Free chapter · Read without an account
PAGE 7
D U H U N D A R E
A 2026 N O V E L
BOOK ONE
ADABI WRITER'S ASSOCIATION
AMEENA IBRAHEEM
OUM-AMEER
Arewapen: @Oumameer2671
Wattpad: @Ummu-Amir
PAGE 7
Misalin ƙarfe biyu na dare. Ammie ce zaune akan sallayah ɗakin Anaam tana addu'a wanda ta jima bayan ta kambala nafila tana addu'ar, ƙarshe ta miƙe da carbi a hannunta ta je a hankali ta buɗe window ta leƙa.
Sosai garin ya ɗinke da duhu sanadiyyar dare da Allah ya sanya ya zamo mahuta a wurin bayinsa.
Mamaki take har yanzu da al'ajabi yanda wasu suka lalata rayuwarsu da mugun nufi da zalunci. Ubangiji da kansa yace ya haramtawa kansa zalunci sannan ya sake cewa ya haramta zaluncin a tsakanin bayinsa. Duk da wannan amma wasu suke keta iyakar Ubangiji ba tare da tsoro ko tunawa da cewa akwai mutuwa, akwai hisabi, kwanciyar ƙabari da kuma tsayuwa domin hisabi ba.
Duk mutanen da za su iya keto DUHUN DARE su shigo gidan mutane kai tsaye ba tare da laifin komai ba su yi wa yarinya fyaɗe, su ƙwace dukiyar da ba su ne suka sha wahala wurin nemo ta ba sannan har da yin yunƙurin kisan kai ai al'amarin waɗan nan mutanen ya ɓaci. Babu Allah Sam a cikin al'amarin su, kuma wallahi da sannu ko a gidan duniya ko kuma lahira za su girbi abin da suka shuka.
Hawayenta ta share a hankali tare da girgiza kai ta janyo windown a hankali ta rufe daga ƙarshe sannan ta koma gefen Anaam wacce ke kwance da bututun iska har yanzu a baki da hancinta ta shiga tofa mata addu'a a hankali tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta sumbaci goshinta idonta cike da ruwan hawaye ta miƙe tana gyara mata duvet ɗinda yake lulluɓe da jikinta.
Ta ka wa ta yi a hankali ta kalli Aysha wacce ke kwance a saman matress a ƙasa, sosai ta ji wani sabon tausayinta tuna yanda hankalinta ya tashi a ɗazu ganin yanda Mijinta Mukarram da kuma Yayan shi Muhammad suka so yin rigima bayan ga halin da familyn yake ciki.
Hasken fitilar ɗakin ta rage musu sannan ta fita ta ja musu ƙofar a hankali ta nufi ɗakin Alhaji Galadima.
Tsaye ta cim mishi jikin window ya buɗe ta yana kallon waje da tarin damuwowi a cikin ransa.
Jin alamun shigowa ya sanya shi waigowa a hankali sai suka yi ido biyu.
"Alhaji! Kana nan har yanzu baka kwanta ba? Ya kamata fa ka riƙa samun baccin yanzu kamar yanda likita ya faɗa maka..."
Jinjina kai ya yi yana mai kallonta ya ce.
"Hajiya Nasmah ke ce zan faɗawa haka. Ya kamata ki riƙa hutawa idan dare ya yi..."
Wasu sabbin hawayen da suka silalo mata ne ta share tare da matsawa a kusa da shi a hankali ta ce.
"Bana iya bacci Alhaji...Wallahy bana iya bacci."
Jinjina kai ya yi yace.
"Ina jin tsoro Hajiya Nasmah...abubuwa da yawa sun faru ko Ince suna kan faruwa. Ina jin tsoron kada na wayi gari ace na rasa Maryam. Idan MARYAM (Anaam) ta mutu ta barni a duniyar nan ban san a wane hali rayuwa ta zata kasance ba, sannan idan kuma ta ci gaba da rayuwa ina jin tsoron halin da za ta kasance a ciki na baƙin cikin wannan abun da ya faru da ita. Tana da buri, tana da mafarkai da yawa, amma waɗan nan azzaluman mutanen sun shigo rayuwarta da mummunan giɓin da har mutu ba za ta manta ba. And again ki kalli gidana Hajiya Nasmah yanda 'ya' yana suka fara rikici a tsakaninsu, Mukarram har yana iya ɗaga wa Muhammad murya... "
Hannu ta kai a hankali ta ɗora akan kafaɗarshi tana shafawa tare da kwantar murya sosai tana mai ɓoye hawayenta domin ta ƙarfafa shi ta ce.
