Free chapter · Read without an account

4

by Hijjart Abdoul · HASKE A DUHU

************"Dan girman Allah ka yi haƙuri, na dena, wayyooooo....

Ta faɗa a firgice tana tashi zaune. Yayin da shi kuma ya ke tsaye yana fesa turare, amma tunda ta fara surutun ka yi haƙuri na dena, yake kallanta ta cikin madubin, ajiyar zuciya ta sauke tana faɗuwar gaba sosai. Kafin a hankali ta fara kallan ɗakin da take, sai kuma ta gan shi. Da sauri ta sauko daga kan gadon tana kallan kayan jikinta. Da sauri ta sake kallon sa. 

"Kai ne ka sauya min kaya? 

"Ai naga ance bakyau namiji yake kallan jikin mace".

"Haka na ji Iya Yelwa ta faɗa min. Kenan kallona na ka yi? 

Gabanta ya ƙara so yana mata wani banzan kallo kafin ya ce, "Wuce ki yi sallah". 

A hankali ta gyaɗa masa kai tana wucewa bayinsa da ya nuna mata. Tsaki ya sake ja a karo na biyu yana zama a bakin gadon yana fara sa takalminsa, be gama sa takalmin ba yaga har ta fito, ta cire kayansa ta maida na ta dake a jike har yanzun. Duk yarda ya so kada ya yi mamaki sai da ya yi. Be gama dawowa daga wannan mamakin ba, ya ga yarda take dungura sallahrta a balcony ɗin sa da ta fita daga waje, bama nan ne gabas ba kawai sallahrta ta dungura ta yi ta gama. Ko kammala da takalmin sa be yi ba, ya ga ta fice ta kwasa da gudu abinta. Kamar ta manta da ciwon dake ƙafarta ne ko me? Anya yarinyar nan tana ƙalau kuwa?

A hankali ya dawo da kan sa ga abinda yake yi, kafin yasa takalminsa ya fita yana cigaba da mamakin wannan yarinyar. Me ke cikin kan ta? Be yi niyyar shiga wurin su Ummie amma takanas Abba ya kira shi yana son ganin sa. Yau ya yi shirin fita ya same shi gaisu ya yi kafin ya samu waje ya zauna daga gefe. 

"Abinci fa? 

Cewar Ummie tana kallansa. 

"Toh". 

Ya iya faɗa yana kallon Abbah dake ce masa. 

"Ka je ma'aikatar Yaya, yana son ganinka". 

Ji ya yi ran sa ya yi wani irin mumman ɓaci amma be wani nuna ba yace. 

"In sha Allah". 

Ya faɗa a hankali yana kurɓar kunun da Ummie ta zuba masa, sai de gaba ɗaya ji ya yi cikin sa ya cunkushe. Kunun ma ko rabin kofi be yi ba ya tashi. Yana fitowa ya ganta tana shara tana dingisa ƙafarta mai ciwo. Wallahi be san dalili ba, amma haka nan ya ji wani irin mumman ɓaci rai ya sake ta so masa. Be san sanda ya yi mata wani banzan kallo ba ya hau machine ɗin sa yana ficewa daga gidan. Banda tsaki ba abinda yake ja ya ma rasa sanin me ya kamata ya yi? Da wannan ƙuncin ya ƙarasa babban ma'aikatar Kawun na su wanda yake wa ne a wurin Abbahn su, Abbah shine ƙarami a cikin su, ga shi da tsananin biyayya shiyasa suke juya shi da Mami a duk sanda suke so suka ga kuma dama. 

Company ne da ake sarrafa filawa da sugar, kusan rabin ma'aikatan Company gaba ɗaya ƴan uwan ne marasa ƙarfi sune mafiya jigon aikin, yayinda ba'a wani ba su babban matsayi ba, daga masu sarrafa abubuwan a wurin machines machines sai ma su shara da masu gadi, kuma wai a hakan murna suke ya taimake su ya ba su....

"Hey Sahal". 

Cewar wani Khalifa wanda yake ɗan uwansa ne na ƙauye. Ɗan murmushi ya yi a hankali yana miƙa masa hannu. 

"Kai ne? 

"Kai ne? 

Shima Khalifar ya mayar masa da tambayar sa, a tare suka saki murmushi dan dama Khalifan ne daidai da shi. Baya ɗaukan wannan shegen shirun nasa. A tare suka yi secondary school, kullum suna cikin faɗa da shi saboda sam Sahal baya da magana idan ya yi masa abu sai yace to me zai ce? Amma idan zance ne ake na rashin kunya, shine number na ɗaya, dan baya da kunya kowa ya san shi da faɗar baƙar maganar, idan ya yi kuma akan Khalifa abin yake ƙarewa. Rashin abin faɗa yace to me zai ce ɗin nan ita ce take ƙular da Khalifa sosai. 

