Free chapter · Read without an account
PAGE 69
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
"Anty Zahra."
Zahra da ta freezing saboda tsoro, ta sauke wani ajiyar zuciya, da ta ji muryar Farida ne, ba Mommy ko Daddy ba. Juyowa tayi tana kallon Faridar.
"Anty Zahra ina kika tafi?"
"Sa min ido kika fara yi kenan?" Zahra ta tambaya tana hararar ta.
"A'a ba haka bane, na gan ba ki saba fita by this time bane, kuma sanɗa na gan kina yi."
"Zo ki zauna." Zahra ta nuna mata waje kusa da ita. Farida ta ƙaraso ta zauna a gefenta tana kallon kayan da Zahra ta juye a kasar, ta ce; "Ina kika samo wannan? Ko dai yau ɗin ma ke kaɗai Yaya Musharraf ya kai shopping?"
Kai Zahra ta girgiza, ta ce; "Ba Yaya Musharraf bane, Yaya Imam ne ya siya min.'
"Yaya Imam..." Farida ta faɗa tana ƙoƙarin tuna waye Imam. "Kar dai boss ɗinki?"
"Shi fa."
Farida ta fara ɗaga kayan tana kallo ɗaya bayan ɗaya, dogayen hijab ne jilbab guda biyar, da dogayen riguna biyar, sai designer turaruka kala-kala, ɗayan ledar kuma; chocolate ne iri-iri a ciki. Farida ta riƙe haɓa, ta ce; "Duk wannan ɗin na me?"
Zahra ta yi mutum shi, ta ce;"Gaskiya Farida ya kamata ki canza course zuwa mass communication, wanan tambayoyi haka."
"Anty Zahra kar ki kaucewa tambayata, ko dai soyayya kuka fara yi ban sani ba."
"Kin san ance ka ɓoye nema ka bayyana samu."
"Har ni za ki ɓoyewa neman, shikenan ba damuwa."
Zahra ta yi murmushi tana tattara kayakin, ta ce; wai ke me ya hana ki bacci ma?"
"Errm, daman na tafi ɗakin Mama ne mu ɗan yi hira da ita, mun kwana biyu rabon da mu yi hira. Ina shiga falonta na ji tana waya daga cikin ɗaki, ban san ko da waye take wayar ba, amma na fahimci mugun shiri suke wa Mommy. Shine na ce bari na zo na faɗa miki, ina fitowa daga ɗakin na gan ki cikin sanɗa kina fita."
Zahra ta zazzare ido, ta ce; "Mommy kuma, me ta yi mata, I thought Mama ta yafe mana koma me muka mata, kwana biyu bata bi ta kanmu ba."
"Zahra..." Sai ta ɗan yi jim, ta shara hawaye, ta ce "Mama ba za ta taɓa barinku ba, saboda tana tare da friends masu zugata, kuma tana baƙin cikin ganin Mommy cikin walwala, don haka duk hanyar da za ta bi wajen kawar da farinciki a rayuwarku a shirye take da bi."
"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un wannan wane irin masifa ce? Yanzu Farida me ake shirya wa mahaifiyata?"
"Gold ɗin Iya Mama za ta ɗauka ta saka acikin akwatin Mommy, kin san kullum iya sai ta duba gold ɗinta saboda tsadar shi, to a ranar da ta wayi gari ta gan babu kin san babu zaman lafiya a gidan nan.
Shirinsu shine idan Iya ta fara tayarwa da kowa hankali sai Mama ta kawo shawarar a rufe gida a yi bincike, Mommy ba zata kawo komai a ranta ba saboda ta san bata ɗauka ba sai ta amince da binciken.
Idan Iya tayi bincike ta tsinci gold ɗinta a ƙasar akwatin Mommy Kinga an shafa mata baƙin fenti, daga Iya, har Daddy, har ma'aikatan gidan nan a ɓarauniya za su na kallonta, wannan zai yi sanadiyar cusawa Iya tsanar Mommy a zuciyarta don iya ta tsani a taɓa mata kayanta.
Baƙin cikin haka kawai ya isa ya sa Mommy cikin baƙin ciki da tashin hankali, kuma idan ba a yi Sa'a ba Daddy zai iya sauwake mata tunda har ta iya yi wa mahaifiyarshi sata. Wannan shine abinda na ji suna shiryawa."
"Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji'un." Zahra ta faɗa tana share zufan da ya keto mata, tana zaune shiru, after minutes of silence ta ce; "I know what to do." Ta miƙe tsaye ta nufi ƙofa, Farida ta yi saurin riƙota, ta ce; "Zahra don Allah duk matakin da za ki ɗauka, kar ki manta Mama Mahaifiyata ce, kuma ina ƙaunarta, ba zan so a ci mutuncinta ba."
Maganganun Farida ya bala'in kashewa Zahra jiki, ta zauna dirshan a kan gado, ta daafa kanta dake juya mata. Farida ta kalleta ta ce; "Sai da safe." Kai kawai ta iya gyaɗa mata.
Farida na fita, Zahra ta kwanta ta fara tunanin yadda za ta hana Mama yin abinda ta ƙuddira ba tare da ta yi hurting ɗin Farida ba. Tana cikin tunani ɓarawon bacci ya sace ta.
Ƙarfe ukun dare, ta tashi ta yi alawla ta yi sallah, tana kwance akan darduma ta fara gyangaɗi. Kamar wacce aka mitsila ta tashi, ta tafi bakin gado ta ɗauki wayarta. Message ta yi typing;
'Nagode da kayan da ka siya min, I really appreciate.' Ta turawa Imam.
Immediately sai ga reply ɗinsa; 'me ya hana ki yin bacci?"
'Yanzun na farka.'
'ok.'
'Thanks for the stuffs once again.'
'Irin tufafin da za ki rinƙa sawa kenan, saboda ke ɗin ƴar gidan mutunci ne.'
'In sha Allah.'
Offline ya tafi, Zahra ta rinƙa bin chat ɗinsu tana karantawa daga farko, tana nan a zaune a wajen har aka kira sallar asuba. Tana idar da sallah, ta yi wanka ta koma gado ta kwanta. Bacci sosai ta yi, saboda rashin isasshen bacci da ba ta samu jiya ba, har sha ɗaya kafin ta farka.
A gurguje ta shirya cikin ɗaya daga cikin abaya da Daddy ya siya mata a wani tafiyarsa Umrah. Ɗakin Mommy ta fara shiga, ta tarar babu kowa sai ƙamshin turaren wuta dake tashi, makulin ɗakin ta ciro daga ciki, tana fita ta rufe ƙofar ta waje ta jefa makulin a handbag ɗinta. Tana saukowa falo ta iske Iya a zaune da zungureren buredi da kofin kakkauran shayi a gabanta.
"Hajiya Iya tamu, ke kaɗai ce a gidan?"
Iya ta yi kamar ba ta ji ta ba, ta cigaba da cin bread ɗinta, tana kurɓa shayi.
"Toh Iya wannan ƙyaliya haka, hala laifi na yi?"
"Au har tambaya kike yi, yaushe rabon da ki zo mu zauna mu yi hira Zara'u? wai ni me na yi miki ne ma tukuna kike wani kakkauce min?"
Zahra ta rungumeta ta gefe, ta ce; "Haba takwarata, ni na isa na kakkauce Miki, kawai dai abubuwane suka sha min kai."
"Wane abubuwan kenan? Ke da ba miji ba balle 'ya'ya."
"Eh to neman mijin ne na sa a gaba."
"Ja'ira ince har gida miji ya biyo ki, kika ƙi, kafin matarsa ma ta zo ta gwada mana hauka."
Zahra ta yi murmushi, ta ce; "Ba irin wannan mijin na ke magana ba, miji mai capacity nake batu."
"Ke kika san papacity da kike magana a kai."
"Kema zaki sani nan kaɗan ba da jimawa. Yanzun dai ina mutanen gidan suka tafi suka bar ki ke kaɗai."
Iya ta taɓe baki, ta ce; "Yanzu mamanki ta tafi wajen aiki, ita kuma dayar ta tafi yawan banzar da ta saba wai ita za ta je suna, Su Farida kuma sun tafi makaranta."
"Yaya Musharraf bai zo bane?"
"Ya zo, ya tarar kina bacci, shi yasa ya yi tafiyarsa kawai. Amma ga wannan wai na baki ki hau adaidaita." Iya ta faɗa tana miƙa mata sabobin dubu ɗaya guda uku. Zahra ta karɓi biyu, ta bar mata ɗayan tana faɗin; "Ki ci goro da wannan."
