Free chapter · Read without an account
MASARAUTAR KAIZUR 48
🗡️👑 MASARAUTAR KAIZUR 🗡️👑
✍️Nusy bee
❤️ Young talented writers association YOTA ❤️
(Under YOTA'S AMAZING PENS)
Page 48
Shiru sarki Iyaad ya yi na wasu ƴan daƙiƙu,kafin ya ce"me za kiyi a can ɗin?"
Sai da ta É—an goge idanunta sannan ta ce "ina so na je na gaishe su ne"
"To ya yi kyau, tsawon wanne lokaci za ki É—auka a can É—in?"
"Ba zan wuce kwanaki goma ba in sha Allah"
Sarki Iyaad ya jinjina kai ya ce"to babu laifi, Allah ya kiyaye hanya,zan saka dakaru su raka ki,tare da kuyanginki"
Gimbiya Hayat ta jinjina kai tana rissinawa ta ce "na gode Abbey
Allah ya ƙara girma Abbey"sarki Iyaad ya jinjina kai, gimbiya Hayat ta rissina sannan ta miƙe ta fice zuwa sashenta
*DAULAR KAIZUR*
Yau ce juma'a ta farko da Sahal zai yi a cikin Garin kaizur, Munaya da kanta ya wanke masa dogon gashinsa ta gyara masa shi,ya yi wanka,ya sanya suturar shi yadda ya saba ya fita zuwa masallacin juma'a
Lokacin da ya isa limamin kaizur Rabee'a yana gabatar da huÉ—uba,waje ya samu nesa da mutane ya zauna yana kalle-kalle, duk da cewa tunaninshi ya cigaba da yi
Sallamar yarima Jamal ce ta dawo da shi hayyacinshi,ya É—ago a sanyaye yana amsa sallamar, sannan ya rissina yana faÉ—in"Barka da warhaka ranka ya daÉ—e "
Barkanka dai yarima,kana lafiya?"
Jinjina kai ya yi a hankali, cikin sanyin murya ya ce "alhamdulillahi ranka ya daɗe"Yarima Jamal ya kama hannunshi ya ce"mu je mu zauna a sahu,nan ba sahu bane "babu musu ya miƙe suka tafi, don yana matuƙar girmama yarima Jamal
A kusa da mahaifin shi sarki Mu'iz ya zaunar da shi, sannan shima ya samu waje ya zauna, Sahal ya rissina yana faÉ—in"Barka da warhaka ranka ya daÉ—e "
Sarki Mu'iz ya dafa kanshi yana jinjina kai da É—an murmushi a fuskarshi
Bayan an idar da Sallah mutane suka yi ta zuwa suna kwasar gaisuwa a wajen sarki Mu'iz da yarima Jamal da shi Yarima Sahal,sai dai babu wanda ya tankawa, sai bin mutane da idanu kawai da yake yi fuskar nan a É—aure
Da ƙyar ya samu hanya ya faki idanun mutane ya tafi zuwa gida, don shi wannan gaishe gaishen ma haushi suke ba shi
Bai samu kowa a bukkar ta su ba,ya buÉ—e ya shiga,ya samu waje ya zauna,ya afka duniyar tashi ta tunani
Ba komai yake damunshi ba irin yadda yake so ya ji halin da abar son shi Hayat take ciki,ya san ta da raunin zuciya, Allah kaÉ—ai ya san iya adadin kukan da ta yi daga lokacin da aljani Shabbir ya mayar da ita zuwa Tayaar zuwa yanzu
Kuma wataƙila ma ace za'a aura mata wani,take zuciyar shi ta buga da ƙarfi, ɗan sarki za'a aura mata ko?
Shi an ƙi aura masa ne kasancewar shi bawa,take ya ja ajiyar zuciya mai nauyi,to gashi shima ya zama ɗan Sarkin,amma muddin ya rasa Hayat gaba ɗaya babu amfanin wannan ƙaddararriyar Sarautar ta suna wadda har abada ba zai manta yadda aka raba shi da iyayenshi da gatanshi akanta ba
Ji ya yi an girgiza shi da ƙarfi,ya ɗago firgigit yana kallon Munaya da take watsa masa wani mugun kallo,ya yi ƙasa da kanshi yana faɗin "Barka da dawowa Ummeey na"
"Menene dalilin da ya sa ka baro iyayenka ka dawo nan?"ta jefa masa tambayar
Lumshe idanunshi ya yi ya buÉ—e ya ce"ana ta hayaniya da sunan gaisuwa,ni kuma bana so"
"Ashe?to sai ka zauna da shirin cewa wannan hayaniyar za ka yi ta watan watarana,don dole dai watarana za ka zama sarkin kaizur"
Kai tsaye ya ce"ni fa bana son sarautar nan"
"Kuma Allah ya zaɓar maka ita tunda duk da wahalar da ka sha baka mutu ba,duk da nisan da ka yi ka dawo,kuma kafin nan na so na ɗauke ka Allah bai yi ba,don haka sarautar kaizur ta wajaba a gare ka
Ka ga ni ajiye wannan batun shirmen,ga abinci maza zo ka ci"babu musu ya matso,ta yi bismillah ta fara ba shi abincin a baki,tana yi tana kule da yadda sam bashi da walwala, kuma bashi da karsashi
"Sahal!"ta ambaci sunansa cikin taushin murya
ĆŠagowa ya yi yana kallonta ba tare da ya yi magana ba,cikin taushin murya ta cigaba da faÉ—in"Sahal menene yake janyo maka yawan tunani ne?