"Yaushe ka dawo? 

"Na je baka nan". 

Kawai ya ce masa be san doguwar magana. 

"Shine na ce tun yaushe ka dawo? 

"About 6 month ago". 

Jinjina kai kawai Khalifan ya yi, dan ya jima be taɓa shi ba ta chat. Daman idan ba shi ne ya taɓo shi to Sahal kam sai de a kar a yi maganar. 

"So yanzu me ka zo yi? 

Ɗan murmushi ya yi kawai yana kallan Khalifan be ce masa komai ba. 

"Wurin Daddy ka zo? 

Be jira amsar sa ba dan yasan amsar kenan tunda be san yana aiki anan ɗin ba balle ya zo wurin sa. 

"Zamu shiga meeting yanzu".

Jinjina masa kai kawai Sahal ya yi, bayan ya karanta tag ɗin sa yaga Entry-Level Officer, wani irin haushi ne sosai ya turnike shi tun ba'a je ko ina ba, duk tarin tulin certificate ɗin sa? Duk yawan certificate ɗin a rasa wanne za'a bashi sai wani enrty level? Ina laifin ace junior staff ko supervisor?

Cike da ƙunar rai ya wuce ya tambaya inda office ɗin sa yake aka nuna masa. Be yi wani sallama kawai ya shiga yana yin sallamar a ciki ciki. 

"Ina kwana". 

Ya faɗa a hankali yana gaida shi. 

"Ahh Sahal kai ne? 

"Sai yau ka ga damar zuwa? Shima saboda na nasa ubanka ya turo min kai ne. Tunda mu bamu isa da kai ba ko? 

Shi de be ce komai ba yana zaune kawai. 

"To ina documents na ka? 

Ya yi masa shiru. 

"Before ka fara akwai wanda zan haɗa ka da shi, sai ya nuna maka abubuwa, kafin nan sai ka yi shekara a Graduate trainee tukunna naga ya abubuwan baka suke tafiya. Da allowance na dubu goma. Kafin ka a baka Entry level ka gane? Sai kuma a ɗan fara biyan ka da kyau". 

Ya faɗa hankalinsa kwance yana duba desktop ɗin sa dake gefensa, kafin ya sake juyowa ɗayan gefen masa da MacBook ɗin sa ke a akai ya taɓa sai kuma ya sake juyo da kallansa wurin Sahal da kan sa ke a ƙasa be ɗago ba amma ta can ciki kam tafasa ce zuciyarsa ke yi ya tabbatar ƙiris ya rage be kama ba da wuta. 

"Kana ji? 

Calmly ya ɗago yana danne duk wani ɓacin ran sa kafin ya kirkiro wani ɗan iskan matsayinci murmushi. 

"Daddy na ce da, ka bari kawai, tunda ba field ɗin na karanta ba, in sha Allah zan samu aiki a asibiti nan da ba da jimawa ba....

Ɗagowa ya yi daga rubuta abinda yake ya kalle shi kafin ya katse shi cike da masifa. 

"Da zaka ce zaka samu aiki a asibiti ni ba zan je ina ƙaramar murya ba ina a baka aiki. Ubanka ba wanda ya sani a cikin manyan mutanen da suke da hannu a wurin sawa a baka aiki, niɗin de ni ne, kuma ba zan yi ba. Ka ji ai ko? Idan zaka zo nan ka fara aiki ka zo ka fara aiki tunda wuri lokacin ka be ƙure ba". 

Sahal ya sake danne ɓacin ran sa yace, "Daddy, In sha Allah zan samu aiki a inda ya dace amma ni ba zan yi aiki anan ba. Sai dan kasan ban saba da wahala ba". 

Ya bashi masa kan sa tsaye yana ɗan kirkin Matsayincin murmushin da shi gwara babu. 

"Baka saba da wahala ba ka ce? 

"Ehh Daddy, ban saba gani na yi wahala ba. Gwara ma kace na je na yi noma da ka ce yi wannan aikin. Ni kawai Daddy dan Allah mu bar wannan maganar". 

Ya faɗa a hankali yana tashi tsaye.

"Daddy da kai na, na samarwa kai na scholarship na tafi karatu. Na je kuma na yi karatuna, na yi degree, na yi second degree na a can. In sha Allah zan samu aiki na. Da kai na, batare da sa hannunka ba". 

"Na Barka lafiya Daddy". 

