Free chapter · Read without an account

Chapter 8 ending

by Salis M Reza · ƳAN MATA

*ƳAN MATA*


_By S-Reza...✍️_


*First class writers ass...*

*🪀Whasop Channel*
***


*Chapter 8 end*
Nura na rufe baki su kuma suka haɗe baki da faɗin "Innalillahi wa innalillahi raji'un, mota fa ka ce, a ina, wai da gaske?" Nura ya ɗaga musu kai alamar tabbatarwa. Haura ta ce "Kuma kace taji ciwo sosai fa?" Ya sake ɗaga kai. Abida ta ce "Waiyoo Amera, a garin yaya, dan Allah ka jira mu yanzu mu shirya ka kaimu gurinta". Ta na faɗa ta kama hannun Haura suka shiga cikin gidan Siyama ma ta biyo bayansu da gudu. Ya bisu da kallo yana girgiza kai ganin sun shiga damuwa. Koda suka shiga cikin gidan ba kowa sai wata yarinya wacce take kamar ƙanwar a gurin Amera ɗin da dama tare suke da ita. Haka cikin sauri suka wanke baki suka yi wanka, izuwa lokacin haura harda kukanta wurjanjan tana maimaita Mota ta bige Amera. Har zasu fito Siyama ta ce "Kunga kowacce ta ɗauki kayanta daga gurin gida zamu wuce". Ta faɗa tana kallon su. Haura ta ce "Mu fara zuwa dai muga jikin nata idan yaso sai mu dawo mu kwashi kayan namu". Siyama ta sake cewa "Wallahi ba zan sake dawowa gidan nan ba, ke ko zuwa gurin Amera ɗin ma Allah dan dai naji ta bani tausayi ne kuma bani da kuɗin Mota, amma ba dan haka ba, ko idona ba zata sake gani ba, ai muddin tana tare da wannan mijin nata aradu ta dinga ganin irin haka kenan". Abida ta ce "Nima fa ina bayanki, muje kawai mu duba ta, ta bamu kuɗin mu mu bar musu gari". Ita dai haura duk ta fisu damuwa da son ganin halin da take ciki. Haka suka koma kowacce ta haɗa kayanta, babu batun wanki bare ma aje ga gogewa, haka kowacce ta cusa su, suka fito su huɗu harda yarinyar. Ganinsu da jakwakkuna niƙi-niƙi yasa Nura ya fito yana tambayr su. Abida ta ce "Gidan iyayaenmu zamu tafi daga cen, ko da matsala ne?" Ya ce "Ana wannan halin zaku tafi, to wa zai kula da ita?" Siyama ta ce "Wanda yaje mata bugewar motar mana, kaga idan zaka kaimu muje idan kuma ba haka ba sai mu sauka maka daga Mota". Nura ya ce "Wannan yaran ba zaku taɓa sauyawa ba wallahi". Ta ce "Eh mun ji" Ya sake kallonta, a ransa yana jin ina ma wannan Ƙasim ya aura ba wacce mai hakurin ba, da kuwa an kwashi yan kallo. Daga haka yaja Mota, ya na ɗan ƙoƙarin jansu da hira ma, amma gaba ɗaya sun yi masa shiru. Siyama dai burninta kawai ta bar garin nan, yadda ta sa barin Kaduna a ranta yau wallahi badan taji batun mota ne ya bugeta ba, da ba zata ko sake zuwa gurin da wannan mijin nata yake ba. 

