Free chapter · Read without an account

Chapter 1

by Ummulkhairi Sani Panisau · ADNAN (The Artist)

ADNAN

2026

PG.1

Fitilun filin wasan na haskawa cike da salo mai ɗaukar hankali, kamar rana na son saukowa ƙasa.Ta ko ina mutane ne suna ihu,suna kiran suna ɗaya tilo. "Adnan! Adnan! Adnan!" Amma Adnan Artist yana can zaune a bayan fage ,ya jingina da kujera yana zukar sigari da hannun sa na hagu. Wayarsa na daga ɓarin daman sa. Fuskar sa babu walwala ko alamar farinciki ko motsin kirki ya kasa yi kamar ma bai san don shi mutanen nan suke tsaye ba suke kuma ihu. Manager ɗin sa,Sahib ya shigo ciki da sauri gumi na tsautsago masa a goshi.
"Don Allah Adnan," ya faɗa cikin rawar murya. "Adnan! Mutane sun cika filin wasa. An biya ka kuɗi masu yawa don wannan show ɗin. In ka yi show ɗin nan za ka kafa tarihi..."
Adnan ya ɗaga kai a hankali,ya kalli Sashin kamar yana kallon wani kwaro. "Shin ni kaɗai ne ke yin waƙa a duniya?" Ya faɗa cike da raini. Sannan ya ci gaba da magana "Ko ka manta da wa kake magana?"
Sahib ya haɗiyi yawu sannan yace "Ba haka bane Adnan amma..."
Adnan ya katse shi. Ya miƙe tsaye,tsayin sa ya cika ɗakin,Warin sigari ya guraye ɗakin da jikinsa. "Na ce ba zan fita ba." Ya faɗa da ƙarfi.
"Idan randa bata yi min daɗi ba ,duniya ma ba zata yi min daɗi ba."
Wani daga cikin mai ba shi tsaro ya shigo da sauri ba tare da ya nemi izini ba yace "Yallaɓai,magoya baya....."
"Yi min shiru ,ka rufe min bakin ka!" Adnan ya daka masa tsawa ,ya ɗauki kwalbar lemo ya maka da garu ya tarwatse. Shiru ya mamaye ɗakin. 
Sahib ya gane cewa ɗaukaka ta ɗaga shi sama ,amma ta cire masa tausayi. Ya leƙa ya ga yadda masoya suka taru suke ihun sunan Adnan the fire suna jiran ya fito wasu har sun soma zagi sun ƙufula. Ya sauke labulen ɗakin ya koma ya zauna ya yi shiru kawai yana ganin ikon Allah.
*