Ya sake faɗa a hankali yana ficewa daga office ɗin ya barshi da bin bayan sa da kallo. Yana fitowa ya ci karo da yarinyar sa. Da dukan ta bata jima da kammala secondary ba kuma a hakan ƴar sace ta biyu bama babba ce ba, Sannan aka bata babban matsayi a Companyn. Amma shine su wanda suka yi karatu suke da kwalin abubuwan amma shine ba'a ba su ba. Su rike baya so, indai taimako ne daga wurin wannan mutumin wallah be so har abada. Da ashj da Mami ba? Da ya tambaye su abu ya gwammace ya je ya yi bara a bashi ko ya je inda ba'a sanshi ba ayi masa wulaƙancin a bashi......

"Har zaka tafi? 

Ya ji muryar Khalifa. Juyowa ya yi ya kalle shi ya ce. 

"Ehh". 

Kai kawai Khalifa girgiza ya ce, "Yanzu ka ce a'a bansan inda zan same ka shine ya zama wani abu Sahal? Nasan kuma ba zaka iya tafiya ba sai mun haɗu? 

Be ce masa komai ba. 

"Akwai ranar da zaka yi magana har ka gaji, ba de kana rasa abin cewa ba? 

Shiru ya yi kawai be kula shi ba. Ya buɗe masa ƙaramin office ya shiga. Suna shiga ko zama be yi ba wani ya zo ya na yi masa masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, yayinda Khalifa ke bashi haƙurin za'a gyara haka ya gama ci masa mutuncin sosai ya fita. 

"A haka ka ke zaune? A wannan halin? Aikin dole ne Khalifa?.

Ya faɗa masa cike da faɗa yana kallansa. Dafe kan sa Khalifa ya yi ya ce,"Anan ka fi kauri Sahal, a rigima ba? 

Tashi tsaye ya yi ya ce, "Ba haka ne ba, Khalifa kasan ba zan juri cin mutuncin ba ko? 

Khalifa ya ce, "Yi haƙuri ka koma ka zauna dan Allah". 

Sai ya sauya da zancen da cewa,"Ka jima da dawowa amma baka nemeni ba. Nasan kuma ka je wurin Kawu. To shima be ce mun ya dawo ba". 

"Uhmmm". 

Kawai Sahal ya ce. 

"Ya garin? Ya shagon an buɗe? Abbah yake ce min zaka bude shago". 

Be bashi amsa ba ya ce, "Nawa ake baka per month? 

"35k". 

"Every week nake biyan cashers ɗina, su uku kawai. Please ka dawo as a manager or accountant". 

Ya faɗa yana kalkansa. Ɗan murmushi Khalifa ya yi ya ce,"A'a na fara jin daɗin aiki na kasan na fi san aikin company". 

Tsaki kawai Sahal ya ja yana kallansa. 

"Bama wannan ba, Kawu be san tare da Daddy nake aiki ba". 

"What?.

Jinjina masa kai ya yi sosai. 

"Kawu kasan be san duk wani abu da zai haɗa shi da Daddy". 

"Be taɓa nuna ya sanni ba, be taɓa nunawa muna da alaƙa ba". 

"Ba zai nuna ba ai". 

Cewar Sahal ciki ciki.....

**********A yau gajiye yake sosai shiyasa da wuri ya dawo ya kuma kammala komai nasa ya yi kwance yana rufe ido. Cikin baccin da ya kwashe shi da ƙyar bayan ya sha fama da ciwon kai ya ji kukan ta mai shegen tsuma zuciya yana shiga zuciyarsa yana girgiza masa zuciya da ruhi. Wani irin mummunan sarawa kan sa ya yi da yasa shi saurin rufe ido yana jin kan nasa ya yi masa wani irin nauyi sosai. Kukan yau kusan ya fi na ko yaushe ya fi na kullum. Kuka ne da ke shiga tsakiyar kan sa yana sake dagula masa sauran lissafin da ya rigada ya rage masa. A wannan gaɓar ji yake tamkar ya fita shiga cikin mawuyancin halin da take ciki. Sai yake ji tamkar ya fita buƙatar shima ace ya yi kukan.

Ga sanyi ruwan da aka yi jiya ga lema amma a haka ta yi zaune a akan kujerar dake wurin tana rera kukanta tamkar aikota aka yi. Ya jima akan ta a tsaye kan sa na warware gaba ɗaya tana hargutsa sauran ragowar nutsuwar sa. 

"Ke". 

Ya daka mata tsawa yana jin zafi a ran sa sosai. A firgice ta ɗago tana kallansa. 

"Uban me me yasa baki da aiki sai zuwa nan wurin ki dameni da kuka? 

"Duk wanda ya buge ki ba zaki je can ki yi masa kukan ba sai ki zo ki isheni da kukan banza? 