Da sallama Nura ya turo ƙofar ɗakin mara lafiyar, su kuma suna binsa a baya kamar marasa gaskiya. Ƙasim ne ya amsa daidai lokacin yana bata ayaba tana ci a hankali. Gaba ɗaya suka bisu da kallo. Chak Ƴan Mata suka tsaya daga ƙofa ganin halin da Amera ke ciki. Sai bin kafarta da kallo su key ganinta a ɗaure ga kanta shima a nade. Ganin haka yasa Ƙasim yin tsaki yana kallonsu da dukkan wata tsana har cikin ransa. Siyama ta saki jakar tata ta fara takowa a hankali har gaban gadon. Suma sauran haka. Haura sarkin kuka tuni kuka ya kufce mata mai karfi. Ta durƙushe a gurin ta shiga rerawa. Siyama ta ce "Mera garin yaya, me ya faru, mai ya kaiki why Mera". Itama ta fashe da kuka tana riƙe mata hannun da ta miƙo musu. Abida ta ce "A garin yaya haka ta faru Amera, baki ganin hanya ne?" Itama cikin kuka ta faɗa tana sake jin wani tausayin kawar tasu. Allah Sarki ashe duk irin tashin hankalin da suka shiga dalilin ɓatan ta, ashe ita nata yafi nasu. Sosai suke kuka gaba dayansu abun tausayi kamar an musu mutuwa. Kallo ɗaya za kai musu kasan wannan ƙawancen nasu tun daga zuciya yake. Sai jero mata tambaya suke da kuma sannu amma ta kasa furta komai. Sai haɗe kai kawai da suka sake yi ana kuka. Ganin sunki dai nawa ne yasa Ƙasim faɗin "Ƴan iska ai dole kuyi kukan munafunci tunda kun kai ta kun baro, ba gashi kun zo da kayan ku zaku tafi ku barta ba, dole ku haɗe kai kuna kuka, kuma wallahi kuyi mana shiru, ku barta ta ci abinci haka". Ya faɗa yana karasowa bakin gadon. Nura ya ce "Wai Meye haka ne, baka ga halin da suka shiga bane suma, wallahi basu so hakan ta faru ba, kaga fa irin kukan da suke yi fissabillahi, kai basu baka tausayi bs". Ya ce "Duk na gulma ne wallahi, dama burinsu kenan akan ta kuma ya cika, ni wallahi bana ko san ganin yaran nan anan Nura?" Har lokacin dai yan Mata basu ko nuna yana yi ba, saima kukan wannan yarinyar da ya ƙaru a cika ɗakin tana kiran Anty Amera. Sosai fa suke kuka kamar wanda aka ce Amera ta mutu. Ana cikin haka wayar Nura tayi ƙara ya daga ya na faɗa musu number ɗakin. 

Ƙasim ya ce "Waye?"

 "Hafiz ne da Faisal".
 
"Yan iskan yara duk sun kusa haɗa ni faɗa da abokaaina ma wallahi". Ya ƙarasa yana harararsu. 

