Free chapter · Read without an account
62
62
Daren ranar ya kasance daya daga cikin mafi nauyi a rayuwar Farhana. Duk kiran da su Fateeha suka yi wa Nusaiba, ba ta daga ba, sannan lambar wayar da aka tura wa Farhana sakon dazu da ita ma ba a daga ba. Shirun ya kara sanya shakku a zukatan su; shin su duka ne suka hada baki, ko kuwa kowa zaman Kansa yake ?
Farhana ba ta runtsa ba, idanunta sun yi luhu-luhu. Ko ta kan tagwayen (twins) ba ta bi ba; Ruth da Sameena ne suka rinka dawainiya da su a Khalil da Sultana a daren.Abun mamaki Yau Ak shi ya tashe su sallar asubah ,Alamun Shima beyi baccin ba ,mutumin da tunda farhana take bata taba ganin yayi Subhi a masjid ba
Tun kiran salla na farko, AK ya shigo dakin Farhana domin ya duba lafiyarta, domin ya san halinta sarai; idan abu ya taba zuciyarta, yakan iya sanya mata zazzabi. Ya same ta zaune a gefen gado, ta zuba wa wuri daya ido.
Inda ya ce mata ya tafi masjid
Bayan gari yayi Haske Ak ya Kara shigowa dakin
"Wifey, mutane sun hallara a falo AK ya fada cikin sanyin murya.
Farhana ba ta ce uffan ba, ta zumbula katon hijab dinta har kasa, ta fito zuwa falon inda ta fara jiyo muryoyin su Yaya Safiyya da Yaya Ramla.
A babban falon, an hallara kowa da kowa. Su Fateeha da Precious suna gefe guda, su Yaya Ramla kuma suna zaune fuskokinsu a murtuke. A tsakiyar falon, Zainab (Zee) take zaune a kasa; fuskarta ta nuna cewa ba ta hayyacinta take ba gashinta ya hargitse, idanunta kuma ba su da natsuwa. Hanadi na gefe daya, kanta a kasa, tana faman murza yatsun hannunta.
AK ya tsaya a tsakiyar falon, ya fara ba su Yaya Ramla takaitaccen bayanin (summary) abubuwan da suka faru a daren jiya; tun daga garden har zuwa kalaman da Zainab ta furta da bakinta.
"Na kira ku ne domin ku ji da kunnenku irin makircin da aka rinka kullawa a gidan nan," AK ya fada muryarsa cike da fushi. "Zainab ta amsa laifinta, kuma ta tabbatar da cewa Hanadi na da masaniya."
Su Yaya Ramla suka kalli juna. Duk da cewa maganar ta girgiza su, kuma sun san Hanadi ba ta kyauta ba, amma girman kai ya hana su nuna hakan a gaban Farhana.
"Haba Abdulkadir," Yaya Ramla ta fara magana tana yatsina fuska. "Yanzu duk saboda maganar kawaye zaka tada mana hankali haka? Ai dama can mun fada maka Maryam bata da kawaye na gari …kuma….
Koda yake sun san gaskiya, sun zabi su kare Hanadi domin kada kishiyarta ta ga rauninsu. Amma Farhana tana kallonsu, ta san cewa yau ne karon karshe da kalaman kowa zai taba mata zuciya.
Wani mugun Kallo Ak ya watsawa yaya ramla
wanda ya sanya ta hadiye sauran kalaman dake bakinta nan take. Ta gyara zama , domin tasan wannan karon AK ba wasa yake yi ba. Ya juya fuskar sa ba ko alamar rahama ya kalli Zainab, wadda take zaune tamkar wadda aka yi wa dukan tsiya.
"Zainab, komai da komai nake son ji yanzu. Karki boye min ko harafi daya," AK ya fada muryarsa tana fitar da sauti mai firgitarwa.
Zainab ta yi dariyar dacin da bai kai zuci ba, ta fara magana muryarta na rawa amma babu nadama. "Nina fara neman Hanadi. Na samu lambarta ne a ranar budar Kai Wajan Yasmin matar jafar . Na fadawa hanadi gaskiya cewa ina son naga karshen Farhana, ita kuma tace tana so Farhana ta bar mata gidan ta. A haka muka fara harka; nake fada mata duk wani sirrin Farhana dana sani, ita kuma take amfani dashi wajen kuntata mata."
