Free chapter 路 Read without an account

23

by Kansa'u Bello 路 KOMAI TSANANI

馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅
    *KOMAI TSANANI* 

             *By*

         *KANSA'U* *BELLO* 
    
   *(OUM FATIMA)* 
馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅


   *PAGE 023* 


 *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*




     "Zan yi mana Ya Ammar ka san ina ji da kai fa." Anisa ta fa蓷a tana masa murmushi.

   "Ok Maza ki kira wo 茩awar taki sai a 蓷auke mu tare." Ammar ya fa蓷a yana hango yan da Nanah ke yiwa Yaya Khalid dake tsokanarta shagwa蓳a.

   "Lah Ya Ammar ai 拼ar gida ce itama grand child 蓷in Mamu ce 拼ar wajen Uncle Khamis wan da ya rasu, 茩anwar Ya Khalid ce."

   "Ok to maza ki kira ta tazo ayi mana tare." Ammar ya fa蓷a yana jin da蓷in cewa tana da ala茩a dasu Anisa.

   "Ok bari na mata magana." Anisa ta fa蓷a tana nufar in da Nanah da Khalid suke tsaye yana 蓷aukarsu hoto a wayarsa.

   "Ya Khalid kuzo muje can ayi mana hotuna da Ya Ammar." Anisa ta fa蓷a tana ri茩e hannun Nanah. 

   "Ok muje to." Khalid ya fa蓷a yana kallon Anisa. Ba musu suka 茩arasa wan da tun tahowarsu gaba 蓷aya hankali da natsuwar Ammar na kan Nanah ne har Nawal ta lura da hakan ta ta蓳o Mabaruka ta nuna mata.

   "Ke haba dai sai dai in wani abin yake kallo da ban, amma dai kin san jin kai irin na Yaya Ammar wan da manyan 拼anmata basu ishe sa kallo ba bare waccen 茩waikar yarinyar da bata jima da fara 茩irgen dangi ba." Mabaruka ce mai wannan maganar tana 茩o茩arin 茩aryata abin da idanunta suka nuna mata. Sai dai ba'a je ko ina ba ta bu蓷e baki cike da mamaki tana kallon abin da ke faruwa lokacin da su Nanah suka 茩arasa in da Ammar 蓷in ke tsaye.

   "Ina yini." Nanah ta furta a hankali tana du茩ar da kanta 茩asa sabo da irin kallon da taga wan da Anisa ke kira da Ya Ammar ke yi mata. Murmushi Ammar ya saki ganin yan da ta du茩ar da kai ta茩i kallon sa, so yake ta kalle san don haka yace.

   "Lafiya lau Maryama (Nanah) ko nayi kuskure." Ai kuwa 蓷agowar tayi suka ha蓷a ido wan da yayi amfani da damar ya sake mata tattausan murmushi yace.

   "Sunana Ammar Mudansir Mai 茩usa da fatan zaki 蓷auke ni a matsayin aboki nima kamar yan da kika 蓷auki wannan 茩awar taki." Rasa abin fa蓷a Nanah tayi don haka tayi shiru ba tare data furta komai ba bayan murmushi da tayi masa.

   "Kina da kyau sosai ." Ammar ya fa蓷a yana kallon fuskarta, kallon juna Anisa da Khalid suka yi kafin suka kuma kallon Ammar daya kasa 蓷auke ido a kan Nanah wacce duk tabi ta takura kanta ta kasa sake wa don abu ne da bata saba dashi ba. Ganin hakan ne yasa Khalid yin gyaran murya wan da ya dawo da hankalin 蓷in Ammar kansa.

   "Barka da rana Ya Ammar." Khalid ya fa蓷a yana murmushi don abin da ya gani a idon Ammar 蓷in a kan 茩anwarsa ya fara saka sa yin tunanin da akwai wani abin a zuciyar Ammar 蓷in a kan 茩anwarsa . Murmushi shima Ammar 蓷in ya masa kafin ya bashi hannu suka yi musabiha.

   "Ok ku gyara ayi mana hoton su Abba suna tafe za'a yi na family gaba 蓷aya." Ammar ya fa蓷a yana kallon Nanah.

   "Ok." Duk suka fa蓷a kafin suka shiga gyara wa. Anisa na ya 茩o茩arin tsaya wa kusa dashi ya 蓳alla mata harara ya nuna mata Nanah da ido alamar ta matsa mata. Murmushi Anisa ta saki mamaki na kamata wan da yasa nan take ta 蓷ora ? A kan Ya Ammar 蓷in nata. Da kanta ta tsayar da Nanah kusa dashi ita kuma ta tsaya kusa da Ya Khalid aka shiga kashe musu Camera wan da hotunan suka yi kyau ba ka蓷an ba.

