Free chapter · Read without an account

PAGE 63

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Imam ya buɗe mata front seat, Zahra ta ɗan kalle shi kafin ta shiga, ya rufe ƙofa ya koma driver's side ya shiga shima.

The drive to Zahra's house was silent; hankalin Imam na kan titi ne, ita kuma Zahra nata na wayarta tana chatting da Farha.

A daidai bakin gate ɗin gidansu yayi parking. Zahra na jin tsayuwar motar ta ɗaga kanta, ta gan har sun iso gidansu.

"Thank you." Ta faɗa tana ƙoƙarin buɗe ƙofar side ɗinta, amma sai ta ji shi a ƙulle, juyowa tayi ta kalli Imam da ke kallon gabanshi, still looking at his front ya ce; "kar ki sake saka irin kayan nan zuwa wajen aiki, or else you'll go back home." Yana faɗin haka ya unlocking motar.

Zahra ba ta ce komai ba ta sauka daga motar ta shiga gida. Iya kawai ta tarar a falo tana bacci da remote ɗin TV a hannu, ta haura sama zuwa ɗakin Mommy. Babu kowa a ɗakin sai sanyin AC da ƙamshin room freshener, ta kulle kofar ɗakin, ta wuce ɗakinta. A gaban mirror ta tsaya tana ƙarewa kayan jikinta kallo, tana son ta gan dalilin da ya sa Imam ya ce kar ta kuma saka su; Baggy jeans ne da top. Ta ɗauki kusan mintuna biyar a gaban mirror tana kallon kanta kafin ta dawo bakin gado ta zauna, ta taɓe baki ta ce "why am I even worried, kamar wacce bata san halin shi ba, kawai dai masifar shi ce ta motso."

Tana ƙoƙarin cire wandon Farida ta shigo, mayar da wandon ta yi, ta ce; "Yauwwa Farida thank God you're here."

"Me ya faru? Kyautar chocolate zaki ba ni? Don na san ba ki rasa su."

"Ni dai ki kalle ni da kyau, sai ki faɗa min me yayi wa dressing ɗin nan."

Farida ta kalleta da kyau kamar yadda ta faɗa, ta ce "Nothing, ya miki kyau. Menene?"

Ɗan guntun tsaki ta yi, ta ce; "Daman na sani, babu abinda ya yi wa kayan kawai dai masifar shi ce ta motsa."

"Masifar wa? Wa yace dressing ɗin bai yi ba?" Farida ta tambaya.

"Waye idan ba Sir Imam ba"

"Gaskiya this your boss is troubling you."

"Mtseew ni nagaji da zuwa asibitin ma wallahi."

"Kar ki damu komai lokaci ne, In Sha Allah very soon zaki daina tafiya."

"Wai ina mutanen gidan suka tafi ne? Na ji gidan shiru." Zahra ta tambaya tana canza topic ɗin Imam.

"Sun ɗan fita ziyara ne zuwa gidan wani colleague ɗin daddy da ya dawo daga umra jiya."

"Ok. Bari na yi wanka to."

A ɓangaren Imam kuwa sai da ya tafi main house ɗinsu, ya yi wanka ya huta, kafin ya fita zuwa gidanshi, cewa Abba ya yi akan kwana zai yi a asibiti yau.

Yana shiga gidan ya nufi backyard, gurin da su Murtala suka ɗaura kassim.

Kassim farkawa kawai yayi ya gansa a ɗaure a wajen da bai san ko ina bane, gashi an toshe masa baki babu halin ya yi ihun neman taimako. Jin motsi da yayi ya sa ya buɗe idon da ya lumshe don gani wanene. Kallon Imam ya rinƙa yi trying to recall wanene, amma ya kasa tuno fuskar. Imam ma kallon Kassim ya ke yi yana mamakin wai wannan ƙazamin shine Zahra ta taɓa aure, ta yaya, gaskiya Zahra ta cutu.

