Free chapter · Read without an account

5

by Maimoon Abdallah · BANI DA HUJJAH!

🌺BANI DA HUJJAH🌺

5. 


Tana tsane gashin kanta da ta wanke shi sosai ba kaɗan ba ta fito daga toilet, baby pink towel ɗaure a chest ɗinta, very fair skin ɗinta sai glowing yake, ta zauna a gaban dresser tana ƙarema ɗakinsu siyama da su kansu su siyama ɗin kallo, ɗakinsu siyama babba ne sosai kuma kasancewar su masu banbancin ra’ayi akan komai yasa ɗakin ya zama kamar wanda akayi splitting gida biyu, ko wacce da side ɗinta with her bed da study area ɗinta, kasancewar lailerh is more girly yasa gefenta nuna hakan, sashinta sai ya kasance is more aesthetic dan har ƙaramin vanity table take da shi a gefenta cike da skin cares ɗinta da perfumes kamar mai sayar da su, itama gefen siyama tana da same table amma nata laptop ɗinta da notebooks da frames na motivational quotes ne akai, kai kana kallo kai tsaye zaka gane cewa ita siyama is a bookworm ita kuma lailerh soft girl life, sai dai duk da haka same dresser da siff suke sharing, Lailerh da tayi tagumi akan gadonta tana kallon Salwa tace 

“Wai bazaki faɗa mana what happened ba” 

“Eh!, bazan faɗa ba” ta faɗa tana matso cream ɗin Lailerh ɗin da ta zo ta ɗauka a table ɗinta kasancewar same cream suke using unlike siyama da ba irin nasu take anfani da shi ba, ko shower gel da na Lailerh tayi using, ta zauna  ta fara lailaye jikinta da cream ɗin kamar tana shafa ƙwai, siyama  dake kan gadonta itama tace 

“Haba Princess, ki faɗa mana pls” 

“Mtsw, sai kuma kuyi, ba dai ni kuka yi ma dariya ba ɗazu! Billah bazan faɗa ba” 

“Stop swearing mana ai da Mami ta ce mu bar dariya mun bari, pls tell us what happened, kullum sai na duba status ɗinki har snapchat da insta story ɗinki u didnt post anything about birthday ɗin raliya, pls tell us what happened”  kamar ba da ita suke ba ta ƙarasa shafa mai ɗin ta buɗe drawer ta fara duba kaya a cikin nasu zata saka, kamar kuma wacce aka yi wa wahayi ta juyo tana kallonsu tace 

“Wallahi bazan taɓa yafewa Aryaan ba” duk buɗe ido sukayi suna kallonta jin ko yayan ma bata sakaya ba wai Aryaan, ji sukayi kamar ta tafka zunubi ambatar sunansa without yaya, kafin su gama comprehending wannan ta cigaba 

“I hate him! Stubborn.. arrogant.. st…” 

“Ke salwa, are u in your right senses kuwa? Shi yayan?” 

Sai da tayi rolling idanunta kafin tace “Eh shi? Waye shi? Tunda ba mala’ikan ɗaukan rai bane ai da sauƙi, ni na daina jin tsoronsa wallahi, kuma wannan abin da ya min koh hmm…” 

Da ƙyar suka rufe bakunansu da suka sake suna sauraronta 

“Me yayan ya miki wai toh?” 

“Ku barni da shi, wallahi zai san ni yayi ma haka, wallahi duk abinda ya mini sai na rama” sai a lokacin Siyama ta ɗan ja guntun tsaki tace 

“Ko kuma ki rame ba, Shegen cika baki, Salwa duk duniya wa ya fiki tsoron yaya Aryaan, ki faɗa mana me ya haɗaki da shi sai kame kame kike kina zaginsa, Allah ya sa ya jiki” 

“To ya jini mana! Sai me?” 

“Wai a ina kika ga yayan? Ni fa na kusa two weeks rabon da na gansa” 

“Dama a ta ina zaki gansa yana can yana walakantani saboda ni ce karamar katangarsa daɗin tsallakewa” 

“Ban gane ba” Lailerh ta faɗa cike da son jin labari. 

Ƙin amsawa tayi ta juya ta cigaba da zaɓen kaya da zata saka, da ƙyar ta samu wani plain gown cikin kayan lailerh su dai kallonta kawai suke yi yadda garin ɗaukan kayan take ta wargaza musu siff, yanzu suyi magana cibi ya zama ƙari tunda Mami ce tace tayi wanka anan ta ci abinci kafin ta tafi gida. 