Meyasa ka kasa samun farin ciki duk da yadda kowa a masarautar nan yake son ya ga ya yi abin da kake so?
Me yasa kullum kana cikin damuwa ne?"
Girgiza kai ya yi a sanyaye,yana shirin magana Munaya ta ce"kar ka yi min ƙarya!!
Ka gaya min menene damuwarka? ko nima baka yarda da ni bane?"
Kwanciya ya yi a gefen kafaɗarta Kamar yadda ya saba a duk lokacin da ya ji zuciyarshi ta yi rauni,tabbas rashin Iyaye ciwo ne babba wanda ba ya taɓa warkewa muddin ba iyayen ne suka warkar da shi ba
Bai taɓa tsammanin zai nuna rauninsa ga wani a duniya ba,amma gashi indai yana tare da mahaifiyarshi mantawa yake yi a kwata kwata a rayuwarsa ya taɓa rayuwa a matsayin Kazuzi ibn Murad, wannan mayaƙin wanda yake iya tarwatsa runduna duk yawan ta shi kaɗai
Bai kai ga yin magana ba aka yi sallama aka shigo,a gigice Munaya ta ɗaga kai tana amsawa, shima Sahal gyara zaman shi ya yi yana rissinar da kai ƙasa
Yarima Jamal ya yi murmushi yana kallon sarki Mu'iz, kafin ya kai ga magana Munaya ta ce"barkanku da zuwa ya mai martaba!
Allah ya É—aukaki kaizur da sarkin ta mai adalci "
Sahal ya kalle ta cikin jin haushi,wai sarki mai adalci,ko a ina yake da adalcin oho?yarima Jamal ya ce"shiyasa kenan ya guje mu,ashe shagwaɓa shi kike yi"suka zauna akan dardumar da ke shimfiɗe, wadda akanta suke kwana,akanta suke dukkan wani uzuri nasu
Yarima Jamal ya sake kallon Munaya da ta rissinar da kai tana murmushi ya ce"wannan ɗan namu da kike gani shi kaɗai ya tunkari yaƙi ya ƙarar da runduna, shekarar shi shida a duniya ya kama maciji ya kashe shi,ya yi artabu da sarkin yaƙin da ya koyar da shi yaƙi ya yi nasara akansa,kuma shine kike sangarta mana shi? salon kawai ki saka shi ya manta yadda ake riƙe takobi?"
Murmushi suka yi sosai, Yarima Jamal ya dubi Sahal da kanshi yake ƙasa har yanzu,ya ce"biko muka zo yi ranka ya daɗe,daga yin Sallah sai muka neme ka muka rasa,gashi muna da magana da kai"
Jinjina kai ya yi,a hankali ya ce"zan iya ƙarasa cin abinci?"
Sarki Mu'iz ya ce"maza gama cin abincin ka,za mu jira ka Yarima "Sahal bai sake magana ba,ya saka hannunshi a cikin kwanon abincin ya cigaba da ci da kanshi
Bayan sun gama yarima Jamal ya dubi Munaya ya ce"Allah ya taimaki uwar Yarima,za mu je mu tattauna da shi,daga baya zai dawo in sha Allah "Munaya ta rissina tana faÉ—in"to a fito lafiya ranka ya daÉ—e "
Kai tsaye turakar Sarki Mu'iz suka tunkara,bayan sun shiga suka zauna akan lallausan kilishin da yake malale a É—akin, sarki Mu'iz ya dubi Sahal cikin kulawa ya ce"É—azu muna tare kawai sai muka neme ka muka rasa,ko wani laifin aka yi maka ne?"
Girgiza kai Sahal ya yi kanshi a ƙasa,a hankali ya ce "hayaniya ce ta yi yawa"
Yarima Jamal ya ce "dole ka koyi iyawa da hayaniya Sahal, don nan da wani lokaci kaine sarkin garin nan"kallonshi Sahal ya yi,a karo na farko ya ce"to baffa kai meyasa ba za ka yi sarautar ba?dole sai ni?"
Sarki Mu'iz ya kalle shi da sauri, tabbas ana samun nasara sosai akan Sahal,zuwa yanzu ya aminta da cewa sarki Mu'iz mahaifi ne a gare shi,amma sai yarima Jamal ya ce"ni masarautar mahaifiyata zan koma ne,ba don kai ba ma da tuni na koma,don Sarkin zai yi murabus ni na gaje shi ne
Ka kasa sakin jikinka da mu gaba É—aya "
Sahal ya yi shiru bai yi magana ba,sarki Mu'iz ya dube shi da kulawa ya ce "ka ce kana da maganar da zamu yi,wacce maganar ce?"
Sahal ya É—aga kai ya kalle shi,a hankali ya ce "so nake a canja dokar garin nan gaba É—aya!