Da sallama suka shigo dakin idonsu akan masu kuka. Suma sunyi mamakin yadda taji ciwo haka sosai, su kai mata fatan samun lafiya, sannan Ƙasim ya basu hakuri akan abun da ya faru, Hafiz ya ce babu komai ya wuce ai. Sai a lokacin ne ma masu kukan suka dan tsawaita da yinsa. Hafiz ya ce "Sannu Amera, amma a garin yaya hakan ta faru?" A hankali kuma cikin muryar kuka ta fara basu labarin yadda aka yi "Tun da muka je gurin nake tsoro, hankali na ya kasa kwanciya, ina ta son nazo gida domin kamar bai dace na fito bai sani ba, kuma nasan idan na faɗa musu ba zasu yarda ba saboda abun da yayi mana, shine na yanke shawarar kawai na tafi gida idan basu ganni ba dole zasu dawo gidan suma. Sai da na fito kuma na tuna na manta da jakata a gurinsu harda wayar Abida dake gurina a ciki. Kuma Ni na manta ma sunan unguwar, gashi bani da kuɗi. Shine na fara tafiya a ƙafa ina tafiya ina rufe fuska kar ma wani ya gane Ni, sai da nayi nisa sosai, dan ma naga kamar na ɓata, a garin tsallake titi mota ta buge Ni". Ta karasa tana sake fashewa da kuka". Nura ya ce "Allasarki, sannu kinji". Ta daga kai. Hafiz ma ya sake mata sannu yana kallon Yan Mata da suke kallonta. Ƙasim ya ce "Idan ma ba rashin hankali da yarinta ba, kin taɓa ji ko a lokacin da iyaye ke miki faɗa wata tace ki ɗauki shawarar ƙawaye? Cewa ake yi banda bin shawarsu, domin ba zasu taɓa baki shawara mai kyau ba, yanzu dai ga sakamakon shawarar tasu, Ai su ƙawayen amarya basu da wani amfani idan ba bangaren yin yayi (anko )ba, da kuma chashewa da rawa ranar dina, daga lokacin da kuwa aka shafa fatiha to sun gama amfani kenan yan iska, domin watsar dasu akeyi, amma da yake daga ke har naki ƙawayen baku san ma me yake muku ciwo ba, ko da yake ba zan ga laifin ku ba, ai yara ne, kwallaye idan ba..." Da sauri Nura ya ce "Wai Kashim meye haka ne, kai abu baya wucewa ne a gurunka, yanzu ta fatan samun lafiyarta zamuyi ko mayar da magana, haba dan Allah, tunda har kasan su ɗin yara ne to ka barshi a matsayin sunyi halinsu na yara kai kuma Babba sai kayi musu faɗa ba wannan zantukan ba". Abida ta ɗago tai masa wani kallo ta kawar da kai kawai ta saki tsaki a fili. Ya ce "Aikin banza, Wallahi Nura abun ne da ciwo ba zaka gane bane". Ya faɗa ya na komawa ya zauna, shi kaɗai idan ya tuna yadda suka jawo yanzu wai amarya ta zama mai ƙafa daya, haka zasu tafi su barshi da cin amarci a lalace. Siyama dai tun da ya faɗi cewar ƙawayen amarya basu da wani amfani daga chashewa sai yin anko, kawai ta faɗa tunani. Da yake wasu lokutan ta kan ji zafin wasu kalaman fiye da sauran, sau tari za'a faɗa musu wata magana da ta shafi rawar kai ko iyayi ko a ce musu yara, amma abun ba zai dame su kamar ita ba. Sai ta fara lissafin ai kuma fa Kamar gaskiya ya faɗa, domin dai haka ne, tunda aka fara bikin nan meye abun da suka tsinta a ciki banda ma kuɗin su da lokacin su, daga karshe kuma sun buge da amsar walakancin ango da cin mutunci da kuma ƙasƙanci, ai ko ba komai ya dace ya mutuntasu a matsayin wanda suka bata lokaci da kudinsu akan amaryarsa, ga shi duk shirin da sukayi babu wanda ya samu, lamari dai sam babu daraja. Hafiz ya ce "Tom Ƙasim zamu koma, Ubangiji ya ƙara lafiya ya tsare. Ya faɗa suna tashi zasu fita. Ya so ya ɗan musu ihisani amma ba kuɗi a tare da shi sosai, amma yayi alƙawari a ransa idan zai dawo dubiya zai musu wani abu. Ƙasim ya bisu har wajen mota sannan yana sake basu hakuri. Ya dawowa ɗakin ya tarar da wata sabuwar chakwakiyar ta tashi.

 Siyama ta ce "Amera muma zamu tafi, Allah ya sawaƙe ya bada zaman lafiya, ina kuɗin mu da aka bamu?" Ta faɗa tana kallonta?" Idanunan nan suyi sosai na kuka. Amera ta ɗan yi jim kaɗan cikin kukan ta ce "Haba Siyama tafiya kuma yanzu, dan Allah ku ɗan zauna min mana ko na kwana uku ne pls?" Siyama ta ce "A irin wannan halin na mijinki mai halin kafirai ɗin ne zamu zauna miki a gida, bama wannan ba, baki ji abin da yake faɗa akan ƙawayen amarya ba ne, tamkar fa Yan iska yake kallonmu, to wallahi daga nan sai Kano, kuma ki bamu kuɗin mu yanzu mu tafi". Ana haka Ƙasim ya shigo. Amera ta kalle shi cikin kuka ta ce "Zaka ga an turo maka kuɗi jiya dubu ɗari ka basu zasu tafi gida nasu ne?" Ta faɗa tana kallonsa. 

Ya ce "Mai ya faru kike kuka, mai suka miki?"

 "Gida suka ce zasu tafi". 

"Shine kike kuka?" 

Ta sake cewa "Ka basu kuɗin su tafi".

 Ya ce "Kina asibiti ne kike zancen a basu kuɗi su tafi, saboda kin gama bukatar kuɗi ko? Su idan ma suna da kunya da mutunci har sa tambayi kuɗi bayan abun da suka ja miki..." 

