Free chapter · Read without an account

SARTSE A ZUCI...! Chapter 10

by Aysha Ɗansabo · SARTSE A ZUCI...!

*SARTSE A ZUCI...!* *Arewabook@ayshadansabo*

*Paid book*

©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻

*Chapter 10*

Ana saura wata ɗaya bikin Yaya Zayd da Hameedah Yaya Zayd ya samu aiki da ma'aikatar NNPC reshen jihar Lagos,kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya tattara ya wuce Lagos.Kuma tunda ya tafi ya rasa dukkanin nutsuwarsa hankalinsa naga Hameedah da shiryawa bikinsu,ta waya suke ta shiri shi da aminansa Suraj Galadima da kuma Mubarak Safana.Ana saura sati biyu biki ya samu ya dawo gida,kuma a washegarin ranar da safe Daddy ya aika Hameedah domin kiran Yaya Zayd.A she da rabon kunnuwarta za su jiye mata wayar daya tada hankalinta ya kuma zamo silar da Yaya Zayd ɗin ya sanar da ita duk irin ɓarnar da suka dinga aikatawa a UK shi da abokanansa,Daddyn ya nemi line ɗin Yaya Zayd ɗin ne yaji line busy shiyasa bayan sun gaisa Daddy ya aiketa yace taje side ɗin Zayd tayi kiransa.Ta amsa ma Daddy ta wuce direct zuwa ɓangaren su Yaya Zayd ɗin domin kiransa,a wajen compound suka haɗu da Yaya Sulaiman zai je ɓangaren Daddyn gaidashi suka gaisa ta wuce ciki domin kiran Yaya Zayd ɗin.Tana isa ɓangaren nasu direct ta wuce room ɗin Yaya Zayd ta shiga knocking ƙofar shiga falonsa,jin shuru bai amsa ba ta murɗa ƙofar falon ta shiga.Jin shuru babu kowa a ciki sai ta nufi hanyar bedroom ɗinsa domin jin koya shiga wanka ne,har ta kai hannu zatai knocking ƙofar kunnuwarta suka fara jiyo mata wayar da yake da friend ɗinsa Najwa Kabeer ƴar asalin jihar Katsina da suka haɗu a UK.Magana suke yana bata haƙuri akan rashin daina ɗaga wayarta da yayi tsayin lokaci kuma ya hana tazo Zaria ta sameshi,yayi mata alƙawarin za su haɗu a KD gidan amininsa Suraj Galadima amma bai cika mata promise ba domin akwai Anty ɗinta dake aure anan Kaduna tana yawan zuwa wajenta ta jima a KD.Babban abinda ya ɗauki hankalin Hameedah ya kuma gigita tunaninta shine jiyo muryar Yaya Zayd ɗin da tayi yana sanar da Najwa irin missing ɗinta da missing soft body ɗinta da yayi,jikinta ya ɗauki rawa a lokacin data jiyo yana mata magiyar ta amince ya kirata vedio call bayan ta cire rigar jikinta domin yaga ƙirjinta da yayi missing laushinsu.Sai taji ƙafafunta sun kasa cigaba da ɗaukarta kamar yadda bata san lokacin data kai hannunta ta murɗa ƙofar ɗakin baccin nasa ba,kuma cikin sa a ƙofar a buɗe take don haka take ta danna kanta ciki tana jin wani irin tashin hankali na mamaye zuciyarta.A lokaci guda Yaya Zayd ɗin ya ɗaga idanunsa ya kalleta yana saurin latse wayar yayi jifa dashi a saman bed ɗinsa,kuma a kallo ɗaya da idanunsa sukai ma fuskar Hameedah ya gano cewa tabbas taji wayarsu da Najwa.Shiyasa a lokacin data jefa masa tambayar cewa wace ce Najwa? Bai iya ɓoye mata komi ba ya sanar da ita cewa friend ɗinsa ce da suka haɗu a UK.Hameedah kishi ya rufe zuciyarta har bata san lokacin data jefa masa tambayar daya tayar da hankalinsa ba domin kai tsaye ce masa tayi,"Yaya Zayd itace wacce ka saba nema acan kuna aikata zina alhali kana ɗan musulmi da aka karantar dakai haramcin aikata Zina da kusantarta? Kaji tsoron Allah ka sanar dani gaskiyar alaƙar dake tsakaninku sannan ina son sanin su nawa kayi tarayya dasu acan ɗin?"Waɗannan sune tambayoyin da Hameedah ta jefa masa suka kuma tayar da hankalinsa tare da jefa tausayinta a cikin zuciyarsa mai tsanani.Kuma kamar yadda ta roƙi alfarmar sai ya buɗe mata sirrikansa ya sanar da ita gaskiya irin ɓarnar da suka dinga aikatawa shi da aminansa Suraj Galadima da kuma Mubarak Safana,waɗanda sune suka fara dilmiyar dashi wajen nuna masa cewa abinda suke aikatawa ƙaramin zunubi ne domin ba babbar Zina suke aikatawa ba iyakar romance kawai su jiyar da junansu daɗi ta hanyar taɓa jikin juna da wasa da junansu suke.Ya roƙi Hameedah akan ta rufe sirrinsa ta kuma yafe masa domin tabbas yayi tarayya da mata da yawa ba iya Najwa bace kawai ya fara faɗawa tarkonta domin yayi mu'amala har da fararen fata,sai dai yayi mata rantsuwar cewa bai taɓa shiga jikin kowace mace ba kuma baya fata ya aikata hakan sai a kanta domin ita kaɗaice zuciyarsa keso yake kuma burin mallakarta ciki da wajenta.Tsananin ƙarfin sha'awa da yadda mata suke shige masa shine dalilin da yasa sukai galaba a kansa har ya kasa riƙe kansa ya faɗa aikata wannan haramcin,sannan ya sanar da ita cewa daga randa ya baro UK bai sake sha'awar aikata komi ba shiyasa sha'awar son ya kasance da ita ya rinjayi zuciyarsa har abinda ya shiga tsakaninsu da ita ya faru ranar da Amal ta kamasu.Duk wasu maganganu na magiya babu irin wanda bai yiwa Hameedah ba,har da zub da mata hawaye yana sanar da ita cewa ya tuba bazai sake ba sannan yace tayi masa promise ɗin cewa za ta jure buƙatunsa bayan aure ba za ta taɓa gazawa dashi ba domin tabbas yana cikin halittar mazan dake buƙatar mace sosai a kusa dasu.Bai bar Hameedah ta fito daga ɗakinsa ba saida ya tabbatar ya rarrasheta ya kuma gama kanainayeta da daɗaɗan kalaman da suka sanyaya zuciyarta daga zafin data ɗauka dashi,suka fito jera da juna domin zuwa ya amsa kiran da Daddy keyi masa suna tafe yana sake kasheta da kalaman dake sake narkar da zuciyarta a kansa.Ya wuce ɓangaren Daddy ita kuma ta nufi na Momy ta wuce direct zuwa ɗakinsu ta faɗa gado tana tunanin abinda kunnuwarta suka jiye mata na wayar da Yaya Zayd yayi da Najwa,labarin irin rayuwar da yayi da mata a UK ya dinga dawowa cikin kwanyarta tana aunashi da irin rayuwar da suke ganin da yawan ƴan matan jami'a nayi na soyayyar shan sweet da maza.Brain ɗinta ya shiga hasko mata ƴan mata da yawa da sukan fita tare da samarinsu su tafi yawon shaƙatawa har su iya dawowa cikin hostel suna bada labarin yadda namiji ke taɓa jikinsu,sai taji a lokacin kishi mai zafi ya sake rufe zuciyarta tana hasaso siffar Najwa a cikin idanunta domin itace taji muryarsa ya kama sunanta har kuma yana faɗin cewa yayi missing laushin fatarta dana breast ɗinta.Ta shiga shafa lallausar fatar jikinta har tana kai hannu saman ƙirjinta ta shiga taɓasu suma domin taji nata suma akwai laushin da yake magana ko babu?Zuciyarta ta gaza samun nutsuwa har tana ji kamar ta kira Amal ta sanar da ita komi.Amma kuma saita tuna magiyar da yayi mata akan ta rufe sirrinsa kuma ta yafe masa tunda itace take shirin zama mallakinsa,ta tuna yadda dama Amal bata yinsa ga kuma yadda ta kamasu a kwanakin baya tabbas idan ta sanar da ita mutuncin Yayan nasu ne zai sake zubewa a cikin idanunta kuma ta sake tsanarsa.Hakan yasa ta haɗiye komi ta barwa cikinta tana masa addu'ar shiriya dafatan cewa idan sunyi aure komi zai sake shigewa har ya manta cewa yayi soyayyar shan sweet da wasu ƴan mata,da wannan tunanin Hameedah ta ture komi a cikin kanta ta cigaba da sabga da hidimar shiryawa bikin aurensu kuma a ranar ne Anty Yagana ta iso daga Borno da Yamma.A kuma washegari ba tare da ɓata lokaci ba aka fara yi mata haɗaɗɗen gyaran jiki ciki da waje ana bata magungunan sanyi masu kyau tana sha,nan da nan cikin sati guda Hameedah ta sauya ta ƙaro wani irin kyawu da cika.Ƙamshi na musamman ya kama fatar jikinta,kuma zuwa lokacin tuni zaman gidan yayi ma Yaya Zayd wahala domin yana can KD ya tare ana ƙarisa gyaran gidan da za su zauna har ma an kammala fenti kawai ake ƙarisawa na ɗakunan waje na masu aiki.Amal Taheer nacan school suna fafatawa domin basu jima da komawa school ɗin daga hutun da suka samu bayan kammala exam ɗinsu na first semester ba,don haka basu iso Zaria ita da friend's ɗinta su Meenal ba sai ranar Wednesday da safe.Kuma sun iso ne sun tadda gidan a cike da ƴan Uwa da dangin Momy da suka iso daga Borno ga kuma Gwaggo Abu da Sakeenah da suka iso daga Jos tun Tuesday suma,suka rungume juna ita da Sakinah da take tsaran Hameedah domin ko a school tare suke tafiya itama ta kammala jami'ar Jos a lokacin.Dukkanin wasu shiri sun kammala hatta ɗinkunansu da suka bayar a garin Abuja sun iso Hameedah ta amsa ta adana mata nata,Jameelah itama ta gama yima bikin Hameedah shiri domin tare da ita Daddy ya basu kuɗin da suka ɗinka suturu na alfarma da za su yi fitan biki bayan ashobin su Kamu da bridal shower da kuma dinner da za ai idan an kai Amarya Kaduna.Dangin Umma Asiya Mahaifiyar Zayd suma duk wasunsu sun iso gidan Daddy tun Wednesday da yamma,cikinsu akwai ƙannin Asiya guda biyu da suka fito ciki ɗaya Anty Salma da Anty Talatu.Ranar Thursday aka gudanar da ƙayataccen kamun daya tashi kan dukkanin wanɗanda suka samu halarta,ranar Friday kuma aka gudanar da bridal shower wanda shima ya tashi kan ƴan matan Amarya da sauran friends da suka samu halarta.Washagerin ranar kuma ya kama asabar aka ɗaura auren Hameedah Taheer Lawal Ƙaura da Angonta Zayd Abdallah Lawal Ƙaura akan sadaki naira dubu ɗari biyar,daga nan aka zarce da yin reception da sauran shagulgula kafin zuwa yamma a kama hanyar kai Amarya ɗakinta dake garin Kaduna.A kuma daren da aka kaita ne aka gudanar da gagarumin dinner party ɗin da abokanan Ango su Suraj Galadima suka shirya masa domin suma ƴaƴan kusoshi ne a ƙasar,Suraj Galadima ɗan Kaduna ne kuma Mahaifinsa Alhaji Abubakar Galadima ɗan majalisar wakilai ne na tarayyar Nigeria.Shi kuwa Mubarak Mahaifinsa Alhaji Lawal Safana shine babban controller na ƙasa,sunci sun tada kai da naira suna kuma sakinma Yaran nasu bakin aljihu suna facaka da kuɗi yadda suke so.Ba ƙaramin dukiya aka kashe a wajen wannan dinner ba domin anci an sha yadda ya kamata,Momy da Anty Mamah duka sun halarci wajen Daddy ne kawai bai halarta ba.Washegarin ranar aka yi buɗan kan Amarya kafin kowa ya watse a baro Amarya a ɗakinta ita kaɗai,dangin Asiya suka tafi suna sambarka da shima Momy da Daddy albarka domin ba ƙaramin ƙayatar dasu gidan Amarya yayi ba.Sannan Uwa Uba irin yadda Momy ta riƙe musu amanan Yaran ƴar Uwarsu da zuciya ɗaya har gashi aure ya ƙullu anyi tuwona maina tsakanin Hameedah da Zayd ɗin,hakan kaɗai ya isa abin alfahari a garesu wanda ba za su gushe suna yiwa Momy addu'ar gamawa lafiya ba domin sukam ta gama musu komi.Ƙawayen Amal Zulaiha da Meenal tun a washegarin kai Amarya da safe suka wuce school,ita kuma Amal Zaria ta wuto ita dasu Jameela domin tace sai ta huce gajiyan biki na sati biyu za ta koma school ɗin.Time ɗin da suka iso sun tadda duk yawancin baƙi ƴan wasu gari duk sun kama hanya tunda safe,dangin Momy ma duk sun tafi ƙannenta biyu Anty Falmata da Anty Yakaka su kaɗai ne basu tafi ba sai zuwa washegari suka wuce Abuja domin bin flight zuwa Maiduguri.Su Gwaggo Abu da Sakeenah suma sun wuce Jos kowa ya kama gabansa tamkar ba a taba yin taro a gidan ba,Amal kwananta biyu ta juya Kaduna domin tana da test ranar Wednesday da safe.A can Kaduna kuma tuni Ango ya samu damar Angoncewa da Amaryarsa Hameedah Taheer,sosai tasha baƙar wahala a darensu na farko har saida ya kira Doctor Rahina tazo har gida ta baiwa Hameedah taimakon daya dace.Sosai Hameedah ke shan wahala domin kwanaki biyu kaɗai ya iya ɗaga mata leg kafin ya cigaba da Angoncewa yana nutsawa cikin duniyar da bai taɓa sanin akwai mai ni'ima da garɗinsa ba,dukkanin haƙurin da yayi na tsayin shekaru saida ya huce haushinsu cikin matuƙar gigicewa da sake dilmiya a zazzafar ƙauna da soyayyar Hameedah a cikin zuciyarsa domin tun daren farko ya fara kiranta da suna zumarsa.Sati biyu ya kwashe baya fita ko'ina inba da dare sun fito cin wani abu koya fita siyan abinci domin ya hanata fara girki holewarsa kawai yake baya ƙaunar duk abinda zai sanya tabar jikinsa idan suna tare,Hameedah sai ta fara ramewa tayi ɗan wuya sabida kullum cikin zullumi take ta kasa sabawa dashi da yawan buƙatunsa.Hankalinsa sai ya fara tashi da ganin yadda take ramewa,tausayinta ya kamashi domin ba ƙaramin ƙoƙari take wajen bashi haɗin kai ba bata taɓa hanashi kanta ba sai dai idan ya gama tayi kukan jigata ta share hawayenta.Ranar Sunday da safe ya tattara ya wuce Lagos bakin aikinsa cike da damuwar yadda zai iyayin sati biyu zuwa uku kafin ya dawo ba tare da Hameedah a gefensa ba,ita ko Hameedah duk ta ƙosa ya tafi ta huta domin dauriya kawai take da nuna jarumta amma tuni ita lamarin ya isheta.Bayan wucewarsa ne ta cire kunya tayi ma Anty Yagana magana a chat akan ta taimaka mata,a lokacin ne Anty Yagana ta fahimci cewa su Falmata sun manta basu damƙawa Hameedah kayan gyaran data haɗa mata domin su taimaka mata ba.Nan ta sanar da Hameedah cewa ta kira Anty Falmata ta sanar da ita inda suka aje mata,kuma tunda ta fara amfani da magungunan ta fara jin canji koda yayi sati biyu a daddafe ya dawo sai taji ta fara jurewa yawan buƙatunsa.Shi kuma kullum sake gigicewa a kanta yake,yana sake jin cewa ita ɗin baiwarta na daban ne ko a cikin mata.Amal Taheer nacan school suna fafatawa sam bata sake waiwayen gidan Amarya Hameedah ba,ita Hameedar ce data ga har anyi sati biyu Amal bata zo mata weekend ko sau ɗaya ba ta kira Amal ɗin tace tayi fishi.Kuma buɗan bakin Amal sai cewa Yaya Hameedah tayi aita bari ne sai Yayan nasu ya gama Angonci ya koma Lagos tunda kullum sukai waya a manne da juna take jinsu,don haka ba za ta kwaso ƙawayenta suzo su tadda abinda idanunsu zai kusa makancewa ba.A lokacin ba ƙaramin dariya ta baiwa Yaya Hameedah ba,kuma nan take Yaya Hameedah ta gane cewa Amal nanan riƙe da wancan lokacin ne a cikin zuciyarta time ɗin data kamasu ita da Yaya Zayd yana romancing ɗinta.Sai a satin da suka cika 4 week's da aure ne Amal ta kwashi Meenal da Zulaiha suka je gidan Yaya Hameedah da zimmar ita za su barta a can tayi wa Hameedah weekend ko hankalinta zai kwanta tunda Yaya Zayd ɗin yazo ya koma,sannan itama Amal tana son Aman Kurfi yazo yaga gidan Amarya domin shima sai da yayi mata ciwon bakin cewa taƙi kaishi gidan Yaya Hameedah.Don haka tun friday ɗin tayi masa albishir ɗin cewa wannan weekend ɗin a gidan Yaya Hameedah za su haɗu,kuma tun a cikin wayar taga yadda fuskarsa ta haska da farin cikin da har yaso bata mamaki domin bakinsa ya kasa rufuwa.....✍🏻

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.