Free chapter · Read without an account

24

by Kansa'u Bello · KOMAI TSANANI

🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂
    *KOMAI TSANANI* 

             *By*

         *KANSA'U* *BELLO* 
    
   *(OUM FATIMA)* 
🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂🍂


   *PAGE 024* 


 *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*





       "Haba nifa tun da naga fuskar nan nake kallonta da tunanin inda na taɓa ganinta amma na kasa tunawa." Mus'ab ya faɗa fuskarsa da yanayin nan irin na wanda ya gane wani abu da yayi ta ƙoƙarin tunawa amma ya kasa. Wani banzan kallo Mooh ya ɗago ya watsa masa kafin yace.

   "Au kai ma kenan idanun ka ƙure ƴar ƙaramar yarinya dasu kana kallon ta, kaji kunya Wallahi ƙaton banza kawai!." Ya faɗa cike da takaicin Mus'ab ɗin. Wata shaƙiyyiyar dariya Mus'ab ya saki har yana dukan gefen kujerar da yake zaune a sama yace.

   "Yau naga ikon Allah, to kai da wani idon ka kalle ta har ka gane ta, ko kai kaɗai kake da idon kallon ne mu bamu da damar kallon abin da muka gani ya mana kyau?." Mus'ab ya ƙare maganar cike da son ƙular dashi. Ai kuwa yayi matuƙar shaƙa masa don haka pilo case ɗin dake kusa dashi ya ɗauka ya jefa wa Mus'ab yana faɗin.

   "Allah idan na ƙara ganin idanunka a kanta sai ranka yayi mugun ɓaci, ƙaton banza kawai!."

   "Eh haka ne kam, amma tukuna mama matsayin ka nawa?." Mus'ab ya faɗa cikin son ƙara ƙure Mooh ɗin. Kamar ba zai basa amsa ba sai kuma yace.

   "A matsayin wan da amanar kulawa da ita yake hannu na daga yau ɗin nan."

   "Masha Allah, amma waye ya baka amanar bani da labari?." Mus'ab ya kuma faɗa. Ganin abin na Mus'ab rainin wayo ne yasa shi miƙewa kawai ya shige bedroom ɗinsa bayan ya jefa masa harara. Dariya Mus'ab ya ƙyal-ƙyale da ita yana cewa.

   "Yo ka tashi ka shige ciki, ai tsaya wa zaka yi muyi magana ta fahimta don nima na ƙyasa da wannan amanar taka, ban sani ba tsakanin nida Ammar ko waye zai bar ma wan..." Bai ƙarasa faɗar maganar ba yaji saukar wani pilo case ɗin a saman fuskarsa.

   "Fita a ɗakin nan Mus'ab." Ya faɗa yana nuna masa ƙofa. Sai da Mus'ab ya tabbatar ya gama ƙure Mooh kafin ya fice a ɗakin yana dariya a ransa yake faɗin cewa.

   'ai na riga na gano ka kana takura min nima zan takura maka.' a zahiri kuwa cewa yayi.

   "In ban da rigimar Mooh uban waye ya bashi amanar kula da ita, kawai Malam ka natsu ka san ainahin mai kake ji a kan ta, ba ka tsaya kwana kwana ba don tsaf wani zai maka ƙafa ya Barka da ciwon zuciya." Ya ƙare maganar murmushi na ƙwace masa, mamaki sosai yake yi a kan yan da Mooh ya faɗa soyayyar ƙaramar yarinya wan da shi kansa bai sani ba. Ko kuma ya sani raina musu wayo yake yi oho, da waɗan nan tunanikan a ransa ya shiga motarsa ya wuce gidansu.

    Yinin biki yaci gaba da tafiya a ko wane ɓangare kowa yana hidimarsa a ɓangaren sa tare da ƴan'uwansa. Su Nanah kuwa suna tare da ƙawayen Anisa da suka zo mata bikin suna nasu sha'anin a ɓangaren Mamu. Ƙarfe biyar nayi aka tafi kai amare wan da duka a nan cikin Abuja ne zasu zauna, sai Aimana da zasu tafi ƙasar Sweden da Mijinta bayan sati biyu kasancewar a can yake zaune.

