Free chapter · Read without an account
SARTSE A ZUCI....! Chapter 23
*SARTSE A ZUCI.....!💔*
*Arewabook@ayshadansabo*
*Paid book ****
©️ _Ayshat Ɗansabo Lemu_ ✍🏻
*Chapter 23*
Kwanan Yaya Hameedah goma aka maidata zuwa ABU dake Shika sabida yadda jikinta ya tsananta,kuma bisa ga dukkanin gwaje-gwaje da akai tayi aka gano cewa wai ƙodarta ɗaya ta sami matsala sannan zuciyarta na kumbura.Babu wanda hankalinsa bai tashi da jin sakamakon da likitoci suka bayyana ba,Amal tafi kowa shiga cikin matsanancin tashin hankali da jin halin da ƴar Uwarta guda ɗaya tilo data mallaka ke ciki.Dukkanin ƴan Uwa da sauran dangi na kusa da nesa suka dinga sintiri wajen zuwa duba jikinta yayinda shi kuma Yaya Zayd ya dage akan cewa barin ƙasar za su yi,domin shi bai gamsu da dukkanin abinda likitocin nan suka bayyana ba.Kuma ba tare da ɓata lokaci ba Daddy ya goya masa baya aka fara processing yadda za a fita da Yaya Hameedah zuwa ƙasar Germany,Momy da Anty Mamah a cikinsu za ka rasa waya fi wani shiga cikin tashin hankalin halin da Yaya Hameedah ke ciki.Yayinda ita kuma Yaya Hameedah take kwance cikin matsanancin jinya domin tasha faɗi wa su Daddy cewa su daina wahal da kansu wajen cewa saisun fita da ita waje domin rayuwarta ta riga tazo ƙarshe,kuma ranar da Ubangiji yayi nufin maganarta zai ɗauke a wata yammaci ne duka su Daddy na kewaye da ita Yaya Zayd yana zaune daga gefen gadon jinyarta yana bata ruwan da tace tana son sha.Amal na daga tsaye a gefen hagunta rungume da Abdallah da bacci ya sace bada jimawa ba,sai Hameedah ta ɗaga kanta ta kalli Amal sannan ta maida dubanta wajen su Daddy tana faɗin,"Daddy ku shaida cewa nayi ma Amal kyautar Abdallah tunda jimawa,tunda yazo duniya nake ji a jikina kamar ba za mu yi doguwar rayu tare ba,don haka kayi haƙuri Yaya Zayd ka tayani tabbatar da wannan kyautar dana yiwa Amal domin itama jininka ce kuma tana ƙaunar Abdallah irin ƙaunar da nake masa koma fiye da haka." Ta numfasa tare da jan numfashi a wahalce alamun maganar wahala take mata,amma duk da hakan saita maida dubanta wajen Amal wacce tuni hawaye suka fara sintiri a saman fuskarta domin a lokacin ji take duniyarta na cika da wani irin matsananci tsoro.Tsoron karta rasa Yaya Hameedah,domin ta fara jin tsoron cewa kada fa ya kasance da gaske rayuwar ƴar Uwarta ya kusa zuwa ƙarshe.Kuma wannan tunanin kaɗai daya haska a cikin kanta ya sanya kuka kufce mata,amma ga mamakin kowa ita kuma Hameedah murmushi tayi.Murmushin daya tsaye wa kowa a cikin ransa,kuma bayan murmushin sai ta sake duban Amal tace,"Ummu Abdallah ina tsananin ƙaunaeki,nasan kina son Abdallah,kina matuƙar ƙaunarsa kuma za ki kula da shi,ki sanar dashi cewa ina ƙaunarsa,Allah ya raya miki shi yayi masa albarka,ke kuma Allah ya baki ikon cin jarabawarki Amal."Tana kai ƙarshen kalamanta Yaya Zayd ya riƙo hannunta yana tausasa harshensa wajen sanar da ita cewa shima ya baiwa Amal Abdallah,ya roƙeta data daina kawowa kanta mutuwa domin cuta ba mutuwa bace za ta tashi har su haifi wani ɗan su saka masa sunan Daddy.Kuma a lokacin daya kai ƙarshen kalamansa murmushi kaɗai Yaya Hameedah ta iyayi idanunta akan Amal har lokacin wacce take kukan hawaye sosai,gabaki ɗaya kaman an sanya salataf an nane bakin Amal ta kasa furta komi sai hawaye kawai take tana sauke ajiyar zuciya.Kuma tun daga wannan tattaunawar Yaya Hameedah bata sake buɗe baki tayi magana ba,domin maganarta a