" yana daga cikin ɗabi'un mumini na ƙwarai yarda da ƙaddara mai kyau ko akasinta. Allah ya kan jarabci bawan sa a duk lokacin da yaso, ya rage ga wannan bawan ya zama mai tawakkali sannan ya rungumi wannan al'amarin hannu biyu ya gode masa domin shi ne Allah wanda baya kuskure. Wanda shi wannan bawan Idan kuma bai yi haƙuri ya zama mai godiya ba, sai Kaga ya taɓe al'amarin rayuwarsa kuma sun taɓarɓare. Allah ya baka yara maza guda uku ya baka mace ɗaya sannan ya shiryar maka da su, ya baka surukai na gari sannan ga jikoki har guda shida, yanzu da ya yi maka wannan jarabawar...Ka yi haƙuri Alhaji, ka mayarda komai a wurin Allah ka yi addu'ar mafi alheri. In sha Allahu komai zai yi daidai, komai zai dawo watarana kamar ba'a yi ba. "
Jinjina kai ya yi tare da kallon fuskarta yana mai jin yanda nauyin da ke ƙirjinsa ya ragu sosai ya ce.
" Haƙiƙa maganar ki haka take Hajiya Nasmah, na gode sosai da wannan tunatarwar...Sai dai kuma, abin da na yi nazari a kai na kuma yanke hukunci shi ne, ina so su Muhammad su janye daga wannan maganar kada su sake zancen Alhaji Gimba har abada indai akan wannan maganar ne, zato ba shi da kyau a musulunci koda ya zama gaskiya, ni kaina ina da abubuwa da yawa da zan iya zargin Alhaji Gimba da su, sai dai ba zan yi hakan ba, domin ko na yi abin da ya faru dani da iyalina ba zai canza ba har abada. Saboda haka duk wani bincike ina so a daina shi, duk wata ƙara da suka shigar ko suke ƙoƙarin shigarwa su janye ta, domin babu wani abin da za ta ƙara janyowa sai matsala da ɓacin suna da zubewar mutunci..."
Girgiza kai ta yi tace.
" To amma Alhaji a haka za ka ci gaba da hulɗa da shi?"
Jinjina kai ya yi alamar eh sannan ya ce.
" Ba komai Hajiya Nasmah, tare muka rayu tsawon shekaru da dama, shi ɗin abokina ne, don abubuwa sun faru haka ba zan daina abota da shi ba, domin bamu da tabbacin shi ne ya aikata mana hakan ko bashi ba ne. Ba komai, mu ci gaba da zamanmu a haka har mai rabawa ta raba watarana."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali sannan ta ce.
" Shi ke nan Alhaji. Allah ya kyauta, Allah ya ci gaba da bamu kariya ya ɗoramu akan maƙiyanmu na fili da na ɓoye. Ya kamata ka kwanta haka nan Alhaji..."
Ta ƙarashe maganar tana mai kallon katafaren gadonsa wanda Mubarak ya gama shirya masa a ɗazu ya kwanta kamar da gaske, sai da yaga mubarak ɗin ya fice ya tashi ya zauna.
Tana cikin ƙara kakkaɓe masa gadon ne ta ji muryarsa yana faɗin.
" Za ki tsaya dani a nan ɗin Hajiya Nasmah?"
Ɗagowa ta yi tare da ƙura ido tana kallon sa na 'yan wasu daƙiƙu sannan daga ƙarshe ta jinjina kai tare da yi masa wani lallausan murmushi mai sanyi ta ce.
"Idan haka kake so zan tsaya."
Zuwa ya yi ya kwanta bayan ta gama gyara shimfiɗar sannan taje ta kashe fitilar ɗakin ta dawo ta kwanta a gefen sa.
******
Washegari, suna dawowa daga masallacin Asuba ya aika Mubarak yaje sashen Muhammad da Mukarram ɗin ya kira su zuwa parlourn sa, bayan ya gama faɗa musu hukuncinsa ya kalli Mukarram ya ce.
"Mukarram! Kana da ɗabi'ar yin fushi sosai, wanda na sha faɗamaka ka riƙa ƙoƙarin iya sarrafa fushinka, manzon Allah S. A. W yace: wanda yake da zafin zuciya yake da tsananin fushi, to a duk lokacin da wannan fushin nasa ya motsa ƙaramar hauka ce take kama shi, wanda a nan ne zai riƙa faɗin maganganu waɗanda ba su kamata ba, ta dalilin wannan ne yace hatta alwala idan ka yi ya kamata ka sake yin wata domin akwai wasu lafuzza waɗanda idan aka furtasu cikin fushi suke karya alwala. Saboda haka ka yarda da maganar yayanka cewa ka aikata kuskure..."
