Free chapter · Read without an account

Page 3

by Aisha Nalado · DAMA TA BIYU

Gaban Zee ya yi mummunar faɗuwa, nan da nan hankalinta ya tashi ta birkice tashi ɗaya. Ganin haka Mom dinta dake zaune kusa da ita tana jin duk abinda suke fad'a ta yi saurin jawota jikinta ta rungume, ganin tana shirin fashewa da kuka, ita kuma bata son tayi kuka a gabanshi a kan wanna maganar,, ba a nunawa namiji irin wannan soyayyar domin basu da alkibla,da dabara ta lallaɓa ta kashe wayar, domin samun damar ci-gaba da rarrashin y'arta.

A cewarta zubar da class ne, mace ta zauna tana yi wa namiji kuka, ai ta gama rainata, don haka da dabara ta datse kiran, tana ci-gaba da rarrashin y'arta.

Aslam jin shiru yayi yawa yasa ya cire wayar a kunnen shi ya duba ganin ta katse kiran sai ya saki, murmushi dama ya riga yasan hakan zai faru, yaga ma ƙoƙarinta abin ya tsaya iya nan, bata yi masa hauka ba, don yasan yanda take son shi idan taji yayi aure ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba. Amma abinda Aslam bai sani ba ranar da Zee ta fara jin labarin yayi aure sai da tayi dan ƙaramin hauka, Mom dinta ne ta dinga lallashinta sannan ita ta hanata nuna mishi ta damu da auren da yayi, ita ta hanata ta kirashi tun lokacin ta zuba mishi hauka, ta gaya mata ta nuna irin abin bai dameta ba, wai don idan ya gane ta na kishinsa ya samu lagonta kenan, ba a nunama namiji mugun so don basu da tabbas.

**********

Zaune Asmah take ta yi irin zaman nan na tahiya kanta a kasa gabanta kadan wani farin kyakkyawan tsohone hannunsa goye a bayansa sai safa da marwa yakeyi fuskan nan nashi a murtike babu alamar fara'a kai da gani kasan ransa a mugun bace yake, Sallama Daddy da Mummy suka yi, Alhaji Baba ya amsa musu, neman guri suka yi daga gefen kafet din dake shimfid'e a tsakiyar parlon suka zauna. Asmah ce ta gaishe su cikin girmamawa sai lokacin dukkan su suka kula da itace a wurin amsa mata suka yi, zuciyoyinsu cike mamakin ganinta da kuma tarin fargaba, ba su taba tsammanin ganin ta a nan a dai dai wannan lokaciba, don koda su zahra suka dawo ba su gayawa Mummy komai ba, kuma koda ta tambaye su dalilin dawowar tasu bayan sun ce mata kwana za su yi, ce mata suka yi lafiya qlau su dai sun dawo ne sun fasa kwanan. Ita kuma ganin yanayin su wani iri sai ta alaqanta hakan da qila yayansu ne ya korosu,

Sallamar da aka kuma yi ne ya katsewa mummy tunaninta, Mami ce tare da Abbah sai kuma Ummi dake bayansu, suma guri suka samu suka zauna suna mamakin ganin Asmah , dukan su hankalinsu suka mayar kan mahaifin nasu dake ta faman safa da marwa. Shima ganin duk ya'yan nashi sun hallara yasa ya juwo ya fuskancesu ransa a matukar bace ya fara magana "Aisha" ya kira sunan Mummy , Dago kai Mummy tayi tana amsa masa da "Na'am Baba Yace" yace inason a matsayinki na mahaifiyar wannan yaro Aslam ki kirashi ki bashi umarni nan da minti goma ko a ina yake yazo ina buqatar ganin shi a falon nan" Nan take gaban mummy ya yake ya fad'i kar aje wani mugun abu Aslam yayi fa, don ita hankalinta bai kwanta da wannan kiran gaggawan da alhaji baba ya musuba duk da bata san kiran menene ba, hankalinta bai qara tashiba saida idanunta suka sauka a kan Asmah, ‘ Tabbas a kwai abinda ke faruwa ya Salam!’ ta raya hakan a ranta. Haka dai jiki a sanyaye ta daga wayarta don kiran aslam din. Alhaji baba yaci gaba da magana cikin dan danne yanayin da yake ciki na bacin rai, a kausasshe ya kira sunan y'ay'a nashi guda uku da ya mallaka a duniya yace ya fara da Babban cikinsu “Abdullah"

"Na'am Baba” Daddy ya amsa.

Ya ci gaba da cewa "Dakai da qannenka Yusuf da Amina da matayenku da yayanku, Allah ya muku albarka" Suka hada baki gurin amsa masa da amin Baba. Daidai nan kuma Hajiya mama ta shigo dakin, tsohuwace mai kamala cikin shiganta na mutunci idanunta sanye da farin glass na qara karfin gani, tana dan dingisawa alamar kafa nadan matsa mata abinka da jikin tsufa, wai donma su tsufan nasu mai kyau ne angode Allah Neman guri tayi ta zauna a daya daga cikin kujerun falon ..

“Tun kuna yara kuka kasance masu yimin biyayya a dukkan abinda na umurceku, sannan haka kuma horas da yayanku akan bin umarnina, Baku taba saba umarnina ba daku da yayan Ku, nagode nagode Allah ya saka muku da alkhairi, kuma insha allahu za ku tsinci ribar biyayya a gaba koda bayan raina ne, sannan kuma Abu na biyu da yasa na kiraku nan shine.

"Maqasudin abin da yasa na tara ku anan shine "miqama Daddy takardan sakin da Asmah ta kawomishi yayi,

Hannu biyu daddy yasa ya karbi pepan amma bai bude ba yana jiran umarni.