duniya ya ƙare ta riga ta gama furta iya adadin kalaman da za su iya fita daga bakinta a duniya.A duka sauran kwanaki uku da suka biyo baya sai dai idan anyi magana ta amsa da kai,Yaya Zayd ya kasa samun nutsuwa duk ya ƙosa visarsu ta samu.Kuma a ranar da visar ta samu a washegari Allah ya ɗauki rayuwar Hameedah,ta rasu a daren alhamis aka wayi garin safiyar juma'a da zancen komawarta zuwa ga Allah.Mutuwar Hameedah mutuwace daya taɓa ilahirin ƴan family ɗin Lawal Ƙaura,mutuwa ce da rabon da ayi mai zafi da ɗacinta tun bayan rasa Abdallah da Asiya da aka yi.Faɗin irin halin da Yaya Zayd da Amal har zuwa kan Momy da Daddy suka shiga abu ne da bazai taɓa misaltuwa ba,domin sun shiga cikin matsanancin yanayin da ƙarfin addu'a ne kaɗai ya taimaka musu har sukai tawakkali suka dangana.Amma fa ansha fama kafin Amal da Yaya Zayd su dawo cikin hayyacinsu domin gabaki ɗaya sun fita a hayyacinsu babu abinda ke dawo masa da kuma tsaya masa a zuci sai rabuwarsu da ita kafin su taho Zaria su wuce bikin Sakeenah,idan ya tuna ƙaryar da yayi mata ya rufe mata gaskiyar inda yaje a daren ranar da yaje wajen Najwa sai yaji ya tsani kansa ya tsani dukkanin kalar rayuwar da yayi a baya da Najwa da Maryama.Itama Amal babu abinda ke dawo mata illa maganganun da sukai tayi a daren ranar da za su taho,da irin yadda Hameedah take roƙonta akan ta rufe sirrin mijinta.Idan ta tuna ranar ƙarshe da maganar da Hameedah tayi mata da addu'arta na ƙarshe a gareta sai taji ta sake gigicewa,sosai suka shiga cikin halin ɗimuwa da ficewar hayyaci har na tsayin sati guda kafin su fara dawowa cikin nutsuwarsu.Sai dai kuma duk da irin halin ɗimuwar da Amal ta shiga bata taɓa yarda tayi nesa da Abdallah ba kullum suna tare,bata yarda kowa yayi hidimarsa ba sai ita.Tana hidimarsa tana kukan zuci dana fili cikin matuƙar ragaita da tarin alhinin rasa Mahaifiyarsa da suka yi,rashin da har abada ba za ta daina jin ɗacinsa da raɗaɗinsa ba.Koda yaushe suna manne a Vedio call da Aman Kurfi yana rarrashinta da sake bata baki akan ta sanya dangana,shima karan kansa dauriya yake domin mutuwar Yaya Hameedah ya tsaya masa arai ya kuma fi kowa sanin cewa dole ta shiga cikin mawuyacin hali.A haka tamkar ƙiftawar idanu kwanaki suka fara ƙarewa,ƙafafun da suke zuwa gaisuwar rashin Hameedah suka fara ɗaukewa amma zukatan makusanta basu daina jin zafi da raɗaɗin rashinta ba.Yaya Zayd ya dawo abin tausayi da kuma riritawa a wajen Momy da Daddy dake tsananin jin tausayinsa,yayin da Amal Taheer ke sake jin wani irin haushinsa da tsanarsa a cikin zuciyarta domin a ganinta bai cancanci tarin riritawar dasu Momy ke masa don ya rasa wacce ta tabbatar sun fishi sonta domin babu abinda ke zuwa kanta sai tarin baƙin cikinsa da Yaya Hameedah ta dinga haɗiya akan lamarinsa da Matan banza.Yadda Amal ta sanya abin a cikin zuciyarta take kuma kallonsa dashi ya zarce tunanin mai tunani,domin gani take ba ƙaramin neman mata yake ba.Hakan ya jefa tsanarsa mai zafi a cikin zuciyarta,take kuma jin zafin abin sosai a yanzu data rasa Yaya Hameedah take kuma zargin cewa jininta da Doctor yace ya hau a ranar farko data kaita asibiti ba bakomi ya janyo mata hakan ba sai bakin cikinsa dana bibiyar matan banzansa data aje abin a cikin zuciyarta yake mintsininta.Da zaran ta tuno abinda ya faru kwana ɗaya kafin suzo zo Zaria su wuce Jos,irin kukan da Yaya Hameedah ta dinga yi kafin ta sanar da