Free chapter · Read without an account

61

by ZAHRA B MRS · Bayan Murmushi

Garden din gidan ya gauraye da sautin numfashi da fargaba. Zainab (Zee) ta tsaya turus, fuskarta ta koma kalar gawayi yayin da kiran sunanta da su Precious suka yi ya riga ya ratsa sanyin daren. Hanadi kuwa, jikinta har rawa yake yi, muryarta tana rawa ta fara magana, "Precious... Farhana... don Allah ku saurare ni, ba abin da kuke tunani ba ne."

Fateeha ba ta ba ta damar karasawa ba, ta kamo hannun Zainab da karfi. "Ba abin da muke tunani ba? Ashe keda hanadi kuke kullawa Farhana wannan zagon kasar? Zainab ke da muke gani a matsayin Aminiyar farhana ?"

Zainab ta yi saurin masking din fargabarta, ta fizge hannunta tare da yatsina fuska. "Me kuke kokarin yi? Sakar mun hannu 

"Wallahi baki isa ba!" Precious ta daka mata tsawa, ta kamo daya hannun nata. Suka fara jan Zainab zuwa cikin premises din gidan, kowa ransa a bace. Hanadi tana biye da su a baya, tana kuka tana rokonsu: "Don Allah ku tsaya mu fahimci juna, kar papa ya jiyo dan Allah

Farhana kam tana tsaye ne tamkar wadda aka dasa, idanunta sun bushe, zuciyarta tana mata zafi. Ta kasa ko kwakkwaran motsi har suka shiga babban falon gidan (Main Parlour).

A Main Parlour

Hayaniyar su Precious ta sa gidan ya fara farkawa. Sameena, dake dakin kusa da falon, ta fito da sauri ganin yadda ake janyo Zainab kamar barauniya. Ganin halin da Farhana take ciki, Sameena ba ta tsaya wata-wata ba, ta juya da gudu ta hau stairs din benen gidan tana kiran sunan AK da karfi.

"Yaya AK! Yaya AK! Ka fito yanzu-yanzu!"ana fada a falo 

A cikin falon kuwa, Precious ta tura Zainab tsakiyar carpet. "Yau asirinku ya tonu." 

Zainab ta gyara tsayuwar ta, maimakon ta nuna nadama, sai ta dake. "Farhana, kin taba tunanin dalilin da ya sa baki taba gani na da saurayi ba? You don’t care to know ko?You are so heartless! Kin hadu da Jafar, kin hadu da Farooq, sannan yanzu kin auri dan Gwamna. Meyasa da kuka rabu da Farooq baki hada ni da shi ba? A yadda yake sonki zai yarda idan kika ce ya aure ni .kiyi har samari uku ba na yarwa amma Sabida baki ciki baki taba damuwa da ni ya nake ji ba .

Farhana ta sandare a wurin, numfashinta yana kokarin daukewa. "Zainab... kina nufin duk wannan kiyayyar a kaina Sabida wannan maganar ne ?"Kina nufin duk sirrina kin fadawa kishiyata?

"Yes of course! Har ma da sirrin da baki san na sani ba, na fadawa kishiyarki. Kina tunanin ina bakin ciki ne da kika shiga depression a USA? A'a, ni na rinka kira ina zuga Diddi Sabida su sa Ak ya sake ki !"

Hanadi ta rushe da kuka tana girgiza kai, "Zainab kiyi shiru!"

Dan Allah .

A dai-dai wannan lokacin, AK ya bayyana a saman benen, sanye da rigar barci, fuskarsa dauke da tsananin mamaki da bacin rai. Ya ji kusan kashi tamanin na kalaman Zainab. Ya fara saukowa stairs din daya bayan daya, takunsa yana bada sauti dake nuna karshen wasan.

Gaba dayansu suka yi shiru suna kallonsa. Farhana ta numfasa, sannan, ta kalli Zainab da wani irin kallo na takaici.

TAS!

Wani irin mari ne Farhana ta tsinakawa Zainab wanda ya sa ta kusan faduwa kasa. "Wannan na cin amanar da kika yi min ne," Farhana ta fada muryarta na rawa. Sannan ta juya ta kalli AK dake saukowa. "AK, ga ex Aminiyata da matar Ka  kaji komai da kunnenka."

