Free chapter · Read without an account

Chapter Fifteen

by The Healer's Pen · ƘWAI BIYU

SHEKARU UKU DA SUKA WUCE


Sauban yana zaune a office ɗinsa, ayyuka sun yi masa yawa birjik. Yana matuƙar shan wahala kwana biyu, saboda yanayin da yake ji a jikinsa, sam baya jin daɗinsa.


Yawan gajiya, kasala ƙarancin bacci, da kuma ciwon cikin da yake damunsa akai akai. Wanda ya alaƙanta hakan da gajiya, saboda da ayyukan da suka taru suka  yi masa yawa.


Tun bayan mutuwar mahaifinsu da kammala karatunsa yake jan ragamar kula da kasuwancin mahaifinsu. 


Komai ya dawo ƙarƙashin kulawarsa shi kaɗai. Shiyasa lokuta da dama yake matuƙar shan wuya, musamman yanzu da abun ya fara taɓa lafiyarsa.


Kwanci tashi haka alamun ciwon suka fara girma. Daga ƙananun alamu zuwa manya. Sai da yayi tunanin ya tuntuɓi likitansu na musamman, amma daga bisani ya canja shawara akan ya nemi boyayyen asibiti saboda gudun abinda zai je ya dawo.


Saboda daga ƙarshe ya fara tunanin akwai wata babbar matsalar.


Haka kuwa akayi. Bayan gwaje-gwajen da akayi masa tabbatar da cewar ƙodarsa dukan biyun sun taɓu, dole yana buƙatar ayi masa dashen sabuwa. 


Wannan al'amarin ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba. Amma dole yaja bakinsa yayi shuru ba don komai ba, sai saboda halin da ɗan uwansa Sultan zai shiga.


Saboda ya kasance sojan sama,  har ya kai matakin Flight Lieutenant . Sultan yana son aikin soja matuƙa, tun suna yara. Daɗindaɗawa, hukumar sojin sama tana alfahari dashi, saboda kwazonsa da kuma jajircewarsa.


Wannan dalilin ne ya saka ya ja baki sa yayi shuru, ba don komai ba, saboda ya tabbatar da cewar idan Sultan yaji labari shi zai ce zai bashi ƙodar. Wanda hakan kuma zai kawo babban naƙasu ga aikinsa. 


Duk da dokar aikin soja bata hana bawa ɗanuwa na jiki sassan jiki ba, amma idan an bincika an ga da damuwa dole sai dai ya haƙura. Amma ya san Sultan sarai, zai iya bashi komai, ko da zai rasa ransa.


Hakan ya saka ya fara shirye-shiryen neman wanda zai bashi ƙodar a sirri ba tare da kowa ya sani ba, saboda ya ƙauracewa duk wani abu da zai iya kawo naƙasu ga rayuwar dan uwan sa.


Duk da ayyuka sunyi wa Sultan yawa a wannan tsukun, baya samun isasshen lokacin da zai zauna a gida, amma ya lura da yanayin da Sauban yake ciki. 


Ya lura yana ƙauracewa hira dashi, idan sunyi abun dariya sai yaja lokaci yake yin murmushin yaƙe, hakan ya saka watarana suna zaune ya kalle shi yace:


"Are you OK?"


"Yes...I'm good." Ya amsa yana yi masa murmushin yaƙe.


Duk da haka jikin Sultan bai bashi daidai ba. Musamman da ya lura da yadda Sauban ya kasa cin abinci, duk da kasancewar idan suna tare babu wanda yake wasa da abinci. Hakan ya saka dole ya fara zargin akwai abinda yake ɓoye masa.


Ganin yanayin da Sultan ya shiga ya saka Sauban ya miƙe ya kalle shi yace:


"Let me use the restroom." 


Ya miƙe a daddafe ya nufi banɗaki. 


Sultan yabi bayansa da kallo yana nazarin yadda yake tafiya da ƙyar.


Cikin zafin nama ya ɗauki wayar Sauban da ya manta. Ya fara bincike aciki. 


Lambar Dr. Jabir ya gani sunyi waya dashi a tsukun kwanakin nan rututu.


Hakan ya saka yayi sauri ya ɗauki number yayi saving a wayarsa, sannan ya miƙe ya nufi gida.


