Free chapter 路 Read without an account
47
47鈱笍馃挰
Hanadi tana zaune taga status din Farhana tare da First Lady ta jihar Kwara.
"Wato har Government House suka je?" Hanadi ta fada cikin kuncin rai. "Abdulkadir, kana so ka haukatani ne?" Cikin zafin nama ta yi screenshot ta tura a group din danginsu.
Ba a dade ba, sai ga reply din Yaya Safiyya:
"Ikon Allah! Gaskiya AK ya sauya. Yaushe ya zama social butterfly? Yanzu na yarda da maganar Ramla dari bisa dari."
Ramla ta karbe zancen: "Wallahi kuwa! Ai na dade ina fada miki Yaya Safiyya, Farhana ce take controlling AK. Idan ba haka ba, kema kin san baya son mutane. Mutumin da sai da Mummy ta yi masa jan ido sannan ya tafi taya Daddy murnar cin zabe? Kuma ai da Hanadi ya kamata ya yi wannan yawon, tunda ba abin da Farhana za ta nuna mata sai siranta kamar mayunwaciya."
Fadila kuwa typing ta fara yi: "Awwwn! Gaskiya sun burge ni, couple crush! Bari ni ma na sa a status dina."
Nan take Ramla ta mayar mata da martani: "Shegiya mara hankali! Wacce ba ta kishin 'yan gidansu. Hanadi dai 'yar uwarki ce."
Hanadi dai tana kallon group din, amma ko uffan ba ta ce ba; domin ba ta ma sa Fadila a lissafinta ba.
Yaya Safiyya ta sake rubutawa: "Hanadi, ki kwantar da hankalinki. Dazu Mummy tace AK ya kira Daddy suna hanya. Mummy tana nan tana jiran su, just watch and see."
Hanadi ta yi reply: "It's okay Yaya Safiyya, nagode. Allah ya bar zumunci. Kuma wallahi ni ba haushi na ji ba, kawai mamakin sauyawar Papa nake yi."
A gefe guda kuwa, Zee Adetayo, babbar kawar Farhana, tana kwance tana duba status sai ta ci karo da hoton Farhana. Idanunta har zaro su suka yi saboda mamaki da farin ciki. Nan take ta yi screenshot ta watsa a group dinsu na kawaye (The Besties).
"Hey babes! See our girly with the First Lady!" Zee ta rubuta tare da emojis na nuna murna.
Nan take group din ya kaure da hira.
"Whaaat! Farhana ce wannan ko idona ne?" Fateeha turo da voice note .
"Gaskiya aure ya karbi farhana ,rich anties vibes precious ta tura da dancing dancing emoji
Zee ta sake yin voice note: "Wallahi ni kaina na rude! Gaskiya Farhana tana jin dadin auren nan, kalli yadda take kyalli. Our girl is representing us well! Gaskiya AK ya iya kula da mace."
Dukansu suka cigaba da sa hoton a nasu status din, suna taya kawar tasu murna, Banda mutum daya ,wato nusaiba
Sokoto
Tafiyar tasu ta zo karshe yayin da ayarin motocin AK suka daka birki a harabar babban gidan Gwamna (Government House) da yake can birnin Sokoto. Farhana ta leka ta taga, ganin yadda sojoji da 'yan sanda suke ta faman kwasar gaisuwa ga maigidanta, ya kara ninka bugun zuciyarta.
Daddy, wanda shi ne Gwamnan Jihar, yana zaune a babban falonsa na alfarma. Yana ganin shigowar su, fuskarsa ta fadada da wani irin murmushin jin dadi. Wannan ne karon farko da ya taba ganin Farhana ido-da-ido tun bayan auren.
"Barka da zuwa maryama ! Barka da zuwa 'yata!" Gwamnan ya fada cikin murya mai cike da karramawa da kauna. Sosai ya ji dadi ganin yadda AK ya fito da ita cikin mutunci.
Mummy kuwa, tana tsaye a gefen Daddy, fuskarta dauke da wani babban murmushin pretending. Ta san sarai idan ta nuna ko da kishin-kishin din rashin son Farhana a gaban Daddy, to lallai za ta ga bacin ransa, musamman yanzu da yake cikin matukar farin ciki. Don haka, ta maze, tana ta nuna kulawa kamar suruka ta gari, alhali a can karkashin zuciyarta wani kuncin ne yake turnuke ta.
Fadila, autar su AK kuma "AK鈥檚 favorite," tana ganin Farhana ta rugo da gudu ta kankame ta cikin kauna. "Awwwn! Welcome home, Sister Farhana! Naga kin kara kyau masha Allah
AK ya kalli yadda mahaifinsa ya karbi matarsa da hannu biyu, wani sanyi ya ziyarci zuciyarsa. Ya ji dadi sosai ganin yadda aka karrama shi ta hanyar karrama matarsa. Bayan sun ci abinci na alfarma tare da dukkan iyalan gidan, AK ya kama hannun Farhana ya wuce da ita zuwa can part dinsa na musamman da yake cikin harabar gidan Gwamnatin, domin su huta daga gajiyar hanya kafin anjima.
