Free chapter 路 Read without an account

PAGE 23

by Aisha Nalado 路 JOY

*AL'AMEEN*

Kwata-kwata babu sauk'i a cikin lamuransa, sai ma kara ta6ar6arewa da abubuwa ke yi i zuwa yanzu tables biyar yake sha kafin ya samu relief, yana cikin matsanancin damuwa, tuni ya fara rama a tsaye.

Ba Ummi ba hatta fatima sai da ta fahimci Yayanta na cikin damuwa, don gaba d'aya ya sauya mata, ko magana yanzu bai cika yi ba, haka firan dare, da ya dawo zai shiga d'aki ya kulle ya kwanta da safe ya fito da idanu jajur kamar gauta a kumbure idan ta tambaye shi ya ce babu komai, tuni duniyar ya fara mata zafi, take kewar aminiyarta ya dawo mata sabo fil dama shi ke dauke mata hankali akanta ba wai don ta manta da ita ba.

Ummi kam damuwar da ta shiga ba'a magana, matsayinta na uwa lamarin ya shigeta matuk'a gaya, tsoranta Allah kar ace shaye shayen nan na zamani Al'ameen d'in ta ya fara, a duk sanda ta yi wannan tunanin, takan shiga kololuwar ta shin hankali, har ta zubar da hawaye, ta zauna da shi ba sau daya ba ba sau biyu ba cikin lalama da dabara ta naimi jin damuwarsa, amma ya ki fad'a mata, sai dai ya girgiza kai ya ce mata "Babu komai Ummi, kawai gajiyan aiki da karatu ne, sai mura da ta saka ni gaba a yan kwanakin nan ki taya ni da addu'a." Ba dan ta yarda ba, dole take hakura, ta san tunda ya nace a haka bazai fada mata ba ne, ta fi kowa sanin halin zurfin cikin shi tun yana dan kankanin yaro.

Da misalin karfe takwas na dare ya shigo gida kamar yadda ya saba, sunan zaune jigum jigum a tsakar gida, duk yadda Ummi take da son sauraren redi'o yau rediyon nata a kashe yake carbi ne rike a hannunta tana ja, Fatima kam notebook din ta ne a gabanta data dauko zata yi karatu amma ta kasa, ta ajiye ta rafka tagumi.

Kallo daya Ummi ta mishi ta kauda kai gefe, sai ga hawaye shaaa! Duk yadda taso ta kauce kar ya gani abin ya ci turo.

Da sauri ya kara sa shigowa, zubewa yayi a gabanta hankali tashe, ya ce "Subhanallah! Ummi." Daga mai hannu ta yi ta ce "Karka kira sunana Al'ameen ni ba Umminka ba ce, ka tashi a gabana." Ta karashe maganar tare da fashewa da kuka mai karfi, Fatima da maganar Ummi ya dawo da ita hayyacinta, rarrafowa tayi ta fada jikin Ummi ta fashe da kuka itama, cikin kuka ta ke cewa "ki yi hakuri Ummi, ki yi hakuri ki yi shiru." Rungumeta Ummi ta yi su ka ci gaba da rera kukan a tare.

Kololuwar tashin hankali Al'ameen ya shige shi, zuciyar sa tuni ta shiga wani irin tsalle kamar zata faso kirgi ta fito, rasa abin yi yasa shi fara zubar da zazzafar hawaye da , sai kawai ya rungume su gaba daya, cikin zubar hawaye da kunar rai ya ce "Ki yi hakuri mahaifiyata ki dena zubar da hawayenki a kaina, na tuba nabi Allah na bi ki." Kalmomin da ya dinga maimaitawa ke nan kamar karatu.

Sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin Ummi ta tattare d'an jarumtarta ta danne zuciyarta, ta zame su daga jikinta ta dago ta kalle shi cikin ido ta ce "Al'ameen shaye shaye ka fara?"da wani irin sauri ya kalle ta yana girgiza kai, ta ce "Karya ka ke yi, idan ba haka ba kuma ka sanar dani damuwar ka, don na tabbata a kwai abin da ke damunki ji yadda ka koma gaba daya ka lalace cikin yan watanni, bazan jura ganin ka haka ba Aminullah."

Shiru ya yi yana kallonta bazai iya yi mata karya ba, kuma bazai iya fitowa kai tsaye ya sanar da ita damuwar shi ba, duk da yasan bashi da kamar ta duk duniya, yana matukar jin nauyinta, kasa ya yi da kai ya ce "Ki yi hakuri Ummi, bazan iya yi miki karya ba, kuma bazan iya sanar miki damuwata ba, amma wallahi tallahi bana shaye shaye, ki taya ni da uddu'a Ummina."

Boyayyar ajiyar zuciya ta sauke ko babu komai ta samu saukin kaso ashirin cikin damuwarta kashi dari.

Sai dai ko da wasa bata nuna a fuska ba, mikewa ta yi ba tare da ta kalli gefen da yake ba ta shige daki.

Fatima ma mikewa ta yi zata bi bayanta, har lokacin kuka take yi, da wani irin raunatacciyar murya wanda basu san shi da shi ba ya kira sunan ta "Fatima." Dakatawa ta yi da tafiyar ta juyo tana kallon shi tana shesheka, girgiza mata kai ya yi tare da cewa "Shiiiiii!" Alamar ta yi shiru, sai kuma ya yi mata alamar ta zo da hannu, da sauri ta karasa gareshi ta fada jikin shi, ta sake fashewa da kukan da dama ba wai ta dai na ba ne. Rumgumeta ya yi, wani irin rauni na kara kaiwa zuciyarsa farmaki.

