Free chapter · Read without an account

Page 81

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

Ranar Lahadi da safe Iyayen Imam suka zo nema masa auren Zahra. Bayan duk wani gaishe al'adar neman aure, aka saka rana nan da wata uku, a nan take Alhaji Buba, Yaya ga Alhaji Sammani ya bayar da dubu ɗari biyar a matsayin sadaki.

Mommy sam ta ji hankalinta bai kwanta da auren ba, tunda Daddy ya yi mata bayani akan kuskuren Imam na baya, hankalinta gabaki ɗaya ya tashi, tana tsoron kar a zo ayi aure kuma ya dawo da tsohuwar ɗabi'a, babu hanyar da ba ta bi ba don ta fahimtar da Daddy, amma sam ya ƙi sauraranta.

"Alhaji ka dubi girman Allah ka duba wannan maganar, saboda abin la'akari ne." Mommy ta faɗa a ladabce.

"Amina ban san ki da kafiya akan magana ba, amma tunda kin nace akan wannan, ki kira min Zahran, idan har ta amince da auren yaron nan bayan ta san komai, to dole a yi auren, idan kuma ta ƙi auren, sai na mayar musu da kuɗin su, na ba su haƙuri."

Mommy ta ji daɗi da Daddy ya saurareta a karo na babu adadi da take kawo masa maganar, ita ta san ko haka zahra ke yi, ba za ta yarda ta aure mutumin da yake da ɗa a wajen aure ba, ta tabbata ɓoyewa ƴarta gaskiya aka yi. Ta ɗauki wayarta ta kira Zahra, ta sanar da ita ta zo falon Daddy ta samesu.

Zahra dake tattaunawa da Musharraf da shigowarsa kenan, ta kalle shi, ta ce; "Yaya mu je falon Daddy, Mommy na nema ta a wajen, na san ba zai wuce magana akan auren nan ba."

Tare suka shiga falon Daddy, Mama da ke laɓe a ƙofa tana sauraren tattaunawar Mommy da Daddy ta yi saurin ɓoyewa da ta gan su, suna shiga ciki, ta koma bakin ƙofar ta laɓe don jin amsar Zahra.

"Mamana zo ki zauna kusa da ni." Daddy ya faɗa yana nunawa Zahra wajen zama a gefensa bayan sun gaisa.

Zahra ta zauna kusa da shi, ta sunkuyar da kanta tana ɗan jan yatsun hannunta a hankali, tana jiran ta ji dalilin kiranta.

Calmly Daddy ya yi wa Zahra bayanin dalilin kiranta, ya ɗan numfasa a hankali, sannan ya ce; "Ina son ki faɗa min ra'ayin ki ƴata, shin za ki iya auren wanda ya taɓa tabka babban kuskure a rayuwarsa sannan ya tuba daga baya, ko kuma kina tsoron ki aure shi ya kuma koma kuskuren baya."

Sunkuyar da kai Zahra tayi, ta ƙi barin idanunta su haɗu da na kowa, a hankali ta fara magana; "Daddy Imam bai ɓoye min komai akansa ba, ya faɗa min kuskurensa na baya da ma wadda ba ku sani ba, a hakan na yarda na fara soyayya da shi, saboda ina da Imanin Ubangiji ma na farinciki da shi na tubar da ya yi, to me zai sa ni na yi judging ɗinshi. Daddy, Ina son Imam, In Sha Allah ba zai koma jiya i yau ba."

Kallon Zahra Mommy ta rinƙa yi da mamaki, wai wane irin so ne take yi wa bawan Allah ɗin nan, Zahra ta taɓa soyayya a baya, amma ba ta taɓa ganin wanda Zahra ta rasa hankalinta a kan shi ba sai Imam.

"Zahra please don't make this mistake, ban son ki sake kuskuren aure a karo na biyu, shifa wanda ya saba da mata da wuya fa ya daina, I don't want to see you cry again my child." Mommy ta faɗa kamar za ta yi kuka, ganin irin kuskuren da Zahra ke son tabkawa.

Musharraf da ke zaune a gefenta ya riƙe mata hannu, ya girgiza mata kai, ya ce; "Ki sa musu albarka kawai Mommy, In Sha Allah babu komai sai alkhairi."

Kai Mommy ta shiga girgizawa, za ta yi magana Daddy ya ɗaga mata hannu, ya ce; " Kin san yadda muka yi, don haka bana son wani dogon magana."

Miƙewa Mommy ta yi, ta fita daga ɗakin cikin ɓacin rai, ta kasa gane meyasa dukkan suke in support of auren nan. Da farko itama tana son auren, amma yanzu dole su yi la'akari da wannan maganar da ta taso. Tana shiga ɗakinta ta faaɗa kan gado, tana tunanin abinda ya kamata ta yi next.