"Muka ja mata ko ka ja Mata, duk waye yaja idan ba kai ba, dan Kawai yar uwar ka ta ɓata maka rai sai kace akan mu zaka rama, to wallahi ka bamu kuɗin mu mu kama hanyar gida yanzu, dama ai kace ƙawayen amarya basu da amfani daga lokacin da aka daura aure ko, to a bamu kuɗin mu zamu tafi?" Amera Ta faɗa da ɓacin ran maganar da yake ta gasa musu. 

Ƙasim ya kafe ta da ido ya ce "Allah ko, to ba za'a bayar da ko sisi ba, idan kuma kwata zakuyi to Bismillah". Abida ta ce "To kuɗin ka ne da zaka ce ba za'a bayar bs, wallahi sai ka bamu hakkin mu, tunda ba naka bane". Nura ya ce "Ƙasim dan Allah basu kuɗin nan tunda dai nasu ne". Ya ce "Babu ruwanka anan, idan ba hauka ba, tana asibiti ta dalilinsu amma su iya tambayr kuɗin dan iskanci". Amera ta ce "Dan Allah ka basu". Ya ce "Wallahi ba za'a basu ba, kalli halin da kike ciki". Siyama ta ce "Tur da auran miji irin wannan walhi, Amera na tausaya miki, domin dai muddin kina tare da wannan kin dinga shiga tashin hankali kenan, kuma ki faɗa masa shine matsiyaci, yaje ya riƙe, amma wallahi Allah ya isa kuɗin mu, ba zamu yafe ba". ta na faɗa ta na daukar jakarta. Ƙasim ya ce "Karki sake bakinki ya zage ni dai, na faɗa miki". Tayi banza da shi zuciyar ta na suya. Abida ta ce "Ubangiji ya kwashe maka albarka mugu mai halin mugwaye kawai, Allah ya isa kuɗin mu". Yayi kanta Nura ya sake riƙe shi yana faɗin wai baka ganin a asbinti ake ne. Har sun kusa fita, Amera ta sake fashewa da kuka tana kiran sunayensu. Ƙasim ya kalli wannan ƙaramar yarinyar ya ce "Kema tashi ki bisu gaiyar tsiya kawai". Ai da sauri yarinyar ta tashi Amera ta riƙe mata hannu. Ta ce "Tare aka hado mu". Ta faɗa cikin kukan wannan cin kashin na Ƙasim. Ya ce "Da izinin wa?" "Izinin Abba". Sai ya kawar da kai yana kallon yarinyar. Nura ya ce "Yanzu haka za'a bar yaranan dan Allah, ba fa Lallai suna da kuɗin Mota ba, wannan abun da kayi kuskure ne, wallahi baka kyuta ba sam". Ya ce "Baka ji irin maganganun da suke yi ba, kuma ina ruwana ko basu da kuɗi, nine na kawo su". Amera dai ta kifa kai tana ta kukan tausayin ƙawayen nata. Babu abun da take tunani sai ƙaryar da tai musu na cewar Ƙasim ya ɗauki nauyin kuɗin motar su zuwa da dawowa harda ma abubuwan kwashewa, da yadda suke bata shawarar yadda zata kula da mijin nata, da shirin su na karɓar kuɗin sayan baki, har suna cewa Mota za'a basu, ta tuna yadda suke ƙoƙarin ƙwatar mata yanci. Sosai take ta tariyo Komai tana kuka.