Ta ƙofar baya Adnan Blaze ya fita. Sanye da baƙin taɓarau. Kamar ba shi ake jira ba sam babu wata damuwa a tare da shi.
"Adnan!" Wata murya ta kira shi da ihu. Ya dakata ya juya don ganin wanda ke da wannan zarar yi masa irin wannan kiran na isa.
Wani saurayi ya gani kusan shekarun sa ashirin da biyu riƙe da takarar shaidar shiga cikin show ɗin a hannunsa. Idanuwansa sun sauya kala sun yi jajir saboda kuka da fushi.
"Na sayar da wayata." Saurayin ya faɗa cike da murya mai sanyi da karaya. "Don na gan ka kawai na sayar da wayar,me yasa zaka gudu ka bar mu? Me ya sa ka fasa show ɗin?"
Adnan ya kalle shi sannan yace "Ka sayar da wayar ka?"
Ya gyaɗa masa kai. Adnan kuwa ya yi murmushin gefen baki sannan yace "Wannan matsalar ka ce, ba tawa ba."
"Kai ne fa Adnan the Blaze Wanda muke kauna muke kuma son ka muke goyon bayan ka amma kake wulaƙanta mu?"
Adnan ya zare gilashin sa yace "ku daina kirana anyhow, ni ba limamin ku bane. Ba na rayuwa don na faranta muku rai."
Saurayin kuwa ga girgiza kan sa yace "Idan haka ne me yasa muke biyan kuɗi? Me ya sa muke tsayawa komai rana ,komai dare?"
Kalmar me yasa ta taɓa zuciyar Adnan amma sai ya dake ba tare da ya nuna ba sai ya ji ransa ya kuma ɓaci sannan ya matsa daf kusa da saurayin fuska na kallon fuska yace "Kai dan ne, ka da ka mata inda kake tsaye."
Saurayin ya ɗaga murya yace "Idan babu mu tauraro ba komai bane!" Cikin fushi Adnan ya sa hannayen sa biyu ya hankaɗa saurayin da ƙarfi. Saurayin ya yi taga-taga ya yi baya ya faɗa ƙasa ya kife.
Sahib ya yi sauri ya kamo Adnan da ke ƙoƙarin kai wa saurayin duka.
"Sake ni Sahib,sake ni nace waye shi da zai yi min magana yadda yake so? " 
Saurayin dai ya zuba masa ido yana ƙasa yana kallon ikon Allah. Idanuwansa cike da rauni fiye da ciwo. A hankali yace mai "Na fi son mawaki, ba tauraro mara zuciya ba." 
Wannan kalmar ta tsayawa Adnan a rai matuka ta kuma tunzira shi kamar ƙusa ya dasa masa haka ya ji a tsakar kan sa. Sai ya zabi ya juya da baya kawai ya shige cikin motar sa ya rufe aka tashi motar suka bar wurin .
Kafin Asuba Adnan ya isa gida.Motar sa ta tsaya ba tare da hanyaniya ba, amma zuciyar sa cike take da ihu fiye da ƙarar motar. Yana shiga cikin falon ,Mami ta miƙe tsaye da sauri fuskarta cike da damuwa tace "Lafiya kuwa?" Ta tambaye shi cike da tausayi.
Ya kalle ta zuciyar sa cike da fushi da gajiya amma bai ce mata komai ba. Ta sa hannu ta taɓa kafaɗar sa ya sa hannunsa ya sauke hannun ta daga jikin sa ya raɓa ta gefe ya shige ya bar ta a wurin a hankali yace "Ba komai."
Be ko ƙara kallon ta ba ya hau sama ya kulle ƙofar sa ji ka ke gam ya kulle ƙofar.
Mami ta tsaya cak a falon a tsaye zuciyar ta na bugawa da sauri. Ta san dan ta.....ta san halin da kuma ta sani wannan shirin ba alheri bane ba. 

Wayar Adnan Blaze ta soma ringing tun kafin ya farka wani kiran ya sake shigowa. Kan sa na juyawa,bakinsa ya bushe,idanuwansa sun yi ja kamar wuta. Ya sa hannu ya ɗaga wayar da kyar ya saka ta a handsfree.
"Ka ga abinda yake faruwa Blaze?" Ya ji muryar Sahib ba tare da gaisuwa ba. Adnan ya lumshe idanuwansa sannan yace da shi "Idan maganar ka game da show ne ,ka rufe bakin ka." 
"Ba a kan show bane." Sahib ya faɗa a hanzarce. "Faɗan da ka yi da fan ɗin nan ne,an samu wani ya dau vedio."
Adnan ya yi shiru na tsawon lokaci,sannan ya yi dariya amma ba ta annashuwa ko jindaɗi ba.
"Wannan sabon abu ne a wurin ka Sahib? Kullum fa ana ɗaukar Adnan Blaze."
"Wannan karon ba haka bane ,vedion ya kai ko'ina. Instagram,TikTok, facebook mutane suna ta rabuwa gida biyu."
Adnan ya gyara kwanciyar sa ya yi tsaki sannan yace "Rabuwa? To sai me don sun rabu suyi ta rabuwa mana wannan ai rayuwar su ce ba tawa ba."
Sahib ya sauke numfashi sannan yace "Wasu sponsors suna tambayar wani show a Abuja." 
"Idan suna jin tsoro tun yanzu su bar ni." Ya faɗa haɗe da kashe wayar.Ya mike tsaye,ya isa gaban mudubi. Fuskar da ya gani ba ta kama da ta tauraron da ake gani a telebijin. Idanu ne wannan masu gajiya. Fuska mai ɓoye da abubuwa,zuciya mai cike da hanyaniya."

Tsaki ya buga ya kuma janyo wata drower ya zaro kwallin sigari ya kunna ya kai mata zuƙa ya koma bakin tagar ɗakin sa ya tsaya.
Runtse idanuwansa ya yi a hankali ya tuna da idanuwan da ya jima bai manta hasken su ba, idanuwan sun yi matuƙar ɗauke masa hankali kuma ya kasa manta su indai zai kulle ido sai ya hange su a cikin na sa. A wani show da ya yi ya ga wannan idanuwan wanda ba zai iya shaidar fuskar mai su ba. Ya buɗe ido a hankali ya saki wani tsakin a fusace ya shige cikin banɗaki. Komai da zafi yake yin sa.