Tsawon shekarun da yayi na aikin soja, da training ɗin da ya samu, ƙwarewarsa a cyber security, da kuma gogewar ya saka cikin sauƙi ya gama binciken sa tsaf, akan abinda yake damun Sauban.


Anan ya fahimci ainahin abinda yake ɓoye masa. 


A tattaunawar da suka yi da likitan, ya tabbatar masa da cewar, ana tsaka da bincika wanda zai bada ƙodarsa. Fa an samu za'a fitar dashi Egypt domin ayi masa aikin.


Ajiyar zuciya Sultan yayi sannan ya kalli likitan yace:


"Ina son a kai shi Germany zan bada ƙoda ta, amma ba tare da yasan ni na bayar ba."


Jinjina kansa likitan yayi, sannan ya kalli Sultan yace:


"Hakan da kamar wuya, matuƙar zaka ɓoye identity ka. Saboda Germany suna da matuƙar tsauri akan safarar sassan jikin ɗan adam, dole sai wanda yake da alaƙa da marar lafiyar ta jini. 


Saboda haka dole zasu tsaurara bincike akan ku. Kuma hakan zai saka Sauban ya fahimta. 


Shiyasa muka shirya zuwa Egypt, Turkey ko India. Amma hakan ba yana nufin suma basu da wannan dokar bane, a'a tasu tana da sauƙi akan sauran ƙasashe kamar Germany, France, Canada, USA da sauransu."


Jinjina kansa Sultan yayi, sannan ya sake kallon likitan yace:


"Just give me two weeks. Zan yi maka magana inshaAllahu, amma a dakata da neman donor, zan bada tawa, amma ba tare da ya sani ba."


Jinjina kansa likitan yayi. Sannan sukayi sallama da Sultan ya tafi.


A matsayin sa na sojan Nigeria doka bata bashi damar ya bada sassan jiki sa kara zube ba, ba tare da ya bi wasu ka'idoji ba. 


Dolen sa ya fara shirye-shiryen gabatar da ƙudirinsa zuwa hukumar sojin sama ta Nigeria. Bayan tabbatar da cewar anyi dace ƙodarsa tayi daidai da irin wadda Sauban yake buƙata.


Bayan kwana uku da shigar da rahoto sa aka kira wani meeting na gaggawa, wanda duk wani mai ruwa da tsaki sai daya hallara, ciki har da Sultan.


Ɗakin taron yayi shuru, duk wani mai ruwa da tsaki ya hallara. Kama daga kan Likitoci, manyan sojoji, hukumar gudanarwar sojin sama da dukkan wani mai ruwa da tsaki.


Sultan yana tsaye a tsakiya, cikin cikakken uniform din sa no.2 na soja, riga light blue, dark blue ɗin wandon kaki da belt, sai hula itama dark blue da tsadadden takalmin sa derby shoe sai daukar ido suke yi. 


Kakun yayi matuƙar karɓar jikinsa, sun fito da kwarjininsa, da kuma tsananin kyawun halittarsa da ƙuruciyarsa.


Ɗaya daga cikinsu yayi gyaran murya, sannan ya kalli Sultan yace:


"Flight Lieutenant Muhammadu Sultan, your request as been reviewed."


Sultan ya jinjina kan sa sannan yace:


"Sir."


Sannan ɗakin taron ya sake yin shuru. Sannan ya sake kallonsa yace:


"No one here questions your right to make this request, It is not against regulation."


Ya sake yin shuru sannan yaci gaba da magana:


"But we are deeply concerned."


Sultan ya ɗan ɗago da idon sa ya kalle shi yace:


"Concern for what, sir?"


"For you."


Maganar ta ɗan yi masa nauyi amma dole ya danne zuciyarsa.


Ɗaya daga cikin medical officers ɗin ya gyara zamansa, sannan yace:


"Your health record is exceptional. Your operational history is exemplary. You are not an ordinary asset, Flight Lieutenant."


Sultan ya ɗan motsa ƙafafuwansa alamar girmamawa sannan yace:


"I am a soldier, No more. No less."


Ɗaya daga cikin senior officers ɗin ya girgiza kan sa sannan yace:


"You are the kind of officer others follow without being ordered to. That matters."