AK ya karaso tsakiyar falon, ya tsaya a gaban Zainab da Hanadi. Wani irin hayakin bacin rai suka turnuke shi.


Bayan marin da Farhana ta tsinakawa Zainab, falon ya yi tsit na wasu daƙiƙoƙi. Zainab ba ta nuna alamar nadama ba; maimakon haka, sai ma wani murmushin cin mutunci da ta ci gaba da yi, tana goge gefen bakinta.

AK ya ƙaraso gaban Zainab, jijiyoyin wuyansa sun tashi. "Zainab, baki da masaniyar abin da kika yi wa kanki ba. Yanzu zan kira jami'an tsaro a fitar da ke daga gidan nan, kuma zan tabbatar kin yaba wa kida."

Farhana tace , "A'a AK! Barta kawai. Ta riga ta gama da kanta tun sanda ta zaɓi cin amana. Na barta da Allah, shi ne zai bi min haƙƙina."

Hanadi dake gefe tana kuka, ta fara ƙoƙarin kare kanta. "Darling don Allah ka tsaya kaji bayani na. Zainab ce ta rinka zuga ni, ta na gaya min karya a kan Farhana..."

AK bai ko kalli inda Hanadi take ba, tamkar ba ta wanzu a wurin ba. Ya matso kusa da Farhana, ya sa hannunsa ya rungume ta sosae a ƙirjinsa. Ya san yadda Farhana take son Zainab; ya san yadda ta yarda da ita fiye da kowa Rungumar ba ta lallashi ba ce kawai, runguma ce ta jin zafi da raɗaɗin da yake ji a madadin matarsa.


AK ya ɗago kai, idanunsa sun yi jajur. Ya kalli Sameena da su Precious. "Ku taimaka ku kwashe Zainab zuwa BQ Kafin safiya 

Haka aka tisa ƙeyar Zainab, wadda ko a sannan ba ta daina hararar Farhana ba. AK ya kaita har ƙofar (B.Q), ya tabbatar ta shiga ɗakin, sannan ya rufe ƙofar ta ciki da maƙulli, ya sa aka sanya jami'an tsaron gidan a bakin ƙofar.

"Magana ba ta ƙare ba," AK ya faɗa yana huci. "Dole ne gobe da safe in kira su Yaya safiyya su zo su ga irin abin da  hanadi ta rinka shiryawa a gidan nan."

Hanadi kuwa, tana ganin irin fushin da AK yayi, ta san cewa lallashi ba zai yi aiki ba. Ta koma gefe tana karkarwa saboda tsoron matakin da zai ɗauka a kanta, musamman yadda ya yi mata shiru bai ce mata uffan ba.


AK ya dawo falon, ya ga su Fateeha sun zagaye Farhana. Ya matso kusa da ita cikin sanyin murya. "Wifey, mu shiga ciki ko? Ina son mu kwana tare yau, ba zan iya barinki ke kaɗai a wannan yanayin ba."

Farhana ta zare jikinta daga nasa a hankali, idanunta suna kallon wani wuri daban. "A'a AK. Ina buƙatar in kasance ni kaɗai (I need to be alone). Zuciyata tana bukatar sarari."

AK ya so yin gardama, amma ganin yadda fuskarta ta koma tamkar ƙanƙara, sai ya janye. Ya bi ta da kallo tana wucewa zuwa ɗakinta, su Fateeha da Precious na biye da ita a baya, zukatansu a sanyaye.


Suna shiga daki, Farhana ta zauna a gefen gado. Ta duba wayarta, sannan ta kalli su Precious.

"Wani abu ne yake damuna," Farhana ta faɗa a hankali. "Me kuke tunani? Shin Zainab da Nusaiba ne suka shirya komai tun farko? Ko kuwa Zainab ce ta haɗa komai da kanta ta rinka amfani da sunan nusaiba ?"

Precious ta numfasa, "Farhana, komai zai fito fili. Amma a yadda naga Zainab Yau, Akwai  maganganu sosai a bakin ta

Farhana ta gyara kwanciyarta, ta lumshe ido tana jin yadda duniyar take juya mata. Gobe akwai babban zama da su Yaya Ramla, kuma tana sa ran nan ne sauran ƙulle-ƙullen za su warware.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.