Da daddare, gaba daya iyalin gidan sun hallara a kan katafaren teburin cin abinci (dining table). Fadila tana ta faman jan Farhana da hira, tana nuna mata kauna, wanda hakan ya sa Farhana ta dan saki jiki. Bayan sun kammala cin abincin, Daddy ya yi musu nasiha mai ratsa jiki game da rayuwar zaman Amurka (USA) da za su koma nan da 'yan kwanaki.
Ya kalli Farhana cikin kyakkyawar kulawa yace, "Maryama ni ma kamar mahaifinki nake. Ki saki jiki da kowa, idan kina da wata damuwa ki sanar da ni. InshaAllah duk sanda muka shigo Amurka za mu duba ku." Farhana ta gode wa Daddy cikin matukar ladabi, shi kuma ya yi musu sallama ya wuce wajen taron jam'iyyarsu (party meeting).
Nan take, iskar dakin ta sauya. Kamar an kashe wuta, murmushin fuskar Mummy ya bace, ta hade rai tamau ta kalli AK da wani irin kallo mai ratsa jiki.
"Abdulkadir, a kan wani dalili za ku je Government House wajen First Lady ba tare da ka sanar da ni ba? Sai dai na ga hotuna a gari? Tunda ka auri yarinyar nan, ka maida ni ba a bakin komai ba, ko?"
AK ya yi shiru, kansa a kasa, bai iya cewa uffan ba. Mummy ta cigaba da masifa, "Har labarin cewa kai ka saya mata kayan daki duk na sani. Yanzu ka nuna wa duniya ba ka da adalci a tsakanin matanka!" Ta juyo ta watsa wa Farhana wani kallo na tsana, "Ke kuma, duk abin da kika sa dana ya yi min ba abin da zan ce. Kema ai mahaifiyarki ta haifa..."
"Mommy!" AK da Fadila suka katse ta a tare, cikin tsantsar mamakin kalaman da suka fito daga bakinta.
Mummy ta daka musu tsawa, "Zagina za ku yi ne? Tun dazu ina magana ka yi mini shiru, sai da na tabo 'yar gold dinka sannan za ku yi magana?
salla-mame kawai!"
Farhana tana zaune kanta a kasa, ba ta ce komai ba, amma zuciyarta kamar tana wuta saboda zafi. Ganin abin ya yi yawa, Fadila ta kama hannun Farhana, suka bar falon da sauri don su tafi part dinsu.
Bayan fitar su Farhana, Mummy ta cigaba da zazzaga wa AK masifa. "Abdulkadir, idan har soyayya ta rufe maka ido har ka kuskura ka gaya wa yarinyar nan sirrin rayuwarka na baya (past), wanda ni da kai kadai muka sani, to wallahi ba zan taba yafe maka ba!
AK ya kalli mahaifiyarsa da jajayen idanuwa, ransa ya kai kololuwar baci. Bai ce mata uffan ba, sai kawai ya yi wani irin murmushin rainin hankali (smarking), sannan ya juya ya fice daga falon ya bar ta nan tana ta kumfar baki.mamakin attitude din Ak ya kashe mummy
A bangaren Farhana kuwa, tana daki tana kuka sosai, Fadila tana ta kokarin kwantar mata da hankali. Bayan Fadila ta fita ne, AK ya turo kofa ya shigo. Ganin yadda idanunta suka kumbura ya sa zuciyarsa karyewa. Ya karasa kusa da ita, ya kamo hannayenta duka biyu ya dora a kan kirjinsa, dai-dai inda zuciyarsa take bugawa.
"Farhana," ya kira sunanta cikin wata irin murya mai sanyi da ratsa jiki. "Kiyi hakuri da abin da ya faru. Na san kalamanta sun miki ciwo, amma ina so ki sani, ba ke aka zaga ba, ni aka zaga. Farhana, ke ce 'yar gold dina kamar yadda mummy ta fada, kuma babu wani abu da zai taba sauya hakan."
Ya dan dagota ya kalle ta cikin kwayar idanuwa, "Kada ki bari kalaman kowa su taba miki zuciya. Kina da ni, kuma zan zama garkuwa a gare ki a kowane lokaci. Burina shi ne mu bar kasar nan mu tafi inda babu wanda zai sake saka miki damuwa a ranki. Ina son ki, Farhana, fiye da yadda kike tunani."
Wadannan kalaman sun sanya Farhana jin wani sanyi, ta dan saki ranta. Suka kara kwana daya a Sokoto, inda Mummy ta daina kula Farhana, ita kuwa Fadila ta manne wa Farhana suka rinka harkar gabansu.