Shuru ya sake biyo baya, sannan ya ɗakko wani file ya ajiye akan table ɗin, wanda yake dauke da duk wasu bayanai na Sultan. Tun daga lokacin da ya fara aikin soja zuwa yau. 


Kama daga rahoton binciken lafiyarsa, hazaƙa da jajircewar sa, da duk wasu kyawawan lambobin yabo daya karɓa a aikin soja, saboda bin doka da ka'idar aiki.


Sannan ya sake kallonsa yace:


"You are a long-term investment. We are responsible for protecting that."


Sultan ya shaƙi iska ya furzar, sannan yace:


"And I am responsible for my brother. Sir."


Ɗakin ya sake yin shuru, dukkanninsu suna tunani iri ɗaya. Tun lokacin da Sultan ya fara aikin soja ake samun cigaba a ɓangaren sa. Babu alamar gajiyawa ko rashin bin ka'ida. 


Hakan ya saka suke alfahari dashi sosai, basa son abinda zai saka a samu matsala ta ɓangarensa.


Duk da sun san cewar wannan abun da zaiyi bai saɓa dokar aikin soja ba, amma suna gudun samun matsala, saboda suna da buri babba akan Sultan. Suna kallonsa a matsayin kadara, wanda nan gaba zai zama wani jigo babba a ɓangaren sojin saman Nigeria.


Hakan ya saka tun kafin su shigo meeting ɗin suka yanke shawarar su lallaɓa shi akan ya haƙura wani ya bawa Sauban ƙodar. Amma sun lura abun da kamar wuya, gurguwa da auren nesa. 


Saboda sarai sun san halin a, yana da kafiya da naci, musamman akan abinda bai saɓa doka ba, wanda hakan shine sirrin samun nasararsa.


Likitan ne ya katse shurun nasu da cewar:


"There are other options. External donors. International registries. You do not have to be the one."


"I refuse." 


Sultan ya faɗa cikin sauri da wata murya mai cike da ƙwarin gwiwa.


Maganar tayi matuƙar basu mamaki, hakan ya saka chairman ɗin ya fara magana cikin tausasawa:


"You would rather risk your career, than allow an external donor?"


"Yes sir."


Sultan ya faɗa babu alamar nadama ko tsoro.


Ajiyar zuciya chairman ɗin yayi, sannan ya sake sassauta muryarsa ya kalli Sultan yace:


"Flight Lieutenant, understand this clearly. No one is ordering you to abandon your brother. We are asking you to consider the wider consequences."


Sultan ya kalle shi yace:


"With respect, sir, I have considered them. For weeks."


Sannan a hankali ya ƙaraso gaban table ɗin da suke zaune ya kalle su yace:


"My brother has carried our family since our father died. He has carried responsibility without complaint. He has protected me from worry even while his body failed him."


Medical officer ya kalle shi yace:


 "Emotion cannot guide..."


"Emotion is not guiding me, Duty is." Sultan ya katse shi.


"Duty to whom?" Chairman ya tambaye shi.


"To the man who shares my blood," Sultan ya amsa masa. "And to the values this uniform claims to represent."


Wannan maganar tasa tayi matuƙar basu mamaki, hakan ya saka suka tsaya kawai suka zuba masa ido na ɗan lokaci.


Ɗaya daga cikin board members ɗin yayi ajiyar zuciya, sannan ya kalle shi yace:


 "You are asking us to approve something that may limit your future deployments."


"I accept that."


"May remove you from certain commands."


"I accept that."


"May remove you from certain operational commands."


Sultan ba tare da yaji wani tsoro ko ɗar ba yake amsa masa da: "I accept that."


Ɗakin ya sake yin shuru. Suka zubawa fuskar Sultan ido wadda take cike da ƙwarin gwiwa da asalin mazantaka ta aikin soja. Sannan medical officer ya jingina bayansa da kujerar da yake kai yace:


"Why such certainty?"


Sultan ya sassauta muryarsa, ba alamar gazawa ba ko tsoro, a'a saboda an taɓo ainahin wajen da yake so a taɓo masa. Sannan yace:


"Because I have nothing in this world like him."


Shuru suka sake yi gabaɗayansu. Domin zuwa yanz…

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.