Saka rigan tayi ta zauna ta fara drying gashinta, ta gama tayi styling ɗinshi tana yi tana tunanin wayanta da ke wajenshi idan ta tuno ji take kamar ta hadiyi zuciya ta mutu. 

Tana gamawa ta miƙe ta nufi ƙofa duk suka bita da kallo, siyama ta miƙe ta tafi siff ɗin ta leƙa taga bata ko taɓa part ɗin kayanta ba, ta ɗan yi murmushi ta kalli lailerh tace 

“Sai ki tashi ki gyara kayanki” daga haka ta nufi ƙofa itama, miƙewa lailerh tayi ta bita ba tare da ta gyara ɗin ba itama gudun kar ta tsaya gyarawa Salwa ta je ta faɗa ma siyama abinda ya faru ita kaɗai. 

Mami na ganin sun sauko ta nuna musu hanyar dining da hannu, ko kallon dinning din salwa bata yi ba ta nufi hanyar ƙofa, Mami ta bita da kallo kafin tace 

“Salwa bazaki ci abinci ba?” 

“Bani da appetite Mami i just want to see daddy” 

“a haka zaki tafi babu ɗankwali…?” Ko kafin ta ƙarasa har ta fice a palourn, Mami ta sauƙe ajiyar zuciya kawai kafin ta juya wajen su lailerh tace 

“Kuje ku ci abinci” 


Al’ameen ne ya shigo ɗakin Mami bayan sallar magrib, ganin tana waya ya sa ya ƙarasa ya zauna a kujera yana jiran ta gama, ganin expression ɗinta yasa ya bada hankalinsa kan abinda take faɗa a wayar

“Eh, na gane! Na gane, to ba damuwa idan baku dawo ba zan sa Al’ameen ya kawo ni”  Ameen dai ya zuba mata ido har ta sauƙe wayar ta dafe kanta a hankali 

“What happened?” Ya tambaya yana kallonta worried 

“Salwa ce wai take hospital” 

“Hospital kuma? Me ya same ta?” 

“da Amminta muke magana yanzu wai bata iya cin abinci babanta ya kaita asibiti” 

“Saboda kawai bata ci abinci ba shine za’a kaita hospital to yaushe ma ta dawo ɗin, kuma sau nawa ne bata ci abincin ba?” 

“Anan ma ai ƙin ci tayi ina jin da ta je gidan ma bata ci bane kuma dai ka san yanda Yaya Ameenu yake akan Salwa, ni wallahi sam ban ji daɗin abinda Aryaan ya aikata ba har fargaba nake ji na abinda zai faru wlh” 

“Ikon Allah” Ameen ya faɗa though ba wai hes very suprised bane kowa ya sani a duka family ɗinnan Uncle Ameenu ko kaɗan baya wasa da lamarin only daughter ɗinshi Salwa, akanta bashi da kara, dama asali ba kirki ya cika ba to akanta kuwa rashin kirkin ninkuwa yake, ko Amminta ba sha take yi ba a wajensa in dai akan Salwa ne, shiyasa yarinyar take abinda taga dama kowa tsoron mata faɗa yake saboda jaraban ubanta dan a gurinshi fa bata laifi,  the only people da suke iya mata magana akan abu Mami ne twin sister ɗin Uncle Ameenu, tunda babansu Ameen ya mutu ta dawo gida da yaranta da dadewa tun kafin su Ameen su kai haka, to itace ma atimes takan yi wa Salwa nasiha idan ya kama harda faɗa sai kuma Bappah, thats Wazeer Turaki himself, grandfather ɗinsu shi kuma dama mutuminta ne duk da tsaurinsa amma sosai take sonshi akwai shakuwa sosai tsakaninta da shi, sai kuma Amminta da take shakkah only idan daddynta baya wajen. Maganar Mami ce ta katse masa tunanin da ya tafi 


“Amminta tace wai hypoglycemia ke damunta wai sugar level ɗinta yayi dropping! Toh ban dai sani ba since babanta ne dr ɗin komai ma zai iya cewa, kuma ka san already ya kira meeting!” Ameen ya sauƙe ajiyar zuciya yace 

