Free chapter · Read without an account
PAGE 41
by Aisha Nalado · JOY
Mikiya Writers Association
*Masu facebook ku yi following wannan account ɗin domin samun damar cin giveaway ɗin da muke yi, da kuma tattaunawa akan yanayin rayuwa*
***
Bayan ya ci abinci ya fuskanci Ummi gabansa na wani irin dokawa yace "Ummi kawun Amira ya kirani d'azu a kan yana son ganina." Dakatawa ta yi da kokarin canza channel din da take yi ta zubawa fuskar shi manyan fararen idanunta masu cike da kwarjini, da sauri ya yi k'asa da nasa kan, tare da ci gaba da cewa; Ya bani nan da sati d'aya in turo magabatana idan har da gaske na ke yi, idan kuma na wuce hakan to za su aurad da ita ga wani dan uwanta wanda yake son ta." Har ya dasa aya bata iya dauke idanu daga kallon shi ba, yayinda shi kuma ko da wasa ya kasa d'agowa ya kalleta, Ajiyara zuciya ta sauke mai nauyin gaske, cikin sanyin murya ta ce, "Kar ka damu yayan Fatima in sha Allah, gobe zan je na samu yan uwan mahaifinku duk da sun min kyakkyawar kashedi a kan babu ni babu su kar na sake na sake ra6arsu yanzu lokaci ya yi da dole na neme su domin su sauke hakkin nauyin daya rataya a wuyansu." Ta karashe maganar cikin karyewar harshen, tare da sauri d'auke kwallar da ta ciko mata idanu.
Hankali tashe ya d'ago ya kalleta, suna had'a ido ta yi saurin d'auke kai, don bata son ya fahimci kuka take yi, sai dai tun a yanayin sautin muryarta ya fahimci kukan ta ke yi, bata son ta ba shi damar da zai jeho mata wata tambaya hakan yasa ta mi'ke da sauri ta shige d'akinta ba tare da sake kallon gefen da yake ba.
Gaba d'aya duk wani ga6a na jikinsa ya mutu, haka ya dinga sauke wani irin nunfashi mai hade da kunci, ya yi zama ya kusa na awa d'aya a tsakar gidan nan ba tare sa ko kwakkwaran mosti ya iya yi ba, shin dole sai sune zasu nema masa aure? Tun bai mallaki hanakalin kansa ba ya san cewa; Yan uwan mahaifinsu basa kaunarsu, a she dama dalilin da yasa Ummi bata yi musu zancensu kuma ta hane su da yin zancen su kenan, me yasa zasu ce kada su ra6e su shin su d'in ba jininsu ba ne, shin ita Ummi ina nata dangin suke? Tambayoyin da ya dinga kai komo kenan a cikin kwanyarsa, sai dai bashi da mai bashi amsarsu.
Ya dade sosai a zaune kafin ya yi karfin halin mikewa ya tashi Fatima ta wuce daki shi ma ya nufi nasa dakin bayan ya nade tabarmar.
Daren ranar ya jima kafin ya iya rintsawa, yayinda a bangaren Ummi yadda taga rana haka taga dare, ta yi kuka sosai bayan shigewarta d'aki, rayuwarta ce ta baya ya dinga dawo mata filla-filla, tabas ta yi rashin masoyi na hakika Al-hussain ya kaunaceta ya tallafeta ya nuna mata hakikanin soyayya duk da irin yadda gaba d'aya kafatanin danginsa su ke kin ta, kamar mujiya a cikin taron jama'a, sun yi mata korar wulakanci tana tsaka da alhinin rabuwa da masoyinta, sai dai dole haka zata sake tunkararsu a wannan ga6ar domin bata sa wadanda suka fisu bata san kowa ba sai su.
Ta yi kuka sosai wanda rabonta da yin irin shi tun rasuwar marigayin mijinta, dakyar ta danne zuciyarta ta mike ta dauro alwala, a kan darduma ta karkare wayar gari ranar, Da safe haka ta wayi gari idanunta sun yi jajur sun kumbura, Fatima ta tsorata da ganinta, sai dai yadda ta tsare gida sai ta kasa tambayarta me ya same ta, hankalin Al'ameen ba karamin tashi ya yi da ganin ta ba, sai dai kamar yadda Fatima ta kasa tambayarta haka shima ya kasa,jiki babu kwari ya shirya ya fice daga gidan zuwa wajen harkokinsa.
Karfe goma da rabi ta gama shirinta tsab cikin riga da zani na atamfa ta sanya hijab dinta gogagge mai matsakaicin tsayi, fes ta fito a matashiyar mace kyakkyawar gaske mai cike da haiba da kamala, sallama ta yi wa Fatima bayan ta bar mata sallahun abubuwan da zata gudanar a gidan kafin ta dawo.
Tafiyar mintuna ashirin a cikin a daidata sahu ya isar da ita unguwar mak'era, a hankali ta dunfari babangidan mai dauke sa babbar k'ofa hadi da babban zaure.
Family hause ne mai dauke da dakuna masu yawan gaske, kai tsaye ta nufi cikin gidan gabanta na fad'uwa sai dai ta dake, don babu alamun hakan a fuskarta.
Kasancewar safiya ce yawancin matan gidan na tsakar gida kowacce na gudanar da sabgar gabanta, sallamar da ta yi ne ya janyo hankalin mafi aksarin jama'ar dake tsakar gidan.
Kamar wata sabuwar halittta haka wasu daga cikin matan suka Shiga kallonta fuskokinsu dauke da tarin mamaki, yayinda bakin fuskoki a gare ta ke binta da kallon rashin sani.
D'aya daga cikin matan ne ta kasa jurewa sai da ta maganta, cikin tu'ajjabi ta ce "Wa nake gani haka Lamar Balkisu? Na kusa da ita ce ta amsa da " Taya ni fada dai, ashe ba gizo bane. Tsaki d'aya daga cikin su ta ja tare sa cewa; Allah ya wadaran naka ya lalace, dai dai lokacin kuma d'aya daga cikin mazan gidan ya sawo kai jin kananun maganganu na tashi daga matayen nasu wadanda dama kullum basu rabo da hakan.
Turus ya yi da farko lokacin da ya yi arba da ita, sai dai daga bisani ya wani irin hade rai kamar hadarin gabas, a kausashe cikin zare jajayen idanunsa ya ce "Meya kawo ki gidan nan Balkisu, Ashe ba mun yi miki kashedi sake rabar inuwarmu ba, shin ke mayya ce, to wallahi wallahi billahillazi la'ilaha illah huwa idan kika kara, minti biyu a cikin gidan nan sai na yi miki mummunar lahani.
Wannan haniyar ta Yaya Al-hassan kamar yadda suke Kiran shi ita ta janyo hankalin kafatanin sauran muatane gidan dake dakunansu, suka Shiga firfitowa d'aya bayan d'aya.
Gyaran muryar da aka yi daga bayansu yasa duk suka maida hankali gurin, sabanin Hassan fuskarshi washe ta ke da wani irin shu'umar murmushi, ............
Oum ummretarh
*** [12/29, 2:50 PM] AyshaNalado: 🌀🌀 *JOY* 🌀🌀
~FARHAT~