   A wannan karon ma Ammar shi ya ɗauki Nanah tare dasu Anisa da sauran ƙawayensu, wan da kafin nan sai da Mabaruka tazo da iya yi zata shiga motarsa ya dakatar da ita. A gabanta ya kira Anisa a waya yace suzo yana jiransu, tana kallo Anisa ta buɗe wa Nanah gaba ta zauna wan da da ƙyar ta shiga gaban. Shi kuma sai wani kallonta yake yana sakar mata murmushi tamkar ya samu wata cikakkiyar Mace, tana kallo ya tashi motar suka fice sai kawai ta fashe da kuka ta koma ciki da gudu. Kai amaren da bata jesa ba kenan tsabar baƙinci.

   Ko wacce an miƙa ta ɗakin Mijinta in da aka bar su Nanah a gidan Aimana sabo da dinner da za'a yi da dare washe gari ayi buɗar kai shike nan biki ya ƙare. Kallon Nanah Ammar yayi yana sake mata murmushi yace.

   "Zan dawo na kai ku wurin dinner, okay." Kai kawai ta ɗaga masa ta juya ta nufi hanyar cikin gidan in da taga mutane na wuce wa.

    "What's?." Ammar ya faɗa yana kallon Anisa ganin ta tsare sa da ido tana murmushi.

   "Da alama dai Sis tayi nasarar yin wuf da zuciyar wani." Ta faɗa tana murmushi.

   "Ba kya jin magana Lil Sis!." Ya faɗa murmushi na ƙwace masa ganin Anisa ta gano sa."

   "Give me a call idan time ɗin yayi." Ammar ya faɗa yana duba agogon dake ɗaure a hannunsa kafin ya shige motar ya fice a gidan yana ta zabga murmushi shi kaɗai, kyakykyawar fuskarta tare da kyakykyawan murmushinta na kara kaina a cikin idanunsa.

   "Oh Allah, I have fallen in love." Ya furta a hankali murmushi murmushi na ƙwace masa.

   Ajiyar zuciya Nanah ta sauke lokacin da taga ya fice a gidan, ta kasa saba wa da yan da yake mata ɗin. Mamaki take sosai data san cewa shine Ya Ammar ɗin da Mabaruka ta haukace a kan sa amma ko kallon arziƙi bata samu daga gare sa, to ita me yasa yake sake mata har haka ne? Da wannan tunanin a ran ta suka shiga ɓangaren Iyayen Sahib Mijin Aunty Aimana kasancewar a can aka sauke ta sai an dawo daga dinner za'a miƙa ta nata ɓangaren in da zasu yi sati biyu kafin su wuce Sweden.

   Kai tsaye ɗakin da aka sauki Aimana suka ƙarasa suma in da suka same ta ita da ƙawayenta da wasu daga cikin ƴan'uwansu, abinci mai rai da motsi aka kawo musu suka ci suka huta kafin lokacin dinner mai shirya amarya ta shigo. Suma su Nanah shiri suka sake yi tamkar yanda kowa ya kimtsa, Masha Allah amarya tayi matuƙar kyau cikin shigar dinner ɗin. Su Nanah ma sun yi kyau sosai cikin leshin da suka saka, abinsu ɗas ƙannen amarya masu capacity.

   Ƙarfe 8 aka fara tafiya wurin dinner ɗin in da Ammar yazo ya ɗauke su kamar yan da yayi alƙawari, yayin da ƴanmata ke ta masa iyayi shi kuma hankalinsa baya kansu. Sai a wurin dinner ɗin ne Nanah taga su Nawal da Ya Yusrah wan da ban da harara babu abin da suke jifanta dashi, babu wan da ta kula taci gaba da sha'aninta ita da Anisa da new friends ɗin da suka yi.

   10:00pm Ya Ammar yazo ya mayar dasu gida ba tare da an tashi ba, don tun ɗazu Ammy keyi wa Anisa waya a kan maza su taho gida. Yana sauke su suka masa sallama suka shige sabo da a gajiye suke sosai bacci suke nema musanman Nanah da bata fiye jure wahala ba. Yujawa Ammar yayi da niyar wuce wa fuskarsa ɗauke da murmushi yaci karo da Ya Mooh dake tsaye a jikin motarsa yana bin sa da wani irin kallo.