Daddy ya shafa kan Zahra ya ce; "Jeki ƴar albarka, Allah ya tabbatar da alkhairi."

Zahra ta miƙe a hankali, jikinta duk ya yi sanyi da ta gan Mommy na ƙin auren.

Tana shiga ɗakinta, ta yi alawla ta yi sallar azhar, bayan ta idar da adduointa, ta ɗauki wayarta, Nana ta kira, ta haɗa ta da Deen. Murmushi ta yi da ta ji muryar Deen a waya, yana faɗa mata yadda ya ke kewanta, sai ta ji wani ƙarfin gwiwa akan auren Imam, ta san dole Mommy ta sauko idan ta nuna lallai tana so, to fa kowa bai da option face su tayata son shi. Tana kashe wayarta ta ji wani kaso na damuwarta ya ragu, miƙewa ta yi, ta fita daga ɗakin. A daidai ƙofar ɗakin Mommy suka haɗu da Musharraf.

"Ina za ki je?" Ya tambaya yana kallonta.

"Ina son na gan Mommy ne, na ba ta haƙuri idan na ɓata mata rai, sannan na roƙeta ta tayani son abinda nake so."

"No, kar ki tafi yanzu, ki barta tukuna, Ni zan yi magana da ita."

Marairaicewa ta yi kamar za ta yi kuka, ta ce; "Yaya Mommy ta sa jikina ya yi sanyi, ina ji kamar auren nan ba zai yiwu ba."

"Kar ki yi magana haka, komai zai yi daidai In Sha Allah."

Musharraf ya shiga ɗakin, ita kuma ta juya ta koma ɗakinta da addu'ar Allah ya sa Musharraf ya iya convincing Mommy.

Tana kwance shiru a ɗakinta, Musharraf ya turo ƙofar, da sauri ta miƙe daga kwancen, Musharraf ya zauna a gefenta a bakin gado, ya ce; "Mommy ta kafe akan ba ta son auren nan, amma ki kwantar da hankalin ki, zan kira Grandpa, don na san shi kaɗai zai iya tankwasa Mommy akan abu."

Zahra ta rasa abin faɗa, shiru ta yi, ta riƙe kanta, tana sauke numfashi hankali. Musharraf ya fita daga ɗakin, ya rufo mata ƙofa.

A ɓangaren Imam shirye-shirye ake yi hankali kwance, Anty ce kan gaba akan shirye-shiryen, zuciyarta fari ƙal tunda ta ji bazawara Imam zai aura, da farko da ta ji maganar auren ta tayar da hankalinta, amma tunda ƴan gulma suka kawo mata labari aka Zahran ta taɓa aure amma saboda ta saba hulɗa da maza ta kasa zaman auren ta fito, ta kwantar da hankalinta don daman irin macen da take son Imam ya aura kenan, wanda ba za a tsinci komai a cikin auren ba.

Imam na kwance, aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakinsa, juyowa ya yi yana kallon ƙofar, yana mamakin wa ke buga ƙofar, don tunda ya ke babu mai zuwa ɗakinsa a gidan, sai dai idan ƙanensa sun zo hutu a gida. Miƙewa ya yi, ya tafi bakin ƙofar, murɗa handle ɗin ƙofar ya yi, tsayuwa yayi still da ya gan wacce ke bakin ƙofar.

"Ango ka sha ƙamshi." Anty ta faɗa tana murmushi, murmushin da bai taɓa gani a fuskarta ba sai yau. Folding hands ɗinsa ya yi a kirji yana jiran ya ji me ta zo da shi, da ta gan zahiri ba magana zai yi ba, sai ta fara magana; "Mijina ya ce ka faɗi amount ɗin da za a tura maka na siyan kayan lefe wa bazawarar amaryar ka."

Da mamaki Imam ya kalle Anty, ya aka yi ta san Zahra bazawara ce. Gira ɗaya ta ɗaga mishi, ta ce; "Kar kayi mamaki don na san wacce za ka aura bazawara ce, ai daman shi labarin duniya ba ta ɓoyuwa, na riga da na ji labari cewa amaryar ƴar duniya ce, ta gagara zaman aure saboda ta saba da biye-biyen maza, ko dai ba ka da labarin wannan?"

Imam na kallonta direct a cikin ƙwayar ido, ya ce; "Labari kuma? Ai idan kika yi la'akari halayyar ta da kika lissafa sun zo ɗaya da nawa, don haka she's the perfect person for me, maganar kayan lefe kuma, ki koma ki cewa mijinki, zan iya haɗawa matata kaya ba sai an tallafa min ba."

Ya na faɗin haka ya shige ɗaki, ya banging ƙofar to her face.

Musharraf na isa gida ya kira Sen. Amma yana fara masa bayanin dalilin kiran, ya ce masa ya riga da ya san maganar, don haka gobe yana nan zuwa Kaduna.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.