Free chapter · Read without an account
MASARAUTAR KAIZUR 46
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 46
Kallonshi kawai gimbiya Hayat take yi ba tare da ta yi magana ba har ya kai aya, cikin ɓacin rai wanda ya taso mata ta ce"Ni wata tsiya ce mana, tunda gashi nan ka zubar da girman da Sarautar ka taho neman yardar aure na, kuma kai ɗin kai wanene da kake jin kanka har kake tunani za ka tsallako har masarautar ubana ka ci min mutunci?"
Murmushin ƙasaita Zohran ya yi,ya ce"ko da yake bai kamata na damu ba,ko na kula,an tabbatar min da cewa ke ɗin rainon namiji ce,a matsayin mahaifinki na sarki guda yana raye ne shi kadai ba aure,bayan ya kashe matansa,kuma don haɗama ya haɗa da babban ɗanshi,to amma ina so ki san wani abu, wannan ɗabi'ar idan kika ce za ki tafi da ita zuwa Kiswa babu ruwan kowa da wata ƙwailar Sarautar ku,a shawarce kenan!"
Maganar ta yi mata zafi, hawaye suka ciko idanunta,amma kafin ta samu zarafin yin magana ya cigaba da magana yana É—an murmushi
"Kuma fa kina da kyau daidai gwargwado,da riba sosai,tunda na zo na taya"
"Da riba kuwa tunda ka zo ka taya!
Da ace na kasance irin matan garin ku da bana jin za ka ga ribar da za ka zo ka taya
To ka sani,bana sonka,bana ƙaunar ka,kuma har abada ba zan taɓa sonka ba,ka je can da sarautar ka da izzarka,kuma maganar da ka faɗa cewa mahaifina ya kashe iyalinsa ka je kai da Allah "tana kai wa nan ta miƙe tana zubar da hawaye ta yi hanyar fita zuciyarta tana zugi,tana jin shi yana faɗin "tabbas sai kin yi nadanar waɗannan maganganun da kika faɗa"ko kallo bai ishe ta ba ta fice daga ɗakin tana sauke ajiyar zuciya cikin kuka sosai
Kai tsaye ɗakinta ta tafi,a bakin ɗakin ta samu huda ta yi jugum,tana ganinta ta miƙe da sauri tana kallonta ganin yadda ta dawo wujiga-wujiga, Hayat ta fashe da kuka sosai, Huda ta rungume ta jikinta yana rawa,ta ja hannunta har zuwa ɗakin ta,suka zauna sannan huda take faɗin"ya shugaba ta lafiya?
Me ya yi miki ne?"
"Huda bana son shi,na tsane shi,ba shi da kirki, Huda ya wulaƙanta ni,yana yi min rashin mutunci,yana gaya min magana mara daɗi, huda ya zan yi?da wanne zan ji?"
Huda ta kwantar da murya ta ce"komai zai wuce ya shugaba ta, aurenshi ne dai ba za kiyi ba,da izinin Allah mutumin kirki za ki aura,ba wannan ba,ki yi haƙuri ya shugaba ta
Bai kai darajar da za ki zubar masa da hawaye ba,ki tuna akwai wani,wanda da zarar wannan hawayen zai zuba a mutunce yake tare shi yana hana shi zuba,babu hujjar zubar da shi ga wanda bai san darajar shi ba
Ki bi komai a hankali ya shugaba ta, in sha Allah mune da nasara"
Cikin kuka Hayat ta ce"na san Abby baya yin alƙawari ya saɓa,na san ba zai taɓa canja magana ba tunda ya bayar da aure na ga yariman Kiswa,ya zan yi?"
"Addu'a ya shugaba ta,babu abin da Allah bai iya ba,shine zai taimake mu, ki daina kuka ya shugaba ta"haka Huda ta cigaba da kwantar mata da hankali,ita dai ta ji Huda ne kawai,amma bata jin wannan ƙaddararren auren da aka haɗa zai tsinke
*DAULAR KAIZUR*
Yau ne bikin al'ada na sarautar kaizur,a ƙa'ida sarki da fadawanshi suna fitowa bakin fada,inda jama'a suke taruwa,ana yin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe,ana cin abinci mai kyau,sarki da fadawanshi suna yin ƙawatacciyar kwalliya wadda take burge jama'a,kuma kusan kowacce shekara da irin kaya da kuma kalar kayan da sarki yake sakawa
Tun safe Munaya da Sahal suka kammala cin abinci bisa umarnin Munaya,ta yi Ć´an aikace-aikacen da ta saba, sannan ta sanya sabuwar suturar da Sahal ya siya mata babu jumawa
Kallonshi ta juya ta yi da mamaki,yana zaune kawai,ya jingina kanshi da jikin bango, idanunsa a lumshe,da alamu ma ya zurfafa a wani tunanin
"Sahal!
Sahal!!
SAHAL!!!"ta ƙwala masa kira da ƙarfi a ƙarshe
Firgigit ta ya gyara zama yana sauke ajiyar zuciya,da kallon tuhuma take bin shi, kafin ta ce"tunanin me kake yi ne haka?"