   "Barka da dare Hammah Mooh." Ammar ya faɗa yana nufar in da yake. Da ƙyar ya iya buɗe baki ya amsa masa kafin ya ɗora da tambayar daga ina suke.

   "Daga wurin dinner na ɗauko su Little Sis Hammah." Ammar ya bashi amsa. Faɗa sosai Mooh ya rufe Ammar dashi irin wan da bai taɓa masa ba a kan daren da suka yi wan da har hakan ya bashi mamaki. Sai dai bashi da damar tankawa don haka haƙuri kawai ya shiga bashi sannan ya wuce yana mamakin fusatar Hammah Mooh ɗin nasa. Dogon tsoki Mooh yaja bayan wucewar Ammar yana raya cewar dole ya ɗauki matakin daya dace don ba zai bari hakan taci gaba da faruwa ba, saboda tun daga waccan ranar daya taimake ta daga hannun azzalumin nan yayi wa kansa alƙawarin kulawa da ita.

   Yana da niyyar koma wa wannan kauyen a kan al'amarinta da zarar ya kammala karatunsa gaba ɗaya ya dawo gida, katsam kuma sai ya ganta a gidansu wan da yayi mamakin hakan sosai. Sai da Mamu ta kira sa tayi masa bayanin komai a game da ita ta tabbatar masa cewa a nan zata ci gaba da zama ba zata koma ba, don haka ta buƙaci ya sama mata makaranta a sakata don ci gaba da karatunta. Don haka yake jin ya samu cikakkiyar damar yin abin da ya dace, da haka ya juya ya nufi ɓangaren Ammy don shigowarsa kenan shima ya gansu sun fito daga motar Ammar ɗin.


★ Biki ya ƙare don haka Yau ne mutanen Kano zasu koma gida, tun da safe kowa ya kammala shirinsa yana zaman jiran Abba yace su fito, yayin da su Mabaruka ke murnar zasu koma gida in da zasu fanshe haushi su a kan Nanah don sun shaƙi baƙin ciki mai yawa a kanta. A ɓangaren Nanah ita ma jikinta a sanyaye yake don har ga Allah bata son komawa Kanon nan, haka ma a ɓangaren Anisa don roƙonta ta riƙa yi a kan tayi zaman ta a nan mana. Bata ce mata komai ba sai dai tayi mata murmushi kawai don ba ita ke da ikon kanta ba.

   Murnar su Mabaruka ta koma ciki ne lokacin da Mamu ta sanar da Abba cewar Nanah da Khalid ba zasu koma Kano ba a nan zasu ci gaba da zama riƙon su ya dawo hannunta. Shi Khalid tuni an fara nema masa makaranta mai kyau a India in da Ammar yake karatu don haka da zarar an kammala shirye-shirye zasu wuce tare. Gaba ɗaya ji suka yi tamkar an buga musu guduma a kai har Abba domin kuwa babu wan da ya tsammaci jin hakan, tsallen murna Anisa ta doka ta rungume Nanah tace.

   "Yes, thank you Mamu naji daɗi sosai da sis zata zauna a nan, shike nan sai a saka ta a makarantar mu mu riƙa zuwa tare." Ta faɗa cikin murna. Itama Nanah daɗi sosai ya kamata musanman jin cewar Ya Khalid ɗinta zai tafi ƙasar waje karatu, wannan yasa murmushi ya kasa barin fuskarta.

    "Amma Yaya Khalid fa yana karatunsa a can Kanon tare da ƴan'uwansa." Abba ya faɗa don shi dai fa in ma ƙasar wajen ce gara ace ɗaya daga cikin yaransa ne aka biya wa.

   "Rufe min bakinka Balarabe tun da kai baka jin kunyar ƙarya a rayuwarka, wai yana karatu da ƴan'uwansa bayan yaron shi da kansa yayi faɗi-tashin yan da yayi ya saka kansa a Makaranta yake ɗaukar ɗawainiyarsa har da ta ƙanwarsa. Bayan nan kazo Ridwan ya baka kuɗaɗen da ya isa ka saka su duka a makaranta, amma sabo da rashin tsoron Allah ka saka iya waɗan da ka haifa shi kuma ko oho. To kan ka ka yiwa amanar ɗan'uwanka ka kasa riƙewa!." Mamu ta ƙare maganar cikin ɓacin rai hawaye na zubo mata. 