Yana fitowa daga cikin banɗakin ya saka wasu ƙananun kaya ,rigar armless ce sai wando ya wuce guiwa da kaɗan. Ya sa wani band fari kamar wani mace ya shafa man leɓɓe a bakinsa sannan ya ɗaura wani agogo ya saka wani band a hannu wanda aka rubuta "Blaze" a jiki.
Ya fesa turare ɗakin ya ɗauki ƙamshi sosai ya ɗau wayar sa ya fito.

Yana saukowa ya hangi Mami da ƙanin sa da yayan shi a zaune a kan kujera suna kallonwl wayoyin su. 
Tuni ya ɓata rai ya isa gaban Mami a tsaye yace "Ina Kwana Mami." Idan baka kasa kunnen ka ba ma ba zaka san ma wai magana ya yi ba. 
Yayan shi Shamsudeen yace "Adnan...."
Da sauri ya katse shi "Please in maganar wancan vedio ɗin ne don Allah ku bar mu bana son jin komai."
Shamsudeen yace "Haba Adnan, ka dinga sassautawa kan ka mana. Wacce kalar rayuwa ce wanann ka ɗorawa kan ka ? Ka kalle ka , ka tuna fa ba haka kake ba a baya.."
Hannunsa ya ɗaga masa yace "Yaya Shamsu, don Allah ka kyale ni babu ruwnan ka da rayuwata, ka kyale ni,wai kashe ni ake so ayi ne? Ku kyale ni na ji da abinda nake ji mana haba don Allah."
Shamsudeen zai kuma magana Mami ta gyaɗa masa kai ta masa alama da ya kyale shi.
"Zo ka zauna ka ci abinci ko ruwan tea ne ka sha ka ji?"
Da sauri ya ce mata "A'a bana ci na ƙoshi. Fita zan yi sai na dawo."
"Yaya don Allah kar ka fita yau." Ƙanin sa Ishak ya faɗa da sauri 
Bai juya ba kuma bai fita ba yace "Dalili?"
"Mutane a fusace suke da kai bana son wani abu ya same ka."
Sai da ya yi wani kalar Murmushi kafin yace "Basu isa ba." Ya sa kai ya yi gaba.
Mami dai ta kasa cewa komai saboda lamarin Adnan ya soma bata tsoro ba haka yake ba da, miskilancin sa da shiru-shirun sa bai kai haka ba totally bayan wata tafiya da ya yi shekaru biyar baya komai ya sauya mai ta yi tambayar duniya ya ce mata babu komai alhalin ta san da akawai abinda yake damun sa. Kamar an sa mai hannu komai ya daina yi masa daɗi, ya daina zama a cikinsu ya daina walwala.
Shamsudeen yace "Mami don Allah ki tashi tsaye a kan yaron nan duk na kasa gane masa bana jindaɗin ganin sa a haka, ko duk samun ɗaukakar ne?"
"Ko ɗaya Deen, ba haka bane dole akwai abinda ya same shi wanda mu bamu sani ba."
"To mene ne wannan?"
"Allah ma sani. Ina son ku dinga haƙuri da shi, ku ƙara haƙuri da shi ya fi ku rauni , wata rana sai labari."
Deen ya sauke ajiyar zuciya yace "In sha Allah Mami." Ya kalli ɗan'uwan na sa yace "Ta so kai na mai da kai in da ka fi wayo."
Ya tashi tsaye yace da Mamin "Sai mun dawo."
"Allah Ya bada sa'a."
Suka amsa a tare "Amin."
Mami ta girgiza kan ta cike da tunanin abinda ya sauya Adnan a Sa'i ɗaya.