    "Kam babbar Bala da rawanin nan! Wace iriyar lukutar masifa ce nake 茩o茩arin gani da rana tsaka ni Mabaruka. Lallai dole ne in yi gaggawar maganin figaggiyar yarinyar can tun kafin ta zame min matsala a soyayyata!." Mabaruka ta fa蓷a tana jin wani 蓷an 茩aramin hauka na 茩o茩arin kamata.

   "Lallai yarinyar can da alama ta samu shiga a wurin Yaya Ammar, abinda kika kasa samu tsawon lokaci." Cewar Nihal tana jima 拼ar'uwarta babu da蓷i.

   "Ai Wallahi bata isa ba, tayi ka蓷an ta shiga tsakanina da Ya Ammar don zan iya nakasata a kan sa!." Mabaruka ta fa蓷a a fusace tana jin tamkar taje ta sha茩o wuyan Nanah tayi ta jibgarta.

   "Ai duk waccen munafukar Anisar ce take 蓷aure mata 茩ugu wallahi." Cewar Yusrah da hankalinta ke kan Mooh wan da suka fito tare da abokinsa daga 蓳angaren Alhaji Baba.

 ******** A 蓳angaren Muhammad kuwa tun da suka fito idanunsa suka sauka a kan Ammar wan da ya zage yana ta yiwa Nanah hira wacce sai dai tayi murmushi kawai don bata san mai zata fa蓷a masa ba bayan murmushin. Mamakin Ammar sosai ya kama shi, ya rasa lokacin daya koyi duka wa蓷annan halayen wan da bai san shi dasu ba . Wani mugun tsoki ya saki wan da har sai da sautin sa ya fito fili.

   "To tsaka Sarkin tsoki kai da waye kuma?." Mus'ab ya fa蓷a yana kallon Mooh wan da ya ha蓷e fuskar nan tasa mai cike da kwarjini. Banza ya masa bai kula sa ba, sabo da ransa a matu茩ar 蓳ace yake da abin da Ammar 蓷in keyi, yo in ban da ma rashin aikin yi da neman raini irin na Ammar, a kan me zai tsare waccen tsakuwar yarinyar ya saki baki kamar wani soko yana mata zance. Kai shifa yana tunanin akwai abinda ya samu Ammar 蓷in don dai shi bai san shi da wannan halin ba, dama dai Haidar ne da sauran ba zai yi mamaki ba.

   Kasa wucewa suka yi lokacin da suka zo dai-dai in da suke sai da ya daka ta yace.

  "Kai baka da abin yine ka tsaya kake wannan shirmen a nan?!." Yayi maganar da alamar fushi a muryarsa wanda yake 茩o茩arin controlling nasa. Sosa 茩eya Ammar yayi yace.

  "Dama ina jiran su Abba su 茩araso ne sai mu shiga ciki Ya Mooh." Kai kawai ya gir-giza ya juya zai wuce dai-dai lokacin Nanah ta bu蓷e baki tace masa.

   "Ina yini." Ta fa蓷a ba tare daya kalle sa ba don tsoron sa taji yana kamata ganin yan da ya ha蓷e rai tamkar zai kai duka. Dakata wa yayi daga tafiyar da yake 茩o茩arin yi wacce tsayuwarsa a gabanta yasa dole ta 蓷ago ta kalle sa. Abin da yake so kenan dama don haka ya ri茩e idanunta da nasa idanun ya ru茩a aika mata da zazzafan kallo mai cike da garga蓷i kafin ya juya ya wuce abinsa.

   "Hammah kazo ayi mana hoto tare mana!." Anisa ta fa蓷a a shagwa蓳e ganin yana 茩o茩arin wucewa bai kulata ba.

   "Ba yanzu ba Auta akwai abin da zan yi yanzu." Ya bata amsa ya juya ya wuce bayan ya amsa gaisuwar da Khalid yayi musu. 苼ata rai Anisa tayi a hankali ta furta.

   "Ina ga dai wani ne ya 蓳ata wa Hammanah rai yau gaskiya." Shima dai Ammar abin da yazo ransa kenan don Ya Mooh 蓷in bai saba masa irin haka ba. A 蓳angaren Yusrah kuwa bata samu 茩warin gwiwar zuwa ko in da Mooh yake ba sai dai kawai ta bishi da mayen kallo mai 蓷auke da tsan-tsar soyayyar da take masa kamar yanda sauran 拼anmatan dake wurin suka yi, sai 茩us-茩us dake tashi a kan ha蓷uwar guy 蓷in da burin da kowa taci a kansa. 

