Free chapter · Read without an account

KUSKURE 11

by Fatimaoumshaheed55 · KUSKURE

*KUSKURE*



By maman shaheed


shafi na shad'aya




     Isar su gdn Ammy , lokacin gd y d'inke d jama'a 'yan uwa da abokanen Arziki anata Shirin tafiya d'aurin Aure Maza, Mata kuwa nata kai kawo da ƙoƙarin ganin komai ya tafi daida. 



    Bayan sun gama gaisawa d baki maza d sukazo daga garuruwa har ma na cikin garin ,sai su mommy noor d su twins suka wuce cikin gidan. 


"Nan ma gaisuwa suka shiga yi, anata raha kowa ka gani cikin farin ciki yake fuskar sa cike d annuri da walwala. 


 Suna gama gagaisawa ,suka Kama shirye _shiryen abubuwan d 'yan d'aurin Auren zasu buk'ata Kama d su Abinci , snacks , drinks, duk da Dai  oder  wasu aka bayar ,wasu ankawo wasu Kuma ba su karaso ba Amman suna hanya dan akwai na ƴan reception. 


Gida y cika yayi taf , a haraban gdn ansa canopy chairs d rumfa. 


Ana gana   d'aura Aure , Ango bakinsa har kunne, shida abokanen sa suka dungumo zuwa gidan, kusa d gdn su Ammy y shiga d jama'ar sa dake Akwai abokin sa gdn Kuma sun Saba sosai yana da girman compound ,gdn Ammy sai ya barma baƙin  su Abba da sauran family sa. 


Ango yayi kyau ya ci d'anyar gezna shi shima kusan irin d'inkin su d'aya d k'anin shi SAFWAN dan Shi ya musu. 


Tun shigar su gdn , momyn su noor take sa Indo Aiki irin ita gata da mai mata hidima wani abun ma d gadara ko Abu taga an zubar ko Ana neman Wanda ze gyara wani Abu duk d Akwai masu tayasu Aiki amman sai tace ga Indo , har wani uban wanke wanke tace wai taje tayi sai da akace" aa ki  Bari Akwai masu yi ai aikin ya mata yawa" sanan ta hak'ura badan ranta yaso ba, irin ta bada umarni an da katar d ita. 


Ga  su Noor da ta Jona mata wai ta dinga kula da shige da ficen su ta sakar Mata komai har kayan da zasu canja indon taba bag clothes din nasu wai da sun Bata ta cire ta canja musu , Indo ba yadda ta iya haka ta karɓi aikin ta take ta fama.



Anata faman yawo da snacks , drinks, Ruwan rubber  ga girki anata kwasa 'yan d'aurin Aure sun dawo , anata wulaƙanta kaza d Naman rago harma na saa ranar nama sun gane kuren su a bikin Ahmad, 


Hidima tayi hidima , indo ta ɓace ma ganin momyn su Noor Dan inba haka ba bazata barta takai ko lomar Abinci bakin ta ba ,Amman Tana kula da movement d'in su Haneef ,amman ko da wasa Taƙi yadda su zauna inuwa d'aya da Uwar ɗakin ta  momyn su noor, gashi su hassana Basu Sami zama ba bare su dinga tare Mata wani wahalan idan momyn su Noor ta  Mata Dan haka Indo ta shiga wasan ɓuya da ita Dan ta samu ta huta itama ta shaƙi iskar ƴan ci kamar kowa. 


Wuni akayi Ana ciye-ciye da shaye-shaye Amman n drinks fa ,Anyi kodimo iya kodimo har yamma ta gabato aka Fara maganar dinner da za a gabatar da daddare .

Kafin Lokacin tafiya dinner Indo ta canjama  Noor da Haneef Kaya kusan so huɗu sha'anin su kawai suke yi ,abinka da yaro .

 Su hassana,ussaina,Asmy,suhaima,huzna sun Sha makeup sun canja Kaya Suma kusan kala uku 3 uku sun Sha kyau sosai .


Magriba tayi ,wasu sunyi sallah wasu ko bansan yaushe zasuyi ba Dan kunsan Akwai masu kara'in sallah a abiki (wa'iyazubillah) Kar kwaliya ta goge Allah yasa mugane Ya ganar da masu yin hakan. 

Da haka su hassana anyi sallah Dan basa wasa da sallah Sam Ammy Bata musu da wasa kwatakwata training ɗin da ta musu ne tun suna yara  Kuma yabi jikin su har sun saba. 


Bayan idar da sallah magriba duhu ya fara shiga , alokacin me kwaliya tasake baje makeup kit d'in ta Dan tsantsara musu wata sabuwar kwaliyar da gyara wacce bata gama gogewa ba Dan Shirin tafiya dinner ko isha'i ba Ayi ba ,wasu dai sunce da alwalar su atare dasu sallah kawai zasuyi su tafi .

