Free chapter · Read without an account

PAGE 95

by Shamseeya Rabi'u Garba · AKASIN TSAMMANI (Beyond All Odds)

A hankali lokaci ya rinƙa tafiya, kwanaki zuwa satittika har Zahra ta kai wata ɗaya da sati da aure. Har a wannan lokacin Imam bai ba wa Zahra izinin komawa aiki ba, don haka kullum safe da yamma tana girki ta kai wa Abba, su sha hirarsu, yanzu shine ya zama abokin hirarta kuma abokin shawararta. Anty kuwa tana kan yin nata shirin akan Zahra da take neman ta wargaza mata ginin da ta sha faman shekara da shekaru wajen ganin ya ginu, dukiya sosai ta narkar wa malamai wajen ganin ta mallaki Abba yadda take so, amma ace lokaci guda komai na son lalacewa, duk magungunan da ta karɓo kwana biyun nan bai yi mata amfani ba, saboda sam Abba ba ya cin abincinta, don haka ya zama dole ta fara kau da Zahra daga hanyarta kafin duk wani tsarinta yayi aiki.

Zahra ta gama haɗa breakfast a basket kenan zata kaiwa Abba, tana buɗe ƙofa kamar daga sama taji maganarsa; "Ina za ki je?"

"Gida." Ta bashi amsa kai tsaye.

"Da waye ya ba ki izinin?"

Zumɓura baki Zahra ta yi, ta juyo tana bubbuga ƙafa ta ce; "Fissabilillahi wane irin rayuwace wannan, Ni ka hanani komawa aiki, wajen da nake zuwa na sami saukin kaɗaici da kake bari na ciki ma ka hana ni zuwa, ya kake son na yi ne?"

Imam ya tsareta da kallo, yace; "Wajen da kike rage kaɗaici ko wajen da kike tafiya ja mini magana. Meyasa ba za ki ji maganata for once ba? Nace bana son kina tafiya gidan nan kindly abide, ba ki fi ni son gidanmu ba, idan kuma kika ƙi ji kiyi kuka da kanki."

Yazo ya raɓa ta gefenta zai wuce, murya ƙasa-ƙasa kamar mai ciwon baki Zahra tace; "Tunda ba ka son ina tafiya, daga yau In Sha Allah na daina har zuwa lokacin da zaka buɗe baki da kanka kace na tafi, amma dan Allah ka yi mini alfarma ɗaya; idan na yi girki zaka taimaka ka rinƙa kai wa Abba."

"Ba sai kin bashi abinci ba, yana da mata wacce ya fifita akan kowa don haka she will take care of his belly." Ya faɗa yana kallonta.

Zahra ta langwaɓar da kai, tace; "Please don't say no, albarkar da Abba ke saka mana a duk lokacin da na kai masa abinci baka san abubuwan da yake tare mana ba, addu'ar iyaye means a lot to us."

Ɗaukar basket ɗin abincin Imam yayi, ya fita daga gidan saboda bai son jin dogon bayani.

Yana shiga gida ya tarar da Abba a zaune a falo, yana zaman jiran Zahra, don a irin wannan lokutan take zuwa, ɗago idanunsa yayi, ya kalle Imam da ya shigo da basket a hannunsa da mamaki, bai gama jin mamaki ba, sai da Imam ya durƙusa ya gaishe shi, yace; "Ga abinci Zahra tace a kawo maka."

"Serve me." Abba ya faɗa idonshi fixed akan TV kamar ba da Imam ɗin yake magana ba.

Kallonsa Imam ya yi yana son ya tabbatar dashi yake yi, plate ya ciro daga basket ɗin, yayi serving ɗinsa abincin, har gabansa ya janyo side stool ya ɗora masa abincin, sannan ya miƙe, yace; "Na wuce office."

"Zauna, idan na gama, ka kai mata kulolinta, I don't want it to be here." Abba ya faɗa yana taunar abincinsa a hankali.

Imam ya ɗan sunkuyar da kanshi, yace; "Ina da emergency."

"Za ka iya tafiya."

Imam ya fita daga gidan zuwa asibiti. Throughout a asibitin maganganun Zahra ne ke ta dawo masa, sai yake ganin kamar zai shiga haƙƙinta idan yace zai rinƙa barinta a gida ita kaɗai babu abokin hira.

Wayarsa ya ɗauka daga kan table ɗin office, ya ɗan latsa sai ya saka a kunne.

Yace; "Ina wuni Yayata."

"Lafiya Imamu ango." Ya A'i ta faɗa cikin zolaya.

"Imam please, not Imamu." Ya faɗa yana harararta kamar tana gabansa.

"Whatever." Ta faɗa tana ƴar dariya.

A hankali yace; "Please I want to ask for a favour."

"Ina jinka ɗan ƙanina."

Guntun tsaki ya ja, sannan yace; "Ina son Zahra ta rinƙa zama a gidanki idan ina office, idan lokacin tashi na yayi sai na biyo na ɗauketa."

"Meyasa, ita ɗin ba za ta koma aikin bane?" Ta tambayi.

"Ba yanzun ba."

"Shikenan ai, daman kaine ka ƙi kawota, amma Ni tun da daɗewa ai nace ka kawota ina da magana da ita"

Washegari bayan Imam ya gama shirin tafiya office, ya leƙa ɗakin Zahra ya ganta gaban madubi tana parking gashinta.

"Kin yi wanka?" Ya tambayeta.

Ta yi kamar ba da ita yake yi ba, ta ci gaba da abinda take yi.

"Ki sameni a falo, zamu je gidan Ya A'i." Ya faɗa ba tare da ya kula sharesa da tayi ba, ya fita daga ɗakin.

Da sauri Zahra ta shirya cikin doguwar rigar atamfa Maroon, ta ɗaura ɗankwalinta ta yafa gyalenta maroon, ta saka takalmi mai ɗan tudu, cikin less than 10 minutes ta gama shirinta ta fito zuwa falo.

Tana fita falon ta ja ta tsaya, Imam ya tashi ya yi gaba, ta bi shi a baya. Sai da ya buɗe mata ƙofa ta shiga, kafin ya shiga ɗayan side ɗin ya ja motar suka fita daga gidan.

Yana parking a parking space na gidan Ya A'i, ya fito ya buɗewa Zahra ƙofa ta fito, ta window Akram babban ɗan Ya A'isha ya hango su Imam, ihu yayi, ya fita da gudu, ƙanwarsa Ikram ta biyosa a baya, da gudu suka faaɗa jikin Imam, Akram yace; "Oyoyo uncle Imam."

Ikaram da maganarta bai gama fita da kyau ba itama tace; "Oyoyo uncle mam."

Rungume su yayi, ya shafa kansu, yace; "Yaran albarka, ya kuke?"

"Fine." suka amsa a tare. Hannunsu ya riƙe suka shiga falon gidan, Zahra na biye da su a baya.

Ya A'i ta fito daga kitchen ɗauke da tray da ruwa da lemu akansa, ta ajiye akan centre table, side hug ta ƙaraso tayi wa Zahra, tace; "Welcome to my house sis."

Murmushi Zahra tayi ta ce; "Thank you", sannan ta gaisheta.

Imam ya tashi, ya ce; "Ni bari na wuce asibiti."

Zahra kamar ta tambaye shi wa zai mayar da ita gida, amma sai tayi shiru kawai.

Bayan tafiyar Imam, Ya A'i ta cika gaban Zahra da kayan ciye-ciye, sannan ta nemi waje ta zauna tana mata hira.

Suna zaune suna hira wata ƴar dattijuwar mata ta shigo, su Akram suka je suka rungumeta suna faɗin; "Oyoyo Mama Nanny."

Matar ta saɓe su dukka biyun tana faɗin; "Hello my little pumpkins."

Ya A'i ta miƙe, tace; "Thank God you're here, Daman zuwanki nake jira."

Ta ɗauki mayafin dake gefenta ta yafa, bayan sun gaisa da matar ta kalle Zahra tace; "Mu tafi, we're leaving the kids with their nanny."

Zahra ta miƙe itama, ta gyara mayafinta, ba tare da ta tambayeta ina za su tafi ba, ta bi bayanta suka fita daga falon.

Ƙofar wani makeken shago dake jikin gidan Ya A'i ta buɗe ta cikin gida, suka shiga. Babban shago ne mai ɗauke da ɓangarori biyu, gefe ɗaya atamfofi ne, da su jakukkuna, takalma, handbags, jewelries da sauran kayayyakin mata, dayan gefen kuma kayan kitchen ne, daga tsakiya kuma, set ɗin cushion ne, da TV, sai daga gefen cushion ɗin drawer ne da Ya A'i ke tara kuɗi a ciki. Wajen zama ta nuna wa Zahra tace; "Bismillah sis."

Zahra ta zauna tana ƙarewa shagon kallo.

"Nima ga office ɗina." Ya A'i ta faɗa tana murmushi.

"Masha Allah, it's fine, Allah ya ƙara buɗi."

"Aameen."

Ya A'i itama ta zauna bayan ta gama saka turaren wuta a burner, ta feffesa air freshner. Tana kallon Zahra da kyau tace; "Sai yau Allah ya ƙaddara za mu yi maganar da muka fara."

