Free chapter · Read without an account

01

by Doctor Hisham · Makomar 'ya'yana

A wani yanki an yi wani mutumi wandai bai damu da rayuwar ƴaƴan sa ba kama daga kan karatun su, tarbiyyar su, lafiyar su, kai harma da sutturar su, yana da mata daya da yara bakwai mata uku maza hudu, yana sana'ar fawa, matar sa kuma tana saida kayan miya a cikin gida.
Suna zaune suna hira malam kawu da matar sa Saratu. ta kalle shi cikin ladabi kana tace malam ina ganin ya kamata a saka Aminu da Halifa a makaranta tunda su sauran matan kaki saka su kuma kaki bari na saka su, ina ganin ya kamata a taimaka a saka su koda islamiyya ce tunda baka son bokon, 
  Malam kawu ya ɗago ido ya kalleta cikin fushi, 
     " Kin ganki saratu ki kiyaye ni wallahi meyasa baki da aiki sai bautar ƴaƴa Aminu, Halifa da saifu sune kadai manyan ƴaƴana Salisu dama karami ne su din kike so nasa a makaranta ita kuma tukubar tawa in kare a wahala babu mai taimaka mun ? "
 Saratu tayi ajiyar  zuciya,
  " To amma fa malam Yakamata kasani ƴaƴan nan da kake gani amana ce gare mu kuma Allah zai tambaye mu wannan amanar "
    " Zai tsaki tare da fadin tashi ki tafi bana son wannan maganar "
Saratu ta miƙe cikin ɓacin rai da damuwa ta nufi dakin ta,
Bayan wasu lokuta malam kawu ya fito ya tisa ƙeyar Aminu da Halifa, saifu kuwa ko kallon mahaifin nasu baiba domin shi dama tun tuni basa jituwa da mahaifin, malam kawu ya kallesa tare da fadin 
   " Kai ! Tashi mu wuce "
  " Baba ni makaranta zani lokaci kawai nake jira ya cika in tafi "
Malam kawo ya kalli saifu cikin fushi tare da kwallawa saratu kira. Tayi sauri ta karasu cikin fadin " lafiya malam ? "
" Wannan yaron da kika goyawa bayan yayi mun rashin kunya to bari na ga ya miki wllh ko ya bini ko mu raba gari, duk lokacin da nace muje kasuwa sai yace makaranta, sabo da gani dan wahala inje in nemo in kawo Amma bazai taimaka mun ba "
 " Malam ay kaima kasan cewa dole ne yaron nan yaje makaranta kuma randa babu makarantar ay yana zuwa ko ? Kuma naga yaron nan har ya gama primary ya gama secondary shi yake daukar nauyin karatun sa, sai yaje gidan bredi yayi aiki yake samun kuɗi ya haɗa da abunda nake bashi amma..."
Malam kawu zai yi waje cikin faɗa 
" Tom yayi daidai kin bashi damar karya taimaka mun ko,? Tom yaje yayi karatun mugani babu abunda zai amfana tunda baisan ya taimaka mun ba "
Ya buga kofa Aminu da Halifa suka bisa badan ransu yana so ba, saratu kuwa binsa tayi da kallo tana mamaki, kana ta ce 
" Kayi hakuri saifu ni kaina hakuri nake kana gani a gidan nan koni mahaifin ku bai barni ba, a gaban ku yake zagina, zagi na tsaman nama yaki baku tarbiyya yadda ya kamata ya zage ni ya zage ku ya gaya muku muna nan kalamai, Tom kuyi hakuri insha Allah za ku yi albarka kuma zaku taimaka masa insha Allah zai ga amfanin ku "
Saifu zai saki Gwauron numfashi tare da fadin " amma umma kina ganin abubuwan da baba yake fada akaina, in na tafi makaranta ya ce na tafi yawon iskanci, abinci ma kina gani cewa yake kar abani abincin gidan sa, kece kadai kike taimaka mana kuma umma in muka tare a bakin tukuba randa kasuwar ta juya yaya za ayi, baka bari munyi aiki a wani guri ba, baka mana sittira ba, baka bamu ilimi ba taya zamu taimaki kan mu gaskiya umma bazan iya rayuwa da baba ba, "
Saratu ta daka matsa tsawa tare da fadin " karna sake jin haka daga bakin ka saifu kaidai ka dage kayi karatu daga boko har islamiyya kodan ka taimakawa ƴan uwan ka da sauran al umma da mahaifan ka baki daya "
     BAYAN SHEKARA DAYA 

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol