Free chapter 路 Read without an account

34

by Kansa'u Bello 路 KOMAI TSANANI

馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅
    *KOMAI TSANANI* 

             *By*

         *KANSA'U* *BELLO* 
    
   *(OUM FATIMA)* 
馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅馃崅

   *PAGE 034* 

 *BISMILLAHIRRAHAMANIRRAHEEM*



  *Washe gari....*


Washe gari Ya Ammar ya tashi zuciyarsa fes domin ya gama gamsuwa da abinda ya tsara zai yi, don haka tun da wuri ya shirya ko breakfast bai nema ba ya nufi 蓳angaren Alhaji Baba ya same sa da maganar hukuncin daya yanke game da nema masa auren Nanah in yaso sai taci gaba da karatun a 蓷akinta bayan auren. Koda ya samu Alhaji Baba da maganar bai Musa ba don haka ya 蓷aga waya ya kira Alhaji Mudansir, Alhaji Ridwan da kuma Mamu. Yaso ace Ya Khalid ma yana 茩asar ayi maganar dashi amma kasancewar baya 茩asar yasa zaman bai yiwu dashi ba.

    Ba'a jima ba gaba 蓷ayan su suka amsa kiran Alhaji Baba in da ya bayyana musu bu茩atar da Ammar yazo da ita, Mamu ya kalla wacce tayi du茩ar da kanta tana jin-jina maganar da Alhaji Baba ya fa蓷a. 

   "Ni na amincewa Ammar yaci gaba da neman auren yarinyar nan, saboda haka zan wakilta Mudansir da Ridwan su shirya suje can Kano wurin Alhaji Balarabe su nema masa auren ta." Alhaji Baba ya fa蓷a yana kallon Mamu. Rasa abin fa蓷a Mamu tayi don ita dai har ga Allah maganar auren Ammar da Nanah bai kwanta mata a rai ba, ba don tana 茩in Ammar ba sai don guje mata irin makircin Inno da kuma izzar Hajiya Basariyya don ta don ta san wace ce ita.

    "Baki ce komai ba Maryama." Alhaji Baba ya kuma fa蓷a yana kallon Mamu, ajiyar zuciya Mamu ta sauke kafin tace.

   "To ni mai zan ce Alhaji ai duk hukuncin daka yanke bani da ja a kai sai dai in yi fatan alkairi... Sai dai ro茩o 蓷aya da nake dashi shine ya kamata a sanar da Mahaifiyar yarinyar da 蓷an'uwanta halin da ake ciki." Mamu ta fa蓷a tana tunanin yanda Khalid zai kar蓳i maganar auren Nanah a yanzu musanman yanda yaci buri a kan karatun ta, a gefe 蓷aya kuma mai babban suna wan da yake jin tamkar shine ya haife ta yake da iko da ita fiye da kowa. To amma ba zata iya yiwa Alhaji Baba musu ba don haka ta bar wa Allah komai tabi Nanah da addu'a da fatan alkairi.

   Sun tsayar da magana kan cewar idan Khalid ya dawo za'a sake zama dashi in yaso sai a tsayar da magana a saka rana sai su shirya suje suga Mahaifiyar tasu a sanar da ita batun auren baki 蓷aya.

 

******* A 蓳angaren Mamah kuwa ita ma da ku蓷irin data kwana a ranta ta tashi don haka bata tsaya sanya ba ta tari Alhaji Mudansir da maganar yaje ya nema wa Ammar 蓷in auren Suhaima 拼ar 茩awarta. Da mamaki Alhaji Mudansir ya kalli Mamah jin abinda tazo dashi yace.

    "Shi Ammar ne yace aje a nema masa auren Suhaiman?." Ya mata tambayar yana tsare ta da ido sabo da sarai ya san halin ta. Shiru ta 蓷an yi kafin ta dake tace.

   "Nice naga ya dace a nema masa auren ayi a wuce wurin tun da Suhaiman yarinyar kirki ce bata da wata matsala, kuma sun riga sun dai-daita kan su." Ta 茩are maganar cike da fatan kar yaja maganar da nisa. Gyara zama Alhaji Mudansir yayi ya dube ta da kyau yace.

   "Ita kuma yarinyar daya je ya ro茩i Alhaji Baba ya nema masa aurenta fa?... Ko dai biyu yake son ya aura ne?." Ya 茩are maganar da sigar tambaya. Wata mummunar fa蓷uwar gaba ce ta ziyarci Mamah lokaci 蓷aya zufa ta fara tsats-tsafo mata tsabar 蓳acin rai, wato Ammar bai ji duk irin jan kunnen data yi masa ba a kan waccen tsinanniyar yarinyar da a kanta ya nuna mata bata isa ba. Wato zagaye wa yayi ya samu Alhaji Baba a kan ya nema masa auren ta. To kuwa in dai ita ce tayi cikinsa ta haife sa ba zai ta蓳a auren yarinyar can ba har abada.

   "Lafiyar ki kuwa?." Alhaji Mudansir ya tambaya ganin yanda take ha蓷a gumi.

   "Shi Ammar 蓷in da kansa yace a nema masa auren waccen yarinyar?." Ta mayar masa da tambaya maimakon amsa.

   "Kina da matsala da hakan ne?." Shima Alhaji Mudansir ya mayar mata da tambaya.

   "茦warai kuwa don ban amince masa ba, kuma matu茩ar nice na haife sa to ba zai auri waccen yarinyar ba Suhaima zai aura." Mamah ta fa蓷a kanta tsaye. Cikin 蓳acin rai Alhaji Mudansir yace.

   "Ai kuwa baki isa Mahaifina ya yanke hukunci ki hana ba domin dake da Ammar 蓷in dani duk ya isa damu." Fuuu!! Ta mi茩e ta fice ba tare data tanka komai ba, kai tsaye kuma 蓳angaren Inno ta nufa.



***** A 蓳angaren Ya Ammar kuwa koda yaje wurin aiki hankalinsa bai kwanta ba sai da ya kira Alhaji Baba ya tambaye sa a kan yanda ake ciki, Alhaji Baba ya sanar masa ya kwantar da hankalinsa babu wan da zai hana sa auren wacce yake so, da Ya Khalid ya dawo zasu ha蓷u aje a nema masa aurenta. Farin ciki tamkar zai kar sa haka yayi ta masa godiya.

   Yana katse kiran ya mayar da akalar kiran nasa ga Nanah don ya raba farin cikin da yake ciki tare da ita. Tana zaune saman dinning tana breakfast ita ka蓷ai tana amsa wayar Anisa dake sanar mata ta shirya da wuri zasu je gidan su Aunty Noorah budurwar Hammah Mooh wacce ta ro茩i suje 蓷in kiran Ya Ammar 蓷in ya shigo.

   "Sorry Sis zan amsa kiran Ya Ammar, i will call you later." Nanah ta fa蓷a wa Anisa, tana kammala fa蓷a ta katse kiran Nata don ta san tsokana ce zata biyo baya.

    "Ina cikin farin ciki masoyiya." Ya Ammar ya furta yana jin ta 蓷aga wayar.

   "Masha Allah, naji da蓷i da kasancewar hakan Ya Ammar." Nanah ta furta a hankali

   "Kin san me?." Ya tambaye ta cike da 蓷oki. Shagwa蓳e murya tayi 茩asa-茩asa tace.

   "Sai ka fa蓷a min mana."

    "Alhaji Baba, Abba, Dady da Mamu duk sun amince za'a je a nema min auren ki a wurin Abban Kano idan an kammala bikin Hammah Mooh!." Ya 茩are maganar cikin tsananin farin ciki. Haka kawai fa蓷uwar gaba ta ziyarci Nanah da jin maganar aure kai tsaye. Kasa shiru tayi sai da tace.

   "Aure kuma Ya Ammar?... Ni 蓷in?." Ta fa蓷i maganar a kunnen Hammah Mooh da shigowarsa kenan zai gaishe da Mamu ya tsinci kalaman data furta wanda suka buga zuciyarsa da matu茩ar 茩arfi.

   A 蓳angaren Ya Ammar kuwa sanyi jikinsa yayi jin yanda ta furta maganar, don haka cikin sanyin jiki yace.

   "茦warai aure zamu yi masoyiya."

   "Ya Ammar ai ban isa aure ba yanzu, ka manta cewa yanzu ma zan fara karatu." Nanah ta fa蓷a da iya gaskiyarta.

   "Ban manta ba masoyiya zaki yi duk irin karatun da kike so a 蓷akin ki, amma dole ayi gaggawar 蓷aura mana aure tun kan a samu nasarar raba ni dake abun da ba zan iya jurewa ba." Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa shi cewa.

   "Wai ko dai bakya sona ne?." Yayi mata tambayar gabansa na fa蓷uwa da fargaban amsar da zata bashi. Ajiyar zuciya ta sauke a hankali tace.

   "Ba haka bane Ya Ammar ina sonka sosai mana, ni kai ka蓷ai na ta蓳a so ma a matsayin masoyi saboda kai ne mutumin daka nuna min tsan-tsar soyayya a duniya bayan Mama da Ya Khalid 蓷ina. Kai ne ka koya min yanda zan soka Ya Ammar, amma ka sani ban shirya yin aure a yanzu ba sabo da ina da muradin da nake son cimma wa." Ta furta maganar cikin sanyin murya, don har ga Allah bata da lissafin aure a yanzu. Babban burin da take dashi shine tayi karatu ta inganta rayuwarta ta zama irin Nanar da tayi wa Mmanta al茩awari, so take ta samu cikakkiyar dama da 拼ancin da zata koma 茩auyen Cigama ta tsaya tsayin daka ta ku蓳utar da Mahaifiyarta da 茩anenta daga 茩addararriyar rayuwar da suke ciki wacce idan ta tuno yanda ta rayu a baya abin yake ta蓳a ta. Bata yi aune ba lokacin data fa蓷a soyayyar Ya Ammar, sai dai duk da cewa tana son sa ba zata bari soyayyar ta hana ta cimma muradinta ba.

   Wani irin runtse ido Mooh yayi yana jin tamkar an 蓷auki wani 茩aton dutse an danne masa 茩irjinsa dashi, wai ma yaushe ne aka yi zama aka yanke hukuncin aurar masa da amanar sa ba tare da sani ko amincewarsa ba. 

    A 蓳angaren Ammar kuwa wani musulmin da蓷i yaji jin kalaman ta a kansa na soyayya, sai da jikinsa yayi sanyi da kalaman ta na gujewa aurensa a yanzu. Don haka ya shiga jaddada mata soyayyarsa a gare ta da irin kulawar da zai bata, kamar an ce ta 蓷ago idanunta suka sauka a fuskar Hammah Mooh wacce tayi jajir da 蓳acin rai. Tsoro taji ya kamata ganin yanayin fuskarsa don haka cikin daburcewa tace.

   "Barka da safiya Hammah." Ta fa蓷a a hankali tana satar kallonsa. Bai amsa ba sai kallo daya tsare fuskarta dashi tasa fuskar babu alamar sassauci, bata san lokacin data datse kiran da Ammar ba cikin hanzari ta mi茩e ta bar dining 蓷in zuwa 蓷akinta. Sai da ta 蓳ace ma ganinsa sannan ya runtse ido da 茩arfi ya dun茩ule hannayensa ya kaiwa iska naushi, 蓷akin Mamu ya nufa don jin ba'asin abin da ke faruwa.

    Saman abin sallah ya same ta ta gama sallar walha tana lazumi, bakin gado ya zauna ya dafe kansa daya masa nauyi sosai. Sai da Mamu ta kammala addu'o'inta sannan ta juyo ta fuskance sa, ta lura cewa akwai abin da ke damun Muhammad 蓷in don duk da kasancewarsa dama ba mai sakin fuska ba amma yanzu abin yafi nada, duk lokacin data tambaye shi abinda ke damunsa sai ya bata uzurin aiki.