   Ba'a jima ba su Dady suka 茩araso don haka aka kira kowa dake familyn aka yi musu hotuna tare da amaren kafin kowa ya tafi yaci gaba da shagalinsa.


***** Zaune suke a kyakykyawan Palon da yayi matu茩ar tsaruwa da tsari mara hayaniya wan da ya dace da rayuwar nutsatstsen matashin 蓷an boko wan da komai nasa yake da tsari da ma'ana, tsaki yake ta dokawa shi ka蓷ai ba tare da yayi magana ba, wan da yasa abokinsa ya tsare sa da ido kawai yana kallon ikon Allah. 

    Muhammad Ridwan Muhammad Ali mai 茩usa kenan, kyakykyawan matashi mai ji da kyawun fuska da cikar zati na halittar jiki, mai kwarjini da farin jinin al'umma a duk in da ya shiga baga Mazan Baga Matan ba, kowa son sa yake tare da son yin mu'amala dashi.

   茒an gata ne wan da Uwa da uba ke matu茩ar sonsa, sannan 蓷an gaban goshi ne a wurin Kakarsa Mamu wacce ta haifi Mahaifinsa. Haka ma Kakansa Alhaji Muhammad Ali mai 茩usa wan da yaci sunansa kenan, shima yana matu茩ar so da 茩aunarsa. Shi 蓷in mutumin kirki ne mai tausayin wan da bashi dashi, idan ka cire muskilanci da rashin fara'a wan da yake 蓷abi'ar sa tun yana 茩aramin yaro to babu wani abu da za'a soke sa dashi.

  Yana matu茩ar so da 茩aunar iyayensa da 拼an'uwansa, musanman ma Mahaifiyarsa da yake tsananin so da 茩auna, tun yana yaro Ammy ta fahimci yaro ne mai 茩ulafucin Uwa wan da baya rabuwa da ita ko ka蓷an. Duk inda tasa 茩afa yana biye da ita, tun tana goyonsa yake da 茩yuuya sam baya yarda da mutane, ko da yaushe yana hannun Ammy ita ka蓷ai sai kuma Dady idan yana free. Sai da ya fara wayo ne sannan ya fara yarda da Alhaji Baba da kuma Mamu da a wan can lokacin bata tare dasu, sai dai suna kai mata ziyara akai a kai.

   Lokacin da ya isa sakawa a makaranta da 茩yar aka samu ya saba yake yarda ya zauna shi ka蓷ai, amma da farko kuka yake yi sosai yace shi dai sai in da Ammy zasu zauna a Class 蓷in. Anyi wayo da duk irin dabarar da za'a masa ya 茩i yarda, don haka Dady ya yanke shawarar 蓷auko masu koya masa karatu a gida, sai da ya 茩ara wayo sosai kafin aka mayar dashi makaranta. Kasancewar yana da sharp brain wacce take 蓷auke duk abin da aka koya masa yasa yake da 茩o茩ari sosai da mai da hankali. Shi yasa koda aka mayar dashi makaranta bai fara daga ajin farko ba kawai aka saka shi a ajin daya dace da shekarunsa a lokacin.

   Lokacin 蓷aya kammala primary Dady yaso kai shi 茩asar waje yayi karatunsa a can amma sam ya 茩i amincewa yace shi ba zai tafi ya bar Ammy ba, dole Dady ya ha茩ura ya sama masa Makarantar da tafi ko wacce a garin Abuja ya saka shi. Hakan ce ta faru a lokacin daya kammala secondary Dady yayi masa maganar tafiya 茩asar waje don ci gaba da karatunsa a can, nan ma yace sam babu in da zai je shi a nan zai yi karatunsa. A wannan karon ma Dady bai takura masa ba ya sama musu makaranta mai kyau shida abokinsa Mus'ab wan da suka ha蓷u a Secondary School suke abota, sabo da nacin da Mus'ab 蓷in ya ri茩a masa har sai da ya fara kula sa. Wan da daga nan ne kuma tasu tazo 蓷aya suke mu'amala sosai har iyayensu suka san da abokantakar tasu wacce rabi Mus'ab ne ke ha茩uri da halin Muhammad na shariya sakamakon shi yana da surutu sosai da sake wa da jama'a sa蓳anin Muhammad 蓷in. Gab da zasu kammala Secondary ne Allah yayi wa Abban su Mus'ab rasuwa wan da mutuwar ta dake sa ba ka蓷an ba, a wannan karon Muhammad ne ya dage wurin kulawa da abokinsa har ya dawo hayyacinsa. Koda suka kammala karatu kuma shi yace Dady ya sama musu makaranta tare.