Momyn su noor ita aka farama kwaliya inda taci wani uban leshin ta mai suna lace wanda ya sha uban shuwariski stones d'inta Mai tsada d matuƙar kyau ,head d'inta ma yayi kyau jaka d takalminta ma masu tsada Suma d'ankune da Abin hanu g zobina ɓarayin gold  masu kyau tacika Jakarta d kudin liki sababi fil dan capacity take son bazawa a wajen. 


Sanan ta tashi aka farama su huzna nasu kwaliyar. 

Anata kwaliya su hassana da ussaina suna can sunata gaisawa d wasu bak'in Alh SU. 

Gashi me kwaliyar ta gama ma kowa su kawai take jira ,da kyar ussaina tazo aka Mata ,Amman har yanzu ba ama hassana ba Ammy ta Kara sata Aiki ma ,Dan haka tazo ta Kara ba Mai kwaliyar hakuri ,ganin kamar ta ƙosa yasa tace ma Indo tazo amata kwaliya , Zo kuga idon indooo Kamar Wacce aka jefa ta a tara ,ta zazaro ido tace "aa ni ai  base nayi ba" Tana sunkuyar da Kai k'asa , Aiko Mai makeup d'in tace 

"kizo Ni na fara yi Miki tunda tace amiki kinaso kina kaiwa kasuwa Dan na kusa tafiya Akwai inda zani yanzu" 


Indo Bata da zaɓi hassana Ce ta kamata ta mik'ama Mai kwaliyar ita Kuma ta tafi Aiken Ammy. 


Indo fa an Fara ba da light , ta Fara tashi dg Indo Tana Shirin komawa Aisha Sanadin kwaliyar bikin Ahmad abin da bata taɓa yi ba cikin wani ƙanƙanin lokaci sai ga Indo ta rikid'e zuwa Aishatu habawa.

suhaima ,Asmy ,ussaina ,huzna dama ta tashi ta tafi , har su sun kasa gane Indo ,sai a lokacin ussana ta tuna ai ko Kaya indon Bata Saba ake Mata kwaliyar. 

Tsaida kwaliyar akayi akace taje ta sa Kaya ,Mai wayo wajen zuwa sa kayan taji anata Kiran sallah isha'i Bata fito ba sai da ta gabatar da sallah ishan ta , dama tanada Alwala itama sanan ta dawo d'an kwalin ta ahannu.


Haka aka cigaba d yi Mata kwaliya har ta gama Mata ta Mata d'auri Mai steps, hmmmm hohoho Indo dai ta koma Aishatu Bamai ganeta sai an Gaya Mai , sun yaba tsarin ta da kyan kayan da tasa su twins da duk wani wanda yasan gaskia Ashe dama tanada kyau sai kankantar shekaru Kawai, atake ƴan matancin ta ya bayyana kamar a sace ta a gudu. 


Ana gama Mata ,hassana ta dawooo ,itama sai da tayi dagaske sanan ta gane Indo, tana ta tsokanar da yaba kwaliyar ta. 

Itako Indo sai kunya takeji  , sai raraɓewa takeyi ,abun Ka da ba saban ba ta kasa sakin jikin ta , 


Bayan an gama ma hassana tata kwaliyar , har d'auri da komai da komai itama ta yi sallah ta har su ussaina sun zame sunje sunyi sallah su time yayi na tifiya dinner ,motoci sun Fara zuwa .


Noor da Haneef ,suna tare d Indo ta canja musu Kaya ,tace suje su nunama momyn su kartace ba su za'asa musu ba ta kunyata ta acikin mutane , Dan bataso su had'u ma ji take kamar zatace taje  tacire kayan jikin ta Dan tasan halin ta .

Aiko akaci sa 'a ta yaba kwaliyar da indon ta musu tace ta rikesu ta aike su wajen indon ba tare d sun haɗu ba atare da ita sukaje suka shiga mota ,suka  Fara gaba aka kaisu wajen dinner , memakon ta rik'e 'ya'yan ta (wasu matan ma dai toh) Indo Mai neman ƙiris tace toh ta d'auko gyalen ta dama shine mahadin kayan da tasa da takalmin ta da wata side bag  d'inta ta Kama hannun su suka wuce zasu fita wajen d motoci suka Fara jeruwa ,sai ga kawarta yarinyar Mai Aikin gdn su Ammy da suka ɗan saba , itama su hassana ne suka siya Mata kayanta ankon  , Amman ita ba a Mata kwaliya ba ,Indo tasan itace daidai ajin ta talaka 'yar Mai Aiki shiyisa suke kawancen su tun Fara bikin Kuma sukan ɗan haɗu dama b sosai ba itama tanada hankali .

Dan haka tare suka tafi suka shiga motar wani driver suna jira afara tafiya atafi dasu su Haneef n hannun su da noor.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.