“Shiyasa ma na zo yanzu in ce Mami as his twin sister pls babu yadda za’a yi ki ɗan masa magana yayi hakuri da meeting ɗinnan? Lokacin general meeting baiyi ba amma yawanci idan kaji emergency meeting toh its always him, yanzu wannan issue ɗin bazaku iya settling a hankali ba sai an sakko bappah a ciki” 

“Kira min Aryaan” Mami ta faɗa ba tare da ta amsa maganar da yake mata ba, wayarsa ya zaro ya shiga dialing lambar Aryaan amma baya connecting ya dube ta yace 

“Baya shiga” 

“Ai ya kyauta saboda ya san bai shuga abin kirki ba shiyasa ya rufe layukansa, idan kayi sallah isha’i kaje ku taho tare da shi, saboda zai iya cewa gobe ba zai zo meeting ɗin ba, ya ƙara ma kansa wani laifin akan laifi, wallahi ni har yaya Umar tsoron yaji maganar nan nake” 

Miƙewa Ameen yayi yana kallonta yace 

“Ke dai ki kwantar da hankalinki Mami, duk abinda sukayi babu ruwanki kar ma ki saka ma kanki damuwa please, ai ya san irin haka zai faru amma ya gwammace ya jawo ma kannasa magana”. Daga haka ya fice a ɗakin ta bishi da kallo kawai, 


Ummah dake zaune a palour ta kalli uncle muhammad dake sauƙowa daga sama da waya a kunnensa har ya ƙaraso cikin palourn ya zauna a kujera ranshi a ɓace yana faɗin 

“Tabbass! To wallahi sai yayi dana sanin taɓa ta Allah ya kaimu goben, toh, toh, shikenan” 

Ummah ta taɓe baki tana kallonsa tace “wa kuma aka taɓa” gyara zama yayi yana kallonta yace 

“Wannan ɗan iskan yaron Aryaan ne wai ya je ya kulle Salwa dan bashi da mutunci, ni dai na cewa Ameenu ya duba ta da kyau kar dai ya mata wani abin dan ɗan iska ne yaronnan kowa ya sani” 

“Mtsw, dama na san wallahi bazai wuce ita ba, kai ai idan anga kana ɗaga jijiyoyin wuya to akan Ameenu ne, kana yayansa amma wai ƙaninka ke juya ka, daga yayanka har ƙaninka su zauna suna juyaka yadda suka ga dama ba abinda ya dame ka suyi ta passing ɗinka kamar ƙwallon ƙafa kowa yana anfani da kai, ga dai hamza ga nan shaheeda sune dolenka amma inaaa ka ƙare a gindin brothers ɗinka da basu san darajarka ba kowa ɗansa ya sani a cikinsu, nan Aryaan ya shaƙe Hamza ka dinga hayagaga bazaka yarda ba amma shiru kake ji babu abinda kayi akan hakan ya daki banza amma da yake salwa ya taɓa yanzu gashi nan har babanta ya kira emergency meeting an taba ƴar gold, kai kuma kana taya sa kana tada jijiyoyin wuya bayan da aka taɓa naka ɗan shi bai yi wannan baloƙoƙon ba, ka cigaba wallahi takaicinka bazai kashe ni ba” tana gamawa ta miƙe ta wuce sama mugun takaicin halin mijinta yana ƙona mata rai, duk cikin brothers ɗin sun fishi kuɗi, sun fishi alƙibla da sanin abinda sukeyi, they are the leaders shi kawai sai yadda suka yi da shi a ganinta, sun fishi iko da say a gidan. 


Aryaan ne a zaune, Mami na tsaye a kansa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba 

“What u did is not right, its very very wrong Aryaan, ko ba komai ai yar uwarka ce amma ka ɗauketa ka kaita ka kulle kamar wata mara galihu? Bayan ka san halin mahaifinta sarai? Meyasa duk abinda zaka janyo ma kanka magana shi ka fi so Aryaan, dama gashi nan kana baki already amma kullum sake saka kanka kake a bakin kowa Aryaan, na tambayeka why u did that kuma ka min shiru koh” 

Ɗaga idanunsa yayi ya kalleta ya sauƙe kan still saying nothing, ta koma ta zauna tana kallonsa tace 