Tape da aka liƙe bakin Kassim dashi Imam ya ja da ƙarfi, Ihun azaba Kassim ya yi, saboda tape ɗin ya ɓare da gashin bakinsa. Wani sharp knife Imam ya Ciro daga aljihun shi, ya saka mishi a wuya, ya ce; "Shut the fuck up!" Da sauri kassim ya haɗiye kukan da yazo mishi. Wayar Imam yayi ƙara a aljihunshi, ya sa hannu ya cire, ya sa a kunne; "Hello." Ya ɗan yi jim kaɗan, sai ya ce "I'm coming."

Imam na barin backyard ɗin Kassim ya fara ihun neman agaji kamar maƙogoron shi zai fita. Tun daga bakin gate da Imam ya buɗe wa Musharraf ƙofa suke jiyo ihun Kassim. Imam ya girgiza kai ya ce; "This guy think we're here to play with him dole ya mayar min da gida gidan mahaukata.

Suna ƙarasa backyard Musharraf ya ɗauke shi da wani wawan mari a baki, Kassim ya rinƙa kallon Musharraf da mamaki; Ashe dai saboda Zahra aka kawo shi nan.

"Har kana da guts ɗin kallo na?" Musharraf ya tambaya yana kai mishi naushi, bugun shi ya fara yi ta ko ina amma hakan bai yi mishi ba, ya kalli Imam da ya folding hannunsa yana kallon su, ya ce; "We need to untie him."

Imam bai ce komai ba ya Ciro wannan wuƙar a aljihunsa, ya yanka igiyoyin da aka ɗaura Kasssim da shi, ya ce; "Don't act silly, saboda idan ka yi wani ganganci zan yi maka raunin da zaka daɗe kana jinya.

Musharraf ya jacking Kassim a gaban riga, ya ce; "Get up you fool, har ka kai da zaka using wannan ƙazamin hannunka ka mare ƙanwata? Ko kana tunanin a duniya akwai wanda ya isa ya taɓa min Zahran ya tafi free bayan ina raye, to ka tabka babban kuskure." Yana kaiwa nan ya tura shi da ƙarfi har saida ya bugi kanshi a jikin gini, jini ya fara gangarowa daga goshinsa, yana miƙewa ya kaiwa Musharraf unexpected blow da yasa Musharraf ya yi tangal-tangal kamar zai faɗi, Imam ya yi sauri ya zo zai tare shi, Musharraf ya ɗaga mishi hannu ya ce; "Kar ka damu, I will handle him, I can see akwai sauran ɗanyen kai a tattare da shi." Musharraf ya fara folding hannun rigar shi, Imam ya yi sauri ya shiga tsakaninsu ya ce; "Musharraf please ka ja baya, I want to handle this guy tunda shi ɗin ɗan iska ne."

"No Imam kar ka yi min haka."

"Please Musharraf, you're a family man, idan ka tafi gida da rauni hankalin matarka zai tashi, but me I have nobody to bother about..." Saukar naushi da Imam ya ji a bakin shi yasa ya daidaita tsayuwar shi, ya tura Musharraf baya ya naɗe hannun rigarsa, togar da miyau da zai yi sai ga jini alamar Kassim ya fasa mishi baki, murmushin gefen baki yayi. Kassim na kokarin kawo mishi wani naushin ya yi saurin tarewa, ya murɗa hannun da ƙarfi har sai da yayi ƙara. Dambe ya ƙaure tsakanin Imam da Kassim, sossai Imam ya daki Kassim ta yadda bai yi tsammani ba. Kassim na durkushe yana mayar da numfashi bayan Imam ya gama dukan shi, Imam ya ƙaraso kusa da shi ya ce; "I wanted to torture you for just one week saboda ka gane kuskurenka ka kuma kiyaye maimaitawa akan wata, but then you proof to me cewa kai ɗan iska ne, abu ɗaya da baka sani ba shine gidan kazo, don haka I'm glad to let you know that you'll be spending three month a gidan nan, zan rufe ka a ɗaki yadda ka rufeta, babu wanka, babu wani jin daɗin rayuwa, amma I will provide you with food sau ɗaya a rana saboda kar ka mutu min a gida." Ya kalli Musharraf ya ce; "Bro leave this fight for me please."