   "Mai babban suna." Mamu ta kira sunansa da kulawa. A nutse ya 蓷ago risunannun idanunsa wa蓷anda suka sauya launi ya zuba mata su yana amsa wa.

   "Wani abu na damunka ne?." Tayi masa tambayar da kulawa sosai sabo da akwai sha茩uwa a tsakaninsu, tamkar ba zai ce komai ba sai kuma ya bu蓷e baki a nutse yace.

   "Yaushe aka yanke hukuncin aurar da ita ba tare da sanina ba?... Yaushe ta isa auren wai da za'a yanke wannan hukuncin?..." Ya 茩are maganar yana kallon fuskarta. Har ga Allah ita Mamu bata gane wa yake nufi ba don haka tace.

   "Wai a kan wa kake magana ne?." Ji yayi kamar ya fasa kuka don gani yake tamkar Mamu tana sani tayi masa tambayar. 
 
   "Nanahh!!!." Ya furta sunan da wani irin sauti. Shiru Mamu tayi tana nazarinsa don ta jima da 蓷ora masa alamar tambaya a kan takwarar ta, shi kuma ganin tayi shiru tana kallonsa yasa ransa fara 蓳aci don haka ya mi茩e a fusace zai fice a 蓷akin, da sauri ta ri茩o hannunsa ta zaunar da shi.

   "Yi h茩uri ka zauna in maka bayani." Zaman yayi ran nan a 蓳ace abin har yana bawa Mamu mamaki, bayani tayi masa a kan halin da ake ciki da kuma matakin da Alhaji Baba ya 蓷auka.

   "Wannan ba hujja bace da zai sa a lalata ma yarinya gobenta, kin san tana da burin yin karatun nan kuma nayi al茩awarin kulawa da ita da tsaya mata a kan komai. Don haka zata yi karatu sosai kamar yanda take bu茩ata, maganar aure a ajiye ta a gefe." Yana kammala fa蓷a ya mi茩e ya fice ya bar Mamu da baki a bu蓷e da mamakin ikon da yake nuna wa a kan Nanah.

   Nanah kuwa tana shiga 蓷aki kiran Ya Khalid ya shigo wayarta, wasu 茩wallar kewarsa ne suka ciko mata ido. Hannu ta saka ta goge idon sannan ta amsa wayar.

   "Ya Khalid???." Ta kira sunansa a shagwa蓳e.

   "Lilyn Ya Khalid, me ya faru ne?." Yayi mata tambayar jin muryarta da alamar damuwa.

   "Babu komai kawai nayi kewar ka ne."

   "Kin tabbata babu abin da yake damunki?." Yayi mata tambayar da tsananin kulawar da yake mata.

   "Eh Ya Khalid yaushe zaka dawo?." Tayi masa tambayar don kawar da wacce yayi mata.

  "Cikin Next week in sha Allah, kin san zan dawo bikin Hammah Mooh." Ya bata amsa, sai da gabanta ya fa蓷i jin ya ambaci sunansa da maganar aurensa. Hira suka yi sosai cike da soyayya da sha茩uwar dake tsakaninsu kafin suka ajiyar wayar cike da kewar juna.

    A 蓳angaren Ya Ammar kuwa yana ta magana yaji shiru, sai kuma yaji kiran ya katse. Bai kawo komai ba yayi tunanin ko wani uzurin ne ya kama ta, don haka ya barshi a kan in ya dawo zai zo ya same ta suyi maganar.


 *Hammah Mooh....*

     Yana fita daga 蓳angaren Mamu in da driver da Pa 蓷insa ke jiransa ya nufa aka bu蓷e masa ya shiga motsr suka wuce, kai tsaye katafaren Company *M.M Master* *Mind Design and Build* suka nufa......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.