A haka suka baro cikin asibitin kowacce ta kasa magana sai hawaye da Siyama keyi, Haura kuma dama bata daina kuka ba, Abida ma kuka take yi suna tafiya basu ma san ina zasu je ba kamar wasu almajirai. Har suka iso bakin titi Sannan Abida ta ce "Yanzu yaya zamuyi?" Siyama ta share hawaye ta ce "Ko a ƙafa ne sai mun tafi Kano Abida". Abida ta ce "A ƙafa dai, a'a wallahi, wacce take da number wani ɗan gida ta kira ko na mota a bamu sai mu nemi waya, ni dai ban riƙe number kowa ba". Haura ta ce "Nima haka bani da number kowa sai tawa da kuma taku". Siyama ta ce "Ina da number Umma da ta Yaya Salim, amma ba wanda zan kira, saboda kowanne Ya bani guzuri na kuɗi naki amsa, dan haka ba zan kira kowa ba". Abida ta ce "To ai dole ce Siyama, ya kike so muyi kenan dan Allah?" Ta ja jakarta tayi gaba suma suka bita a baya. Siyama ta tare musu mai kake Napep ta ce ya kaisu gurin da zasu samu motar Kano. Ya ce kuɗin su ɗari shida duk su ukun. Suka shiga gaba ɗaya. Abida ta shiga tambayr ta tana da kuɗi ne, ta girgiza mata kai alamar babu. Haura ta riƙe baki tana kallonta. Suna sauka Siyama ta ce "Dan Allah kayi hakuri bamu da kuɗi wallahi". Ta faɗa hawaye na zubo mata idan ta tuno da abun da ya faru. Mai keken ya ce "Mai yasa baku faɗa min ba tun kafin na dauko ku, ai ba'a haka, Abida ta ce "Idan muka faɗa ba lailai ka dauko mu ba ne yayana". Ya ce "To gaskiya ba zan yarda ba sai kun bani kuɗi na, ai ba haka mukayi da kuba". Sosai ya shiga musu ihu har aka fara taruwa a gurin. Haura cikin kuka take rokonsa haka Abida, ita ma Siyama bata fasa ba, amma ina, yawancin mutane ma suna basu laifi akan mai zai sa su hau masa keke basu da kuɗi. Siyama a ranta ta ce "Allah mun tuba da irin wannan tozarci, Allah ka ƙara rufa mana asiri kar ka bari mu wulakanta duniya da lahira, Allah idan akan rashin jin da nayi ne ka yafe mana. Tana rufe baki taji ance Siyama lafiya dai?" Da sauri ta buɗe ido ta sauke a kansa, ta kalleshi ta sake kallonsa, Abida ta ce "Ba komai". Hafiz da suka tsaya ana gyara musu taya ya kalli mai keke Napep ɗin ya ce "Nawa ne kuɗin?" Ya ce "Ɗari shida ne". Ya zaro ya bashi. Ya bar gurin yana cigaba da maganganu. Siyama ta saɓi jaka tayi cikin tasha bata ce komai ba. Ya biyo su a baya yana tambayr ina zasu je. Ita dai Siyama shima haushin sa take ji kasancewarsa abokin Ƙasim. Haura ce ta labarta masa cewa gida zasu je kuma basu da kuɗin mota. Babu yadda baiyi da Siyama ba amma ta ce ba zata bishi ba, sai dai su idan zasu shiga. Duk da shima ba hanya ɗaya bane amma ya yanke zai kai su.

Sai da aka yi da gaske wanda Abida ta sa baki sannan suka shiga. Shi kuma Faisal ya ce "Wallahi ba zai je Kano sannan ya dawo ya tafi Joss ba, hakan yasa ya sauka a motar. Haka suka kama hanyar Kano. Siyama ta lumshe ido tana ta tunanin daga lokacin da aka fara shagalin bikin Amera. Yadda suka dinga uni a gurin biki, sukayi yayi har uku, aka zo tafiya ta dinga kuka da magiya har aka barta. Suka shirya yadda zasu karbi kuɗin sayan baki da yawa, da yadda zasu ci uban kwalliya a garin, harda shirya kwana uku zasuyi. Amma daga karshe duk kiɗa ya sauya, sun dawo babu ko jakar kwalliya babu waya, kuma babu mutunci, sun baro amarya da ƙafa a karye tare dan Dan iskan miji. Tabbas wannan tafiyar tasu darasi ne ga ƙawayen amarya, kuma abun da Ƙasim yayi musu shima izina ne ga ƙawaye masu dagewa da nuna zaƙewa a bikin kawa, tabbas kusan da yawan angwaye irin fahimtar su daya da Ƙasim akan ƙawayen amarya, ba'a karɓar shawarinsu, kuma daga an shafa fatiha sun gama amfani.  Kasancewar Abida na gidan gaba yasa ta nuna masa har cikin unguwar su kofar gidan su Siyama. Babu ko godi bare na gode Siyama ta buɗe ta fita. Abida ce ta tsaya tayi masa godiya sosai ya ce ba komai. Wani irin farinci da natsuwa da kwanciyar hankali ne ya shige su gaba ɗaya lokacin da suka gansu a cikin unguwa, tamkar bawan da ya samu yanci.