   Kunya sosai ta kama Abba in da yayi ta ƙoƙarin kare kansa wan da duk zance ne mara kan gado bare ma'ana yake yi. Ana cikin haka ne Mabaruka tace.

   "Mamu nima ba zan koma ba a nan zan ci gaba da zama to." Tayi maganar cikin tashin hankalin jin cewar a nan Nanah zata zauna, kenan ta samu damar samun kusanci da Ya Ammar ɗin ta. 

   "Karatun naki fa waye zai ƙarasa maki shi?!." Hajiya Masa'uda ta tari Mabaruka tun kafin ta ƙarasa rufe baki. Tuburewa Mabaruka tayi a kan ba zata koma ba ita ma, yayin da Hajiya Masa'uda tace bata isa ba. Ƙarshe dai dole Dady ya lallaɓa ta a kan tayi haƙuri taje idan ta kammala karatun sai tazo.

   Haka dai aka ƙare zaman zuciyoyin wasu da yawa babu daɗi a kan abin da ya faru wan da basu tsanmata ba. Gaba ɗaya ahalin Alhaji Bala sun yi dana sanin wannan zuwa Abujar da Nanah domin kuwa babu abin da suka tsinta sai tarin takaici. A ɓangaren Abba haka ya tafi rai a matuƙar ɓace domin bai samu amsar kuɗaɗen da yayi niyyar amsa a hannun Dady ba sabo da abin da ya faru, sai tarin kunya daya koma da ita. Sauƙin sa ɗaya shine rashin ɗago maganar gadon yaran da ba'a yiba, da bai san ina da zai kama ba.


___________★

    Sosai Nanah ta sake take rayuwarta a ɓangaren Mamu hankali kwance babu mai zagi ko kyarar ta, yayin da Mamu ta dage mata a kan cin abinci ko bata so. Haka ta saka Baba kullum take dama mata kunun sabaya ana zuba masa wadatacciyar madara tana sha safe da yamma, har kuka Nanah keyi idan Mamu ta matsa mata akan sai taci wani abun wan da hakan ya fara bawa Mamu tsoro take ganin kamar ba lafiya take ba. Wannan dalilin yasa ta ƙudiri niyyar saka wa a kaita asibiti likita ya duba mata ita don ita kam abin yana damunta, taya za'a ce ɗan mutum ba zai ci abinci yanda ya kama ta ba. Har idan aka matsa sai kuka, kai ina wannan abin bana lafiya bane gaskiya.

   Nanah da Anisa sosai suka ƙara shaƙuwa don koda yaushe suna tare a ɓangaren Mamu ko na Ammy, dama can Anisa bata shige-shigen sauran ɓangarorin mutanen gidan sabo da kowa rayuwarsa yake sai in wani abu ya haɗa. Inno kuwa dama can tun kafin zuwan Mamu gidan basa samun sakin fuska daga gare ta, musanman daya kasance ba son Ammy take yi ba. Daga jikokinta sai yaran Hajiya Badariyya sune nata, gaba ɗaya yaran gidan basa da irin wannan shaƙuwa da junan idan ka cire Muhammad da Ammar wan da Inno ta kasa raba wa.

   A halin yanzu babban abinda Inno ta saka a gaba shine kawar da Mamu daga mansion ɗin gaba ɗaya domin ta lura hankalin Baba Alhaji yana a kanta ne, don tana da labarin yana shiga ɓangarenta da sunan gaisa wa.

   Lokacin da Hajiya Badariyya ta sanar mata cewa ai Mamu ta ɗebo riƙon jikokinta na can Kano ba ƙaramin ɓaci ranta yayi ba.

   "Lallai ina da aiki, taya ma nayi saken da matar nan ta ƙara dawo wa cikin ahalina ta miƙe ƙafa har da ɗebo riƙon Jikoki don ta nuna wa duniya cewar ita ke da ikon zartar wa a gidan nan, to kuwa zan nuna mata cewar na fita matsayi da cikakken ikon faɗa aji a gidan ɗan nata da take taƙama!." Inno tayi maganar cikin matuƙar ɓacin rai.......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.