*
Duk kiran da Sahin ke yi masa bai ɗauki wayar ba don ba shi da ra'ayin amsa kiran kowa ma. Ya dinga jera tsaki daga ƙarshe ya kunna waƙa a cikin motar yana bi yana girgiza kai. Kwalin sigari ya zaro ya ciri guda ya sa a baki ya kunna lighter ya saka a bakinsa ya kai mata zuƙa.
Ya sauke gilashin motar a hankali cikin bazata ya ji saukar ruwa a kan fuskar sa. Kafin ya ɗago kai ya san me yake faruwa ya ga gilmawar adaidaita sahu ta wuce fuuuu da gudu sai gyale ya hango na reto cikin sakan guda ta leƙo da kan ta tana kallon motar kuma sai ta maida kan ta da baya ta koma. 
Ya taka burkin motar cikin fushi da ɓacin rai domin kuwa ta gama dizga shi idan be yi batan lissafi ba wannan ruwan da aka zubo masa a fuska na baki ne tuno hakan da ya yi kuwa ya saka ya ji wani irin ɓacin rai ya ziyarce shi ya sa hannu ya ɓalle murfin motar ya sa hannu ya kama ƙugunsa yana huci sai dai ko adaidaita sahun ya daina hanga. Tsaki ya kuma yi ya sa hannu ya naushi iska har hannun sa ya daki kan bonnet ɗin motar. 
A lokacin yadda zuciyarsa ke tafasa da zai ga yarinyar sai tayi kuka da idanuwan ta,har shi za a zubawa ruwa a fuska a tafi ba tare da an bashi haƙuri ba babban ɓacin ran sa bai ga fuskar wace ce ba. 
Wayarsa da ke ta ƙuwa ya sa hannu ya ɗaga a fusace.
"Wai wanne mayen ne yake addaba ta da kira haka haba bashi na ci ban biya bane ko yaya?"
"Mayen uban ka ne yake addabar ka Adnan."
Sai a lokacin ya sassauta ya koma cikin nutsuwarsa yace "Barka da rana Abba ,ka yi min afuwa ban san kai bane."
"Yaya za ayi ka sani kullum baka cikin hayyacin ka? Ka zama wani banza ka zama sususu sunan da ka sha wuya wurin gina shi ka fara rusa shi da hannun ka da kan ka me yake damun ka ne Adnan? Me ya shiga kan ka nace?"
Ya sa haƙoransa na gaba ya taune leɓɓensa na ƙasa yana ƙoƙarin ganin ya yi controlling ɗin zuciyarsa saboda yadda sheɗan yake ingiza shi kan ya kashe wayar kowa ma ya huta.
Ta cikin wayar ya ji tsawar Abban. "Are You stupid ina magana ka yi min shiru?"
Adnan ya kulle idanuwansa da sauri ya ce "Am sorry Abba...ba.."
"Ka yi min shiru shashasha ka na son ka ɓata min suna da ƙima da martaba ta ba zan ɗauki wannan halin ba tun wuri ka dawo cikin hayyacin ka."
A hankali yace "Am sorry."
"Ba sorryn ka nake buƙata ba so nake yi ka zo gida ka same ni na lura komawar ka hannun mahaifiyar ka ya sake sawa ka zama wani gaula in ita bata damu da martabar ta ba ni na damu da tawa martabar saboda haka ka zo nan da awa ɗaya ina son na gan ka iskancin ka ya ishe ni."
Ba don ya so ba ya amsa ta "To zan zo." Abban ya katse wayar ya bi wayar hannunsa da kallo yana jin kamar ya fasa wayar ko ƙi zuwa kiran Baban ba sam duk zafin kansa baya ƙin bin umarnin Abba. Motar ya koma ya shiga ya mata key ɗaya ya ɗauki hanya.
*

Sahib zaune kan kujerar sa a cikin ainihin office ɗin su. A hankali yake nazartar sabbin clients ɗin da suka zo suna son Blaze ya zo ya yi musu show na awa ɗaya a bikin wani ɗan hamshaƙi. 
Sahib ya san yanzu fa kan Artist rawa yake yi Iskanci kala-kala yake bugawa sai sun gama amsar kudin mutane sai an zo ya ce ya fasa wasan ma kwata-kwata. Ya yanke shawarar zai fara tuntuɓar sa tukunna kafin ya ce musu komai haka ya saka ya gayra zaman sa sannan yace "Zan neme ku yanzu Artist baya nan bana son na amshi contract ba tare da izinin sa ba."
Client ɗin yace "Haka ne na fahimce ka zamu jira bayanin ku amma don Allah ka sa ya yarda yar yallabai ta faɗa da babbar murya idan har Blaze bai zo bikinta ya mata waƙa ba tabbas sai ta fasa auren."
Sahib ya ƙarawa idanuwansa girma cike da mamaki kuma da dariya. A ransa yace "Wacce wawiya ce take son ta lalata rayuwarta saboda Artist? Mutumin da shi kan sa wahala yake sha da kan sa bare kuma har ya wani damu da fasa auren ta. Lallai akwai ƙura abu guda ne zai faru ko dai Artist mutuncin su motsa ya je show ɗin ko kuma lallai a fasa auren amaryar nan."
Amma a fili sai ya miƙa musu hannu yace "Zan neme ku yadda aka yi zaku ji daga gare ni,na gode."
Suka fita daga office ɗin.
Wayar sa ya zaro ya duba tsarin ayyukan su amma bai ga alamun yau Artist zai shigo ofishin ba haka ya saka ya kulle ya fita shi ma.
Can gida kuwa a haukace ya faka motar. Hatta ma'aikatan gidan sai da suka shiga cikin taitayinsu suka nutsu. Kowa gaishe shi yake yi amma ina babu wanda ya samu zarafin amsawa gaisuwar sa kawai kai yake dannawa cikin gidan.