Sannan kuma a samarwa mahaifiya ta tabbataccen cigaba a cikin garin nan"
Shiru suka yi suna kallon juna, kafin yarima Jamal ya ce"to wacce dokar kake so ayi amfani da ita?"
Kanshi tsaye ya ce"dokar musulunci nake so a yi amfani da ita,a daina yanke hukuncin kisa ba bisa ƙa'ida ba,kamar wasu mutane sun zama tsuntsaye
Sannan idan mahaifiya ta za ta cigaba da zama a garin nan to fa ya zama wajibi ka aure ta!!!idan ba ka aure ta ba zata bar garin nan zuwa wani wajen don ta kafa rayuwa mai kyau,ni kuma ba zan iya rayuwa a inda mahaifiya ta bata wajen ba,don haka dole zan bi ta,na zaɓi zama da ita sama da sarauta da duk wani ƙyale-ƙyale da nake gani a masarautar nan"
Shiru yarima Jamal ya yi yana kallon sarki Mu'iz don jin me zai ce,babu zato babu tsammani ya ce"na amince Sahal,bayan wannan akwai wani abu a gaba ko kuma shikenan "
Murmushi mai kyau ya bayyana a fuskar Sahal,ya ce"shikenan,na gode Abbey, Allah ya ƙara girma"
Gefen kumatunshi sarki Mu'iz ya shafa yana murmushi,ya ce"to da fatan zuwa yanzu za'a yafewa wannan uban mai son kanshi da yawa ko?"
Sahal ya yi ɗan murmushi kawai ba tare da ya yi magana ba, kan shi a ƙasa, Yarima Jamal ya ce"to mu je na mayar da kai wajen umminka ko?
Daga yau zuwa gobe in sha Allah mai martaba zai dawo da ku cikin gida,za ku daina zama a waccan bukkar "Sahal ya jinjina kai kanshi a ƙasa
Har bakin bukkarsu Yarima Jamal ya raka shi, cikin hikima ya cigaba da ba shi baki yana sake kwantar masa da hankali
Shi kam kai tsaye zai iya cewa ya fi ganin kirki da nagartar Jamal fiye da ta mahaifin shi ma, Kamar yadda ita ma Mahaifiyarsa Munaya ta gani,suka yi sallama,ya shiga bukkar ta su da sallama,shi kuma Jamal ya koma fada
Yanzu ma Munaya bata É—akin,ya samu waje ya kwanta ya lumshe idanunshi, tunanin Hayat da a yanzu ba ya barinshi ya sake kawo masa farmaki
A jikinsa yake ji cewa akwai wani abu mara daÉ—i da yake faruwa da Hayat É—inshi,ya rasa abin da yake yi masa daÉ—i
Kamata ya yi ya kasance cikin farin ciki da walwala yau É—in nan,amma a dalilin rashin Hayat da tunaninta da ya addabi rayuwarshi ya kasa samun sukuni a rayuwarsa kwata kwata
Yana wannan tunanin har bai san sanda Munaya ta dawo bukkar ba,ta yi sallama ta shigo,ta bi shi da kallo
Kallo ɗaya ta yi masa ta gane ba bacci yake yi ba,ta girgiza kai cike da takaicin wannan yawan tunanin da yake yi,ta ƙarasa kusa da shi ta kama kafaɗunshi ta girgiza,ya yi firgigit ya tashi zaune yana jan ajiyar zuciya yana kallonta
"Sannu da shigowa Ummeey!"ya faÉ—a yana rarraba idanu na rashin gaskiya
Shiru bata amsa ba,ya yi ƙasa da kanshi ganin irin kallon da take jefa masa, kafin ta ce"Sahal menene yake damunka ne? wannan yawan tunanin na menene haka?
Ko har yanzu akwai wani abu da bai yi maka ba a kaizur,ko kuma ka gaji da zama da mu ne?"
Girgiza kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba,kuma har yanzu kanshi a ƙasa, Munaya ta ce "buɗe baki za kayi ka yi min bayani,me ya same ka haka ne?"
"Ummeey mafarki nake yi mara daɗi a kanta,kuma.... kuma......"sai kuma ya kasa ƙarasawa
Ita Munaya mamaki ne yake kama ta a duk lokacin da ta kula da illar da soyayyar mace ta yiwa É—an nata,zuwa yanzu ta tabbatar a duniya mace ita ce raunin É—an nata,ita ce ta farko, wannan yarinyar da yake tsananin so kuma ita ce ta biyu
Cikin son ba shi ƙwarin gwiwa ta ce"na fahimce ka yaro na
Yanzu me kake so a yi?"
Shiru ya yi kawai yana sauke ajiyar zuciya a jere, ta janyo shi ta kwantar akan cinyarta,tana kallonshi da murmushi a kan fuskarta ta ce"ba ni labari É—ana,wacece ita? kuma wacce iriyar soyayya ce wannan mai tasiri haka tsakanin É—ana abin alfahari da wannan Ć´ar tawa?
Na ƙagu da jin wannan labarin "ta ƙarashe tana murmushi,tana gyara masa gashinshi da ya ɗan tarwatse
#Nusy_bee
***