Abun mamaki ashe labarin komai ya iso cikin unguwar tasu, ana ganinsu aka fara ihun ga ƴan mata sun dawo ga yan Mata sun dawo, har an fara cewa ƙawayen amarya. Kowacce ta ɗauki kayanta ta shige cikin gidan su. Shima Hafiz ya ja motarsa ya ƙara gaba abunsa. Ai tana shiga cikin gidan ta samu Umma zaune ƙafar nan tata mai ciwo a mike tana cin abinci, ta faɗa jikinta tana fashewa da kukan kewarta. Itama Umma ɗin da ta samu labarin komai da ya faru, ta rungume ta, domin suma yau ne komai ya zo musu, gashi suna ta kiran number baya tafiya. Sosai take kuka ta kasa magana. Sai cen tace "Umma na tuba ki yafe min duk abin da nayi miki, dan Allah Umma kice kin yafe min?" Umma ta ce "Baki min komai ba Siyama, na sani duk yarinta ne, kuma na yafe miki". "A'a Umma wallahi nayi, Allah nayi taurin kai". Ana haka sai ga su Saddiƙa da karamin ganinsu sun shigo gidan da gudu sun dawo daga makaranta da labarin dawowar yan Mata. Suka rungume ta suma suna kuka.  Misalin ƙarfe takawa na dare bayan sun gama cin abinci Umma ta tambaye ta abun da ya faru, ai kuwa ta kwashe komai ta sanar musu tun daga gurin shigar su Mota da za'a tafi. Saddiƙa kuwa mai zatayi Banda dariya. Sai da ta gama ta ce "Yanzu haka kuka baro kuɗin sayan bakin kenan harda dubu darinku?" Ta faɗa tana sake kwashewa da dariya. Siyama ta ce "Ni da garin Kaduna hayata-hayata har a bada". Saddiƙa ta ce "A haba nan da wata tara zamu koma gidan suna, daga nan kuma wallahi sai an bamu kuɗin sayan bakin mu". Siyama tayi murmushi kawai tana tausayawa Amera. Umma tama rasa mai zata ce. Saddiƙa dai ta samu abun tsokana. 

Bayan wata guda da faruwar abun sai ga Hafiz ya dawo neman izinin soyayyar Siyama domin dai shi yaga mata. Lokacin da ya fara bi ta gidan su Abida ya faɗa mata ta ce masa anya kuwa, yadda Siyama ta tsani duk abun da ya shafi Ƙasim, bata jin zata yarda. Ya ce shi dai zai jarraba kawai ta kira masa ita. Suna fitowa Abida ta ƙara gaba abunta. Ta kalleshi da kyau, abubuwan da suka faru wata Daya baya na dawo mata, sai kawai ta fashe da dariya shima ya biye mata😀 📝

Alhamdu lillah, tammad Bihamdillah. Anan na kawo karshen wannan labarin na yan mata, wanda dama nace muku bashi da tsayi, kuma goran Sallah ne gareko masoya na. Ina fatan labarin ya nishdantar daku, kuma ya fadakar daku. 

Muna roƙon Allah ya yafe mana kuskuren dake cikin sa, ladan kuma ya haɗa mu a ciki. Labarin yan Mata darasi ne mai kyau ga kawayen amarya dama Yan mata masu zafin kai. Tabbas idan kuka matsu da Kyu zaku gane tun daga farkon labarin har karshe ana nuna mana wani abu ne da ya dace ace mun kula da shi a harkar biki da bijirewa iyaye. Komai yana da iya ka, zaƙewa na sa a rasa ƙima da mutunci har ma da aminci.

Mu haɗu daku a sabon labarin da zan fara mai tsayi in sha Allah Mai Suna *MATAR MAZA* Duk mai san karanta labarin matar maza ya shiga cikin wannan Channel ɗin nawa, ina muka fatan alkairi. Kar ku manta da sunan sabon Littafin na  S Reza. *MATAR MAZA,* labarin da zai zo muku da wani irin rikiceccen salo Kamar dai yadda aka saba a dukkan labarai na kamar.  Addininmu Tsinuwar uwa, Tazara, Amera da dam, a bar wa rai, Ina muka dosa da ma dai wasu.

Barkanmu da Sallah. Taƙabbalalahu minna wa'alekum 🕋

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.