Daga nan suka dunguma zuwa Abuja, inda ya rage saura kwanaki shida kacal su tafi Amurka (USA). Isar su Abuja, Hanadi ta fito ta yi wa AK tarba ta mutunci da nuna karamci, kamar ba ita ce take kulla makirci a group ba. Yara ma sun yi murna sosai da ganin mahaifinsu, suka rinka tsalle suna murna.
A dakin Hanadi AK ya kwana, inda suka sha hirar Yaushe gamo. Hanadi ta bashi kulawar dayake bukata .Washegari da safe, AK ya sanar da Farhana cewa Intisaar, ba ta jin dadi. Cikin sanyin jiki da tausayi, Farhana ta yanke shawarar zuwa bangaren Hanadi Karon farko don gaishe da yarinyar.
Tana shiga falon Hanadi, ta tadda gidan tsaf, ga wani kamshi mai dadi yana tashi. Tabbas idan ba soyyaya ba ,ba dalilin da zai sai Ak ya aureta ,uwargidansa ta hada duk wani qualities da ake bukata ,kyau ,tsafta,iya girki Hanadi tana zaune a kan kujera, ta kalli Farhana da wani irin kallo mai cike da mamaki, ba ta taba tunanin Farhana za ta zo har falonta ba. , "Ina kwana? Ya jikin Intisaar?" Hanadi ta amsa ba yabo ba fallasa, tana mamakin yadda Farhana take kokarin nunawa duniya Kamar ita mutuniyar kirki ce
Bayan Farhana ta fito, ba ta tsaya wata-wata ba, ta fara kiran masu yin cakes da snacks domin tana son shirya wa Mimi shagalin murnar zagayowar ranar haihuwa (birthday) na musamman nan da kwanaki biyu.
Ranar birthday din ta zagayo, tun safe Farhana ta bar gida ta nufi gidan Halima, inda za a gudanar da taron. Farhana ce da kanta take jan motarta, rataye da L-sign a baya, alamar tana kan koyon tuki ne har yanzu. Halima ta yi matukar mamakin ganin irin tsarukan kyaututtuka da kayan cakes din da Farhana ta kawo wa Mimi. Ita da Abdulkarim suka dinga godiya
Wajen karfe biyar na yamma, sai ga su Yaya Ramla, Yaya Safiyya, da Hanadi sun iso tare da yaransu. Idanunsu suka zaro ganin yadda Farhana take komai a gurin; ita ce mai bada umarni, ita ce mai raba abubuwa. Abin da ya fi ba su haushi shi ne yadda Mimi ta makale wa Farhana, ko ina ta tafi tana biye da ita Kamar Sun shekara da sanin juna
Farhana ta nufi inda suke zaune don gaishe su. Ta duka cikin ladabi, "Barka da zuwa Yaya Ramla, Yaya Safiyya."
Ramla ko kallonta ba ta yi ba, balle ta amsa gaisuwar. Ita kuwa Safiyya, amsawa ta yi a sanyaye ba tare da ta nuna fara'a ba. Farhana tana kokarin juyawa, sai ta ji muryar Ramla ta daki kunnenta:
"Farhana! Wai ba motar nan da muka baki a matsayin gift ba ce naga ana ta yawo da ita? Jiya na ga wani tsoho dattijo yana tuka ta a cikin harabar University of Abuja lokacin da na je wajen wata kawata. Na dauka sace ta aka yi, amma sai na ga kamar..."dattijon yana Kama da ke
Ta yi shiru tana kallon Farhana da wani irin kallo na raini.
Farhana ta gyara tsaiwarta, maimakon ta nuna bacin rai ko damuwa, sai kawai ta saki wani kyakkyawan murmushi mai cike da natsuwa.
Laaa ay abbi ne,da kin karasa kun gaisa
"Ikon Allah! Yanzu shi Abbin motar da aka baki kyauta yake hawa?" Ramla ta fada tana wata dariyar raini, tana kallon su Yaya Safiyya don su taya ta.hanadi na dariya kasa kasa
Farhana ta dan yi dariya kadan, sannan ta kalli Ramla ido-cikin-ido tace: "Wallahi kuwa Yaya Ramla, ai kin ga amfanin haihuwa kenan. Honey (AK) ne ya matsa masa lallai sai ya amsa tunda Shima mahaifinsa ne."
Ta dan gyara mayafinta, ta kara da cewa cikin takun isa, "Shi ya sa ake cewa haihu mai rana yanzu Kinga abbi ya sami mota daga sama .
Kafin Ramla ta samu damar magana, Farhana ta yi gaba tana fadin, "Bari na je na kula da sauran bakinmu, Yaya Ramla. Enjoy the party!"
Ramla ta saki Baki ranta ya baci fiye da yadda take tsammani. Ta so ta kunyata Farhana ne, amma sai Farhana ta yi amfani da damar ta nuna mata cewa ita 'yar babban gida ce mai tarbiya. Mimi kuwa tana ganin Farhana ta taho, ta rugo ta sake makale mata, hakan ya kara kona ran su Hanadi.