Ya faɗa yana ƙarasawa da jan tsaki. 

"Tashi ki fice min". 

"Dan Allah kar ka koreni. Yanzu ya rufe gida wallahi idan na je na buga sai zai iya kasheni indai ya san bana nan. Dan Allah ka barni anan. Ko ka kaini gadon ka na yi bacci irin na jiya da wancan jiyar". 

"Waye ? 

Ya faɗa batare da ya san ya faɗa ba. 

"Mahaifina mana". 

Ta faɗa masa itama kan ta tsaye. 

"Babanki? 

Ya faɗa yana jin abin be yi wani making sense ba. Kafin ya ɗaure fuskarsa sosai yana cewa. 

"Yau dole zaki bar gidan nan, dan ba zaki hanani bacci ba da kukan nan naki". 

"Dan girman Allah ka yi min rai, kar ka koreni daga gidan nan, nan wurin ne kawai inda nake samun farin ciki a kaf duniyata, ai kai ne ka dawo ka sameni ba wanda ya san ina zuwa nan din". 

Ta faɗa tana haɗa hannunta sosai hawaye na zubowa a idan ta sharrrr sosai. A ransa ya furta ' ji ƙarfin hali'

"Kika ce Babanki ne? 

Da sauri ta gyaɗa masa kai. 

"Karya kike". 

Ya faɗa kan sa tsaye yana ƙaryata ta. 

Da sauri ta ce, "Dagaske nake ba ƙarya na ke ba". 

"Kuma bansan me nake yi masa ba. Kawai duk sanda ya dawo ne yake buguna". 

"Nan ne duniyata kawai. Nan ne nake samun farin ciki a duk sanda yake nan". 

Ta faɗa hawaye na ziryowa sharrr a idan ta. Dagaske zuciyarsa bugawa take yi. Dagasken kan sa ya ƙarasa kwance da kuncewa, a wannan gaɓar be san me zai ce ba ko ya dace ya ce, be san sanda ya kai zaune ba a gefenta. Sassanyar Ƙamshin turarenta na bugar masa da kai gaba ɗaya. Hannu bibbiyu ya sa ya dafe kan sa saboda wani irin zafi da kan na sa ya dauka wanda baya jin kan sa ya taba kuncewa haka irin yau ba. Wani irin labarin take bashi na rayuwarta da yarda ta ta so cikin ƙunci da raɗaɗi....

"Hawayena sun zama sirri tsakanina da dare. Idan yau aka ce ya dawo gari na yi bankwana da farin ciki har abada. Ana cewa Wasu yara suna tasowa da dariya, wasu kuma da hawaye, nima nawa kalar labarin kenan. Amma ka sani ba kowane uba ne yake zama inuwa ba, kamar nima nawa uban be yi ba". 

"Hatta sunana bansani ba ban iya karatun da zan iya karantawa ba". 

Ta faɗa tana cire rigarta ta fito da hannunta tare da daga hannunta, sunanta ya fito raɗau akan hannun. 

"Shine sunana, sanda na tambaye shi, yace mahaifiyata ta rubuta min a hannuna, shine ya nuna min bayan ya zaneni, kullum sai na kallan sunan, amma ban iya furtawa ba. Ban san yadda zan furta ba". 

'RAUDAH'

Ya karanta sunan tas a cikin zuciyarsa. Bayan ya ɗago da idan sa da ya gama rinewa bayan sauraren duk labarin ta. 

"Wanna shine labarina, na baka ne saboda ka dena ƙaryata ne, kai ne kuma wanda ka fara sani na yi bacci mai daɗi a cikin wannan duniyar tawa. Ka kuma bani dukkan taiamakon da sanda na ji ciwo". 

"Na ce maka na gode? Bayan ba zaka min murmushi ba? 

Ta faɗa a hankali tana kallansa. 

"Dan Allah kar ka faɗawa kowa wannan labarin ka ji ko? 

"Alƙawari". 

Ta faɗa tana miƙa masa hannu.

"Aww ashe kai baka dariya fa ko? 

A hankali ya ɗaura hannunsa a kan nata yana kallanta hannun ya riƙe shi a cikin sa yana wani irin sanyi sosai hannu. Sai de ya kasa magana ya kuma kasa furta komai. Wani irin dumi ne sosai ya ratsata hannun nata saboda hannunsa dake da ɗumi. 

"Je ki kwanta". 

Washe baki ta yi sosai. 

"Akan gado? 

Be kulata ya saketa yana kulle idan sa. Da sauri ta tashi tana dingisa ƙafarta da ta cire bandage ɗin ta shige cikin dakin sa ta haye gadon ta kwanta......


#share
#vote
#follow
Please 😩🥺🙏

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.