Babban falo ya shiga mai cike da kayan alatu. Yana shiga ya ci karo da family picture ɗin su baya mantawa da yadda aka yi ya shiga hoton. Sai da allurar Abba ta tashi ya yi masa fata-fata tukunna ya shiga hatta gashin kan sa sai da ya saka shi ya sake shi sannan ya saka manyan kaya har da hula sannan ya shiga hoton.
Matar baban shi da suke kira da Ammi ya kalla ya tsane ta makirar mata ce wadda ta tarwatsa musu rayuwa su kam. Amma Abba ba ya ganin munanan hallayen ta yaranta huɗu mata uku sai namiji ɗaya.
Da a gidan yake amma shekara biyu baya ya koma wurin Mami mahaifiyar shi da zama bayan wani dogon lokaci duk da Abban na shi ba ya son hakan amma haka ya koma saboda wani dalili na shi.

Tun kafin ya zauna a kan kujera ƙanwar shi ta fito daga kitchen da kofi a hannun ta tana cin Sandwich. Tana ganin shi tace "Yaya Artist, yaushe ka zo?"
Sai da ya manna mata harara kafin yace "Ban sani ba."
Taɓe bakin ta tayi ita ka sannan ta juya ta haura saman steps tana shan tea ɗin ta a haka.
Wayarsa ya zaro daga cikin aljihunsa ya kira layin Abba. Sai da ta yi ringing sau biyu sannan ya ɗauki wayar.
"Abba na zo." Ya faɗa a taƙaice.
"Gidan baƙon ka ne? Ba ka san inda zaka same ni ba ne?"
"Na sani." Ya faɗa a ƙasan maƙoshi.
Abba ya kashe wayar. Ya sauke wani nauyayyen ajiyar zuciya sannan ya sa hannunsa ya kama ƙugunsa ya kalli saman benen sau da ya ɗauki kusan mintuna biyu kafin ya fesar da iska daga bakin sa ya hau saman.
Yana shiga cikin falon turus ya yi. Abun da ya shuɗe ne ya dawo masa sabo fil. Ya hango lokacin da Mami take tsaye a tsakiyar falon,jakarta a hannun ta, idanuwanta sun yi ja saboda kuka. Da kalmomin da ta faɗa a ƙarshe "Ba zan iya rayuwa a gidan da ba ni da daraja ba," ta faɗa cikin rawar murya. Abban na gefe shi da Ammi suna kallon Mami. A kan idon sa Mami ta bar gidan ita da yayan shi Shamsudeen sai shi da Abban ya hana a tafi da shi ya riƙe shi gam...."
Ya buɗe idanuwansa da sauri saboda yadda yake da ƙiyayyar matar mahaifinsa da yake da shi a ransa.
Abba yace "Shigo ciki ka ji."
A hankali ya zare takalmin sa ya shiga ciki a ƙasan kujera ya zauna ya sunkuyar da kan sa.
Abba yace "Na yi lallacewar da zaka zo gaba na da wannan askin Adnan?"
Adnan ya manta shaf ya sa hannu ya shafa kan sa ya ɗan miƙe kaɗan ya zaro wata rigar sanyi daga cikin aljihunsa ya saka hular a kan sa.
Abba kuwa bai ɓoye fushinsa ba. Ya soma magana cike da fushi da ɗaga murya. Kalaman Abban na sauka da nauyi kamar hukunci.
"Tun da ka shahara, ka daina mutunta aiki,kana ƙoƙarin ɓata sunan ka da nawa ,kana wulaƙanta duk wanda ya taimaka maka ka kai wannan matakin wato masoyan ka magoya bayan ka."
Shiru ya lulluɓe falon. Shiru mai nauyi ya ratsa falon. Zuciyar Artist tafasa take yi kawai tsakanin laifi, fushi da kuma ƙiyayyar da bai san inda zai sauke ta ba.
Zai yi magana Abba yace masa "Kar ka ce komai! Shekaru nawa nake biye da kai? Wa ya tsaya da kai tun kana babu kowa? Yanzu da sunan ka ya cika hari , sai aka ce ka fara raina komai da kowa?"
