranar Imam was over worked saboda MD ya koma ɗayan branch ɗin su, kuma MD is the only person he enjoy working with.

Da daddare bayan ya koma gida, ya yi wanka da dukkanin night routine ɗinsa kafin ya kwanta a kan gado, ya ɗan lumshe ido. Da sauri ya buɗe idanunsa, ya ɗauko wayarsa a kan side drawer, ya ɗan latsa sai ya sa a kunne; "Ammi..." Ya furta bayan ya ɗaga kiran.

"Imam ya ka ke?"

"Lafiya ƙalau, how's your leg?"

"Alhamdulillah. I guess you have been busy today."

"Wallahi, na gaji sosai, har na kwanta na tuna ba mu yi waya ba."

"Allah sarki, Allah ya taimaka kuma ya yi jagora."

"Aameen Ammi. Ina Deen? Ya yi bacci ne?"

"Yau rigima ya ke ji, gashi can zaune."

"Me ke damun shi?"

"Wai Nana ta zo su tafi shan ice cream, kuma dentist ɗinsa ya yi magana akan a rage mishi zaƙi."

"A rage ga aka ce Ammi, su je ta siya mishi half ɗin yadda ta saba sha, zan tura ma ta kuɗi."

"Gaskiya Imam ba ka da kara, shikenan zan faɗa mata."

Imam ya ɗan sosa ƙeya, shifa duk abinda ya shafi Ammi da Deen to fa bai san kara ko kunya a kai ba. Suka yi sallama da Ammi.

Imam na lumshe ido a wannan karo sai picture ɗin Zahra lokacin da ta ke ba shi haƙuri akan suspension da ya ba ta. Guntun tsaki ya yi, ya ce; "little brat."

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.