CI gaba Allah ji baba yayi da fad'in "wannan shine sakomakon abin da Aslam ya sakamin da shi , Tunda nake kaf cikin zuri'ata babu wanda ya taɓa aikatamin abinda Aslam ya yi mini a yau, amma ba komai rayuwace" Alhaji baba ya qarashe a raunane, hakan ya kara sanyaya jikin ya'yan nasa tare da haifar musu da karin fargaba musamman Mummy

"Abdullahi bude takardar Ku gani mana" Daddy da duk jikin shi yayi sanyi qalau yayi karfin halin bude pepan da bismillah a bakin shi.....abinda ya gani rubuce cikin pepan ne ya sakashi sakin pepan ba tare da ya shiryaba, abbane ya miqa hannu ya dauki takardar ya duba..... Miqewa shima yayi a zabure ya maimata innalillahi wa innailaihi rajiun, mun shiga uku wani irin haukane aslam ya aikata haka" Ummi ta karbi takardar ta duba itama ta miqa ma mummy da mami , kowa hankalin shi ya tashi a falon nan idan ka cire asmah da Alhaji Baba.... A zabure daddy ya miqe yayi hanyar waje, Alhaji baba ya dakatar da shi da cewa "abdullahi dawo ka zauna" ba musu daddy ya dawo ya zauna , Alhaji baba kallan mummy yayi yace "Aisha kin kiramin shi ?" Amsawa mummy tayi da "na kirashi bai yi picking ba amma na mai text nasan inya gani zai kira yanzu" gyada mata kai Alhaji Baba yayi alamar gamsuwa......

Daidai wannan lokacin kuwa aslam ne ya fito wanka daure da towul a qugun shi, yana goge kanshi da karamin tawul d'in dake hannun shi, saida ya gama goge jikin shi ya dauki body lotion dinsa ya shafa da body spray dinsa mai shegen tsada da tsananin dadin kamshi, ya shirya cikin kayan barcinsa farare riga da wando marasa nauyi, pray mat ya shimfida ya gabatar da shafa'i da wutiri yayi addu'o'inshi , so yake ya kwanta barci da wuri , kallon agogo yayi ganin goma da rabi na dare yasa ya dane gado ya kwanta ya kashe fitila mai haske yabar dim light. Kamar jira ake ya kwanta sai wayar shi tayi qara alamar message ya shigo kamar ya share Dan d'azuma yana ji ana kiran shi ya share ko dubawa baiyiba balle yasan waye, shi duk zaton shi zee ce ko yanzuma yana zaton ita ce ta mai message , daukar wayar yayi da niyar kashe wa gaba daya don da gaske bacci yakeson yi da wuri, sai kuma ya tsaya don ganin message din daga mummy ne, ganin abinda ta rubuta ya sakashi saurin lalubo numberta ya kira jiki na rawa, daidai lokacin Alhaji Baba ke cema mummy ta sake kiran shi, Ringing wayar mummy ya fara ganin Aslam dinne yasa yasa mummy saurin d'agawa ko amsa sallamarsa batayiba tace a kausashe"kasameni a gida nan da minti goma kuma umarni nake baka ba shawara ba idan har ni na haifeka...... Idan kuma nima zaka bijiremin d'inne to bismillah shege ka fasa" git ta kashe wayarta ta barshi da way a manne a kunne, Nan shima hankalinshi ya tashi jin yadda mahaifiyarshi ta mai magana cikin bacin rai, ga dukkan alamu sakon abinda ya aikata ya iskesu kenan.....hankalinshi ya dan tashi jin muryar mummy cikin bacin rai da tsananin fishi don yasan fishinta ba sauqi har gara fishin daddy yafi sauqi akan nata, amma ko dar baijiba akan abinda ya aikata balle yayi nadama.

Tashi yaya ya shirys cikin qananan kaya ya dauki key din mota da wayarshi ya fice daga hotel din zuwa gida minti 15ya kaishi gida , direct sashen alhaji baba ya nufa son yasan sunacan suna jiranshi , Da sallama a bakinsa ya shiga parlon Abba da mami da hajiya mama ne kawai suka amsa mishi a fili , samun guri yayi ya zauna kusada abba, kanshi a qasa ya fara gaida mutanen parlon, kamar dazu daddy da mummy basu amsa mishi ba amma alhaji baba ya amsa mishi wannan karon,

Kallon Asmah yayi kanta duqe a kasa nan take ya qarajin tsanar yarinyar a ranshi, kamar ya shqeta ta mutu kowa ya huta haka yake ji a ranshi duk ita ta jawo mishi wannan matsalar da yace ciki iyayenshi na fushi dashi akanta,

Kowa ya nutsu a parlon ana jiran hukuncin da alhaji baba zai yi, gyaran murya yayi kafin ya fara da fadi "fadin Muhammad naga saqonko kuma na gode amma ka Sani ka tabka babban kuskure Wanda zakayi Dana Sani nan gaba , lokacin da Dana sanin bazai amfaneka da komai ba zakayi nadama loacinda nadaman ka baida amfani, kuma ka rubuta wannan maganar ka ajiye ko bayan raina zaka tina na taba gaya maka shi, "dago kai aslam yayi zai fara bada haquri,, Dakatar dashi alhaji baba yayi da cewa"banyi fushiba Muhammad kankan ka cuta baniba, wlh kayi babban asara , domin zabin da namaka zabine daya a ciki dubu amma kasa qafa kayi tafali dashi, har kana sakinta ranar da aka daura muku aure waidon ka kunyatani..kanka kama,

ita kuma Asma'u zataci gaba da zama damu anan, Allah zai bata mijin da yafi komai tayi aurenta na aurad da ita kamar yadda nama kakanta aminina alkawari

Yusuf inason idan zaka je yima yan biyu da amira registration ka hada da asmah, tunda auren bai yuwuba karatu zata ci gaba da shi kafin Allah ya kawo mata wani mijin "

Sannan Abu na gaba"Abdullahi ,Aisha,Yusuf, maryam da amina, inason Ku zama shaida na kamar yadda aslam ya Nina baya qaunar zabina asmah, to naji amince, amma babu aure zakanin shi da asmah a nan gaba na harantashi.......na haramta aure tsanin Muhammad da asmah ko bayan raina ban amince ba duk Wanda ya sake bashi auren asmah ko bayan raina ban amince ba,"

"Abu na karshe kai Muhammad ka sanar da iyayen ita yarinyar da kake so din cewa rana ita yau iyayenka zasu shigo gida ayi magana"

Yana gama fadin haka ya miqe yabar parlon matarsa ma bin bayanshi tayi don ta rarrasheshi ganin ranshi ya baci sosai ,

Daddy ne ya fara miqewa yabar parlon Mummy ma bin bayansa tayi ko kallon inda aslam yake basuyiba , ummi ma da ranta ke matuqar bace da abinda aslam yayi ta kama hannun asmah suka fice daga falo.

Sosai abbah kema aslam fada mami na tayashi.. Saida suka tabbatar jikin shi yayi sanyi sannan suka qyaleshi ganin dare yayi, bayan sun qara tabbatar mai lallai lallai ya nemi gafarar iyayen shi da kuma alhaji baba domin fushinsu a gareshi ba alkhairi bane.....dole aslam ranar a gida ya kwana don dare yayi sosai,

Washe gari gida ya tashi a hautsine sakamakon farkawa da sukayi da wannan mummunan labari ...

Baqi da sukazo daga nesa duk suna nan wasun su dama yau zasu wuce, sai ga wannan labari mara dadi,

Duk wani masoyin wannan familyn saida yaji ba d'ad'i akan abin da aslam ya aikata...abune da bai taba faruwa ba a tarihin familyn ...yayinda a daya bangaren wasu da dama keta farin ciki da faruwan hakan kamar su zuna ruwa a qasa su sha saboda tsabar farin ciki, bama kamar Zee don tuni labari ya isketa kunsan abin duniya baya boyuwa musan abin da bana alkhairi ba irin wannan an dinga yama d'id'i dashi kenan,

Alhaji baba da kanshi ya sanarma kakan Asmah Wanda yake babban aminin shi abinda ke faruwa, bai samu halartar bikin ba saboda baya qasa yaje aikin hajji kasancewar lokacin aiki haji ne... baiji d'ad'i ba amma kuma haka ya d'auki qaddara karshema shiya koma rarrashin alhaji baba Dan ganin alhaji baba yafishi d'aukan zafi akan lamarin ...

Baqi dangin mahaifin asmayh da dangin mahifiyarta da suka zo daga garuruwa mabanbanta don halarta bikinta a ranar suka jujjuya da labari Mara dadi ...suka bar asmah a gidan ba wanda yace zai tafi da ita tunda sunsan nan ne gidanta don tun tana qarama Alhaji Baba ya d'aukota bayan rasuwar mahaifanta yazo ya danqata a hannun mummy da daddy suka zame mata sabbabbin iyaye suka hadata da nasu yayan suka riqe ba tare da sun nuna mata wani banbanci ba ,,, yayinda a gefe guda alhaji baba da alhaji Mallam kakan asmah su kadai suka San dalinsu na zaman asmah a gidan..

Ba wani dalili bane kuma illah nason hada zuri'a a tsakanin su domin tun akan yayansu sukeda wannan burin, sai kuma ya kasance yayansu duka maza suka haifa alhaji baba Nada yaya uku, abdullahi mahaifin aslam Wanda ya kasance shine babba yana da matar shi d'aya Aisha mummy yayansu hudu Muhammad aslam ne babbah Wanda yaci sunan alhaji baba sai mai bi masa rabi'ahtu itama taci sunan hajiya mama ne tayi aure last year harda yarta daya hanifa, sai kuma yan biyu mummy wato zahra da batool

Sai mai bi mishi Amina take auren wani Dan uwanta suna zaune a abuja itace mahaifiyar, amir Wanda ya kasance amini kuma Dan uwa ga aslam kasancewar tsararrakin juna Dan rana daya akayi bikin ta Dana daddy saboda kasancewarta mace, Sai kuma Yusuf shine mahaifin kamal da amira shima matan shi daya maryam mami, amira tsaran su batool ne shi kuma kamal ya kasance mate din rabi'ah , Daddy da abbah dukansu suna zaune ne a gida daya da mahaifinsu babban gidane kowa da part d'inshi

Shi kuma Alhaji Mallam kamar yadda jikokinshi ke kiran shi yaya biyu ya haifa kuma duka maza mahaifin Asmah Aminu shine babba sai kuma qanin shi Ahmad mahaifin Khadijah,

Amintarsu ya samo asaline tun akan iyayensu da suka kasance suma aminai haka aka haifesu suka tashi tare ko ina zasu tare makaranta da gida yau suna gidan can gobe suna can har suka gama secondary school alhaji baba mahaifin shi shararren Dan boko ne kuma Dan kasuwa yayinda mahaifin alhaji Mallam ya kasance babban malamin addini.... Haka kowannensu ya gaji mahaifinsa yanzu haka alhaji Mallam babnan malamine da akeji dashi a fadin Nigeria,, inda iyayensu suka rasu suka barsu, amintarsu har taso tafi na iyayensu Dan daya baya aiwatar da komai saida shawaran daya....lokacin da sukayi aure sun qudurci niyyan idan Allah ya basu zuri'a zasu hadasu aure domin zumunci ya tabbata na har abada... saidai kicin ikon Allah yayansu suka kasance maza mace daya alhaji baba yake da ita Amina kuma sai ta kasance tsaran aminu( mahaifin asmah )saboda alhaji baba ya Riga alhaji Mallam yin aure Dan haka ya rigashi haihuwa,,lokacin da amina ta isa aure kasancewarta mace aminu ya mata yaro don haka tayi aurenta da wani Dan uwanta ta dangin mahaifinta....

Haka su Alhaji baba suka haqura da wanna burin nasu na hada zuri'a ganin yadda Allah ya tsara lamarinsa, saidai lokacinda da suka fara samun jikoki burinsu nason had'a zuri'a ya dawo sabo dal ganin Allah ya fara azurtasu da jikoki maza da mata... Iyayen asmah sun rasa ransu ne ta dalilin hadarin mota da sukayi lokacin asmah na noziri sun ajiyeta a school kenan zasu wuce anguwa da kannenta biyu kasancewar ita ta fara zuwa school baza aje da itaba suka biya suka ajiyeta tana kuka zata bisu suka mata wayau suka wuce basuyi nisa da school dinba tayar motar ta fashe, motar ta dinga tambul akan titi, nan dai gaba dayansu suka mutu, sai mummunan labari alhaji Mallam yaji, sunji mutuwarnan sosai kowa sai tausayin asma u yakeji , bayan share makoki alhaji baba ya nemi abashi riqon asmah ya hadata da yan biyu tayi karatu don tafi sakewa cikin yara tunda nan ba wasu yaran tunda lokacin Ahmad baiyi aure ba ana dai shirinyi ne, anan alhaji baba yace idan ta girma kuma sai a hadats aure da dan'uwanta aslam,, nan take alhaji Mallam yayi na am da hakan saidai yace shi baida burin ya mace tayi karatu mai zurfi yafison tayi iya secondary in yaso in mijin ta ya aminci taci gaba a gidanta, take kuwa alhaji baba ya mishi alqawarin indai tagama secondary zai aurad da ita ga aslam din taci gaba a gidan shi anan suka binne wannan sirrin nasu suka barshi a ransu sai lokaci yayi kowa yaji inda sukayi fatan Allah ya hada kan aslam da asmah kafin lokacin don komai yazo musu da sauqi, sai dai kuma hakan bata kasance ba,

Zuwan Asmah gidan lokaci tanada shekara hudu a duniya yayinda Aslam keda goma sha hudu, hannun mummy da daddy alhaji baba ya danqa amsah inda suka hadata dàsu batool suka riqe tsakani da Allah amira qaurowa tayi daga part din mami ta dawo part din mummy kullum tanacan in akace tazo ta wuce part dinsu har kuka takeyi ganin haka yasa mami barinta wa mummy ta hada duka su hudun ta riqe yayinda mazan kuma suka kasance yan dakin mami

...tun fil azal aslam baya qaunar asmah domin tun ranar daya fara ganinta ya dauki karan tsana ya daura mata bata mai komai ba shidai kawai abinda ya Sani idan ya hada ido da ita gaban shi faduwa yakeyi tun daga gani na farko hakan yasa ya tsaneta baya so ganinta har mayya take kiranta a cewarshi inba maitaba ya za'ace daka hada ido da mutum gabanka ya ringa faduwa, haka ya takura wa rayuwarta kwata kwata a gidan idan aslam nanan asmah bata da sukuni... Wani irin mugun tsoranshi ya dasu a zuciyarta saboda yadda yake azabtar da ita, duka zagi mari punishment haka yake sakata, yasha kulleta a toilet tun safe sai yamma, suma sauran qannenshi bawai sun sha bane a hannunshi suma yana dukansu amma ba kaman na asmah ba, a haka har suka shiga jss 1lokacin ne kuma aslam ya gama secondary school shida amir inda aka shiga fafutukar naman musu admission a qasar waje har lokacin ba abinda ya canja a tsakanin aslam da asmah yanda yakejin mugun tsanarta itama haka ta tsane shi......

Duk wannan abinda ke faruwa a tsakanin su iyayensu basu da labari, iya yara yaran gidan ne kawai suka san abinda ke faruwa su kuma ba daman fada tsoranshi sukeji kar su fada ya dake su, Kamal ne ma yake qoqarin hanashi in yana dukkanta yai ta bashi haquri amma ko kallon banza baya isansa, Rabi'ah kuwa tun ranar da tayi mai magana ya tsinka mata mari lokacin batayi aure ba taja bakinta tayi shiru ta zuba ma sarautar Allah ido.......

Kamal yana matuqar tausayin asmah saboda irin abubuwan da Aslam ke mata, haka zai sameta yaita rarrashinta yana bata baki akan tayi haquri wata rana sai labari, wani irin kulawa yake bata Wanda ko qannenshi baya basu irin wannan kulawan, kamal ya kasance mai yawan magana Dan haka zaizo yasata agaba yaita mata labaran ban dariya duk Dan ta manta da abinda Aslam ke mata agidan... A hankali wani irin shakuwa ya shiga tsakanin,

Su asmah sun shiga jss 1 lokacin Aslam na shirye shiryen wucewa karatu kasan waje,,, FGC Abbah yakaisu inda asmah da batool A class zahra da Amira B class su hudu suke rayuwarsu gwanin sha'awa,, basuda wasu baren qawaye su hudun nan sune qawayen junan su.

Ranar da Aslam da Amir zasu tafi makaranta a kasar Malaysia zo kuga murna gurin y'an mata mummy, bama kamar asmah har wani Dan qaramin party suka hada a dakinsu su hudu na murnan tafiyan Aslam ...

Tabbas y'an matan mummy sunji dadin tafiyan Aslam, Asmah tuni ta saki jikinta a gidan don dama aslam ne kadai matsalarta ... Agidan kowa nasonta babu mai nuna mata wani banbanci ta zama yar gida babu mai sanin rikonta akeyi a gidan ,,, alhaji baba ma qarara yake nuna mata soyayya fiye da sauran jikokinsa, domin ita din jinin amininsa ce mutum mafi soyuwa a gareshi, sosai yake kula da dukkan lamarinta,, hakan ya saka mata wani irin matsanancin kaunar tsohon da ganin girmanshi a zuciyarta, sosai take girmama shi, sosai take girmama dukkan lamarinsa, yanda ko layi yaja yace kar ta tsallake to bazata taba tsallakewa ba kuwa har illah masha Allah,

Ta bangarenb kamal kuwa shaquwan dake tsaninshi da asmah ya rikide ya koma soyyaya a gare shi ,domin kuwa shi kadai yake kidanshi da rawanshi ita batasan yanayiba, ta dauka kawai sabon da sukayi ne yasa yake mata wasu abubuwan kamar na soyyayya, saidai kuma duk Wanda yaga yadda suke mu'amala saiya saka musu ayar tambaya❔, su zahra sunsha tambayarta wai kod'ai soyayya takeyi da yaya kamal, takanyi murmushi tace musu a'a ita yaya kamal yayanta ne ba wannan maganar a tsakanin ta dashi,, sukance mata ba wani nan intayi wari maji,

Su aslam sunacan kasar Malaysia suna karatu hankali kwance tunda ya tafi bai taba dawowa gida Hutu ko ganin gida ba , yanadai kiran iyayenshi a waya suma suna kiranshi musamma mummy da mami, zuwansu da shekara shida suka hada karatunsu akan business, amir ya tattaro ya dawo qasarmu ta gado, shikuman gogan ya zauna ya fara aiki acan da wani babban kamf [1/31, 8:07 AM] Sis Aysha: 🌀 *DAMA TA BIYU* 🌀

A kwana a tashi ba wuya a gurin Allah, kamar wasa har gashi yau ne su Asmah suke candy, sun kammala secondary school dinsu. Sun zana waec & neco harma da jamb ɗinsu cikin aminci, sai zaman jiran sakamako.

Sun samu kyaututtuka da dama musamma ma Asmah da ta kasance head girl din su kuma daliba mafi qoqari da hazaƙa a duk set dinsu.

ƙanin mahaifin ta Alhaji Ahmad da mai dakinshi mahaifan Khadijah , sunzo mata daga Suleja inda su ke da zama harma da Khadijah da kannenta maza guda biyu.

A daidai wannan lokacin kuma ya Aslam cika shekara 7cif cif a Malaysia kuma ya ke shiri dawowa ƙasarsa ta haihuwa.

Ranar wata asabar gaba daya gidan ya hautsine da shirye shiryen tarban Muhammad Aslam, kowa ka gani a gidan yana cikin farin ciki ba ga y'an ƙannenshi ba ga iyayensu ba, to ai dole ‘Shekara 7 fa ba kwana 7 bakwai ba’ cewar Mami.

Asmah kam tunda taji labarin dawowar Aslam har zuwa yau da jirginsu ya ta so gabanta faduwa yake ko kad'an bata farin ciki da dawowar shi, dariyar ya'ke kawai take yi a y'an kwanakin nan dan kar jama'an gidan su gane halin da take ciki, su zahra sunyi matuƙar mamakin yadda take nuna itama tana farin ciki da dawowarshi bayan sunfi kowa sanin tsakanin su...Ita kam a zuciyarta takance “hmmmm kudai kawai fuskata kuke gani, bakusan abinda ke zuciyataba”

Kamal ne kawai ya fahimceta, saboda kusancin da ke tsakaninsu, ya kuma yi iya kokarinsa wajen kwantar mata da hankali yakan ce mata ai yanzu ta girma ba zai dinga mata abinda yamata shekarun baya ba , haka dai da ire iren wadanda kalaman na kamal ta ɗan samu natsuwa.

Mummy, daddy, abbah, da kamal su hudu suka je dauko shi a airport, jirgin su na sauka mutane suka fara saukowa daya bayan daya shine kusan na karshen sakkowa.

Zaro ido waje mummy tayi tare da d'aga hannunta kamar zatayi addua ta kulle bakinta, ganin yadda Aslam dinta ya koma kamar wani baƙin balarabe ya girma ya zama cikakken namiji kwata kwata ya sauya ya qara kyau kamar bashi ba. ...shima saida yayi arba da iyayen nashi ya tabbatar yayi missing dinsu sosai da sosai, rungume shi Mummy ta yi hawayen farin ciki na kwaranyo mata, sai fadi take "idonka kenan babana" shi kuma sai maimaita "mummyna mummyna I miss u.” yakeyi haka suka rankaya suka dawo dawo gida...... Lokacin da yayi arba da yan qannenshi sai murna sukeyi sukazo suna mishi barka da dawowa , ya kallesu duk sun zama yanmata yace "lallai yaran nan kune kuka girma haka kuka zama yan mata Ashe mun kusa shan biki ya fada cikin zolayarsu " amira da zahra boye fuska sukayi waisu irin sunji kunya nan, batool da yake itace rasa kunya tace kai ya aslam mufa yarane bamu isa aure ba,.... Kallonta yayi yace ja'ira kina nan yadda kike da shegen surutun nan har yanzu ko tayi dariya ,,,,,,, hajiya mama dake zaune gefe tace, "eh lallai ba shakka aslam ka shahara harda wani cewa wadannan berorin sun girma ka kusha shan biki ko.....to ai sai ka bari ka fara auren tukkunna kafin kace zaka aurad da qannenka" ,,,, Sosa qeya yayi yace "nayi aure ke kuma nayi yaya dake matas, ai daga kanki na rude qofa "hajiya mama tace"ja'iri maji ma gani ai"

Duk wannan bidirin da akeyi asmah bata wajen, hasalima ko haduwa da Aslam din batayiba tunda ya dawo tana jin qaran diran motocinda sukaje tarboshi ta shige toilet su kuma su batool basu jirata ba suka wuce abinsu, yanzuma da suke zaune basu lura bata wajenba , don hankalinsu gaba daya nakan yayan nasu, haka ya wuni tareda yan uwanshi, sai dare ya samu ya huta sosai .

Saida aslam ya kwana bakwai da dawowa amma bai hadu da asmah ba yana son ya tambaya ko anmaidata gidan kakantane bayan tafiyarshi, amma sai wani zuciyar yace mishi to kai ina ruwanka ma da wannan yarinyar mai kwala kwalan idanu kamar fitilan mota, kawai sai ya share zancen ya basar, sai a rana ta takwas da dawowarshi ya shiga part din mummy ya tarad da yan matan dukansu harda asmah da batason zai shigo yanzuba data gudu d'aki , gabanta ne yayi kwance kwance ya bada rassss, amma sai ta dake , gaishe shi suka shiga yi daya bayan daya ya, yana amsawa a dake kamar yadda ya saba amsa musu can baya, asmah ne qarshen gaishe shi, Suna hada ido gabanshi ya shiga faduwa kamar yadda yake mai a can baya, harma yaso yafi na da , dakewa yaya ya amsa mata kamar yadda ya amsawa sauran wato a dake, tashi suka yi dukansu zasubar falon don ya hanasu zaman falon indai yana nan, ‘sai kace falon shi’ cewar Batool.

Daidai zasu hau step din da zai kaisu sama, da yake dakinsu na upstairs ne ya daka musu tsawa da cewa "ke zonan". Dukansu suka juyo amma sai yayi pointing din asmah yace "ke mai idon kamar na kwadi, dake nakeyi" dukkansu kallon asmah suka yi suna don sunsan ita yake kira mai idon kwadi, don su dai basu tabajin ya kira sunantaba saidai yace mai idon kwadi ko mai idon mazuru ko kuma yace mai idon mayu , Su kuma basuga aibin idanun asmah ba su haslima I danun nata a birge su yakeyi, don irin sexy eyes din nan ne gasu farare tas kamar tana wanke su da ruwan madara, har ji sukeyi dama su keda irin idanunta,...