Musharraf ya kaɗa kai alamar it's ok.

"Tashi na nuna maka ɗakinka, ko na kaika da ƙarfi."

Kassim ya tattara duka ƙarfin da ya rage a jikinsa, ya ruga a guje zuwa bakin gate, yana kaiwa gate ya gani a ƙulle,sai ya kama fence zai haura, shocking da ya girgiza shi yasa ya sake fence ɗin ba tare da ya shirya ba, ya yi wani irin mugun faɗuwa.

Imam da ya biyo bayan shi ya ce; "kar ka yi tunanin zaka iya fita daga gidan nan domin gidan nan ya fi gidan yari tsaro, za kuma ka iya ihu iya yadda kake so, babu wadda zai jika balle ya kawo maka taimako. Don't waste my time, now get up and follow me to your room. Kassim ya kasa tashi saboda shocking ɗin ya kashe mishi dukkanin gabobin jikin shi. Imam ya kama ƙafar shi ya ja shi kamar kayan wankin zuwa ɗakin da karensa ke ciki kafin ya mutu; "Wannan shine ɗakinka for three month, enjoy your stay." Ya yi banging ƙofar da ƙarfi, sannan ya sa key ya rufe shi ta waje.

Musharraf da ke tsaye a gefe ya ce; "Thank you Imam, but I really want to deal with this guy myself."

Imam ya girgiza kai, ya ce; "No, this guy is dangerous." Sai ya ɗan shafi gefen bakin shi da Kassim ya fasa, ya cigaba da faɗin; "Da kai ya ji wa wannan raunin me zaka faɗawa Zainab idan ka tafi gida?me zaka faɗawa Mom, Dad da Fatima? Amma ni nobody cares, ba lallai ma wani ya lura ba, Ammi ce kawai za ta iya noticing, amma zan yi avoiding yin video call da ita har sai ciwon ya warke."

"Imam I'm so sorry." Musharraf ya faɗa yana ƙoƙarin taɓa ciwon da ke gefen bakin Imam ɗin.

Imam ya kaɓar mishi da hannu; "Ya kake bani haƙuri? Kana son nuna min cewa Zahra ba ƙanwata ba ce kenan?"

"No ba haka bane, Zahra ƙanwar ka ce mana."

"Idan haka ne, to ka ɗauka wannan ba komai bane, saboda idan wani ƙato zai ɗaga hannu ya mare ƙanwata na tabbata zafin da zan ji ya fi zafin wannan ciwon."

"Wallahi Imam you're more than a friend, you're a brother from another mother, Allah ya baka matar da za ta baka dukkanin kulawa, ta yaye maka dukkanin kewa, ta sanyaka farin ciki a kowane lokaci, sannan ta sauya ka daga wannan miskilin zuwa lively person." Ya faɗa yana ƙoƙarin rungume shi rungume shi. Imam ya tura shi, ya ce; "Go home, is getting late, idan ka kai gida ka rungume Zainab but not me."

Musharraf ya yi dariya, ya ce; "Allah ya baka mata shagwaɓaɓiya mai son jiki na gan yadda zaka yi."

Imam ya juya baya ya fara tafiya zuwa falo, ya ce; "Sai ka yi kuma. Idan ka fita ka tura gate ɗin kawai, I will lock it idan na fito." Ya shiga ciki ya bar Musharraf a wajen.

***

AKASIN TSAMMANI

(Beyond All Odds)

Young Talented Writers Asso...YOTA

YOTA ID/023

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.