“Shikenan tunda bazaka faɗa min ba gobe ai dole ka faɗa a gaban kowa Allah ya kyauta”  shiru yayi kamar bazai ce komai ba sai kuma can yace 

“Kiyi hakuri Mami” Al’ameen takaici kamar ya kashe sa yana zaune dai yana kallonsa, Mami ta girgiza kai tana kallonsa tace 

“Ah ah ni kuma ina ruwa na, duk abinda zaka yi dai ni dai ina mai tabbatar maka ka dinga tunani, yanzu na tabbata umminka bata ji ba bata gani ba zaka jawo mata magana dan kai ka sani ko miye zaka yi a wajensu fa Umminka ce ta saka ka, bata nan ɗinma bata tsira ba kullum cikin sakata a bakin yan gidannan kake ka dinga mata adalci ni dai na faɗa maka” shiru yayi bai ɗago kansa ba tace 

“Yaushe rabonka da kaje wajenta?” Sai a lokacin ya ɗago ido ya kalleta yayi shiru 

“Tambayarka nake” 

“Three days ago naje” 

“Kunyi magana da ita?” Girgiza kai yayi alamar

 “ah ah” 

“And why is that” shiru yayi bai ce komai ba, ta sauƙe ajiyar zuciya tace 

“Tashi kaje sama ka kwanta” ya ɗago kanshi ya kalleta 

“Mami zan zo goben i promise”

“Story for the Gods, ka ga ni kar ka saka ni magana, kaje sama ka kwanta gobe after meeting ɗin sai ka tafi” 

Ɗan kallon Ameen yayi, Ameen ya ɗauke kansa daga kallonsa yana pressing phone hakan ya sa ya kalli Mami yace 

“Zan ɗauko kaya” 

“Use Al’ameen’s”  gyaɗa kai yayi ba don ransa ya so ba yace 

“Okay” ganin yanayinsa tace 

“Idan kuma zaka tafin, amma promise zaka zo goben” 

“Ah ah i’ll stay back” 

“Toh shikenan, Allah yayi albarka” 

Ya amsa da “Amin” ba tare da ya kalli Ameen ba kawai ya mike ya nufi ƙofa Mami ta bishi da kallo. Ba’a jima ba Ameen ma ya miƙe yabi bayansa shima ya nufi ƙofa ta raka su da ido kafin ta sauke ajiyar zuciya ta miƙe ta wuce sama. 

Kujera da ke compound Ameen ya ɗauka ya kai har gaban motar Aryaan da ya bar door ɗin gefen a buɗe ya zagaya side ɗin da ke buɗen which is not facing the compound ya ajiye kujeran ya zauna yana kallon Aryaan da ke zaune a driver’s seat kafafunsa na ta waje da cigarette a hannunsa da ya kunna  yana sha a hankali, Ameen ya zauna yana kallonsa yace 

“Har yanzu baka yi niyyar faɗa mini me ta maka ba kenan?” Ko kula Ameen baiyi ba sai yatsarsa da ya sa yana kaɗe jikin tabar tokar ta zube ya mayar bakinsa yana sha a hankali yana furzar da hayakin, shi kaɗai ya san irin ƙunan da ke damun zuciyarsa. 

Ameen ya kai hannu ya zare taba ɗaya daga kwalin da Aryaan ya ajiye a gefensa ya sa a baki ya kalle shi yace 

“ina lighter ɗin?” Kamar bazai tanka sa ba sai kuma ya ciro a aljihunsa ya jefa masa, ya ɗauka ya kunna shima yana sha yana taɓa wayarsa, sai da suka kusa shanye duka kwalin kafin Aryaan ya miƙe zai wuce ciki, Ameen yace 

“Mami will perceive  the smell stay back a little” 

Komawa yayi ya zauna yana haɗe rai ya jingina kansa da kujera, shima Ameen ɗin bai kulasa ba ya cigaba da chat ɗinsa abinsa. 

Murmushi Ameen yayi bayan wani lokaci ya kalleshi kafin ya ɗaga kiran dake shigowa wayarsa, Aryaan da idanunsa ke lumshe ya buɗe su yana kallon Ameen jin yace 

“Kin samu kin ci abincin?” Ganin waya yake ya sa ya mayarda idanunsa ya rufe sai kuma kawai ya miƙe yayi wucewarsa cikin gida ya barshi a nan zaune. 


#Banidahujja
#Maimoon
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.