Free chapter · Read without an account
Page 72
by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)
Zahra ta kalle Musharraf, don itama tana son jin bayani daga bakinsa.
"Eh ya taɓa aure, amma ba su tare da matar yanzu." Musharraf ya yi musu ƙarya, don shima bai san komai game ga Deen ba.
"Yaro za ka ci zogale?" Iya ta tambaye Deen, tana nuna masa plate ɗin zogalen da ke gabanta. Kai ya girgiza mata da sauri.
Zahra ta miƙe zata shiga ɗaki, Deen ya yi saurin sauka daga jikin Iya, ya bi bayanta. Hannunsa ta riƙe suka fara hawa stairs.
Suna shiga ɗakin ta kai shi bathroom, ta yi mishi wanka. Ɗakin Khalil ta tafi ta nemo ɗaya daga cikin kayan shi da ya kaasa masa. Ta dawo ɗaki, ta sa wa Deen, tana faɗin; "Manage this, kafin mu je mu siya naka."
Ta ciro chocolate daga cikin wardrobe ɗinta, ta miƙa masa, ta ce; "Jeka downstairs wajen kaka, idan na yi wanka zan fito.
Har bakin stairs, sai da ta gan ya fara sauka daga stairs ɗin kafin ta koma ɗaki.
Tana zaune a gaban mirror tana shafe-shafenta, Musharraf ya turo ƙofar ya shigo. A bayanta ya tsaya, yana kallonta ta cikin madubi, ya ce;"Mrs Imam Ali."
Zahra ta yi murmushi, ta ce; "Yaya zolayar ko?"
"Gaskiya dai, Baga shi abu na tafiya yadda mu ke so ba, su Daddy sun yarda da alaƙar ku, Ammi ma ta yi na'am, to me ya yi saura?"
"Yaya tsoro nake ji." Ta faɗa kamar zata yi kuka.
"Tsoron me."
"Yaya Imam bai sona, ina tsoron irin zaman da za mu yi idan har muka yi aure."
Daafa kafaɗarta ya yi, ya ce;"Don't worry about that princess. A da cewa nake yi Imam zai so ki idan har kun zauna tare, amma yanzu na fahimci ba wai zai so ki bane, sonki ma yake tun yanzu."
Zahra ta juyo da mamaki tana kallon Musharraf, ta ce; "So na kuma yaya?"
Gira ya ɗaga mata, ya ce; "Eh, yau na gan zallar so da ƙaunar ki a idanuwar Imam."
"Yaya are you just saying this to make me feel good?"
"Not at all Princess. Na fahimci Imam ma yana sonki, sai dai shima bai gane hakan bane, yanzu ke za ki sa ya fahimci hakan."
"Ni kuma? Ta yaya?"
"Ba komai bane zan faɗa miki Zahra, ke ɗin mace ce, ya kamata a ce kin san yadda za ki yi ki fahimtar da shi."
"Wallahi Yaya ban sani ba."
"Shikenan, Zainab za ta zo ta yi miki duk bayanin da ya kamata."
Wayar Zahra da ke kan drawer ɗin standing mirror ya fara vibrating. Sunan da ta gani a kan screen ɗin wayar ne yasa ta kalli Musharraf.
"Pick your call." Ya faɗa yana zama a bakin gado.
"Hello Ina wuni." Ta faɗa a lokacin da ta yi picking call ɗin.
"Hope you reached home safe?"
Kai ta gyaɗa masa kamar yana ganinta.
"Where's Deen?"
"Yana tare da Daddy."
"Ba zai dame shi ba?"
"A'a."
"Errm thanks for your time, I really appreciate."
Shiru ta yi ba ta ce komai ba.
"Deen drinks tea at night, sorry for the stress I will put you through."
"Babu komai wallahi."
"Thanks. Good night."
Tana sauke wayar daga kunnenta, ta kalle Imam, ta ce; "Yaya da gaske Deen ɗan Imam ne?"
"Eh haka ya ce min."
"Yana taɓa aure kenan?"
"Princess abin is kind of complicated. Imam ya ce min bai taɓa aure ba, kuma Deen ɗansa ne, nima na kasa fahimtar abun, amma ban tambayesa ƙarin bayani ba, saboda a tunanina idan abinda ya kamata na sani ne zai faɗa min."
"Bai taɓa aure ba, kuma yana da ɗa?"
Kai Musharraf ya gyaɗa mata, ya ce; "Haka ya ce."
"But how comes?"
"Time shall tell, dole wata rana zai faɗa mana ta yaya."
"Alhaji ina ka samo yaro kyakyawa haka?" Mama ta faɗa tana zama a gefen Abba.
"Jikana ne." Daddy ya amsa yana shafa kan Deen da ya lafe a jikinsa yana kallon wayarsa.
"Jika kuma Alhaji?"
"Eh, ɗan saurayin Zahra ne."
"Saurayin Zahra?"
Kai Daddy ya gyaɗa mata.
Wani abu ne ta ji ya tokareta a kirji, daurewa ta yi kar wani ya fahimci halin da take ciki, ta miƙe tana faɗin; "Waash na gaji, bari na je na huta."
Ta wuce ɗakinta kai tsaye. Iya ta taɓe baki, ta bi ta da kallo har ta ɓata wa ganinta.
Bayan tafiyar su Deen, Ammi ta kalle Imam ta ce; "You made a good choice, domin kuwa mace dake son jininka ita ce matar aure."
Imam ya sosa ƙeyarsa cikin rashin sanin me zai faɗa.
Suna shiga falo, ya ce; "Ammi I'm scared."