Jinjina kai ya yi cike da ladabi ya kalli Alhajin na su sannan ya mayar da kallon su gun Yaya Muhammad ɗin ya ce.
" Haka ne Alhaji, Haƙiƙa na yarda cewa na aikata kuskure, don Allah ina neman afuwarku da ku yafe mini, Kateh ina neman alfarma da ka yi haƙuri..."
Jinjina kai Muhammad ɗin ya yi yace.
"Ba komai, Allah yasa mu dace. Allah ya bata lafiya amin."
Gyara zama mubarak ya ƙara yi sannan ya kalli Alhaji ya ce.
"Alhaji ka yi haƙuri, ba don ina so in ƙetare maganar ka bane da kace a rufe wannan maganar. Alhaji zuciyata ta kasa samun sukuni da nutsuwa akan wannan wanda aka kira da JAK na cewa wai ya ɗauki fansar sa. Har da cewa wannan dama ce a gare sa...hankalina a tashe yake, da yanzu ka mutu Alhaji bayan shi JAK ya hana ɗan uwansa ya kashe ka...Ina tsoron kada su sake farmakarka ko su sake dawowa gidan nan watarana..."
Cikin zallar mamaki Mukarram ɗin ya ce.
" What?"
Jinjina kai Mubarak ya yi sannan ya ce.
" Na ga komai da idona Yaa Mukarram. Shi ne wanda ya ture ɗayan bayan ya harɓi Alaji, wannan dalilin ne yasa harbin ya sauka a hannun sa maimakon wani wurin mai hatsari a jikin sa..."
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke a hankali sannan ya kalle su ya ce.
"Mukarram, kai ne kaɗai baka tare dani, kana can Indiya wurin aikin likitancinka, amma kai Madu da kuma Mubarak daku nake kasuwanci na, komai tare daku nake yinsa, kunsan kaso saba'in na daga cikin mutanen da nake mu'amala da su, a iya sani na bani da abokin faɗa, bani da abokin gaba, bani da wani wanda faɗa ko tashin hankali ya taɓa shiga tsakanina da shi, Gimba ne kaɗai wanda ko shi bai taɓa fitowa kai tsaye ya yaƙe ni ba sai dai ya yi ta abubuwansa cikin habaici da sauransu. "
Jinjina kai Muhammad ya yi ya ce.
" Wannan haka yake Alaji. Wata ƙila an samu kuskure ne ma'ana ya kuskure daga abin harin sa ya za ta kai ne, wata ƙila sai daga baya ya gano cewa ba kai bane hakan yasa ya fasa kuma ya hana a kashe ka ɗin..."
Ajiyar zuciya Alhaji ya sauke a hankali ya ce.
" Touh! Muna fata Allah yasa haka ne, Allah ya kyauta ya tsaremu daga sharrin maƙiyyanmu."
"Amin amin Alaji."
"To a ta shi a yi haramar tafiya."
Jinjina kai mukarram ya yi yace.
"In Sha Allahu Alaji. Allah ya baka lafiya mai amfani, yasa wannan abun ya zamto kaffara. Amin. Amma kuma ace har da Common award! Idan ba na kusa da kai mai yin hassadar ka ba waye zai yi maka haka?"
Sai yanzu Hajiya ta girgiza kanta da mamaki ta ce.
"Hmm! Duniya kenan! Ai ni wannan al'amarin ya yi matuƙar bani mamaki da al'ajabi. Allah dai ka ci gaba da bamu kariya daga sharrin mutum kowane iri ne, domin wallahy mutum bai shi da kyau, duniyar ce ta riga ta gurɓace da abubuwan zaluncin wanda a yanzu sun fi yawa a cikinta. Hassada da baƙin ciki da ƙyashi ya taru ya yi wa zuciyar wasu katutu, wani fa ko wata alaƙa ba shi da ita da kai amma kuma haushinka yake ji. Shiyasa yawaita sadaka yana da kyau kuma yana fa'ida, domin manzon Allah da kansa yace mu yawaita yin sadaka, domin sadaka tana maganin masifa. Allah ya kyauta ya sa mu dace."
Da amin suka amsa sannan suka tashi suka je suka shirya inda Muhammad ya nufi Abuja su kuma suka kama hanya gabaɗaya ahlin gidan zuwa ƙasar Indiya har da Alhaji Mas'ood bayan ya tabbatarwa su Baba Salisu cewa lallai su janye kowace irin ƙara su manta da komai, kawai abin da yake so shi ne su tayashi addu'a.
******
Alhaji Gimba kuwa, yana zaune a parlournsa Faris ya shigo wanda shi ne kaɗai ƙwallin ɗan da yake da shi a duniya.
Cikin farin ciki ya ce.