Sanin da tayi ita yake kira da mai idon kwadi ya sakata nufoshi zuciyarata kuwa sai bugawa takeyi da qarfin gaske, anashi bangaren ma hakane saidai daurewa yakeyi karta rainashi ,.. Tsayawa su zahra sukayi suka fasa tafiya wani mugun kallo ya watsa musu, sum sum suka bace a falon.

Dan duqawa tayi a gabanshi tace "ya aslyam gani " saida ya gama hararanta yace waike wacce irin mayya ce, Ashe dama har yanzu kina gidan nan baki koma gidan ubanki ba , hawayene suka fara tsere a fuskarta jin yadda ya ambaci marigarin babanta, dago dara daran idanunta da yake kira da idon mayu tayi ta sauke cikin nashi idon,, bugan da qirjinshi keyi ne ya ninku, fiskewa yayi yace "bazaki daina kallona da wadannan shegun idanuwan nakiba na mayu , saina tsokale miki su" saida ya gama zage tass ya qare da cewa "wlh na tsaneki ban taɓa tsanar wani Abu araina kamar yadda na tsaneki ba ". Tsaki yaja yaci gaba da cewa "shima wanna kinibabben tsohon mai shegen iyayin tsiya garin shegen kwashe kwashen shi na tsiya ya kwaso mana jaraba ". Dan qurawa fuskarta ido yayi kafin ya tattaro miyan bakinshi ya tofa mata a fuska sannan yace "tashi ki bani guri kafin inyi qasa qasa dake a wajan nan,... mayya kawai nafi qarfinki wlh kurwata kurr "

Tashi tayi bata ko ganin gabanta ta wuce dakinsu, tana shiga ta fashe da wani irin kuka ta fada jikin batool data tarota su zahrama tasowa sukayi suka rirriqeta cikin kuka take fadin"na tsaneka bana bana sonka bana qaunarka, kuma bazan taba kaunarkaba har qarshen rayuwata,....na tsaneka!na tsneka!!na tsaneka aslammmm " Ta qarashe maganar da qara fashewa da , rarrashinta suka shigayi donsu a ganin su dukanta yayi kamar yadda ya saba shiyasa take kukana nan

********** Gaskiya fans in banga comment ba bazan sakeyin posting ba tunda naga kamar bakujin dadin labarin shikenan kawai gamma mu haqura, Don in baku comment sai naga kamar Baku karantawa ne jikina duk yayi sanyi.

Haka rayuwa yaci gaba da tafiya, tsakanin Aslam da Asmah kuwa babu abinda ya canja saima abinda ya qaru, tunda ya dawo walwalarta a gidan gaba d'aya ya ragu ba qaramin uzzurama rayuwarta yakeyi,

Saida ya cika wata uku cif da dawowa ya huta sosai har ya kama aiki a daya daga cikin kamfanonin Abba a matsayin general manager na kamfanin, Alhaji baba ya kira dukkan yayanshi ya gaya musu qudirinsu shida aminshi Alhaji Mallam akan son had'a Asmah da Aslam aure, Dukkan su sunyi farin ciki sosai saidai daddy ya kawo qorafin maganar karatun Asmah d'in, nan Alhaji baba ya sanar dasu yadda suka yi da Alhaji Mallam ranar da zai dauko Asmah na cewa baya son tayi karatun boko ya wuce secondary, dukkan su sun gamsu duba da yanayinsa na babban malamin addini, shike ma wasu fadan su aurad da yayan su in sun kai minzali kunga ai bazai bar nashi ba,

Sosai mummy taji d'ad'in wannan maganar don dama tunba yau ba takeda wannan buri ,

Nan Abba ya sake kawo maganar ko Aslam da Asmah din suna son juna , nan Alhaji baba yace ko basu son juna sai anyi wannan lamari saje can su daidaita, abar komai a hannunshi shi zai sanar musu da kanshi, nan dai meeting ya tashi kowa zuciyarshi fal farin ciki domin Asmah yarinyace nutsatsaya mai hankali da duk wasu iyaye na gari zasuso ta kasance surika a garesu

Alhaji baba da Aslam zaune suke a sitting room din Alhaji baba , fuskantarsa Alhaji baba yayi yace "Muhammad Aslam ba komai yasa na kiraka ba sai domin inason muyi wata magana dakai mai muhimmanci kuma na fahimtar juna, inason kabani aron dukkan hankalinka nan ,". gyada kai Aslam yayi yace "ina saurarenka alhaji" nan alhaji baba ya shiga sanar dashi abinda suka yanke nason hada shi aure da yar uwarshi Asmah cikin kwantar da murya alhaji baba yake mai magana da lalama,,... Tun kafin alhaji baba ya gama jawabinsa gaba daya aslam ya jiqe da zufa duk sanyi AC daya cika falon kuwa , qure alhaji baba yayi da ido kamar ranar ya fara ganin shi, daqar ya bude baki yace meyasa saini zaku aura ma ita meyasa bazaka aura mata wani cikin jikokinka ba , naga dai bani kadai bane jikan naka ai, to ni baba so akai kasuwa, idan hada zuri'ar Allah da annabi za ayi a aura mata kamal mana ko amir naga ai suma jikokin kane, kuma suma sun isa aure, to barin gaya maka gsky mallam tsoho bana son yarinyarnan bana kaunarta bata cikin tsarin matan da nake burin yin rayuwar aure dasu, don haka kayi gaggawar kwance wannan kullin da kayi , donni inada wacce nake son aura, wayyayya mai aji yar boko ba irin wannan kucakar yarinyar ba,"yana gama fadin haka ya miqe ya fice daga falon a fusace, Alhaji baba da mamaki ya gama kasheshi a zaune kasa ma magana yayi tunda yake wani daga cikin jikokinshi bai taba mai rashin kunya irin Wanda Aslam ya masa yau ba , shiru alhaji baba ya zauna yanata saqe saqe a zuciyarshi kafin daga bisani ya saki wani qayatatccen murmushi a fuskarshi bayan ya samarwa kanshi mafita,

Aslam ranar daqar bacci ya daukesa bayan ya samarwa kanshi mafita yasan tunda alhaji baba ya fara wannan maganar to sai ya aiwatar,yasan tsohon da hegen nacin tsiya , don haka ya qudurci zai samu Asmah ya buga mata kyakkyawan warning akan karta kuskura ta amince da wannan hadin, yamasan ita karankanta baza tayi gogin amin cewa da auren shi ba, Haka aka ci gaba da shirye shirye Asmah bata da labari , su zahra kam sunji lbr saidai ba wacce tayi qarfin halin sanarda asmah a cikinsu , don su karan Kansu ranar da suka fara ji abin ya matuqar firgitasu ya basu tsoro don su kadai sukasan irin tsanar da Asmah da ya Aslam sukai wa juna....