Waro idanu ya yi yana É—an murmushi,ya ce"Ni kuma?
Ba tunani nake yi ba fa,kawai bacci na fara ji ne"
"To kuwa ba za ka yi baccin nan ba,ai dama Kai kake hana kanka bacci da dare da iyayi irin naka ka ce za ka tafi wani wajen ka yi ta shirme
Maza ka tashi,zan raka ka har cikin masarauta,a shirya ka, idan ya so sai ku tafi zuwa bakin fada"
Fuska a É—aure ya ce"a shirya ni kuma? kuma ni da wa? sannan mu je mu yi me?"
"Eh a shirya ka,kai da babanka da ƙaninsa,kuma za'a gabatar da babban bikin masarauta ne da ake yi duk shekara,ko za ka ce min tun jiya baka ga canjin komai a masarauta ba?"
Taɓe baki ya yi ba tare da ya sake magana ba, Munaya ta cigaba da faɗin"wai tukunna ma,anya ka je kiran da mai martaba ya yi maka kwanaki kuwa?"
Ya fara gajiya da tambayoyin nan,ya yatsina fuska a shagwaɓe, bata kula ba ta ce"tashi ka shirya Sahal
Idan kuma ka ƙi shikenan,ka nuna min ban isa da kai ba"
Miƙewa ya yi akan dole ya shirya,shi fa Ummeey bata san halin da yake ciki ba ta zo zata takura masa a kan wata fita da bata gabanshi,mafarkin da ya yi da masoyiyar shi Hayat ya ɗaga masa hankali sosai,kukan da ya ga tana yi ya dame shi sosai,a jikin shi yake jin cewa tana cikin matsala
Tare suka fita zuwa bakin fadar,tun sanda suka fita ko ina suka bi sai an zube ana gaishe shi,ko kallo babu wanda ya ishe shi,sai bin kwalliya da ado da aka yiwa masarautar yake yi yana taɓe baki
Shi kanshi ya sani,bai taɓa ganin masarauta mai tarin arziƙi,wadata,da isa irin MASARAUTAR KAIZUR ba a tsawon rayuwarsa, masarautar da tsabar isa Irin tata ba dai a kawo mata harin yaƙi ba, kuma idan ta kai ma yawanci tana saka dakarun abokan hamayya su yi gudun tsira ko su miƙa wuya,amma sam bata burge shi ba, tunda ya zo kaizur bai ga wani abu ɗaya a ciki da ya burge shi ba, tunda babu Hayatynshi a cikinta
Har bakin turakar Sarki Mu'iz Munaya ta kai shi, sannan ta sa a nemo musu iso a wajenshi
Jim kaÉ—an aka ba su izinin shiga,suka shiga da sallama,duk da tsoron da Munaya take dannewa sai da ya bayyana akan fuskarta
A gaban sarki Mu'iz suka zube, cikin girmamawa Munaya ta ce "Barka da wannan lokaci ya mai martaba!"
Kallonta ya yi,cikin izza irin ta sarakai ya ce"Barka dai Munaya!
Ina yi miki maraba da dawowar É—anki gare ki"
Kanta a ƙasa ta ce "ai ikon ka ne shi ya mai martaba!"
"Ba dai iko na ba Munaya!
Ikonki dai,to!ba zan yi miki musu ba,duk da kasancewarki baiwa a idanun duniya ke É—in sarauniya ce a idanun É—anki,a matsayin ki na wadda kika kawo shi duniya
Ba zan yi miki musu ba, wannan matsayi ne da Allah ya ba ki,babu mai ƙwace miki shi,amma kuma kin nuna son kai,irin wanda kika so nunawa tun yana jariri sabuwar haihuwa"
Sake rissinawa ta yi,shi dai Sahal har yanzu ko uffan bai ce ba,ta ce"ka gafarce ni ya shugaba na,idan na yi wani abu ba daidai ba,mai girma Yarima har yanzu yana cikin zafin rai ne,bana iya tanƙwara shi akan abin da bai yi niyya ba,yana jin zafin yadda ya rayu ne,da kuma yadda ya zo ya samu mahaifiyarsa a cewarshi,yanzun ma sai da aka kai ruwa rana Sannan ya yarda ya zo
A yi mana aikin gafara ya shugaba na "
Shiru ya yi na wasu ƴan daƙiƙu kafin ya ce"kina iya tafiya!"
Munaya ta sake rissinawa ta ce"na gode ya shugaba na!
A fito lafiya mai martaba "
Miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin, Sahal da yake jinsu shima ya miƙe zai fita, Sarki Mu'iz ya kama hannunsa ya riƙe
Juyowa ya yi yana kallon sarki Mu'iz,sai ya ji ya yi masa kwarjini, cikin dakakkiyar murya ya ce"Muhammad zauna!"
Babu musu ya dawo ya zauna, kamar wani Yaron goye yana kallon hanyar da mahaifiyar shi ta bi,abin ma sai ya ba wa Sarki Mu'iz dariya,ya yi murmushi mai sauti,har sai da Sahal ya kalle shi sannan ya yi ƙasa da kanshi
"Muhammad Sahal ibn Mu'iz, ibn Ammar, ibn Suhaif,ibn Yassar!