AK ya daure fuska, "Waye ya kira Farooq ranar da muke je Abu Zaria?"
Zainab ta daga kai ta kalle shi kai-tsaye. "Nice. Ina da sabon layi da na saya tun tuni, na dauki lambar sa a wayar Farhana tun da dadewa,ban taba gaya mata ba. Na kira shi ne don in hada ku fada, kuma hakan ya yi aiki."
Jin hakan ya sanya hawaye masu dumi suka fara zuba a fuskar Farhana. Ta tuna irin wulakancin da AK ya nuna mata a daren da suka dawo daga Zaria. Ta tuna yadda Nusaiba ta rinka kuka tana rantsuwa cewa ba ita bace, amma Farhana ta ki yarda da ita.
Ashe kishin zuciya da kiyayya ne suka sanya Zainab yin dukkan wannan dambarwar. Haka Zainab ta ci gaba da fallasa dukkan kage da tuggun da ta rinka kullawa.
Sai a sannan Farhana ta sami karfin magana, muryarta na rawa. "Zainab... why? Why? Me na miki a rayuwa da zaki nuface ni da wannan muguntar?"
Zainab ta kalli farhana , idanunta sun yi jajur. "You are selfish Farhana! Shine abin da kika yi min. Ni ban yi deserving din farin ciki bane? Maza uku suka zo rayuwarki ko wanne ba na yarwa ba, amma ko sau daya baki taba tunanin hada ni da daya daga ciki ba? Ga brothers dinki ma, amma baki taba cewa Zainab ga daya ki aura ba. You are very wicked, Farhana! Komai naki nake so, shi ya sa nima na yanke shawarar ba zaki taba samun nutsuwa ba."
Dakin ya dauki shiru, kowa jikansa yayi sanyi. Su Yaya Ramla suka rasa abinda zasu ce, domin wannan muguntar ta Zainab ta wuce hankali. Farhana ta koma ta zauna a daya daga cikin kujerun falon, ta rufe fuskarta da hannayenta biyu.
Ashe "wickedness" a wurin Zainab shi ne Farhana ba ta hada ta da maza ba? A nan ne Farhana ta gane cewa babu abin da zata kara fada wa Zainab wanda zai sanya ta fahimta, domin zuciyarta ta riga ta baci da hassada.
, dakin ya yi tsit, ba abinda kake ji sai kukan Farhana—kuka ne mai cin rai, wanda AK yake jinsa tamkar ana soka masa mashi a zuciyarsa. Ya juya ya kalli Hanadi, wadda ta yi shiru tamkar ruwa ya cinyeta, ganin yadda asirinta ya gama tonuwa a gaban kowa.
"Darling tsaya kaji!" Hanadi ta fashe da kuka tana kokarin karasowa gaban AK. "Wallahi Zainab ce ta ce min su Diddi (mahaifiyar Farhana) sun asirce ka. Wai idan ban fitar da Farhana daga gidan nan ba, ni za ta fitar da ni. Shiyasa hankalina ya tashi na biye mata."
AK ya kalli Hanadi da wani irin kallo na kyamata. "Yau Zainab ta fara zuwa gidan nan?"
Hanadi ta girgiza kai muryarta na rawa. "A'a... tana dan zuwa. Ko da kuna USA ma har wata daya ta taba yi a gidan nan. Yau ma tazo, tana B.Q ne wai zata tafi da asuba."
Hanadi ta juyo gun Farhana cikin marairita, "Farhana... don Allah ki yafe min."
Farhana ta goge hawayenta, ta kalli Hanadi da sauri. "Hanadi,lokacin da nake amarya, ni na ce miki AK ya ce ni nake yi wa abaya kyau?"
"A'a," Hanadi ta amsa muryarta kasa-kasa. "Jinku na yi a waya. Na kira shi, ya manta bai kashe ba, sai na ji duk abinda kuke fada."
Farhana ta juyo ta kalli AK da wani irin kallo. AK ya yi saurin sunkuyar da kansa kasa saboda tsananin kunya da nauyi. Su Yaya Ramla kuwa suka rasa abinda zasu ce a wurin, sai suka fara neman hanyar kare Hanadi.