   Lokacin da suka kammala degree 蓷in su aka tura su bautar 茩asa jahar Zamfara, kowa yayi mamaki da amincewar Muhammad kai tsaye ba tare da wata gardama ba. Babu yan da Dady bai yi dashi ba a kan ba sai yayi service 蓷in ba amma ya dage a kan zai sauke nauyin sa ya hidimta ma 茩asar sa, Dady yaso yayi magana a dawo dashi nan cikin Abuja yayi Service 蓷in amma yace a bar sa zai je in da aka tura sa 蓷in. Ba don yana so ba ya amince ya bar su suka tafi tare da Mus'ab wan da aka tura can Kudu amma Dady ya sa aka mayar dasu wuri 蓷aya suka tafi.

  Wannan shine silar zuwan su Zamfara in da aka tura su 茩auyen Cigama, wan da a can ne duk abin da ya faru a baya ya faru. Lokacin da suka dawo gida kuma babu 蓳ata lokaci Dady ya sama masu wata Makaranta mai kyau a London don 蓷ora master's 蓷insu, ya kuma ce dole sai yaje a wannan karon umarni ne. Bai yi musu ba a wannan karon suka wuce London tare da Mus'ab wan da a yanzu bai fi watanni uku su kammala su tattara su dawo ba, in da zai ci gaba da kula da Kasuwancinsa kamar yanda ya fara domin kuwa tun tuni ya fara ayyuka da manyan Company's dake harkar gine-gine kasancewar sa artists mai zanen gine-gine don abin da ya karanta kenan.

  Wannan kenan.

     "Malam ka ishi mutane da tsoki haka kawai, mai zai hana kaje ka zane wan da ya 蓳ata maka rai mana ka huce haushinka!." Mus'ab ya fa蓷a a 茩ufule yana hararar Mooh. Harara Mooh ya doka masa yace.

   "Kai baka ga abin da Ammar keyi bane, ya wani saka 拼ar 茩aramar yarinya a gaba yana zubar da girmansa. Wai yaushe ma Ammar ya fara wannan shirmen ne?!." Ya 茩are maganar a fusace tamkar Ammar 蓷in ne a gaban sa zai hau sa da duka. Sakin baki kawai Mus'ab yayi yana bin sa da kallon mamaki, zuwa can ya furta.

   "Ikon Allah! To kai kuma miye matsalarka da abin da yake yi tun da ba kai ne ka zubar da girman ba?." Wani mugun kallo ya watsa wa Mus'ab wan da yasa dariya ta kama Mus'ab 蓷in don bai taba ganin Mooh na irin wannan harararar ba.

   "To ni mai na maka da zaka harareni?, ka sani ko ri茩o Ammar 蓷in yake don Hausawa sun ce : idan kaga kare yana shin-shina takalmi to 蓷auka zai yi."

   "Tashi ka bar 蓷akin nan Mus'ab tun kafin in sa蓳a maka kammani, ya ina fa蓷a maka abin da ya dace kana kawo min wani shirmen banza. Duka ma yarinyar guda nawa take da har zai yi 茩o茩arin lalata mata tunani ne?, a wa蓷an nan shekarun nata karatu ne ya dace da ita ba wannan shirmen banzar ba.!." Ya fa蓷i maganar cikin serious tone wan da ya bawa Mus'ab mamaki sosai don bai san Mooh da shiga abin da bai shafe sa ba.

   "In tambaye ka Mooh?." Mus'ab ya fa蓷a yana tsare sa da kallo. Bai bashi amsa ba sai ido daya zuba masa alamar yana sauraron sa.

   "Miye ala茩arka da yarinyar nan da kayi ruwa da tsaki a al'amurinta irin haka?." Mus'ab ya fa蓷a yana tsare sa da ido don jin amsar da zai bashi. Kamar ba zai amsa masa ba sai kuma yace.

   Wai ka san wacece yarinyar can kuwa?." 

   "Sai ka fa蓷a min." Mus'ab ya fa蓷a.

   "Ita ce wannan yarinyar wacce wannan tsageran yaron yaso wulakanta wa a wan can 茩auyen da muka ta蓳a yin service a can!." Ya 茩are maganar yana jin 蓷acin abin da ya faru na dawo masa. Shiru Mus'ab yayi zuwa can yace.

    "Kana nufin yarinyar da kasa aka 蓷aure wa蓷an nan yaran a kanta, wacce muka baro 茩auyen da muke service a kanta ba tare da mun kammala ba?."

   "茦warai kuwa." Mooh Ya bashi amsa yana 蓷auke kai daga kallon da yake masa......

   Malam Mooh irin wannan ha茩i茩acewar haka?.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.