An tsaida lokacin biki nan da wata daya masu zuwa, alhaji baba ya tura Asmah gidan alhaji Mallam tace ta musu kwana biyu kuma ta duba jikin Mallam din Dan kwana biyu baiji dadi ba, da murnarta ta shiya kayanta don ta kwana biyu rabonta da gidan , ta nemi rakiyar su zahra amma dukkan su sukace mata baza su samu zuwaba, tayi mamakin yadda yau tayi musu tayin zuwa gidan Mallam suka ce a'a , alhali da su suke cewa azo aje gidan alhaji Mallam ayi Hutu, haka ta shirya ita kadai bello driver ya kaita, ta tarad da kowa lfy sun tarbeta da murna da nuna jin kewanta kamar yadda suka saba , a dakin kakanta wacce take kira da kaka mahaifiyar mahaifinta ta sauka , domin matan Mallam biyu ne ya qara aure amma matar bata haihuba har gashi tsufa yazo , gidan cike yake da yayan yan uwa da kuma daliban Mallam wasu ma harda iyalansu, domin gidan Mallam babban gida ne sosai mai dauke da sashe sashe , ..

Sai da daddare ta samu ganawa da alhaji Mallam bayan sun gaisa ya tambayeta yadda ta baro mutanan can gidan nasu tace lpy qlau nan suka Dan taba hira yana ta janta da Dan wasa na kaka da jika ita kuwa sai kunya takeji don bata saba irin wannan wasanda shi ba kuma gata bamai yawan magana bace, saida suka Dan taba hiran ya koma serious face dinshi shima, nan ya shiga sanar da ita abinda suka yanke akan aurad da ita ga dan uwanta Aslam, ya daura da yi mata nasiha mai ratsa jiki ya qare da cewa "wannan shine babban dalilin da yasa nace a turomin ke ni zan sanar miki da kaina, Don haka ki zama mai biyayya a garemu, wannan wata dama ce Allah ya baki domin samun miji natsattse mai hankali kamar aslam a wannan zamanin abune mai matuqar wuya dan haka sai ki gode ma Allah da irin zabin da ya miki" tuni Asmah ta daina fahimtar abida alhaji Mallam ke fad'a tundai ta fahimci aure ne akeson a hadata da babban maqiyinta mutumin da ta tsana a duniya fiye da kowa ,,,... Take wani zazzafan zazzabin farad daya ya lullubeta ci gaba Mallam yayi da yi mata nasiha wanda duk bata fahimtar komai ta Lula duniyar tunanin makomar rayuwarta, kaka ma data shigo ta same su daurawa tayi da nata nasihar, Kafin magriba zazzabin nan yaci qarfita saida Mallam ya kira family doctor dinsu yazo ya dubata ya bata magani da allurai, kafin Safiya zazzabin ya sauka saboda qarfin alluran da akamata , Kwanata biyu a gidan alhaji Mallam ta dawo gida, bayan dawowanta sai ta koma wata iri da ita bata walwala gata dama ba mai yawan magana ba sai ta qara komawa wata silent , kullum saidai ta zauna tana tunani duk ta rarrame kamar wata Mara lpya , koda yake itama Mara lpy ce don garama wani na kwance a asibiti a kanta ,.....

Alhaji baba ma yasa an kirata shima dai nasihar ya mata sanna ya maimaita mata abinda Mallam ya riga ya fada mata, ya qara da cewa "amma baza muyi miki dole ba inkinga zaki cutu game da wanna lamari to kiyi magana wlh ni zan tsaya miki a fasa wanna auren, duk da cewa wanna cikar burinmu ne zamu haqura , haka Allah yaso ". Duqad dakai Asmah tayi qirjinta na bugawa wata zuciyar tana raya mata kawai ki gaya mishi bakison shi suyi haquri, yayinda wata zuciyar kuma ke tuna mata matsayin alhaji baba, daddy da mummy, a gareta bazata ta'ba iya cewa bata son jinin su ba intayi haka tayi butulci ,, wata zuciyar ta qara tuna mata da karatunta kenan yanzu onta yarda burinta na zama yar jarida yasha ruwa kenan sai dai taga su zahra suna zuwa school ita banda ita ,,,dago kai tayi da niyar furtama alhaji baba batason aslam kawai sai ta tsinci kanta da furta"alhaji bani da ja akan wannan zabin da kukamin, kune gatana , ban isa in take maganrku ba duk da kun bani zabi ,na amince da auren Dan uwana kuma yayana ya Aslam domin cikar burin ku na alkhairi , Allah ya tabbatar mana da alkhairi " qara duqad da kanta kasa tayi tana dauke hawayen dake zubo mata a idonta da wayau don kar alhaji baba yagani, ...

Murmushi alhaji baba yayi yace alhamdulillahi, Allah ya yi miki albaraka dama nasan ke mai biyayyace a garemu, bazaki taba kunyatamu ba tashi kije insha Allah zaki samu y'ay'an da zasu miki biyayya fiye da yadda kika mana ,...

Ta bangarn kamal da yaji labarin auren Aslam da Asmah ba qaramin tashin hankali ya shiga ba ranar da zazzabi ya. Wuni saida yayi kwana uku a kwnace kafin daga bisani ya lallashi zuciyarshi , ya tabbatar ya rasa asmah rashi na har abada, .... Shi babban tashin hankalinshi yadda aslam da Asmah zasuyi rayuwa a gida d'aya daki d'aya a matsayin mata da miji, yafi kowa sanin abinda ke tsakanin su ,tabbas yasan in akayi auren nan akwai matsala , yana dai roqon Allah yasa komai yazo da sauqi , ji yakeyi aranshi da zai iya da yaje ya samu iyasumu alhaji baba ya fada mai , amma ina! Ko giyan wake yasha yasa bazai taba iya tunkaran alhaji baba da wannan maganar ba

*********

Biki nata gabatowa yau saura kwana goma , kota ina sai shirye shirye akeyi , amma banda amarya Asmah , ta zama wata iri da ita kullum cikin kuka, amma batayi gaban mutanen gidan, shiga toilet takeyi ta kulle kanta taci kukanta ta koshi,......