Yaya Ramla ta gyara zama, "Ai Hanadi wayo Zainab ta mata. Kuma tunda ta ji ana maganar asiri, dole hankalinta ya tashi. Ni a gaskiya ban ga lafinta ba."
Farhana ta mayar da kallonta ga Zainab, wadda har yanzu take zaune ba ko alamar nadama. "Zainab... kika ce Diddi ce take tayani muna wa AK asiri?"
"Eh, haka nace," Zainab ta fada ba tare da shakku ba, tana kallon cikin idon Farhana.
Yaya Ramla ta yi saurin amfani da damar, "Ehen! AK ka gani ko? Dole Hanadi ta tsorata , tunda maganar asiri ce."
Farhana ta mike tsaye, hijabinta na ja a kasa. Ta kalli Zainab, sannan ta kalli Hanadi. "Zainab... ko zan yafe muku akan komai na duniya, ba zan taba yafe muku sharrin da kika wa mahaifiyata ba. Na barki da fitowar rana da faduwarta. Allah shi ne zai yi mana hisabi.
Ta juya ta bar falon da sauri, tana kuka sosai. AK ya bi bayanta da kallo, ransa a bace, ya san cewa yau Farhana ta kai makura.
"Hanadi, ki bi su Yaya Ramla gida yanzu! Kafin in yanke shawarar yadda zan yi da ke," AK ya faɗa muryarsa tana rawa saboda tsananin ɓacin rai, yana ƙoƙarin mikewa daga kujerar da yake zaune.
Yaya Ramla ta yi hanzarin shan gabansa, idanunta jajur. "Ban gane ta bi mu ba? Abdulkadir, ka duba lamarin nan mana, itama fa Hanadi yaudararta aka yi! Ba lafinta ba ne..."
"Wallahi, wallahi... sai ta tafi! Kin ji na rantsé!" AK ya katse ta da wata irin tsawa da ta sa gidan ya ɗauki sauti. Ya nuna ta da yatsa, "For the last time Ramla Tahir Tambuwal, ki fita daga sabga ta! Idan ba haka ba, abin da zan miki ba zai miki daɗi ba."
Ganin AK ya riga ya kai maƙura kuma yana ƙoƙarin matsar Ramla kamar zai shaƙe ta, Yaya Safiyya ta yi saurin shigowa tsakaninsu.
"Ki ƙyale shi ya dake ni mana!" Ramla ta faɗa cikin tsiwa tana kukan baƙin ciki. "Dama ba yau ya saba ƙoƙarin duka na akan Farhana ba! Kuma an faɗa, asirce ka aka yi shi ya sa kake wannan haukar."
AK bai sake bi ta kansu ba, ya nufi hanyar fita yana huci. "Kar na dawo na same ku a gidan nan!" Ya buga ƙofar falon ya fita, ya bar su a nan tsaye.
Su Yaya Ramla suka ja hannun Hanadi zuwa sama domin ta haɗa wasu 'yan kayayyakinta. Suna shiga ɗakin, Yaya Ramla ta juyo kan Hanadi da masifa:
"Kin ba ni kunya Hanadi! Uban me ya kai ki haɗa kai da ƙawar kishiyar ki? Ke ba ki iya kissa ba ne? Kin kunyata mu a gaban yarinyar nan, duk na ji na muzanta a gaban Farhana!"
Hanadi kam sai kuka take yi mai ban tausayi, "Ni dai don Allah ku ba Papa haƙuri. Wallahi mutuwa zan yi idan na rabu da shi! Don Allah Yaya Ramla..."
"Dalla yi mana shiru!" Yaya Safiyya ta daka mata tsawa. "Kin riga kin zubar wa kanki mutunci. Har Farhana tana tambayarki kina 'confession'? Me ya sa ba ki yi 'denying' (musu) ba? Kin tsaya kina bayyana sirrinki?"
Hanadi ta kasa magana, sai ajiyar zuciya. Yaya Safiyya ta numfasa, ta kalli Ramla sannan ta kalli Hanadi. "Ki bi mu gida yanzu, kafin AK ya dawo. Ka san shi ba mutunci ne da shi ba idan ransa ya ɓaci. Ki bari ya huce, sai mu ga yadda za a lallaba shi."