"Allah sarki ɗiyar albarka, Nagode Allah ya yi miki albarka, ya baki miji na gari da zuri'a ɗayyiba."
"Aameen." Ta ɗauki handbag ɗinta ta fita ta bar Iya na ta kwarara mata addu'a.
Tana shiga harabar asibitin ta hango motar Imam a parking lot, murmushi ta yi ta nufi hanyar office ɗinsu.
Turo ƙofar ta yi a hankali ɗauke da sallama a bakinta. Imam da ke haɗa coffee da coffee maker ya juyo ya kalleta.
"Ina kwana sir."
"Lafiya." Ya amsa a takaice.
Zahra ta yi murmushi ta zauna, tana farin cikin yau Imam ya amsa gaisuwarta.
"Why are you just coming?" Ya tambaya a lokacin da ya koma desk ɗinsa.
"I'm sorry, Bacci na yi ban san lokaci ya wuce haka ba."
"Ko wane lokaci da bacci kike fakewa ai."
Zahra ta sunkuyar da kai, ta yi shiru tana wasa da yatsun hannunta. Imam ya kafeta da ido yana kallon siraran dogon yatsunta masu kyau da suke ɗauke da fararan ƙumba da ya sha gyara, ya ɗan numfasa, ya ce; "I hate lateness, ki kiyaye."
"In Sha Allah."
Yau daga Imam ɗin har Zahra sun kasance very busy, ba su samu damar zama a office ba tunda suka fita.
Lunch da Musharraf ya kawo mu su ma babu wadda ya samu damar taɓawa.
Zahra ce ta fara shigowa office ɗin, ta janyo basket ɗin lunch, ta yi dishing abinci ta fara ci kafin Musharraf ya ƙaraso don lokaci ya tafi. Tana tsaka da cin abincin Imam ya shigo looking very exhausted, ruwan sanyi ya ɗauko daga fridge ya sha, ya kalli Zahra ya ce; "zuba min abincin."
Zahra ta ɗaga kai da mamaki ta kalle shi, idonta ya shiga cikin nasa saboda daman his eyes were fixed on her, da sauri ta sunkuyar da kanta, ta ɗauki plate ta fara zubo masa abinci tana mamakin wai yau ita ce zata zuba mishi abinci. All this while da kansa ya ke zuba abincinsa, ko me yasa yau ya buƙaci ta zuba mishi oho.
"Ya isa hakan, I'm not a glutton." Imam ya faɗa da ya gan yadda Zahra ke ta zuba masa abincin a plate absentmindedly.
Maganarsa ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, sai ta rufe kular abincin, ta dau spoon ta saka masa, sannan ta dau abincin ta kai masa har kan desk ɗinsa.
"Thank you." Ya furta a hankali.
Zahra ba ta ce komai ba, ta koma desk ɗinta, ta fara packing abunuwanta kafin Musharraf ya ƙaraso.
Imam ya miƙe ɗauke da empty plate da ya ci abinci, ya saka acikin lunch basket ɗinsu. Ya kalle Zahra ya ce; "Mu je na yi dropping ɗinki."
Yana parking a ƙofar gidansu ya ce; "Henceforth ni zan rinƙa dawo dake gida."
Zahra ta ɗan kallesa cikin rashin fahimta. Gira ɗaya ya ɗaga mata, ya ce; "Yes, idan closing time ɗinki ya kai, ni zan rinƙa dawo da ke gida, saboda Musharraf is occupied, kina stressing ɗin shi sosai."
"Ok, Nagode Allah ya saka da alkhairi."
Bai buɗe mata ƙofa ba, kuma bai ce komai ba, can dai sai ya ce;"You look better on this outfit."
Murmushi Zahra tayi ta ce;"Thank you."
"The smile also looks good on you."
Zahra ta yi murmushi ta rufe fuskarta da tafukan hannunta. Murmushi Imam ya yi ya buɗe ƙofa ya fita, gefen Zahra ya tafi ya buɗe mata ƙofar, a hankali ta zura ƙafafunta ta fita, ta ce; "Thank you."
Bai amsa ta ba, ya koma driver's seat ya ba wa motar wuta.
***
AKASIN TSAMMANI
(Beyond All Odds)
Young Talented Writers Asso...YOTA
YOTA ID/023