Free chapter · Read without an account

Page 5

by AISHA YUSUF HANWA · Gaba Kura

Follow this link to join my WhatsApp group: ***

 GABA KURA


AISHA HANWA


PAGE 5


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Wani kallon hadarin kaji ya mata kafin ya ce "Ke kar ki kawo mini maganar banza! a ina wannan yarinyar ta yi miki kama da me farar? dallah matsa ki bani guri in ji da abun da ya dame ni, abun da nake ji a gari yau ga shi a cikin gidana ka fita mutane su dame ka da gulmammiyar gaisuwar jaje". 


Daga inda Inna ta koma bayan ya koreta ta ce "Kanka ake ji wai mahaukaci ya so gulma" Ba haka ta so ba; Ta so ace yau gidan ya yi musu kaɗan su da shi amma ya watsa mata ƙasa a ido.
 

Tana ganin ya zabura ya shiga ɗakin Mama ta figi hijabi ta fice a gidan.


Duk diramar da suke yi shi da Inna muna jin su amma ba wanda ya tanka sai da muka ji ya gwasale ta tukuna na ji Mama ta ce "Allah na gode maka ai dama shi Allah ba ya barci".


Shigowar shi ɗakin nasu ba ƙaramin haddasa mata wani mummunan faɗuwar gaba ya yi ba abun da ya saka ta ɗan ji sassauci shi ne ganin da ta yi fuskar shi da ɗan rahma da kuma maganar da wanzu tsakanin sa da Inna a waje.


Be tsaya jiran tabarmar da Maman ta je ɗauko mishi ba ya ja kujera a zauna a kanta ya fuskance ta "Na je na samu Munzali amma ga dukkan alamu yaron nan ba shi da albarka, domin ba ki ji maganganun da ya daddatsa mini ba; Saboda haka ki zauna za mu taya ki da addu'ar Allah ya fito miki da wani mijin da gaggawa ki kama kanki domin har ga Allah bana son buɗe idanu in ganki a gidan nan a matsayin bazawara sai dole, dan haka ba sakin jiki za ki yi ba da kin gama idda za miji ya samu za ki tattara ki kama kanki kin ji na faɗa miki ko?", da sauri ta amsa da "Na ji Baba kuma na gode ubangiji ya saka da alkhairi".


Bai sake cewa komai ba ya miƙe ya fice a ɗakin.

Maganar mutuwar aurenta kamar wutar daji haka nan da nan ya ɓude  unguwar har wani jaje ake zuwa ma Mama, ita kuwa da zuciya ɗaya take amsawa.

A hankali rayuwa take ta matsawa da ka tashi za ka ga dare ya yi a haka Munari ta gama iddar ta nan ma maza suka fara kawo mata caffa amma da ance su turo sai ka ga mutum ya ɗauke ƙafa  kuma ko a hanya suka gamu da ita ɗauke kai suke yi. 

Abun yana ɗaure mata kai har ta gaji ta faɗawa Mama ganin yadda Baba ya fara sako su a gaba da zancen 'me take jira ya ji shiru'.



  Kwantar mata da hankali ta yi ta ƙarfafa mata guiwar ta dage da addu'o'i komai zai wuce. Ana haka sai ga Malamin islamiyyar su shi ma ya aiko wurin Baban akan yana son ya fara zuwa zance a wannan karon ma ba tare da bincike me zurfi ba ya ce su turo da Mama ta yi magana sai ya rufe ta da faɗan "Malamai magada annabawan take so ya yi bincike akan su?, ai duk wanda aka ce maka Malam ne to ya gama da duniya lafiya".

Haka aka rugungunta aka ɗaura aure, wannan karon da bambanci tana ɗan son shi ba kamar lokacin Munzali ba shi yasa bata wani damu kamar waccan lokacin ba.


An kai amarya ɗakinta gidan daga ita sai sarakuwarta, da yake saurayi ne bai taɓa aure ba shiyasa ko bikin ma na saurayi suka yi abinsu.



Komai ta nema bata rasawa a gurin mijinta, inda ta fara fuskantar zata samu matsala shine ƴan uwan mijin nata kamar basu amshi gaɗar na shi ba.

 Ganin haka ya saka take  takatsantsan da su. Kiris suke jira ta yi abu su tsinka ta.


A hankali ta fara gano abunda ya ɗaga mata hankali. 

Duk da bata tabbatar ba amma sai ta dinga ganin  kamar kwakwalwar Mijin nata ba daidai yake ba, a da idan ta ga bai damu da magana ba ɗauka take miskili ne, sai a hankali ta fara gano a kwai matsala don abun ya yi yawa.  Idan abun ya motsa sai ya yi kwana biyu bai ce mata komai ba hakazalika bai fita ko ƙofar gida ba. Hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba.

Mamanta ta fara faɗa mawa duk da hankalinta ya tashi amma bata yarda ta fito mata da shi ta gani ba ballantana zuciyarta ya karaya.

Ta bata shawarar ta je ta samu mahaifiyar shi ta ji me zata ce.

Ba tare da wani jinkiri ba ta nufi wajen sarakuwar ta ta. Bata musa mata ba a cewar ta an riga da an zama ɗaya babu amfanin ɓoye ɓoye, ta tabbatar mata da cewa da gaske ne bashi da lafiya amma bai yi tsanani ba domin ba'a ganewa sai dai idan kana makusancin shi tukuna zaka gane.

A ranar ta yi kukan da bata taɓa yin shi ba tunda ta yi wayau. Ga shigar ciki tana jin alamun shi a jikinta.


Ga ƴan uwan shi da suka sako shi a gaba da bani bani, komai da ya mallaka sun amshe da sunan aro. A hankali ta gane yan uwan shi sun maida shi ne bawa duk abunda ya samo za su amsa da sunan ajiya. Ga shi Allah ya bashi nasibin nema duk abun da ya noma ko ya kasa za su zama kuɗi amma a banza.

Hankalinta bai ƙara tashi ba sai da abinda za su ci yake nema ya gagare su, idan ta mishi maganar ya amso kuɗin da suke aje masu ya ce 'kar su ji haushi ta yi haƙuri kawai'

 Tun daga nan ta gane bayan giya akwai wata cacar kenan.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.