ita cewa ya fita wajen wata mace sai taji an ninka mata tsanarsa a cikin zuciyarta.Hakan yasa a dukkanin kwanakin da suka biyo baya na rashin Hameedah a cikin duniyarsu take baƙin cikin ta buɗe idanunta taje ɓangaren Momy taga yadda take sanyashi a gaba tana ciyar dashi abinci a baki don kawai yana cikin halin jimimamin da ko kaɗan baya birgeta,domin tasani nan da ɗan wani lokaci kaɗan zai manta da ƴar Uwarta ya ɗaura barikinsa yadda yake so.Sai dai abinda bata sani ba shine da gaske mutuwar ƴar Uwarta ya taɓa Yaya Zayd tare da yin tsananin nadamar dukkanin abubuwan daya aikata mara kyau a rayuwarsa,domin shi ma a karan kansa tsanar kansa yake ji a duk lokacin daya tuna irin reaction ɗin da Hameedah keyi idan ta kamashi yana waya da Najwa.Idan ko har brain ɗinsa ta dawo masa da zuwan Maryam gidansa ya tuna irin kalaman da Hameedah tayi sai yaji tamkar zai haukace,sai yaji duniyarsa na juyawa da tarin nadamar da baisan ranar dainawarsa ba idan har bai yiwa Hameedah adalcin daina kusantar Zina a bayan ranta ba.Daga Najwa har Maryam sunji labarin mutuwar Hameedah kuma sunyi masa gaisuwa ta waya,ita Najwa ma anyi aurenta da sati guda ne abin ya faru kuma da gaske mutuwar ya taɓata sosai duk da cewa a hoto kaɗai ta taɓa ganin Hameedah.Maryam kuwa ba ƙaramin dukanta mutuwar yayi ba domin kwana da yini tayi tana bitan kalaman Hameedah da irin magiyar data dinga mata akan ta rabu mata da mijinta,jikinta sosai yayi sanyi ta kuma tausayawa Zayd Abdallah domin a cewarta yayi rashin kyakykyawar mace mai sanyin hali da kuma nutsuwa.Duniyar Amal Taheer ya sake hautsinewa a ranar da Yaya Hameedah keda wata guda da rasuwa,kuma har lokacin Yaya Zayd ya kasa komawa bakin aikinsa domin bashi a cikin yanayin da zai iya taɓuka komi koda ya koma bakin aikin.Kuma sai akai sa a suka duba alfarmarsa daya roƙa akan su bashi hutun wata guda domin samuwar nutsuwa a cikin rayuwarsa gabannin ya koma bakin aikinsa,dukkanin waɗanda suka zo masa gaisuwa daga Port Harcourt sun tausayawa halin da suka samesa a ciki akan rashin matarsa da yayi musulmai da kiristansu kuwa.Aman Kurfi ya sanar da Amal cewa yana son yazo 9ja domin yi mata ta'aziyyar Hameedah face to face,domin zuciyarsa ta kasa nutsuwa da irin halin da Amal ke ciki na kewar rashin Ƴar Uwarta daya taɓa rayuwarta matuƙa.Don haka ya sanar da ita cewa a kowani lokaci za ta iya ganin ya dawo,kuma itama sai taji tana son ya dawo ta ganshi taji rarrashinsa gaba da gaba bata waya ba.A ranar wata Friday da daddare bayan sallar Isha'i ne Daddy ya sanya Anty Mamah tayi masa kiran Amal,bayan sun gama zantawa da ɗansa Zayd Abdallah wanda yazo masa da ƙoƙon barar da bazai taɓa iya tankwaɓarwa ba koda ace kuwa jini bai ratsa a tsakaninsa da Zayd ɗin ba.Domin Zayd ɗin yazo da buƙatar da dama Daddy da tunanin hakan yake kwana yake tashi tun bayan da nutsuwa ta dawo masa na rashin ƴarsa mai tarin haƙuri da nagarta da yayi,sai gashi Zayd ɗin ya rigashi furta buƙatar hakan a fili.Kuma ba wata buƙata bace da alfarma Zayd ɗin ya nema ba face Daddy ya taimakeshi yayi masa alƙawarin bashi auren Amal domin ta maye masa gurbin ƴar Uwarta daya rasa,kuma yayi wannan roƙo ne guiwarsa a ƙasa kuma idanunsa na zubar da hawayen zafi da raɗaɗin rashin Hameedah dake sake kassara zuciyarsa.Kuma sai akai sa a yayi sara akan gaɓa domin Daddy ba tare da yayi kowani irin tunani ba ya riƙe hannuwan Zayd biyu tare da