Yau dai ga ka ga Abbey É—inka bayan shekaru da dama,na rasa ka tun kana É—an jariri, sai gashi na same ka a lokacin da ban yi zato ba,amma kuma sam bana burge ka, asalima a fusace kake da ni,ta mahaifiyar ka kawai kake yi
Kwanaki ma na aika a kira ka,aka tabbatar min da cewa ka ce ba za ka zo ba,sai da ta turo ka ka zo ka zauna a wani wajen,wato dai ka gwammace ka zauna a wani wajen ba tare da mahaifiyar ka ba ma, da ka zo inda nake ko?bayan cewa ni kuma ina ƙaunarka, tsawon shekaru ban huta da tunaninka ba,amma yadda ka yi min a yanzu ya saka jikina ya yi sanyi
Yanzu dai a yi ta ta ƙare,ka gaya min,me kake so na daina? menene abin da baka so game da mahaifinka?mhm?
Ina sauraren ka"
Gyara zama ya yi,kai tsaye ya ce"so nake ka gaya min ƙimar abin da zan fanshi mahaifiya ta,ina so na ɗauke ta daga nan ne,na gaji da kiranta baiwa da mutane suke yi"
Murmushi sosai sarki Mu'iz ya yi,ya ce"ai tuni na Ć´anta mahaifiyar ka, dama yarjejeniyar tana haifar ka ta zama Ć´antacciya ne"
Cikin zafin rai Sahal ya ce"to menene dalilin da ya sa aka kawo mahaifiya ta don ta haife ni?
Saboda me? saboda na zama sarki ko?na gaji kaizur?
To ni bana son wannan sarautar, shi wanda ya ɓatar da ni don ya yi mulkin na bar masa,ya je ya yi
Ni dai yanzu ina son ka gayawa dakarun masarautar ka su bar mu mu fita daga garin nan,bana son ganin garin nan ma"
Hannu sarki Mu'iz ya saka ya ɗago haɓar Sahal, idanunsu suka gauraya da na juna,take wani rauni ya daki zuciyarshi, idanunshi suka fara tara ƙwalla,a take ya ji ya saki gaba ɗaya, yanzu ya sake tabbatar da cewa haushin sarki Mu'iz kawai yake ji,amma ba ƙinshi yake yi ba,dole akwai soyayyar ɗa da uban a tsakaninsu
"Muhammad! Wanene ya gaya maka saboda sarautar kaizur na haife ka?
Kar ka sake wannan tunanin,na haife ka ne saboda ina son ganin ƙwai na a doron ƙasa, shekaru na ashirin da aure, ƙanina Zaffar da ya yi aure bayan na yi ya aurar da ƴaƴanshi mata guda uku,ba don shi ba kawai, kowanne ɗan adam yana da burin haihuwar yara,a ce wannan nashi ne
Bani da burin ƙara aure kamar yadda sauran masarautu suke yi,kakana Suhaif ya sha wahalar matan uba, mahaifina ya sha wahalar matan uba, kazalika Ni na ga rarrabuwar kai a gidanmu, mahaifiyar Jamal sam bata ƙauna ta da ni da Zaffar, shine dalilin da ya sa gaba ɗaya wata sabgar ƴan ubanci ta fice min a rai
Sahal! babu wani bawa da ya isa ya kaucewa ƙaddararshi, Amna ce ta buƙaci kawo baiwa don ta haihu,bayan an kawo baiwar sun yi magana da ita magana ta fahimta,amma a ƙarshe ta canja shawara,shawarar kawai ta kashe ka
Maganar mulki kuwa,ko da ace ba'a bani ba a yadda nake jin Zaffar zan iya bar masa,da yace yana so,amma sai ya nuna son zuciya,ban yi baƙin ciki da hakan ba,na karɓi hakan a matsayin ƙaddara ta kenan
Ya kamata ka gane babu laifi na anan,kuma ko da akwai laifi na ina neman yafiyar wannan sadaukin jajirtaccen gwarzon É—an nawa wanda nake so fiye da yadda nake son kaina,ina alfahari da kai É—ana"
Shiru dai babu niyyar zai yi magana, sarki Mu'iz cikin damuwa ya sake ɗago da kanshi yana kallon idanunshi da har yanzu ba su daidaita ba,ya ce"zan ba ka lokaci ka sake tunani,na san in sha Allah a ƙarshe za ka haƙura ka yafewa wannan mahaifin naka ko?"
Kanshi a ƙasa ya ce"so nake na tafi da mahaifiyata inda za'a daina ce mata baiwa"
"Mahaifiyarka ba baiwa ba ce kamar yadda na gaya maka tun a farko,an hukunta ta ne kamar yadda ake hukunta mutanen gari"
Sahal ya É—aga kai ya kalle shi, fuskarshi a É—aure ya ce"to wane irin hukunci ne wannan azabtarwa ta tsawon shekaru ashirin da É—aya?"
#Nusy_bee