"Daddy da gaske ne iyalin Alhaji Galadima sun janye ƙarar da suka shigar?"
Miƙewa ya yi tsaye daga zaunen da yake yana mai fuskantarsa ya ce.
"Haka na ji! Daman na san ba za su iya ba. Kuma ni hakan nake jira, saboda haka ni zan shigar da ƙara a yanxu..."
Da sauri Faris ya girgiza kansa ya ce.
"Noo Daddy please! Kamar yanda suka fasa please kai ma ka manta."
Cikin wata irin tsawa ya yi mishi wani kallo ya ce.
"Akan me zan manta? Shin ba ka ji irin wulaƙanci da tozarcin da mukarram yazo har gidan nan ya yi mini ba?"
"Duk na ji komai daddy, please ka yi haƙuri, ko su nasan fushin zuciya ne yasa haka, and again kuma ni har yanzu gaskiya Ina son Anaam..."
Wani irin gigitaccen mari ne Alhaji Gimban ya sauke masa wanda hatta Hajiya Salamatu dake tsaye jikin ƙofar shigowa parlourn daga ɓangarenta sai da ta razana. A fusa ce ya nuna shi da yatsa ya ce.
" Ashe kai mahaukaci ne ban sani ba? Shashasha wanda bai san ciwon kansa ba? Ragin ɓarayin ce kake iƙirarin cewa kana so?"
Shima Faris ɗin a zuciye yace.
"Ni babu ruwana! A haka nake sonta. Ai kai ne wanda ya goya mini baya daga farko kuma ka yi mini alƙawarin cewa zan same ta..."
"To na janye maganata, kuma na soke wannan soyayyar. Because there's no way zan barka ka kaje ka auro wacce en daba suka gama da rayuwarta gabaɗaya. Miye ya rage wanda za ka samu a tare da ita har ya sanya ka yi farin ciki da aurenta??"
Girgiza kai ya yi ya ce.
" wannan ya rage naka kuma! Matuƙar za'a bani Anaam to tabbas sai na aure ta, duk abin da za ka yi sai dai kayi. Kuma ina baka shawara da gargaɗin ka akan kada ka sake tada wannan maganar ballantana har kace za ka shigar da su ƙar..."
Cikin wani irin tashin hankali Hajiya Salamatu ta daka masa tsawa da cewa.
" Faris!! Kana cikin hayyacinka kuwa? Mahaifin na ka kake faɗawa irin waɗan nan kalamai??"
Idanunsa ya sauke akan mahaifiyar ta shi a hankali waɗanda suka rine sosai suka canja launi tsabar ɓacin rai, kamar zai yi magana sai kuma ya girgiza kai kawai ya juya ya fice daga gidan.
Juyawa Alhaji Gimban ya yi ya kalli matarshi tashi na tsawon sakanni sannan ya girgiza kai daga ƙarshe ya ce.
"Na sani! Na san cewa kema goyon bayan ɗanki za ki yi. Daman kin fi son fiye dani. Tun da har yace na janye ko na ce ba zan janye ba za ki iya kema ki ga laifina. Alhali a gaban idon ki Mukarram ya zo har cikin gidan nan ya ci mini mutunci tamkar ni ɗin ba ubansa ba ne..."
Ƙasa ta yi da muryarta sosai ta ce.
" To ai Alhaji gaskiya ce baka so. Amma ni ma da za ka ji shawara ta da ka ƙyale su sun je sun ji da abinda ya dame su..."
"Miye ya dame su ɗin? Na ce miye ya dame su ɗin da har za ki goyo musu baya ki bar ni mijin ki? Ni da suka maƙalawa sharri har za ki bi bayan su ko?"
Parlourn ta bar masa itama ta koma ciki domin ba za ta iya da wannan fitinar ta sa ba a yau.
Shi kuma sai mi ta yake ci gaba da yi yana ƙara ɗaga murya yana faɗin.
"Wannan wace iriyar masifa ce? Waje baka ji daɗi ba haka ma gidan ka baka ji daɗi ba. Kai ba za ka dawo a tarairayeka a lallashe ka! Sai dai a barka da baƙin cikin da ka ƙunso daga waje ya yi ajalinka? Yanzu a gabana take tausayin Galadima da iyalinshi ni kuma na faɗi na mutu kenan? Wallahi aure zan ƙara. Na rantse da Allah auren da bakya so shi zan ƙaro. Yarinya zan samo 'ƴar shala wacce za ta saka na manta da komai ke kuma ta shiga gasa miki aya a hannu. Daman ai shi ne bakya so, kice da girman ki an auro miki 'ƴar cikin ki."
Daga haka ya ƙwafa ya haura ɗakinsa.
✍️ OUM-AMEER ✍️