Ammi ta miƙe tsaye ,ta matsa kusa da Artist cike da kissa tace " Ba don baya son ka bane yaka maka faɗa ba, yana son ka yana kishin ka baya son ya ga ana taɓa martabar ka.Wannan shaharar tana cin ka a hankali ka duba mana ka gani waye kai a da a yanzu kuma ya ka koma? Ka sauya ka canja fa."
Kalaman ta duka saka zuciyar sa ta girgiza kalmar ka canja ta buɗe masa wata ƙofa da ya rufe a wasu shekaru da suka wuce. Bai san lokacin da ya ce "Kin ce na canja ko?" Ta girgiza masa kai.
A cikin maganar sa akwai zafi da sanyi a lokaci guda.
"Kin manta lokacin da Mami za ta bar gidan nan? Kin hana ta tafiya ne? Ba kina kallo ta tafi ba? Tun daga ranar komai ya mutu a duniya ta." Ya faɗa da zafi-zafi.
Abba ya daki teburin dake falon na tsakiya ya ce masa "Ka isa! Kada ka ɗora laifin ka a kan wani. Matsalar ka ita ce girman kai da wulaƙanci."
Artist ya yi murmushi mara daɗi sannan yace "Eh Abba....girman kai. Amma ku ne kuka ɗora ni a hanya kuka koya min yadda ake tsayawa cikin kaɗaici."
Abba ya buɗe baki zai yi magana Ammi ta riga shi.
"Ka kyale shi Abba. Gaskiya ya faɗa nima ina da kwamasho da na bari ta tafi ban tsayar da ita ba...."
Abba ya ɗaga mata hannu sannan yace "Ni nace ta tafi? Ni na hana ta zama?"
Adnan ya miƙe tsaye ya juya ya fice da sauri. Abba ya bi bayansa da kallo kamar yana ƙoƙarin rasa shi a karo na biyu."
A fusace ya fice daga gidan kamar wutar lantarki. Bai tsaya a ko ina ba sai a club. Wurin cike yake da hayaniya. Waƙa mai ƙarfi na dukan kunnuwan shi,fitilu na walƙiya kamar yadda zuciyar sa ke karyewa kashi-kashi. Ya zauna a ɓarin mashaya ,ya nunawa bartender wani lemo ya kawo mai. Ya sha cup biyu kafin ya ji sanyi ba wai sauƙin raɗaɗin da ke zuciyarsa ne ya ragu ba kuma ba buguwa ya yi ba saboda duk iskancin sa baya shan giya bar shi dai da zuƙe-zuƙe.
Daga baya wani yace "Kai kun ga Artist Blaze." 
Sai ɗayan yace "wanda ake biyan shi yake ƙin yin show?" Ya faɗa da isgili ya saka dariya.
Dama mai neman kuka ne sai kuwa ya juya yace "kar ka kuma ce min haka."
Suka kalli juna suka ce "In muka ƙi fa?"
Hannunsa na rawa ya ture gilashin kofin lemon da ya sha ya faɗi a ƙasa ya tarwatse. Mutane suka tsaya suna kallon su a fusace yace "Ka san ni waye?" 
"Na sani wanda ya manta inda ya fito mana."
Ai kuwa Artist ya sa hannu ya mazga mai mari a ƙuncin sa tuni faɗa ya ƙaure a tsakanin su aka rasa mai rabawa suka mai taran dangi amma yana maida martani wani ya soma yin vedio. Sahib da ya shigo ya sa hannu ya zare wayar daga hannunsa ya maka ta da ƙasa. Security ɗin Artist ya sa hannu ya damƙi wuyan yaron ya saka ƙara.
Sahib ya yi sauri ya shiga tsakani ya kuma ɗaukar wata kwalbar ya saki a ƙasa ta bada sautin tushhh ta fashe a ƙasa.
Sannan suka dakata.
Sahib ya ce "Ka nutsu mana Artist. Meye haka ne kake faɗa da waɗanan cikon becin, ko ka manta waye kai ne?"
Artist yace "Cika ni Sahib ko ina naje sai rikici ya biyo ni?" 
Suka fita waje wutar da ke cin sa a rai tana ƙara ruruwa kamar za ta ƙona shi.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.