Zahra ta sunkuyar da kanta tana jin wani iri.

"Zahra..." Ya A'i ta kira sunanta.

Ɗago kai tayi, tace; "Na'am."

"Yau zan yi magana dake ne ba a matsayin sister in-law ba, amma a matsayin Yayar ki, don haka zallar gaskiya nake buƙata daga gareki, idan kin san ba za ki iya faɗa min gaskiya a duk abinda na tambaye ki ba ki faɗa mini kawai don kar na ɓata lokaci na."

Zahra ta ja numfashi kafin a hankali tace; "In Sha Allah za ki sameni mai faɗa miki Gaskiya a duk abinda kika tambaye ni."

Ya A'i ta gyara zama, tace; "Zahra tsananin ki da Allah kina son Imam ko a'a?"

Zahra ta sunkuyar da kai, ta fara wasa da mayafinta.

Ya A'isha ta ce; "Ba shiru za ki yi min ba I need an answer."

Wasu hawaye ne suka fara gangaro wa Zahra kamar an kunna famfo.

Ya A'i ta yi tagumi tana kallon yadda Zahra ke goge hawaye wasu na ƙara gangarowa, sai tace; "Kukan na me? Tambaya kawai na yi miki saboda na san yadda zan ɗora maganata, amma kin sa ni a gaba kina kuka, kin san meyasa na matsa lallai ki zo mu yi magana?"

Girgiza kai Zahra tayi. "Saboda taƙanas Ammi ta kirani ta faɗa min ba auren soyayya kuka yi ba, don haka na saka muku ido kar Imam ya cutar dake, saboda na fita kusa da ku, amma ni sam na kasa yarda ba auran soyayya ku ka yi ba, saboda soyayya nake gani a ƙwayar idonku a duk lokacin da na gan ku a tare, tun daga ranar farko da na fara ganinku tare, wato ranar da kika treating ɗinsa bai da lafiya, amma Ammi ta tabbatar min da ita tayi noticing, kuma da ta ritsa Imam ɗin da ɗan uwanki Musharraf akan maganar sai suka tabbatar mata da cewa matsawa Imam da ta yi akan maganar aure ne ya sa suka haɗa ki da shi saboda baya da budurwa a lokacin, but still I'm finding it hard to believe. Yanzun Ina son in tabbatar ne, idan tabbas ba ku son junanku zan iya taimaka muku ku so junanku cikin ƙanƙanin lokaci saboda kuma ku ji daɗin zaman aure kamar ko wane ma'aurata." Ta ɗan yi jim, sai tace; "For the last time Zahra shin kina son Imam? Idan kuma a'a meyasa kika amince kika aure shi."

Share ido Zahra tayi, ta gyara zamarta, ganin mafita Ya A'i ke son ta nema mata, yasa ta buɗe baki ta fara magana; "Maganar gaskiya Yaya shine ina son Imam, amma shi baya sona kuma kullum sai ya yi wani abu ko kuma ya ma faɗa akan ba soyayya tsakanin mu, na yarda na auri Imam ne ba wai don son da nake dashi mishi kaɗai ba, amma saboda a duniya babu abinda Yayana zai nema na yi masa da ba zan yi ba, sai dai idan ya fi ƙarfina, ko da bana son Imam dole zan aure shi tunda har Yayana ya nemi hakan daga garemu."

Ya A'i ta gyaɗa kai, tayi murmushi tace; "Zahra wa yace miki mijinki ba ya sonki? Wallahi ko rantsuwa na yi ba zan yi kaffara ba Imam na sonki, it's written all over his face, ke ɗin ce ba ki fahimci hakan ba, sannan shima kansa he's yet to find out."

Baki buɗe Zahra ta ke kallon Ya A'i dake bayani.

Ya A'i ta dafe kafaɗarta, tace; "Kina son ki tabbatar Imam na sonki?" Ba ta jira amsarta ba, ta cigaba da faɗin; "Ni zan ba ki hanyar da za ki fahimce Imam na sonki, har kuma ya bayyana miki hakan, Ni zan ba ki sirrin da Imam ba zai iya kallon wata mace da sunan soyayya ba sai ke, saboda na ɗaukeki ƴar uwa, kuma har zuciyata nake jin sonki tun ranar farko da na fara ganin ki, ke ɗin irin mace da na daɗe ina yi wa ƙanina Addu'ar samu ne, kuma Ina sha Allah zamanku sai ya zama abin koyi."

Rungumar Ya A'i tayi ta fashe da kuka mara sauti, kukan da ba ta san ko na menene ba, Ya A'i ta na bubbuga bayarta a hankali.

***

AKASIN TSAMMANI

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.