rungumesa a jikinsa yana share masa hawayen da yake jin zafin zubarsu na sake dukan zuciyarsa tare da raunatata da abubuwa guda biyu,abu na farko tausayin rashin Iyaye Uwa da Uba da Zayd ɗin suka rasa.Sai abu na biyu tausayin yadda ya rasa Hameedah a lokacin da dukkaninsu keda buƙatar su rayu da juna kodan su tarbiyyanci ɗansu Abdallah,amma kuma shi Ubangiji babu ruwansa da wannan tsarin tunda tsarinsa shine gaskiya kuma shi baya kuskure akan dukkanin abinda zai zartar akan bayinsa.Cikin muryar rarrashi da jin tarin tausayin ɗansa Zayd ya sanar dashi cewa ya bashi Amal,matuƙar shi ya haifeta to yana bashi tabbacin cewa Amal itace za ta maye masa gurbin ƴar Uwarta Hameedah da suka rasa ko domin ɗansu Abdallah.Kuma wannan albishir da Daddy yayi ma Zayd shine abu na farko daya fara sanya nutsuwa a cikin zuciyarsa karon farko bayan ya rasa matarsa Hameedah,domin tun daya rasata har kawo lokacin daya iya buɗe baki ya roƙi wannan alfarmar a wajen Daddy da wani irin tsoro da taraddadi yake kwana yana tashi a cikin zuciyarsa.Domin lokuta da dama idan ya jiyo kukan Abdallah ko suka haɗu da Amal ya ganta rungume dashi ko tana masa wani hidima sai yaji tsoro yana lulluɓe zuciyarsa,wani irin tsoro dake ratsa har ƙasusuwan jikinsa yana jin ko kaɗan baya fata Abdallah ya rasa wannan kulawar koda ta ƙiftawar idanu ce daga gareta.Sai ya tuna kyautarsa da Hameedah tayi wa Amal har kuma ya buɗe baki shima ya jaddada kyautar da ko kaɗan baikai har cikin zuciyarsa ba,domin a lokacin ya jaddada kyautar ne domin ya samawa Hameedah nutsuwa da kwanciyar hankali a halin da take ciki na jinya.Don haka tun ba a rufa sati biyu da rasa Hameedah ba zuciyarsa ta fara ɗarsa masa cewa mafita guda ɗaya ce kaɗai da zai basu damar samun maslaha shi da Amal,kuma ba wata mafita bace daya wuce su auri juna domin su raini Abdallah a inuwa ɗaya ba tare da ɗaya ya zargi ɗaya akan rashin kyautatawa ko rashin adalcin ƙin barinsa ya rayuwa da abu mafi soyuwa a cikin zukatansu ba,domin yana da tabbacin cewa raba Amal da Abdallah ba abu ne da bazai taɓa yiwuwa ba tare da hankula sunyi dubu sun ɓaci ba.Shima kuma a ɓangarensa bazai taɓa iya kallon ɗansa a gidan wani yana rayuwa ba matuƙar ba a hannun Momy bace,kuma yasan hakan bazai taɓa yiwuwa ba domin dukkaninsu tausayin Amal suke ji da irin ƙaunar da take ma Abdallah tabbas babu wanda zai iya tunkaranta da batun ta bashi riƙon Abdallah koda kuwa aure za ta yi kamar yadda yake da tabbacin cewa duk wani wanda Amal za ta amince da aurensa shima ya zame masa dole ya ƙaunaci Abdallah ya kuma yi mata alƙawarin rayuwa tare da Yaron.Shiyasa a dukkanin lissafin daya buga bai hango wata mafita mai sauƙin daya wuce Amal ta maye masa gurbin Hameedah ba,duk da cewa yasan irin tsanar da tayi masa da kuma yadda tun fil azal basa shiri da junansu.Amma duk da hakan sai yake ganin zai Iya jure komi matuƙar dai bazai rasata ya kuma rasa ganin ɗansa a kusa dashi ba,shiyasa tunda Daddy yayi masa albishir ya fita yana jin tarin nutsuwa na cika duniyarsa.Yayinda ita kuma Amal a daidai lokacin ta samu saƙon kiran da Daddy yake mata daga bakin Anty Mamah,a lokacin tana yima Abdallah shirin bacci kuma bata tafi amsa kiran ba sai bayan data kammala ta goyeshi tsaf a gadon bayanta sannan ta zura slippers da hijab ɗinta ta tafi amsa kiran da ya zamo mata mummunar kiran daya sake tarwatsa farin ciki da nutsuwarta baki ɗaya.........✍🏻