Aslam ne ya fito daga part din Alhaji baba ranshi a hade da kaganshi kasan ranshi a mugun bace yake idanun shi yayi jajur.....direct part dinsu na samarin gidan ya nufa , da baya da baya ya fada kan daya da cikin manya manyan sofa set d'inda ke falon hannayenshi ya hada cikin juna ya dunqulesu da karfi...rintse ido yayi yana sakin wani zazzafan nunfashi ,......ba komai ne ya jefa shi cikin wannan yanayin ba sai d'an kace nace daya faru tsakanin shi da alhaji baba..... Aslam ya kafe kaida fata na cewa bazai auri Asmah ba nan dai alhaji baba ya shiga rarrashin shi, rufe ido Aslam yayi ya shiga zazzagawa alhaji baba rashin kunya yana gaggaya mishi maganganun dayasan zai fusata shi har yasa yayi fushi yace a fasa auren, saidai kuma hakan bata faruba don alhaji baba miqewa yayi ya wawwanke Aslam da zafafan maruka har guda har sau biyu sannan ya nuna shi da yatsa yace "kai Muhammad wlh karya kakeyi baka isa ba, ni zaka kawowa rashin mutunci," nuna shi da yatsa yayi yace "to ko ubanka abdullahi bai isa ba, ballantana kai qaramin alhaki, kuma ka sani aure ne sai an daura babu fashi, kaje kayi duk abinda zakayi, dai dai nake da kai , duk rashin kunyar dake damunka ni nan zan sauke maka shi"hmmm ran maza ya baci,.... Miqewa Aslam yayi yace "yace haka kace ko to shikenan" yayi kwafa ya fice daga falon..... Dalinlin shigar shi halin da yake ciki kenan, saqa ya shiga yi da warwara har ya samar wa kanshi famitan da yake ganin zata fille mishi, mataki biyu zai dauka idan ya kwada na farkon bai yuwuba, to zai aiwatar dana biyu Wanda zai girgiza kowa,

Asmah bata qara tsanar Aslam ba sai ranar da yasa mummy ta turo mishi ita part dinsu , mummy da kanta ta shiga har d'akinsu , ta sakata ta wanke fuska ta shafa hoda da 'kolli, Wanda rabonta da su tun ranar da zataje gidan alhaji Mallam , hijab ta zumbula har qasa ta dauki hanky tana tafe tana share hawaye da majina ,

mummy kam ganin ta tafi ba musu yasakata a ranta ta dinga yin hamdala tana murna gani take duk yadda akayi sun fara sasanta Kansu ne tunda gashi har yana kiranta su tattauna, Dan shi cema mummy yayi zasu Dan tattauna ne yaji shirye shiryen ta akan bikin,

Asmah na qara kusantar part dinsu Aslam gabanta na tsananta faduwa haka dai ta daure ta qarasa ta shiga falon da sallama a bakinta , ganin shi tayi zaune a falon sanye da qananan kaya yayi kyau sosai fuskarnan nashi a hade ba alamar mutunci, amma ita a idonta gani takeyi ba Wanda ya kaishi muni a lokacin , ko sallamarta bai amsaba ya watsa mata wani mugun kallo mai cike da tsana .....tsugunawa tayi daga can gefe ta rakube kamar tana jira ace tak ta ruga da gudu, watazabgegiyar wuqa Aslam ya zaro daga cikin gidanta mai shegen kaifi irin Wanda tsab za'a iya fille kan mutum dashi tashi daya, miqewa yayi daga inda yake zaune da wuqar a hannun tsirara , nufo inda take tsugune yayi gadan gadan , ganin haka yasa jikin Asmah ya fara rawa ta sadaqar yau kwananta ya qare,tasan tabbas Aslam zai iya mata abinda yafi kisa ma a yadda ya tsanetan nan, don haka ta fara maimaita Kalmar shahada a zuciyarta rintse idonta tayi da qarfi donma kar taga sanda zai caka mata , ji tayi yace cikin tsawa"keee mayya look up " dago da kanta tayi da sauri jikinta na rawa cike da tsoro , guntun murmushin mugunta ya saki saboda hango tsantsar tsoratan da tayi a cikin kwayar idonta, dama abinda yake son gani kenan kafin ya kora mata kyakkyawan warning din da yake son ya mata .........

Waning ya shiga kora mata da kashedin cewa , idan ta kuskura ta bari aka daura auren nan har aka kaita gidan shi a matsayin matarsa saiya yankata da wannan wuqar ya kasheta kowa ya huta, ya qarashe maganar yanayin alamar yankata da hannun shi, nan ya tsatsara mata abinda zatayi da zaisa afasa auren. Kuma karta kuskura ta bari sunan shi ya fito, ya qare da zageta Tass kafin yace ta bace mai da gani ,..... Aikam da sauri ta miqe ta fice daga part din cikin gudu gudu sauri sauri tana sharar hawaye, ta shige part din mummy, allah yasa mummy bata falo tana dakin daddy don haka direct dakinsu ya wuce ta fada kan gadonta tanata risgan kuka abin tausayi , su batool dake zaune zugum zugum suna zaman jiran dawowarta, dama tunda ta wuce jinin su a qumba yake, sai gani sukayi ta shigo da kuka dama sun tsammaci hakan, lalkashinta suka shiga yi cike da tausayawa, gani duk sun shiga damuwa yasa ta tsayar da kukanta, amma a ranta ta qudiri aniyar saidai Aslam ya kasheta amma baza taba aiwatar da. Abinda yace tayi ba, ta yarda in an kaita gidan [1/31, 8:07 AM] Sis Aysha: 🌀 *DAMA TA BIYU* 🌀

By Aysher Nalado

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.