A yau ya kara tabbatarwa, shine cikin farin cikin yar uwarsa tilo, da kuma mahaifiyarsa wacce itace komai na shi a rayuwa.

Muryarta ne ya katse masa tunani, cikin shesheka take cewa "Yayana ka canza, yayana ka dawo kamar yadda ka ke da don Allah, da ni da Ummi muna cikin damuwa kai ne haske ka jagoran rayuwar mu." Bubbuga bayanta ya shiga yi, ba tare da ya iya bude baki ya amsa mata ba, sun dauki tsawon lokaci a haka, kafin ya samu ta yi shiru, sai ajiyar zuciya da take saukewa jefi jefi.

Dagota ya yi daga jikinsa ya shiga share mata hawaye, yana yi yana cewa "Kar ki sake yin kuka My luv na miki alkawarin zan dawo muku da farin cikin ku ke da Ummi. Al'ameen din Ku zai dawo Yaya Ameen din ki zai dawo kin ji ko." Ta gyada kai ya ce oya wuce kije ki kwanta,

Babu musu ta wuce shi jiki a sanyaye, sai da yaga shigewarta daki sannan ya kwashe tabarman ya jingine, kamar mara laka haka ya nufi dakinsa.

Ranar damuwa biyu ne ya hade masa, ga na azababbiyar ciwonsa gana tunanin halin da ahlinsa suka shiga a dalilin sa, bazai iya jurar ganin su cikin wannan yanayin ba, bazai iya jurar zafin zubar hawayen uwa ba, ya san wata kila Ummi ta na fushi da shi, dole ya tsayar da mafitar da yake ganin ita ce dai-dai.

Ranar yadda yaga rana haka yaga dare.

Da safe kamar yadda ya saba gudanar da komai haka ya gudanar, hankalinsa ya kara tashi lokacin da ya hada idanu da Ummi, bai taba ganinta cikin irin wannan kamar ba, gaba daya idanunta sun kumbura sun yi jajur, sai dai bata nuna masa wani sauyi a fuska ba, ya san ta kwana cikin damuwa, abin da ya fi daga mai hankali ganinta da ya yi kwance a dai-dai lokacin da kullum yake samunta zaune ta na lazumi tabbas! Bata da lafiya, kuma yasan shine sila, shikam ina zai kai girman sannan zunubin uwa tafi gaban wasa,zai iya sadaukar da komai domin ganin farin ciki ta, a koda ya tambayeta ko bata da lafiya ne, cewa ta yi kalau ta ke.

Ko breakfast bai iya tsayawa yi ba, ya shirya afujajan ya nufi asibitin Dr Abdul Hafiz S Alto don a nan ne kadai yake ganin zai samu total solution.

Lokacin da ya isa Dr bai iso ba, zama yayi a waiting area shi da sauran patient din da ke nan.

Sun dauki almost gud 2 hours kafin Dr Abdul ya iso, tun daga nesa ya hango Al'ameen, boyayyar ajiyar zuciya ya sauke, yana tuna wayar da su ka yi da Aboki, shekaran jiya.

Sama sama ya amsa gaisuwar ma'aikata ya shiga office ya fara duba patient dinsa, gefe guda kuma zuciyarsa cike da fargabar da me yaron ke tafe fatansa Allah yasa ya zabi cancanta kar ya zabi son zuciya.

Mutum bakwai ya gani kafin layi ya iso kan Al'ameen, tun da ya turo kofar office din Dr Abdul ya dago yana kallon shi, shima jemammun idanu shi na kan Dr din.

Guri ya samu ya zauna a inda aka tanada don zama, da wani iron cool voice ya ce "Dr na dawo gareka ka taimaka ka yi mini wannan alluran da ka ce shine zabina." Rasss! Rasss! Haka gaban Dr Abdul ya yanke ya fadi, ya san za'a rina dama.

Shiru ya yi yana kallon Al'ameen din ba tare da ya amsa shi ba, gajiya da zaman shirun ya saka Al'ameen sake cewa "Don Allah Dr ka taimakeni ina cikin matsanancin damuwa." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce "Wacce irin damuwa ce sannan data saka ka kake shirin kashe rayukar a tsaye." Ya ce "Duk abinda kaga ya koro bera daga rami har ya fada wuta to hakika yafi wutar zafi, ni dai don Allah ka taimake ni." "Ta yaya zan maka injection irin wannan mai hatsari alhalin ban san matakin ciwonka ba, kar ka boye min komai ka gaya min gaskiya mekefaruwa?"

Tuni idanun Al'ameen suka kara kadawa, a raunace ya shiga labartawa Dr halin da yake ciki, ba tare da rage komai ba kamar yadda Dr ya roka.

Tun kan ya kai kar she tuni Hankalin Dr ya ta shi, ranshi yayi mugun baci, bai taba sanin akwai mutane kidahumai ba a duniya sai yau.

Cike da wani irin bacin rai ya katse shi ta hanyar jiran sunan shi a tsawace "Muhammad!!!! "........

***. [12/29, 2:40 PM] AyshaNalado: 馃寑馃寑 *JOY* 馃寑馃寑

~FARHAT~

DAGA AL茦ALAMIN馃憠 *AyshaNalado*

茦AR茦ASHIN JAGORANCIN馃憠 *Mikiya Writer's Association*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.