"Tsoro kuma Imam?"
"Eh Ammi, I'm really scared."
Ammi ta riƙe kafaɗar shi, ta girgiza shi, looking directly to his eye ta ce; "Anya wannan Imam ɗina ne da na sani? Haidar ɗina, ban san ka da tsoro ba, kai ɗin jarumi ne, don haka ban son na ƙara jin kalmar tsoro a bakinka."
"Ammi dole na ji tsoron, saboda na yi amfani da Zahra ne saboda ki daina yi min maganar mata, amma sai ta shiga zuciyarki lokaci ɗaya. Tsoro na ke ji ko Zahra za ta yarda ta aure ni idan ta ji labarin past ɗina, tsoro nake ji ko za a aminta a gidansu ko da ta yarda, tsoro nake ji irin zamar da zamu yi idan mun yi aure tunda dukkan mu ba son juna mu ke yi ba. Ammi dan Allah ki ba ni lokaci na natsu na nema mace da take sona despite everything, kuma nima nake sonta, please."
"Hmmm Imam ban ƙi taka ba, amma idan ka gan ba ka aure Zahra ba sai dai idan ita ce ko family ɗinta sun ƙi, batun soyayya kuma, za ku developing wannan bayan aure. Imam..." Ta kira sunan shi with all seriousness.
Calmly ya amsa "Na'am."
"Ka faɗa wa Zahra asalinka, da kuskuren da ka yi a baya, idan ta ƙi ka, sai ka nemo wata, amma idan ba ta ƙyamaceka ba, to matarka kenan In Sha Allah."
"Ammi akwai abinda ya kamata ki sani; Fatima bazawara ce, ta taɓa yin aure, amma auren bai daɗe ba. Aurar da ita aka yi zuwa ga mutumin da bata san shi ba, kwata-kwata ba ta ji daɗin auren ba, don't you think yanzu ya kamata ta aure wanda take so, shima ya ke sonta."
"Wane irin ta taɓa aure?"
A takaice Imam ya ba wa Ammi labarin Zahra iya wanda Musharraf ya sanar da shi.
"Ai wannan shi zai daɗa sa na so auren nan ya faru, saboda na san a gidanka Zahra ba za ta taɓa fuskantar baƙin ciki ba, duk da kana iƙirarin ba ku son juna, na san ba zaka wulaƙanta Zahra ba, ko don albarkacin hallaccin da Musharraf ya yi maka, da kuma so da nake mata. Yanzu saboda abu biyu nake son auren nan; shiryuwar ka da farin cikin Zahra, kuma In Sha Allah zai tabbata."
Imam ya miƙe ya nufi hanyar ɗakinsa ganin zahiri Ammi ta kwallafa rai a tarayyar sa da Zahra.
A ɓangaren Deen kuwa, har masallaci suka tafi tare da Daddy. Bayan sun dawo daga masallaci, Daddy ya kai shi dinning area, ya yi serving ɗinshi dinner.
"Grandpa I want to eat with my mom." Deen ya faɗa a lokacin da Daddy ya tura masa plate ɗin abinci a gabansa.
Mommy da ta shigo dining area ɗin, ta ce; "Daga ina mu ka samo yaro?"
Daddy ya yi murmushi, ya ce; "Zahra ta kawo mana ɗa." Ya yi mata bayani akan yaron Imam ne. Mommy ta yi mamaki, don ba ta taɓa sanin Imam na da ɗa ba. Daddy ya katse mata tunani, ya ce; "Kira Zahran ya ce tare da ita zai ci abincin."
Mommy ta ja kumatun Deen, ta ce; "Ba za ka ci abinci da grandma ba?"
"Grandma is at home." Ya amsa yana pointing mata ƙofa.
Zama Mommy ta yi a kujerar da ke gefensa, ta ce; "I'm also your grandma. Ko baka so na ne?"
"Ina sonki saboda kina da kyau." Ya faɗa yana murmushi.
Daddy da Mommy couldn't help but to laugh. Mommy ta miƙe, ta ce; "Let me call your mom so that we can eat."
Zahra na kwance a kan darduman da ta yi sallah, tana kallon hotunan da suka yi da Deen a gidansu. Har Mommy ta turo ƙofa ta shigo ba ta sani ba, sai jin maganarta ta yi a kanta; "Maman yaro, yaron ki wai ki sauko ku ci abinci."
Zahra ta ɗago ta lalle Mommy, tana murmushi ta ce; "Yaushe kika dawo?"
"Yanzu na dawo na gan yaro daga sama."
Zahra ta yi murmushi, ta ce; "My Deen. Mommy ina son yaron."
"Ai dole ki so shi, tunda kina son ubanshi."
Murmushi Zahra tayi, ta ce; "Shima yana sona, kuka ya yi sosai wai zai bi ki, shine Yaya ya ce mu zo da shi, gobe sai ya komar da shi gida."
"Daddynku have explain to me. Yanzu ki tashi mu je mu ci abinci."
Zahra ta miƙe, ta yi folding kayan sallarta, ta saka hula ta rufe kanta. Mommy da ke kallonta, ta ce; "Your hair is beautiful, wace ta miki kitso mai kyau haka?"
"Nana, Yaya Imam's younger sister."
"Oh your sister in-law."
Zahra ba ta kuma cewa komai ba da ta fahimci zolayarta Mommy za ta ti. Ta yi gaba Mommy ta bi ta a baya
***
AKASIN TSAMMANI
(Beyond All Odds)
Young Talented Writers Asso...YOTA
YOTA ID/023